Showing 30001 words to 33000 words out of 278032 words

Chapter 11 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1020

da duk abinda ya fada masa domin tasan farin cikin Dansa shine gaba da komai nashi , Allah baxa ta tava auran lateef ba ,saidai idan gawarta xa'a kai masa ita,ya hanaf ne ya daka mata tsawa ,tai sauri ta matsa kusa da mamah tana kuka qasa qasa,mamah ta rungumeta itama ranta a bace , ganin duka ransu a bace yasa shi saukowa ya hau bawa mamah hkr, dacewa babu abinda uncle sunusi ya isa yayi itama ruky ganin tsawar Daya mata ta qara tsorata ta,yasa ya sassauta yace ta daina kuka ya shaida mata cewa babu Wanda ya isa yayi mata auran dole,...


Haka mamah itama taita karfa fa mata gwaiwar karta damu,baba hasiya da take xaune bayan ta fito daga kitchen Jin hayaniyar yasa ta cewa hanaf Allah ya huci xuciyarka ,kuyi hkr,ya hanaf ya mike yay wa mamah sallama ya koma part dinsa, Dan gabadaya lateef ya Bata masa Rai,mamah ta kama ruky ta kaita dakinta ganin yadda take kuka gabadaya jijiyoyin kanta sun tashi rudu rudu, baba hasiya itama ta shige Daki tana mamakin karfin halin laleef,..


Mamah koh kama hannun ruky tai ta kaita har dakin ta ta qara rarrashin ta sosai da tabbatar mata cewa in Sha Allah babu abinda xai faru haka tai ta lallaba ta tai wanka ta shirya Saida ta tabbatar da ta cire Damuwar data ke ciki tavata magani Tasha svd kar tai ciwon kai svd kukun data Sha,ta rufa mata duvet ta kwanta tana nana ta mata data saki jikinta sannan itama ta wuce dakinta tunani fal ranta,,...


_________?&


Alhaji sunusi ne tsaye a falonsa sai matarsa Dake xaune kan kujera sai lateef da shima yake tsaye ransa a bace,kamar yadda shima Alhaji sunusi ransa ke a bacen, cikin kakkausar murya yace ita Hajiya Halima da Bakin ta ta fadi Hakan , lateef ya jinjina masa kai, Alhaji sunusi yace da kansa hanaf din shima ya mareka, wato a takai ce Taran dangi suka Maka, Allah ya kaimu gobe wlh sainaje har gidan na tabbatar musu da cewa aurannan yaxama dole ayi shi Kuma,sun jawa kansu auran ma nan da sati biyu ZA'A yishi sainaga Wanda ya isa ya hana ni , zanga Wanda ya fini iko akanta nidasu,muxu ba mugani nidasu gabadayansu tunda sun nuna min su Basu da mutunci, lateef yace nidai Dan Allah daddy amaida aurannan Nanda sati Daya, Alhaji sunusi ya jinjina kai, Hajiya SA'A ta numfasa cikin bacin Rai tace itama Hajiya Halima Bata kyau taba,ya ZA'Ayi tace bakada baka da tarbiya duk wacce muka baka,to me take nufi,aida bata fadi haka ba,da saita bika ahankali sannan, banji dadin Marin da hanaf yay Maka ba, Amma kaima lateef da laifinka ya xa'ayi kaida kake Neman 'ya ai biyayya ya kamata kayi ba haka ake xuwa wa surukai ba , Alhaji sunusi ya daga mata hannu yace ya isheki SA'A agaban ki akayi daza kice ba haka ake xuwa wa surukai ba to saiki fadi yadda ZA'Ayi Hajiya SA'A tace ai Alhaji dole sai an koya masa matukar Yana San yarsu . ..


Alhaji sunusi yace to baxai koyaba indai akansune muxuba mugani tsakanin nidasu zanga Wanda yake da iKo akan ita Rukayya,ya juya ga lateef Wanda ke jifan mom dinsa da Wani kallo, yace lateef ka kwantar da hankalinka sunma xugani aure xa'a yishi nan da sati biyu, lateef cikin damuwa yace daddy sati Daya dai, Alhaji sunusi ya girgixa kai yace Ina da dalilina nayin Hakan daga Haka ya dauki wayarsa fuuu ya shige daki ....


