Showing 222001 words to 225000 words out of 278032 words

Chapter 75 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1029

tace kamar ya? bangane zuwa na musamman ba ?,ta fad'a tana jiran k'arin bayani.


Baba hasiya tai murmushi kafin ta ce.


"Nifa Hajiya Ina tunanin kamar fa soyayya ta k'ullu tsakanin uwata da baba na,(wato AA Arab da Rukayya saboda shima sunan Baban ta gareshi) Mamah ta rik'e hab'a kafin tace.

"Anya ko hasiya?".


Baba hasiya tace .

"Hajiya hasa she nake ban tabbatar kawai alamu na gani"ta fad'a tana sunkuyar da kanta k'asa...

Mamah tai murmushi kafin tace .


"Shikenan kuje ku shirya masa abinda zaku tarb'eshin dashi"


Baba hasiya ta mik'e tana cewa "toh Hajiya,ta fita daga d'akin, mamah ta bita da kallo tana murmushi tana tunanin Wani Abu aranta...


Babu Bat'a lokaci baba hasiya ta had'a masa lafiyayyan abinci da Kuma kayan ciye ciye kala kala da fruits da lemuka ,ke komai dai babu abinda ba'a had'a masa ba,aka shirya a falon Bak'i....



Da yamma wajen k'arfe biyar da Rabi AA Arab ya iso gidan su Ruky wannan Karan ba'a matsayin sir yazo ba, amatsayin hayati Yazo. lol=??,bayan ya iso ya d'auki wayarsa ya k'ira ruky, ruky tana tsaye gaban mirror tana shiryawa taga K'iran nasa take taji Wani Irin sanyin jiki,tai picking a Sanyaye tai shiru batai magana ba,AA Arab yace .


"Fiancee nazo"ya fad'a da wata murya...


Ruky ta Sauke numfashi kafin tace.

" ok sannu da zuwa kashigo ciki bari yanzu zan sa akai ka inda zaka sauka"ta fad'a cikin sanyin murya...


AA Arab ya ce .


"What happened naji muryarki so silent haka",


Ruky tace " nothing",

Ya sauke numfashi kafin yace alright bari na shigo" daga haka ya kashe wayar..


Bayan ruky ta sauke wayar ta k'arasa jikin bangon d'akin ta danna wata waya acikin d'akin,ta kira ma'aikatan gidan, bayan anyi picking take ta sanar masu da tayi bak'o su Bud'e masa gate sannan su kai shi bangaren Bak'i ,babu musu suka ansa mata cikin girmamawa,ta sauke wayar tana komawa g gaban mirror,ta zubawa mirror ido tana k'arewa kanta kallo taga shigar da tai tayi,sanye take cikin Wani maroon d'in less Mai ratsin golding yellow Wanda ya fito da ainihin kyanta d'inkin doguwar riga fitted gown Amma Bata kama taba ta sosai saidai ta fito da dirin ta ,ta d'auki mayafi golding yellow shima ta yafa a saman kafad'ar ta,take ta Bat'a Rai tana tunanin ta sauya kayan kota barshi ganin kamar surar ta tafito kawai dai ta hak'ura tunda mayafin ya sauko har kasan mazaunan ta ya rufe su ruf ,kai bamu ma ta inda tsirai cinta ya fito,fuskar ta Babu make up d'in nan,Amma kuma tayi light make up,ba karamin kyau tai ba


