Showing 246001 words to 249000 words out of 278032 words

Chapter 83 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1026

kan k'ofar d'akin ummah Wanda ake ta jibge kayan abinci,su lawisa Dake kan barandar baba asabe da ita Kanta Baba asaben idonsu yana kan k'ofar d'akin ummah kamar zai fad'o haka suke kallan kayan abincin da ake ta jibgewa,yaran su lawisa kuwa kawai suka d'auki murna da wak'ar ga shinkafa ga shinkafa sai kace Basu ta'ba ciba .sai da aka gama kawo kayan nan tas sannan ya Kalli Ameenah wacce itama mamaki ya kasheta ganin wannan uban kayan da aka kawo,yace.


"Ameenah tashi ki shirye Kije waje shamsu ne yazo zaku gaisa",ya fad'a har lokacin bakinsa Ya kasa rufuwa saboda farin ciki.


Ummah data lek'o daga d'aki Jin hayaniyar 'ya'yan su mardiya Dake ta ihun shinkafa shinkafa tana kallan malam Auwalu Jin abinda ya fad'a tace.

"Wani shamsu Kuma?", ta fad'a tana kallansa.

Ya ce da cikin farin ciki.

"shamsu dai tsohon saurayin Ameenah Wanda muka Had'u dashi a Kaduna ranar.ya fad'a cikin fara'a..


Cikin mamaki ummah tace .


"To iKon Allah,shine yazo?",ta fad'a tana K'arasa fitowa daga cikin falon.


Malam Auwalu Yace .


"eh yanzu ma haka yana waje yace yanaso ne su gaisa da Ameenah kafin ya tafi".


Ummah ta kalli Ameenah kafin tace cikin sanyin murya.

"to tashi kije ki Sako hijab D'inki",ta fad'a tana kallan Ameenah..


Batai musu ba ta Mik'e cikin mamakin Mai zaisa ya K'irata yace sai sun gaisa kafin ya tafi,Bata da ansar tambayar ta Hakan yasa ta kauda tunanin ta..

Baba asabe kasa Gane wani shamsu suke magana akai tai dan hankalinta yana kansu duk abinda suka fadamin akan kunnan ta suka fad'a,ta dai zuba musu ido tana kallansu gaban ta na fad'uwa, ganin komai sai ummah tai mata fintunkau.itako gata kullum cikin ganin masifa take da tashin hankali Irin iri,waye Kuma shamsu?ta tafi duniyar tunani,abinda zuciyarta ta Bata ansa dashi ne yasa ta soma girgiza kai aranta tana cewa "a'a bama shi bane wannan ai bazaima tab'a yiyuwa ba Dan baza su tab'a had'uwa dashi ba, idan har shamsun da take hasa shene SHikan yanzu ma ai ya mantama da Ameenah" ,ta fad'a tana girgiza kai cikin damuwa kawai saita fashe da Kuka k'asa k'asa ganin abinda ranta ya ayyana mata shi zuciyarta ke San gas gata mata kafin ta mik'e da k'yar shige falonta tana Jin jiri na Neman kada ta .


Tai sallama bayan ta k'araso ta tsaya nesa dashi kanta a k'asa.

Barrister shamsu Dake jikin motar sa ya zuba mata ido Yana ansa sallamarta tare da murmushi.ya shafa kansa Yana kallanta ya k'ira sunan ta da .


"Ameenah!",

Ta d'ago tana kallan sa kafin ta ansa masa cikin Jin kunya..


Yay gyaran murya kafin yace.


"Kin ganni Babu zato ko? wallahi kullum Ina ta Saka ran zanzo to kuma ayyuka sun hanani, bama iya wannan ba ina ta Lissafine lokacin da zanzo ya zamto dai dai da lokacin da kika gama iddarki idan Kuma lissafina yazo dai dai to yau kika gama iddarki koh?",ya fada Yana kallan ta da murmushi a fuskarsa.


ta d'ago tana kallan sa da mamakin zancen sa. yay murmushi yace.


"Ko ba haka bane ?",

Ta jinjina masa kai alamar eh.

Ya Sauke numfashi kafin ya k'ira sunanta da..


"Ameenah!,ya cigaba Ba Wani abunne ya kawo Ni kunkiba illah dalili guda d'aya, inaso Kuma idan kika ji Dan Allah ki tausayamin ki amince da abinda nazo miki dashi hannu bibbiyu", ya fad'a Yana kallan ta


Ita dai Ameenah tai shiru kanta yana k'asa har lokacin batai magana ba, ya cigaba Yace.