Hajiya SA'A tabishi da kallo itada lateef kafin ta Maida dubanta kansa tace lateef kadinga sassautawa xuciyarka,idan kaje gidansu yarinyar nan kaga ba'a karbar soyayya ta karfi dole sai ana lallabawa sannan gidansu ai gidan ba inda xakaje kai hayaniya bane tunda Neman AURE kake,ya mike tsaye yace please mom banasan haka Dan Allah ki barni da bacin ran danake ciki, tunda ke baxaki goya min baya ba kibar dadyn man dayake goyamin,daga haka yay ficewarsa daga falon ma gabadaya, Hajiya SA'A ta jinjina kai tana mamakin inda wannan abun nasu daga shi har uban nasa zai kaimusu Dan sarai tasan Hajiya Halima, Bata daukar raini itama,.....


_________ZARI'A________


Nana kina nufin Ameenah har jinya tai Amma yarannan Bai kira malam ya fada masa ba,nidama Saida nace jikini gabadaya ya bani Ameenah ba lafiya take ba Amma malam ya. Hanani xuwa,yanxu badan Allah yasa kinje ba da ya xatai kenan ,kikace har kitchen dinma kinduba babu kayan abinci ,to ya tai da wannan me yawan dana aika mata ,ai baici ace sun Kare ba ,bari malam yadawo goben nan xanje na duba jikinta ai baxai hanani xuwa dubata ba koh tunda Bata da lpy , ....

Nana tace wlh ummah gara kije kawai ki Gani da idanki ahakanma danta ki fadamin duk abinda Kabirun yake mata ne kinsan ta da xurfin ciki wai Batasan abinda xai ta-da miki da hankali, ummah tace Yoh bagara ya tadamun da hankalin ba akan ita hawanjini ,ya kamata tana qaramar ta da ita,nifa wlh nagaji da wannan AURAN,wlh bari malam yadawo goben nan xanje Dan ko ya hanani xuwa wlh baxan yadda ba, akashe auran nan kowama ya huta,wlh saidai idan Nima sakin nawa zaiyi ,daga haka tace Nana tashi ki tafi makarantar Nana ta mike tama gama shiryawa ta dauki Jakarta,tai wa ummah sallama ta tafi....


Tana fitiwo tai kicibis da baba asabe Dake xuba kunun siyarwa na yamma Wanda zaliha xatakai Tasha,Nana tasa kai tafice Bata ko kallesuba, baba asabe tabe Baki zaliha Kuma ta bita ta harara, asabe akace ayidai mugani idan tusa xata hura wuta,ta dubi zaliha wacce ke chava ado tace Maza Mai qashin arziki Yi kiyi ki shirya kixo ki dauka kar ai ta jiranki,zaliha datake kwalliya ta aje madubin tace ganinan fa baba tana turo Baki gaba Wanda yasha uban Jan Baki babu kyan Gani kamar bakin jaba,,baba asabe akace zaliha naga jiya kinkai dare ko abincinne Bai kare ba,Amma naga ai bakya dawo wa dashi, zaliha ta tabe Baki tace wlh kudi na tsaya hadawa wasu ne idan sukaci saikayi ta bin kansa kafin su baka, baba asabe tace aiyo to tunda ana siyarwa ba kwantai akeba aida dadi, Dan hada kudi ai ba abune na damuwa ba tunda suna Baki, zaliha ta qaraso ta dauki bokitin kunun din ta fita waje xuwa wajen me napep dinta Daya xo,asabe ta washe Baki ta raka ta da kirari da habaici akai kaice Wanda akewa ummah,...



*Sbd Yana yin hidin dimun sallah anan xamu tsaya sbd ayyukan da nake dasu ina Mai bada hkr idan Allah ya kaimu bayan sallah sai mu dora daga inda muka tsaya*


*Karku manta dai da salon novel din daban yake ,sbd wannan Wanda muka fara kamar Dan tavawa mukai kadan daga cikin LABARIN,kamar sharar fage ne,nan gaba kadan xamu tsunduma cikin LABARIN in Sha Allah, JAMI'AR TSARO lvr ne ka gagge, kudai ku kabiyoni kuji yadda xata kaya*.....


*Domin akwai chakwa Kiya,xamuji yadda case din shafa xai kasance shin DCP muktar xai iya handling Case din,shin idan angano Wanda yay wannan xalincin ko Dan gidan waye ,ko Dan talakane ko Dan masu kudine ko dan masu siyasa ko sarauta shin xa'a bi case din ko baza a biba, case din xai koma hannun ruky ko baxai koma ba duk da dama rukon kwarya ta Bada,duk wannan ansa tana gaba idan har Kuna biye Dani*.....