Ta fito daga d'akin ta bayan taiwa mamah sallama ta fita daga falon gabad'aya tai hanyar d'akin bak'i,Koda ta Isa da sallama abakinta kanta Yana k'asa ,AA Arab Yana passing k'ofar folon yana zaune kan D'aya daga cikin kujerun falon Dan haka ya samu damar kallan da kyau tun kafin ta k'araso shigowa falon yake kallanta ,ganin ta shigo yasa ya zuba mata mayun idanuwan sa Yana yiwa Allah tasbihi ganin wannan halittar,ya Mik'e tsaye Yana ansa mata sallamarta, ruky ta tsaya a inda take ita itama ta zuba masa idonta ganin yadda manya kaya sukai masa mugun Kyau,Ash color d'in shadda ce ajikinsa Wadda tasha D'inkin zamani ga hular kansa kalar kayansa ya ilaihi haka ta fad'a azuciyarta Dan bak'aramin kyau Yayi mata ba,ganin yadda yake binta da Wani mayen kallo, yasa ta sunkuyar da kanta k'asa ganin Wani Irin kallo da AA Arab yake mata Wanda yake neman susu tata,AA Arab Neman zaucewa kawai Yayi saboda yadda Ruky ta k'ara tafiya da duka hankalinsa,ya k'ura mata ido kafin ya fara takowa a hankali zuwa gabanta ganin tak'i k'arasowa cikin falon......









07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y





*____JAMI'AR TSARO ____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*_____(MRS SARAKIES =؋?)=?1?____*




*('TAURARI WRITER'S ASSOCIATION ('*



*TEAM 4 GOLDEN STAR (' WRITER'S*



*Bismillahirrahmanirrahim*



_____ season two ep 8?? 7??



____________?&


AA Arab ya k'araso har gaban Ruky sannan ya tsaya gab da ita har suna iya Jin numfashin juna,ya zuba mata ido Yana kallan ta,ruky tai saurin matsawa baya tana juyar da kanta gefe tama k'i yarda ta d'ago da kanta bare bar ta kalleshi,AA Arab ya zuba mata mayun idanuwan sa Yana kallan ta ,kafin yay k'asa da murya yace .


"Fiancee! ".


Ruky ta d'ago da kanta ta dubeshi ganin Irin kallon da yake mata yasa ta sadda kanta k'asa tace cikin sassanyar murya ta


"sir muje ka zauna ta fad'a tana Mai rab'awa ta gefensa ta wuce zuwa kan D'aya daga cikin kujeran falon,AA Arab ya sauke numfashi sannan yabi bayan ta shima ya zauna kan to seater Dake opposite d'in ta_ta ganin yadda ta zauna kan one seater ita.


Ya zauna Yana kallan ta har lokacin, ruky ta ce cikin daddad'ar muryar ta.


"Sannu da zuwa". Ta fad'a tana wasa da yatsun hannun.

AA Arab ya sauke numfashi Mai makon ya ansa saiya kauda gaisuwar da take masa kafin yay k'asa da murya Yana kallan ta har sannan yace .


"Fiancee!",

Ruky tai shiru Bata ansa ba ,ya K'ara K'iranta anan ne ta d'ago ta kalleshi da kyawawan idanuwanta, Amma Batai magana ba


AA Arab ya ce cikin deep voice d'insa.


"You are very very beautiful"ya fad'a Yana bin duka jikinta da kallo .


Ruky ta sunkuyar da kai tana murmushi,ya cigaba Yace.

"Allah Alhamdulillah, daka bani matar AURE ta gari ,wacce bana tunanin akwai Wanda ya kaini dace, Alhamdulillah ya Allah, Allah ka nuna min Ranar da zan mallaketa amatsayin matar AURE nah,ya fad'a Yana wani kashe mata Jiki da salon maganar sa.


Ruky ta rufe fuskarta da tafukan Hannunta sannan ta Bud'e lokaci D'aya tana mik'ewa kafin tace .

"Stop it please, Bayanzu ya kamata kayi wannan maganar ba ,tace bari ka fara sniffing ko ruwa ne ta fad'a tana K'arasawa gaban table d'in Dake shak'e da kayan alatu.


AA Arab ya lumshe ido kafin ya ce .