"Ameenah nasan a Baya munyi soyayya munso Junan mu ,sai dai Allah Bai nufa da zamu zauna k'ark'ashin inuwa D'aya ba saboda Wani dalili da ubangiji ne kadai yasan ma'anar yin Hakan ,Amma Kuma ni har yau na kasa cireki a Raina,Dan Dana ganki a ranar sai naji soyayyar ki ta dawo min sabuwa fill acikin zuciyata",ya fad'a Yana kallan reaction d'in ta kafin ya cigaba yace.

"yanzu tambayar da zan miki itace Ameenah kina sona har yanzu kamar yadda Nima nake sonki?"ya fad'a Yana kallan ta


Ta sunkuyar da Kanta k'asa Amma Batai magana ba gabanta Yana fad'uwa tunowa da tai ata raiyar su ta shekaru uku da suka wuce, tunanin ta ya katse ne lokacin da taji yace .


"Kice Wani Abu mana",ya fad'a Yana kallan ta ganin tak'i magana yasa ya cigaba Yace.


"Ameenah wallahi tun ranar dana K'ara Ganin ki a kaduna har muka rabu bank'ara samun kwanciyar hankali ba har yau da nake gabanki",ya fada da sigar tausayi.nan ma dai batai magana ba.


Yace ."Dan Allah kice Wani Abu mana Ameenah!?", ya fad'a Yana kallan ta..


Ta kalleshi cikin sanyin murya tace.

"Ni yanzu bansan me zance ba ".ta fad'a tana sunkuyar da kanta k'asa..


Ya Sauke numfashi yace.

"Kin sani mana kawai sai dai fad'a mun ne baza kiyi ba",

Ta girgiza masa kai alamar a'a.yace .


"To ki fad'a min Ina sauraranki", ya fad'a Yana kallan ta .

ta rufe fuskarta da jihab d'in jikinta tana k'in yarda ta kalleshi.ya sauke numfashi yace.


"Ok na Gane"but Kina da waya ?",

Ta Jinjina masa kai alamar eh.yace .

"To kawo na sa miki number ta",idan yaso sai muyi magana Koh?",

Tace "na bar ta a gida",

Yace "ok wacce kala ce ?",


Tace .

"Keyfad ce".

Ya Jin Jina kai Kafin ya Mik'a mata wayarsa yace .

"Samun digit d'in ki",ya fad'a Yana Mik'a mata wayar .


Ta karb'a tasa masa tare da Mik'a masa,ya karb'a Yana furta thanks a saman lab'b'ansa kafin yace .

"Kije gida idan na sauka anjima zamuyi waya kinji", ta ce .

Nagode Allah ya kiyaye",ta fad'a a Sanyaye.

Yay mata murmushi yace.

"Nike da godiya meenah sunan Daya k'irata dashi kenan kafin ya shiga mota ganin lokaci na tafiya kuma Kaduna zai koma ,sai da ta shiga gida sannan ya tada motar yay reverse ya tafi Yana Jin Wani nauyi Daya tokare masa a k'irjinsa Yana narkewa kad'an kad'an.....




07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y





*____JAMI'AR TSARO____*



*___THE WOMEN POLICE ___*



*NA*



*___NAJA'ATU UMAR FAROOQ ___*



*____(MRS SARAKIES =؋?)=?1?____*



*Bismillahirrahmanirrahim*



_____season two ep 9?? 7??



__________?&


Shirye shiryen biki kawai akeyi , Ruky tana samun gyara yadda ya kamata,idan kukaga yadda ta koma sai kunyi mamaki ,Dan antyn Sudan gyara take mata na musamman bana wasa ba, ko wurin aiki ma ta d'auki hutu ta daina zuwa sai bayan biki,gabad'aya jikinta ya sauya fatarta ta k'ara murjewa tayi kyau sai shek'i take tana Wani santsi kamar Babu gobe, washe garin ranar da aka fara grayan da AA Arab yazo zai kawo mata Sak'o taje zata karb'a daya ganta sai da ya kusan sakin layi saboda yadda ta sauya masa lokaci D'aya Allah ne dai ya taimaka ya kai zuciyarsa nesa Amma da anyi Abun kunya,Dan gabad'aya Gani yayi ruky ta sauya masa Dan komawa tai kamar wata shuwa Arab Kuma a hakanma iya na kwana D'aya akai mata Dan antyn Sudan duniya ce indai wajen gyaran Amare ne ke harma da uwayen gidan baki daya suma ba'a barsu a Baya ba.....