*Shin Alhaji sunusi xai Aurawa lateef ruky ,ko auran baxai yuba,shin Mamah xata yadda koko ita Rukyn xata yadda ,duk wannan ansar sai a gava xa'a samu ansarta,*....


*Ga Kuma chakwakiyar gidansu Ameenah,ga Kuma ta gidan mijinta Kabiru,shin ya abun yake duk sai Kun kasance da (Mrs sarakies) Sanna xaku samu ansar tambayar nan*.....


*Ina muku patan alkhairi ayi sallah lpy Allah ya nuna mana nagode sosai da Kuka kasance dani acikin labarina na JAMI'AR TSARO*...



07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD



*_____JAMI'AR TSARO_____*


*_____THE WOMEN POLICE____*



Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD



*NA*


*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ____*


*____(MRS SARAKIES)____*


*=?1?QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION (QUWA) =?1?*


*Bismillahirrahmanirrahim*


____season one ep 1?? 5??

_______
'?
'?

*Assalamualaikum barkanmu da dawowa hutun babbar sallah patan anyi sallah lpy,to Allah ya maimaita mana, yasa muna da raban ganin na badi,idan Kuma bamu kaiba Allah yadatar damu Rahmarsa,....*


_________?&

Washegari asabar alhamdulillah ruky Bata tashi da ciwonkaiba,Amma kwata kwata bata cikin good mood, asibiti taso xuwa Amma zata kira Khalil idan yaje ya hadata da baba lami suyi magana taiwa shafa ya jiki,...


Haka ta Mike ta fita Tai break fast sbd kada mamah ta biyota,idan taga Bata fitoba, tana sauka ta tadda Baba hasiya da tea flask a hannun ta tai hanyar dining alamar yanxu ma Ake hada table din ganin Ruky tai hanyar falon, baba hasiya tana dire tea flasks din kan dining tace a'a uwata taso ki karya ai nama gama ,kafin tai magana Mamah ma ta sauko, cikin shiga ta Alfarma,ta qasara saukowa tai hanyar dinning din itama baba hasiya ta gaidata mamah ta ansa da murmushi, ruky ma ganin mamah yasata mikewa ta qaraso dining din ta gaida baba hasiya tana Jan daya daga kujerun dining din, ....

Baba hasiya ta ansa da murmushi a futkarta tana tsokanarta,ta juya ta gaida mamah wacce ke lura da yanayinta, mamah ta xuba mata ido tace auta lpyanki kuwa,kodai tun Abin jiyane daya faru, cikin damuwa tace banace kicire komai ba Dake ranki ,saitai murmushin yake tace a'a mamah me kika gani,mamah tace naga yanayinki ya canxa kwata kwata ba kamar ko yaushe ba, ruky tace a'a, mamah ta sauke numfashi tace aishikenan,xuba abinci kici,babu musu ta xuba mamah ta xuba nata haka Dining din yay shiru sai qarar spoons kawai ke tashi,sunyi nisa acin abincin hanaf ya shigo,da sallama abakinsa sanye da jallabiya ash color,wacce tai masa kyau sosai kamar sa ta fito sak shida ruky Dan dai kawai shi namijine ,Yana kokarin xama ya gaida mamah, mamah ta ansa masa , ruky ta gaida shi ,ya ansa mata Yana bayan ya xauna,ruky tai serving dinsa abincin da tasan Yana so,bayan ta hada masa coffee,ya kalleta yay murmushi yace thanks Auta,itama murmushin ta sakar masa,ta cigaba da cin abincinta shima haka,.. .


Saida suka gama tas sannan suka koma falor suka zauna ya dauko laptop dinshi zaiyi aiki da ita Amma ganin har lokacin ruky Bata saki ranta yadda ya ta sava ba yasa shi xama kusa da ita,yace xo muyi kallo,babu musu ta matso domin tasan film din da takeso xai kunna mata,Wani American film ne me bala'in kyau, Dan haka ta nutsu ta fara kalla tayi nisa cikin kallan gabadaya taji kamar ancire mata damuwar Dake damunta sbd yadda film din ya dauko Dadi,....