"Aini kinfi yemin komai arayuwa, idan zan zauna nai ta kallanki bazan tab'a gajiya ba"ya fada yana kallan ta.


ruky ta mik'e daga duk'en da take bayan ta tsiya ya masa ruwan gora a glass cup ta k'araso har Inda yake zaune ta risina tana Mik'a masa ta d'an shagwab'e fuska ta ce.


" Bayan Baka ansamin gaisuwar da nake maka ba shine zaka ce haka' ta fad'a cikin shagwab'ar data sabayi.

Ya Allah AA Arab ya fad'a Yana k'ureta da ido ya Mik'a hannu zai karb'i ruwan yace .


"Fiancee!do u want killed me".


Ruky tace cikin Rashin fahimta" like how' ?.


AA Arab ya karb'i ruwan yace .

"Bakisan wannan shagwab'ar da kike min ba susu tani kike ,da zautar Dani aduniyar sanki ba, please Bana so kidinga min yanzu karna kasa jurewa nayi abin kunya ki adana ta idan aka kaimun ke gidana amatsayin matata Kya yimini yadda ranki yakeso".ya fad'a Yana kashe mata ido D'aya.


Ruky tai saurin barin wajen tana rufe fuskarta kafin tace tana murmushi.

"Nidai kadaina min haka Babu kyau"ta fad'a tana shagwab'e fuska.


AA Arab yace.

"Hmmm zaki sani ne",


Ruky tace.

"Nidai Abar zancen kasha ruwa tukunna"ta fad'a tana kallon sa .


AA Arab yay Wani killer smile sannan ya kai cup d'in bakinsa, ruky ta k'ura masa ido tana kallansa tana Yaba wannan kyau nasa Wanda ya had'u ruwa biyu ,Dan daga ganin wannan ba iya Fulani bane Kuma ba Hausa ba ,itako zata tambayeshi taji Wani yare ne su.


Ta shagala da kallan sama Bata saniba, saida taji Yana cewa,


"Hey wannan kallon fa?ya fad'a yana Wani kashe mata Ido d'aya.

Ruky tai saurin d'auke idon ta akansa tana rufe fuskarta da tafukan Hannunta saboda kunya tana murmushi tace.


"Niba kallan ka nake ba",


AA Arab ya ce .

Inji wa kallo mana kike nida na kama ki kina kallon nawa,wato Kinga D'an kyakkyawan saurayi,Mai jini ajika,kin mace akansa kince Idan ba Shiba Sai teku",ya k'arasa fad'a Yana murmushi.


Ruky ta harareshi kafin tace.


"Inji wa?ai kaima kasan ba haka bane,Kaine dai ka mace akan nawa har kana Neman mutuwa ta fad'a tana tunowa da abinda ya fad'a mata ranar.


AA Arab yay wata dauriya wacce ta kusan zautar da Ruky saboda yadda taga Tsan tsar kyau azuciyarta tace dama Yana dariya har haka,kafin taji yace .


"Uhmm ahakan shiyasa naga ana kishina har ana Neman yin fushi Dani lokacin da doc Fatima tai min magana".


Ruky ta Bat'a Rai tace.

"Wato har yanzu tana Zuciyarka koh?,Ta fad'a a shagwab'e kamar wata qaramar yarinya.

AA Arab ya d'aga hannunsa sama kafin yace.


"Sorry Amma ni babu wata 'ya mace azuciyata sai ASP Rukayya", ya fad'a Yana kashe mata ido D'aya, ruky tai murmushi kafin ta mik'e ta tana kallan sa ta D'ora hannun ta kan Leben ta ce .

"It's ok ,bari kaci abincin tukunna koma miye ayi daga baya ta fad'a tana Isa gaban table d'in Dan had'a masa abinda zaici.

AA Arab ya bita da kallo ganin yadda take tashin kamshi ga komai nata abin burgewa ne,cikin nutsuwa take komai nata uwa uba Kuma surar ta followed by kyau ya ilaihi haka kawai yake furtawa a cikin zuciyarsa Yana tunanin SHikan an sallame shi.