Yanzu haka wajen K'arfe biyar da Rabi na Ranar tana kwance acikin d'akin ta tana hutawa akan gadonta Dan tun safe da antyn Sudan ta K'irata akan ta fito a cigaba daga inda aka tsaya na gyaran da ake tai mata Bata samu ta huta ba sai wajen k'arfe uku na yamma sallah ce kawai take tsaidasu idan anan gyaran nan , Aiko data dawo d'akinta shine ta kwanta tana hutawa Dan gabad'aya jikinta ya mutu mus saboda gajiya Dan har bacci ma ya fara d'aukar ta Dan wallahi ji tai gabad'aya Abun yama fita aranta.


Anty mufeeda ta biyo bayan ta da Wani turare Wanda zatai awa D'aya da Rabi anayinsa da Kuma Wani ruwan tsumin a cikin kofi.ta nufo d'akin Ruky dashi.


Knocking d'in da akai tare da Bud'e k'ofar d'akin da akai aka shigo da sallama yasa ta runtse idonta da k'arfi kamar bacci take Dan tasan me ya kawo me shigowar.aiko ita d'ince Dan saida gaban ta ya fad'i saboda far gaba Dan e wannan lokacin akeyin turaran ,Anty mufeeda tai K'iran sunanta bayan ta shigo cikin d'akin,Bata ansa ba tana K'ara runtse idonta da kyau.sai da ta zagayo har Inda tasa kanta kafin ta tab'o ta tana K'iran sunan ta da "Auta! tashi",ta fad'a tana k'ok'arin shafa fuskar ta.


Ruky ta Bud'e ido kamar Mai bacci kafin ta ansa a Sanyaye tana zubawa anty mufeeda idanuwan ta Wanda suka sauya lokaci D'aya saboda gajiya.Anty mufeeda ta mik'a mata kofin hannun ta kafin tace.


"Tashi ki shanye,bansan kuma gardama"ta fad'a tana tsuke fuska Dan kullum sai sunyi wannan dramar ita da ruky kafin tasha.


Ruky ta tura Baki gaba kafin tace tana ya Mutsa fuska.


"Gaskiya anty na gaji da Shan wannan kayan d'acin wallahi bakiji yadda yake tsayamin amakogaro ba idan Nasha", ta fad'a kamar zatai kuka.


Anty mufeeda ta k'ara hade Rai kafin tace.

"Baza ki tashi Kisha ba,ke ba kisan gata muke miki ba ,to wallahi akan wannan abun ko mutuwa yake akanki saboda soyayyar da yake Miki wallahi sai ya sauya miki Kuma ki gwada ki Gani wallahi sai kince ai dama na fad'a miki,ai kowa ma haka yake daurewa yake Sha ba don San rai ba, idan kuma so kike ki zauna karki kan karowa kanki mutunci to Shikenan saina k'yaleki ki zauna akai ki gidan nasa a hakanki lami,Dan wallahi keda kanki sai kinzo kina Nema da kud'inki ma watarana ,Kuma Zaki ce na fad'a miki,zaki karb'a ko in tashi in tafiyata", ta fad'a tana hararar ruky.


Ruky ta tura Baki gaba tana Jin wata matsnanciyar kunya na rufe ta,ta mik'e Zaune daga kwancen da take tana B'ata Rai ta karb'i kofin ta kafa a Baki Tasha tana ya Mutsa fuska harta shanye tas,itadai anty mufeeda Kallan ta kawai take tana tunanin dole ma taiwa ruky karatun ta nutsu duk da tasan antyn Sudan ma tana mata Amma itama zata K'ara Yi mata Dan tasan cewa aure ba k'aramin Abu bane ba,harta shanye ta ajiye kofin kafin ta juya baya tana Jin kamar zatai amai.


Anty mufeeda ta d'auki kofinta kafin ta kalleta tace.

"Ga wannan turaran ki tashi kiyi shiyi shi baba hasiya zata kawo Miki garwashin Irin yadda mukai jiya zakiyi kinji ko Baki ji ba?", ta fad'a tana kallan Ruky.

Ruky ta Jin jina mata kai ,anty mufeeda tace.


" ba Jin Jina min kai zakiyi ba ansamin zakiyi sannan Kuma ki shirya anjima ma ma akwai Wani tsumin",tana fad'ar haka tai hanyar k'ofar fita daga d'akin.ruky tasa kuka kafin tace .

"Wallahi anty nidai kawai na hak'ura da auranma gabad'aya indai haka ZA'Ayi tayi gabad'aya bakina yanzu baya tasting komai saina wad'an nan abubuwan baurin", ta fad'a tana tura Baki gaba.anty mufeeda tana jinta Amma batace komai ba ta ficewarta daga d'akin gabad'aya tana tunanin lallai ruky Bata da hankali.Ruky ta koma ta kwanta tana Jin gabad'aya auran ma Yana Neman fita mata arai , haba ace Abu yak'ici yak'i k'arewa tun yaushe ake wannan Abun taja tsaki tana K'ara gyara kwanciyar ta.