Sunyi kusan Rabi ta kalli ya hanaf Wanda shima film din yake kallo sosai sbd kawai ruky ta cire Damuwar Dake ranta,tace ya hanaf please minti biyu Ina xuwa ,ya kalleta yace Ina xaki tace dakina,yace ok saikin dawo ya Danna stop, ruky ta mike tai hanyar stairs da sauri sbd tunowa da tai cewa zata kira Khalil awaya , bayan ta shiga dakinta ta dauki wayarta Wanda babu Miss call din Wanda ta fara cin karo dashi saina lateef, tai tsaki tashiga call log tai blocking dinshi,ta manta ma jiya batai blocking nashiba,...


Talalumo contact din Khalil,tai darling babu musu yay picking, suka gaisa cikin girmamawa,tace ya asibitin kaje yace a'a yanxu dai nake shirin tafiya tai murmushi tace sannu da kokari yace kema sannu ranki dade ruky tai murmushi tace kajika fa danai me, shima murmushin yayi yace da kikai kokari kema,tai dariya tace,kasan Ina taso na fada Maka,jiya dai munkai headwater case din nan ,Hanan ta takurani Saida muka kai, but Yana hannun DCP Dani kaina,shi muka sako cikin case din,ya shaida min in Sha Allah xaiyi iya bakin kokarinsa,wajen goyan bayan case din, Khalil da har ransa yaji dadin Sako DCP da akai yace Masha Allah ranki dade , Allah yasa adace,Kinga xamuyi case din in Sha Allah Batare da Wani far gava ba,ruky tai fari da ido kamar Yana ganin ta,tace matsoraci gsky anyi matsoracin Dan jarida,yay dariya yace ranki dade ba tsoro bane kawai dai kinsan ko case indai a kasar nan ne Saida uban gida,ta sauke numfashi tace gsky, Amma Khalil Ina tunin Wanda yay raping shafa kamar fa Yana da kudi ko Kuma Dan masu kudinma kansa,Amma ba wannan nake dubawa ba DCP nake dubawa Allah yasa ko Dan waye yay wannan barnan Allah yasa idan angano kada abar case din nan,....

Khalil ya sauke numfashi yace tun ranar da mukaje gidan da naga gidan nake sake sake araina, ruky tace karkiji komai nidai in Sha Allah zan tsayu tsayin daka wajen naga anhukanta koma waye ,indai har mungano,wlh Khalil Ji nake ko ciki Daya muka fito da mutum kaga dai shine karewar kusanci koh,matukar shi yay wannan aika Aikan wlh sai inda karfina ya kare, wajen ganin an hukuntashi addu'a kawai zamu cigava dayi, Khalil yace in Sha Allah ranki dade Allah dai ya bamu SA'A, ruky ta ansa Mai da Ameen,tace idan kaje please ka hadani da babar shafa inaso xamu gaisa, vaxan samu damar shigowa ba yau bana Jin Dadi ,cikin damuwa Khalil yace subhanallah ranki dade bakida lpy ne,tai murmushi tace bawani jinya bane kawai dai jikinane nakejin Babu Dadi,yace ayya ranki dade Allah ya Baki lpy , Allah ya qara lpy,....


tai murmushi ta ansa da Ameen,Jin yadda ya ta-da hankalinsa,tace turo min da account details dinka xan aje Wani kudina aciki,cikin Rashin damuwa yace ok bari na turo miki yanxu, babu dadewa ya turo mata,itama babu Bata lokaci ta tura masa, Yana Gani ya kirata yace ranki dade ya shigo,babu damuwa,ruky tace ok ,babu komai Khalil, ka rike awajenka,yace eh xan aje Miki in Sha Allah babu komai,ruky tace Ina nufin na Kane ,ya xaro ido waje yace ranki dade,nawa Kuma Tai murmushi tace eh na baka ne,yace a'a ranki dade wlh baxan karbi kudin kiba,tace ni badan wata hidiman da kakeyi na bakaba,kawai baka nai,ya girgixa kai yace a'a ranki dade wlh baxan karbi kudinkiba , ruky ta hade Rai kamar Yana gabanta tace saidai idan Rainawa kai ,yace ko kadan ranki dade,tace toka karva,yarasama me xaice svd mamakin yawan kudin yace ranki dade kudinfa dayawa ai sunyi yawa,tace babu Wani yawa ,bari na barka haka saika dawo ,cikin jindadin wannan kyautar vazata da ruky taimasa yace nagode sosai ranki dade Allah ya qara girma ya kareki aduk Inda kike tai murmushi tace Nima na gode sai anjima,daga haka ta kashe wayar tana murmushi,.....