Yana wannan tunanin yaji ruky na cewa "kaci abincin ,gashi Kuma yanzu dai na K'ara Maka kana kallona Yay murmushi kawai baice komai ba, kafin tace ka cinye duka sannan na K'ara Maka Wani ta fad'a tana murmushi.

AA Arab ya zaro ido waje ganin Irin abubuwan Data loda masa agaban sa Yana kallan ya ce.

"Wazai ci wannan?,ya fad'a Yana kallan Ruky.

Ruky tana murmushi tace."kai mana",Kuma iya plate nake son gani" ta fad'a in a serious face.


AA Arab ya marai raice kafin yace.


"Please fiancee billah bazan iya cin komai ba cikina ma aciki yake"ya fad'a Yana shafa Cikin nasa.

Ruky ta kauda kai ganin yadda yake Wani shagwab'e fuska kamar Wani k'aramin yaro ta ce.


"Nidai saika ci "ta fad'a tana tura Baki gaba.


Ganin itafa da gaske take kuma shi bayason B'ata mata Rai yasa yace .


"Ok Amma dai kad'an kad'an zanci indai saina ci duka ne saboda wallahi ko agida ki tambayi ummi wallahi bana iya cin abinci dayawa", ya fad'a Yana wani narke mata tare da marai raice cewa kamar me..

Ruky taji tausayinsa ya. Kamata ganin yadda yake Abu bil hakk'i da gaskiya tace.

"Ok naji Amma fa saika ci ko wanne" ta fad'a tana tsareshi da ido .

AA Arab ya saki murmushi kafin yace.

"Thank you fiancee" sai Kuma yace "ko zaki Bani abaki", ya fad'a Yana wani k'ura mata ido.

Ruky ta kau da kanta tana murmushi.shima murmushin yayi kafin ya d'auki spoon ya fara cin abincin,yanayi Yana Wani lumshe ido, sannan lokaci lokaci ya d'ago ya kalli ruky kafin ya kashe mata ido D'aya,ita dai ruky ta sunkuyar da kanta k'asa tana Jin yadda idanuwansa ke yawo a duka sassan jinkinta gabad'aya taji ta ata kura da irin Kallon da yake mata...


AA Arab Saida yabi ya d'an tsakuri ko wanne abincin kafin ya tsiya Yi ruwa yasha Yana kallan Ruky yace .


"Alhamdulillah"ya fad'a Yana shafa Cikin sa.


Ruky ta kalli plate din abincin ganin duka yadan ci yasa tai shiru kafin ta Maida Kallan ta kansa tana kallan sa..


Taga shima ita yake kallo. ya sauke numfashi ya ce cikin cool voice d'insa.

" thanks u fiancee abinci yayi Dad'i Ina fatan ke kikayi ?"

Ruky tai murmushi tace.

" thank u sir ni nayi Amma tare mukai da Baba hasiya",ta fad'a tana kallan sa


AA Arab ya jinjina kai kafin yay k'asa da murya yace .

Lallai na more tunda na samu mata hundred percent", ruky ta harareshi kafin tai murmushi, shima murmushin yay kafin ya komai serious face yace.


"Rukayya kamar yadda kika sani yanzu zan Baki d'an ta kai taccen tarihin Ahmad Aliyu Arab",ya cigaba yace.


"ni sunana Ahmad Aliyu Arab Wanda a bokai Dama wasu mutanan sukafi sanina da AA Arab,ya fad'a Yana kallan ta ganin yadda itama lokaci D'aya ta d'ago tana kallan sa ,ya kauda kansa kafin ya cigaba Yace.