*Washe gari*


Yau ya kasance Laraba za'ayi cocktail party,kamar yadda suka tsara wannan Karan ma iya 'yan matane zasuyi Banda maza, k'arfe biyar da Rabi na yamman Ranar na hango ruky a cikin Wani d'aki Dake downstairs Wanda yake kusa Dana mamah,tana gaban wata Me kwalliya tana tsara mata kwalliya ta kece raini.sanye take cikin Wani rantsatstsan material Wanda yay mata bala'in kyau head d'in shima kalar maroon ne, a kan katifar Dake cikin d'akin k'awayensu ne 'yanmata Wanda sukai school dasu tare dama wad'anda suke aiki tare yawanci ma duk Hanan ce ta jawosu tunda Wanda suka zo bikinta ne Dan ita Bata da k'awaye ma, suma kansu k'awayen cikin ankon Wani yadi suke Mai kalar Golden yellow ko Wacce taci kwalliya ta kece raini sai hira suke suna Murmushi,Hanan ce ta shigo d'akin itama cikin Wani dank'areran material Dunkin' doguwar riga fitted gown golding yellow Irin yadin jikin 'yan matan wanda d'inkin yayi mata bala'in kyau sai zuba walwali take tayi Wani fresh abinda Yo abunka da sabuwar amarya, Kuma yazo ya had'u da gyaran da aka mata Wanda Bai gogeba na amarci.


Ta k'araso har gaban Ruky wadda ake d'aurawa Head tight tana ajiye mata highheel d'in da zata Saka da Kuma Pos d'in da zata rik'e kalar Golden.


Kafin ta d'ago tana kallan Ruky tace ..


"Wow! Masha Allah sister in-law na,kinganki kuwa Anya ko ya Ahmad zai gane ki kuwa", ta fad'a tana rike hab'a da mamakin ganin yadda Ruky ta sauya kamar ba itaba,dan ta fito sak a amarya Mai capacity.


Su kansu k'awayen kallon ruky kawai suke tun lokacin da aka fara mata kwalliyar kafin su shiga Yaba kyan da tai itadai batai magana ba tana jinsu Dan wallahi Wani Irin fad'uwar gaba kawai takeji da Kuma tsoro na shigar ta ,me kwalliyar ta sa mata jewelry din gold din da zata Saka kafin ta dago tana Kallan ta ganin angama kwalliyar Masha Allah kawai ta furta tana yiwa Allah tasbihi acikin zuciyarta kafin tace a fili.


"Gaskiya wannan angon dole yazo ya k'aro wasu Kash d'in kodan yadda amaryarsa tai bala'in kyau,danni kaina na Dad'e Banga amaryar da naiwa kwalliya datai kyau Irin wannan ba",ta fad'a tana murmushi.


Hanan tai murmushi kafin tace.


"Karkiji komai ki Fad'i kome kike so Dan wannan angon ba kamar sauran angwaye yake ba, bana tunanin akwai abinda zai so sama da ruky,Dan ko kad'an baya k'yashin ganin ya biya ko nawane akan ta,ke in tak'aice Miki bayanima ko ransa zai iya badawa fansa akan aminiyata",ta fad'a tana murmushi, gabadaya k'awayen nasu shewa suka sa da ihu kafin su had'a baki wajen cewa gaskiya ne wannan, domin Muma kanmu shaidane Dan ashobe ma kyauta aka Bamu suka fad'a suna ta yabon kirkin AA Arab.


Saudat Mai kwalliya ta rik'e baki cikin mamaki kafin tace .


"To gaskiya Rukayya ki rik'e mijinki da kyau Dan na Dad'e banga ango Irin wannan ba gaskiya Yana sonki so ma ko Bana wasa ba , Allah ubangiji ya Baku zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba",ta fad'a tana murmushi.gabad'aya suka ansa da Ameen.itadai ruky tai shiru tana jinsa Amma Batai magana ba,kafin saudat make up ta shiga Yi mata pictures da videos kala kala,bayan ta gama ta D'ora a ashafukanta na SADA zumunta....


Bayan angama Hanan ta Matso kusa da ita suka fara pictures tare da k'awayen nasu harma da videos, suna cikin Yi anty mufeeda tashigo itama cikin shiga ta Alfarma cikin Wani less sai zuba k'amshi take da walwali tana kallan Hanan tace.