Ruky ta aje wayarta ta sauka qasa, ta koma wajen ya hanaf dayake latsa wayar sa,tace ya hanaf na dawo yace ok,daga haka ya dauki laptop din ya danna continue suka cigaba da kallo, mamah tana dakinta Dake qasa, baba hasiya ma ta shige dakinta tunda ta gama , saikuma na Rana, sallamar da akai da kakkausar murya ce tasa suka Jiyo, ganin Alhaji sunusi ne yasa su ansa masa suna Kuma gaidashi lokaci daya,...


Bai ansa musuba Fuskar nan tasa babu alamun fara'a ya Kalli hanaf yace kai marar kunya Ina Hajiya Halima take , Ruky ce ta mike jikinta na rawa ta tafi ta sanarwa mamah, mamah Dake xaune kan darduma tana karanta al'qur'ani saida ruky taga takai Aya sannan ta sanar mata xuwan Alhaji sunusi,mamah jinjina mata kai tace kice masa ina xuwa, ruky ta fita,ta sanar masa ta koma wurin xamanta jikinta gabadaya rawa yake Dan Batasan Kuma me uncle sunusi yaxo dashi ba, mamah ce fito sanye da hijab dinta har qasa, ganin Alhaji sunusi tsaye ko xama banyiba cikin nuna babu komai a xuciyarta yasata cewa a'a Alhaji sunusi xauna mana ,tana Mai qarasowa cikin falon ta xauna ita,....

Alhaji sunusi cikin bacin Rai yace ba xamane ya kawoniba Sako ne naxo na fada muku ,duk gavakidayanku ya fada Yana nuna su har hanaf ,wanda ya juyo Yana masa wani Irin kallo, yace jiya lateef yaxo gidannan kunfada masa magan ganu San ranku, Harda hanaf ya mareshi, Hajiya Halima meyasa bakyason lateef ya auri Rukayya ne,mamah tai murmushi tace ni bani ce me AURAN nasa ba da dazakace meyasa banasan sa Daya auri Rukayya ba,ita wacce xata xauna dashi ai ita xaka yiwa wannan tambayar, yarinyar tace Batasan sa ai ba'a mata dole ba, Alhaji sunusi yay mata Wani kallo yace Ina lokacin da kuke ta bamu,mamah tace wannan Kuma ai lokacin da kake xance ai shine wannan Wanda muke ciki, Alhaji sunusi yace me kike nufi tace ai kasan abinda nake nufi, yace to ba maimaita magana ce ta kawo niba , xuwa nai na shaida muku cewa na tsaida ranar AURE Nanda sati biyu,Danna fasa wata Dayanma tunda naga damar dana baku ce yasa kuka saki jikinku kuke duk abinda Kuka ga dama,....

Ya hanaf da ransa yay mugun Baci ya yunkuro xai Yi magana tareda mikewa tsaye mamah ta daga masa hannu tace wannan ba maganar ka bace Hanaf, Alhaji sunusi yace a'a kyaleshi kila Nima Marin nawa zaiyi kamar yadda ya Mari lateef,Mamah ta Kalleshi tace wannan ba tarbiyar gidan nan bace kaima ka sani,ta kalleshi ido cikin ido tace baxan ma yata auran dole ba tunda tace bataso wlh babu Mai mata dole wai ana so dole ne, Alhaji tun Ina Jin kunyar fada. Maka magana har ka jawo na daina,tun muna girma da arxiki a bar xancennan,...

Wlh Allah babu Mai yiwa Rukayya auran dole, Alhaji sunusi yace haka kikace to xanga idan har kin fini iko da ita nanda sati biyu,ya nuna ruky wacce tunda ya fara magana ta makale a bayan kujera take Kuka kamar ranta xai fita,yace nan da sati biyu kishirwa AURANKI keda lateef kinsan bana magana biyu daga haka yasa kansa ya fice daga gidan gabadaya tareda securities din dayaxo dasu, Yana fita ruky tai hanyar stairs da gudu ta shige dakinta,ta dauki wayarta cikin ihun kuka ta kira ya Tahir ta fada masa abinda Alhaji sunusi yaxo ya fada,ya Tahir ya rude Jin autar tasu tana kuka kamar ranta zai fita,yace Auta relax babu Wanda xai Miki auran dole indai Ina nan please ki daina Kuka,ta qara sautin Kukan ta cikin muryarta da Bata fita sosai sbd Kuka tace Dan Allah Yaya kazo gobe ka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login