ASALIN mu _mu ba hausawa bane sai dai nace miki mun had'a da sirki da yaran Fulani tunda ummi nah Fulani ce , Fulanin Yola, abban mu kuma shima ruwa biyu ne,mahaifinsa sunan Arab ASALINsa D'an k'asar saudiya ne,aikine ya kawo shi Nigeria anan ne Kuma ya had'u da matarsa 'yar ASALIN garin Yola itama har ya nemi auranta aka bashi ita,daga nan suka koma saudiya da zama , kafin ya dawo bayan Wani lokaci tunda dama kaita Yay wajen 'yan uwansa Dan su Santa, Abbanmu su biyu aka haifa Shida yayarsa Hajiya Aisha ita ba'a Nigeria take zaune ba tana can tana AURE a saudiya cikin garin makka ,sai shi Abba yake ya ke zaune a Nigeria a cikin garin Kaduna wajen k'anwar maman sa saboda Bata tab'a haihuwa ba shiyasa suka Bata shi ya cigaba da zama tana rainon sa ahannun ta har ya girma ya Gina kansa ,Hakan yasa ya cigaba da ZAMA a kaduna , ya fara aiki da kuma kasuwancinsa a k'asa shen ketare,saboda iyayensa sun riga da sun koma saudiya da zama gabad'aya tun tuni, yanzu iya abban mune a Nigeria, sai mu yaransa .


Abbanmu ya auri ummi wacce take 'yar uwarsu ta bangaren babarsa,kafin shima ya aurota su cigaba da zama a Kaduna tunda komai nashi indigene d'in Kaduna ne,dukan mu a cikin garin kaduna aka haifemu,Dan haka shiyasa muka zama ASALIn Yan jihar Kaduna, muke amfani da komai na 'yan aslalin jihar, wannan kenan,mu shida ne iyayenmu suka haifemu, Aisha itace Babba wacce muke ce mata ukty saboda sunan marik'iyar Abba taci wato Hajiya Aisha shine mu Muke ce mata ukty, Hajiya Aisha wadda tun bayan Abba yayi aure ta rasu, saini Ahmad sai kuma Rasheeda ,sai Maryam sai Zainab Mai sunan kakarmu muke ce mata Ameerah sai Kuma Auta zuhrah wacce taci sunan ummi Kuma itace nan autrmu,to ataikaice dai wanne shine ta k'aitaccen historyn Ahmad Aliyu Arab ya k'arasa fad'a yana murmushi.




Ruky ta jinjina kai,kafin tace .


"Masha Allah Allah ya albarkaci rayuwar ku"AA Arab yace ."ameen kafin yace kema ki bani naki ,"


Babu Bat'a lokaci ruky ta gyara zaman ta itama ta bashi labarin ta akaice .


AA Arab ya jinjina kai kafin yace .

"Masha Allah, Allah ya kare had'a kan mu ".

Ruky tai murmushi ta ansa da Ameen.


AA Arab yay k'asa da murya kafin yace ."fiancee",

Ruky ta d'ago da dara daran idanuwanta tana kallan sa yace.

"please ki bani dama azo anemar min AURANKI gobe",ya fad'a Yana tsareta da ido.

Ruky tai k'asa da kanta kafin tace "sir gobe Kuma?,


AA Arab ya shagwab'e fuska yace "so kike na shiga Wani Hali ?",

Ruky ta girgiza kai yace.

"ok please idan har kina Sona,zakuma kiyi rayuwa Dani ,Dan Allah kinl Amince min zan turo goben Dan banaso ne a bat'a lokaci dayawa ki fad'awa Mamah idan kin koma ciki ",

Ruky ta sunkuyar da Kanta ta tana sauraran sa,yace.


" I love u fiancee" ya fad'a da wata iriyar murya, ruky tai shiru yace.

"Please fiancee Nima ki fadamin kalmar da zanji Dad'i mana Baki taba cewa fa kina Sona ba iyace nine kawai nake fad'a", ya fad'a da Wata siga, ruky ta rufe fuskarta da tafukan Hannunta kafin ta. Rintse ido tace.

" I love u too".