"Hanan ku fito fa ga motocin sun iso tun d'azu ku ake jira",ta fad'a tana k'ok'arin juyawa ta fita.hanan ta ansa mata da girmamawa kafin ta Kalli k'awayen tace.

" kuje ku fara shiga motocin bari mu fito", ta Kalli wata cousin sister d'in Ruky Mai suna Salma tace .


"Salma zo mu kamata mu fita da ita", Babu musu Salma ta taso ta kama hannun ruky itama ta kama d'ayan kafin su fita daga cikin d'akin gabad'aya.


Motocine na Alfarmar sukai parking a bakin gate d'in gidan gabad'aya kawayen amarya dana 'yan uwa sun shiga cikin motocin,iya motar amarya ce kawai aka shigo da ita cikin compound d'in gidan aka shigar da ruky bayan motar sai Hanan Dake gefen ta ita da anty mufeeda sai Salma a gaban motar,suka fita daga gidan bayan an wangale musu gate d'in suka fita...


Awani babban hole da ake ji dashi a agarin Kaduna sukai parking kowa ya fiffito daga cikin motar,anty mufeeda ta kamo hannun ruky ta tayata saukowa ya Allah haka jama'ar wajen suka shiga furtawa dan kayan sunyi mata bala'in kyau ba kad'an ba kamar ki sace ta ki gudu Dan kyau,hanan ta zagayo suka kama hannun ta suka shiga da ita cikin tangameman hole d'in Wanda already iya k'awayensu ne sai cousin sister's d'inta 'yan mata da wasu daga cikin yayunta mata Wanda suka kasance cousin d'insu dan duk k'awayen anty mufeeda ne ,komai an tsarashi yadda ya dace ,wajen yayye daban wajen k'awaye ma daban ga Kuma JAMI'AR TSARO fans suma table d'in su daban an ware musu sai kallan Ruky suke suna Yaba kyan da tai.aka shigo da amarya photographers suna ta aikinsu na d'aukar pictures da videos,aka fara gudanar da aparty yadda ya kamata babu hayaniya babu hargitse babu komai,akai komai na masu aji ,kusan 3 hours akayi anayi kafin a tashi Hanan ko harta turawa AA Arab pictures d'in da taiwa ruky,bayan antashi suka kamo amaryar kamar yadda suka shigo da ita suka shiga mota Dan tafiya gida kafin kuma idan Allah ya kaimu gobe ayi dinner ga Kuma sword crossing, Dan events d'in gobe ma ai shine za'a Sha shagali sosai amore.......



*JAMI'AR TSARO fans ku shirya Dan gobe akwai shagali =؃?=؃?=؃?=؃?*





07066598376________
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y







*____JAMI'AR TSARO____*




*___THE WOMEN POLICE ___*



*NA*




*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*




*____(MRS SARAKIES =؋?)=?1?____*




*Bismillahirrahmanirrahim*



______season two ep 9?? 8??



_____________?&


Washe gari Alhamis, yau ya kama kenan,za'a Yi dinner da Kuma sword crossing saboda kunsan abun na masu d'amara ne=??,gidan mamah cike yake da Bak'i ta ko Ina duk da sunzo bikin su ya Tahir Amma hakan Bai Hanasu zuwa bikin ruky ba saboda Auta ce daga kanta Kuma mamah ta rufe aurar da 'ya'ya shiyasa duk sukai mata Kara suka K'ara zuwa duk da wasu Basu Samu damar dawowa ba , Amma Kuma Hakan Bai Hana gidan cika ba,sai naga kamar bikin ruky ma mutane sunfi zuwa sosai Dan har yafi bikin su ya hanaf cikar mutane ,Dan har yau mutane Basu daina zuwa ba..


Wajen k'arfe biyar da Rabi na yamma saudat Mai make up ta fara D'an d'asawa Anty mufeeda kwalliya,bayan angama mata sai Kuma ayiwa Hanan , saudat make up tanyiwa anty mufeeda pictures bayan angama kwalliyar Tana kallan da murmushi a fuskarta tace .


"u look more beautiful mom mimie".ta fad'a tana kallan anty mufeeda.


Anty mufeeda ta Mai da mata da Martanin murmushin ta kafin tace" thank you" ta fad'a tana mik'ewa daga zaunan da take tare da kallan hanan wacce ta shigo d'akin Bakin d'auke da sallama tana kallan ta da murmushi a fuskarta tace .


"Anty har angama fa, sai Kuma ta tsaya ta rik'e baki ganin yadda anty mufeeda ta koma kamar ba itaba saboda yadda tai Wani kyau na musamman,sai Kuma ta k'ara sakin Wani murmushin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login