Ai AA Arab dawani Irin mamaki ya kalleta Dan bai tab'a tunanin zata fad'a cikin sauk'i haka ba,kafin yace .

"Thank u fiancee I love more " daga haka ya mik'e ganin Yana Neman zaucewa yace .muje na gaida mamah lokaci na tafiya Ruky itama mik'ewa tai _tai hanyar k'ofar falon Yana binta a baya suka fita..


Suka shiga har cikin falon,ya samu wuri ya zauna Yana Mai Jin kunya Dan wallahi jiyay kamar ya nutse ko Kuma ya juya ya tafi ,Amma bazai iya tafiya baizo ya gaida mamah ba,har ruky ta dawo tace masa ga Mamah na zuwa ta Zauna kan wata kujerar.ba a d'au lokaci ba mamah ta shigo falon da sallama a bakinta AA Arab ya ansa tare da saukowa daga saman kujerar da yake ya tsugunna a kasa Yana gaida mamah ,

Mamah ta ansa masa da fara'a kafin tambayeshi aiki da mutanan gida,da Kuma Yi masa godiya akan k'ok'arin da yay musu shidai AA Arab kansa Yana k'asa, mamah ta mike tace ya gaida mamansa, yace.

" zataji In Sha Allah".


Ya mik'e Yana kallan Ruky yace.


"tafiya zaiyi,haka ruky ta rakashi har compound bayan ya shiga mota Yana kallan ta yace .


"I love u fiancee", Amma Dan Allah karki manta da sak'ona ya fad'a Yana wani kashe mata ido, ruky ta rufe fuskarta da tafukan Hannunta kafin ta Jin jina masa kai sannan ta juya ta koma cikin falon direct d'akin baba hasiya ta nufa Dan zuwa ta fad'a mata sak'on AA Arab ita Kuma ta fad'awa mamah Dan Allah Yana Gani bazata iyaba.....



___________?&


Da daddare AA Arab Yana zaune duk'e a falon Abban sa a gaban Abban, Abba kuma Yana zaune kan kujerar falon,kafin ya dubi AA Arab Abba yace .

" Ahmad naji duk abinda mahaifiyar ka ta fad'a min kuma nasa ayimin bincike sosai akai babu laifi 'yar gidan tarbiya ce , Kuma ma ai nasan mahaifin ta Marigayi AIG umar MaiTama Allah ya masa Rahma ",


AA Arab ya amsa da Ameen kansa har lokacin Yana k'asa Bai d'ago ba Yana sauraran abban nasa.AA ya cigaba Yace .


"shikenan Babu damuwa tunda kace gobe kake so aje nemar Maka auran nata shikenan kaje ka Sanar mata dan ta sanar da magabatan nata ,Nima anjima zan fad'awa kawunnan ka gobe su zo suje suyi tambayar Allah yay Maka albarka,yasa albarka anemanka ,ya fad'a cikin farin ciki Dan dama wanna ranar suke jira daga shi har ummi, wannan yayi musu Dad'i sosai daga shi har ummi,Dan lokacin da ummi ta fad'a masa sai yaga harma tafi shi farinciki da abun.


AA Arab yayi farin ciki sosai da iyayen na sa suka amince Cikin k'an k'anin lokaci haka,da murna da farin cikinsa Daya kasa b'oyuwa har a saman fuskar sa ya shige d'akinsa ya d'auki wayarsa Dan sanarwa da Ruky wannan daddad'an labari...





07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y




*____JAMI'AR TSARO ____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*




*____(MRS SARAKIES =؋?)=?1?____*




*Bismillahirrahmanirrahim*



_____season two ep 8?? 8??



_____________?&


Washe gari kamar yadda Abba ya fad'a Za'a je nemarwa AA Arab auren ruky to Allah dai ya nufa Ayau ake shirye shiryen za'a je tambayar wa AA Arab auran Rukayya a gidan su,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login