Showing 201001 words to 204000 words out of 278032 words

Chapter 68 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1048

Dake falor tana jinsu tai saurin cewa "Yo Babar mu Baga muba, ki barmana shi kawaymu cinye muda 'ya'yan mu daga nan har dare zai ishemu"baba asabe ta d'aga murya da k'arfi ta ce "idan uban kine ya bani jarin ba sai na gani ba"Mardiya ta ce "yo aini Gani nai tunda Mai kaiwar Bata da lpy da abarshi ya lalace ba gara ki bamu mu cinye ba kin samu Lada ba"Baba asabe ta ce"to baxan bayarba, idan Kuma k'wata zakiyi sai nagani" jakar banza Jakar wofi wacce Batasan komai ba sai cikin ta"mardiya ta ce"yo ya baxan so abinci kuwa "baba asabe ta ce "to xageni, dama ai kin Saba"mardiya tai shiru ta fara k'unk'uni qasa qasa, baba asabe tai k'wafa ta dubi zaliha Dake mata magana.....



Zaliha ta Kalli baba asabe cikin dauriya ta ce "Babar mu bari na k'ira Wanda muke saida abinci tare dasu a tashar, akwai Wanda xasu Saida min ko bana nan ,bari yanxu xan k'ira idan Ali yaxo kawai ki bashi ya kai"baba asabe ta ce "wa zaki bawa ya siyar d'in zaliha? zaliha ta ce"tunda nace ki bayar ki bayar mana sai dai kawai kiga an kawo Miki kud'in ki"baba asabe ta washe Baki cikin xumudi ta ce "to shikenan bari na k'arasa had'a kayan" daga haka ta fita daga d'akin.ganin baba asabe ta fita yasa zaliha d'auko wayarta tai darling number Alhaji tanko,babu dad'ewa yay picking,kafin tai magana ya ce "Yaya baby na kin fito ne? Zaliha ta ya Mutsa fuska tai qasa da murya yadda babu Mai jinta, tana k'ok'arin danne aman dake San taso mata" ta ce "Alhaji bani da lpy ne yau baxan fito ba,gashi munyi abinci, shine nace Ali zai kawo abincin Dan Allah idan ya kawo zai bawa sailuba,Dan Allah kayi mun juyan abincin yau sai kasa ta Rabawa 'yan tashar kamar yadda kake min"Alhaji tanko ya ce "Babu damuwa baby, Amma meyake damun ki? zaliha ta yamutsa fuska ta ce "zazzabi ne", Alhaji tanko ya ce "Allah ya sawake sai naxo dubiya da daddare,me kike so nazo miki dashi? zaliha ta ce"bana tunanin xan iya fita yau sbd gabad'aya bani da k'arfin jiki,zazzabi nake sosai "Alhaji tanko ya ce cikin damuwa"Allah ya sawake to duk abinda kike buk'ata ki fad'a mun sai na kawo Miki"zaliha ta ce "to shikenan Alhaji na nagode sosai"Alhaji tanko yay murmushi ya ce"Amma wannan zazzabi yau yamin cikas yau kenan baxan samu abinda nake so ba"zaliha ta ya Mutsa fuska ta ce" nidai sai anjima"daga haka ta kashe wayar.....


Baaba asabe ta shigo d'akin tana kallan zaliha ta ce"Alin yazo zaliha"ya fita ma da abincin me za'a ce masa , zaliha ta ce "kice masa idan ya je ya bawa sailuba ai yasan ta wacce muke zama waje D'aya da ita,zan ma K'irata yanzu na fad'a mata" baba asabe ta ce "toh shikenan" daga haka ta fita daga d'akin, zaliha ta lalumo number sailuba sai da tai mata miss call biyu sannan tai picking, hayaniyar Jama'a tai ta Ji,alamun tana tashar kenan, sailuba ta d'aga tace "zaliha"zaliha ta D'an d'ago daga kwancen da take ta ce "na'am sailuba"sailuba ta ce "naji muryarki haka ,ko bakida lpy ne? Zaliha ta ce "wlh Banda lpy sailuba"sailuba ta ce" Allah ya sawak'e,shiyasa kenan bakixo ba "zaliha tana ya Mutsa fuska ta ce "eh"Dan Allah sailuba Ali me napep D'ina zaixo da abincin , Alhaji tanko zaixo zai Baki kud'in abincin na fad'a masa Dan Allah sai ki bawa mutanan da nake bawa abincin"sailuba ta ce "to shikenan Babu komai sai yazo "zaliha ta ce kud'in Kuma da yamma zan Aiko a karb'a min"sailuba ta ce "Babu komai Allah Ya kaimu"zaliha ta ce "Ameen nagode"daga haka sukai sallama,tana sauke wayar Wani amai ya taso mata take ta mik'e ta sauka daga kan gadon da gudu ta fito tsakar gidan,tana kwara ra amai , Malam Auwalu Daya fito daga d'akinsa Yana kallan zaliha yadda take ta kwarara amai ya d'auke kansa daga kallanta yay hanyar waje, Baba asabe ta taso da sauri taiyo kan ta tana ta faman Yi mata sannu , ganin Malam Auwalu yay hanyar waje ga Yana kallan zaliha tana wannan aman Amma ko yay magana bare ya tambayi me yake damun zaliha,yasa Baba asabe ta ce cikin d'aga murya da malam Auwalu ya ji ta "yanzu fi sa bilillahi malam kana kallan zaliha Bata da lpy Amma shine zaka tsallake kayi tafiyar ka?.....



Malam Auwalu Kamar Bazai juyo ba sai Kuma ya juyo Yana kallan Baba asabe Yana mamakin k'arfin hali Irin nata ya ce "oh sai Yanxu kika San Ina da amfani asabe?ai kince Karna K'ara shiga sabgar ki a gidan nan keda 'yarki,Koba haka akaiba ? Baba asabe tai shiru tana kallan sa ,ya cigaba Ya ce "shiyasa na zuba miki ido Ina kallon ku, keda ita Kuma shine yanxu zakice Wani nan Ina kallo Bata da lpy to me kike so nace asabe ?Baba asabe ta ce cikin b'acin Rai"Amma ai 'yar kace malam , Kuma hannun ka ai baya tab'a ribewa kace zaka yanke kayar"Malam Auwalu ya ce "sai Yanxu kikasan da haka?baba asabe ta ce "wlh malam abinda kake min Agidan nan sai Allah ya Saka min dagani har 'ya'ya na" kamai damu kamar wasu bare Agidan nan, maimuna itace mata awajen ka,ni Kuma ko oho 'ya'yan tama sune 'ya'ya Amma Banda nawa,yanzu kace wannan adalci ne?ta fad'a tana girgixa,malam Auwalu ya ce "ke har kina da bakin da zaki Fad'i haka asabe?baba asabe ta ce "k'warai kuwa ai tun ba yau kake nuna banbanci tsakaninmu ba"malam Auwalu ya tsaya yana kallanta da mamaki ganin xata Bata masa Rai yasa ya girgixa kai ya fice ya bar mata gidan,baba asabe ta dinga ban bami kamar zata Ari Baki ,ta mik'ar da zaliha bayan ta gama aman ,ta zari hijab d'inta suka fita zata kai ta chemist Dake nan unguwar su , ummah tana d'aki ita da Ameenah tana jinsu , Amma Bata tanka mata ba ,Dan ita yanzu taiwa asabe uxuri abinda ke damunta ma ya isheta,tai mamakin yadda zaliha tai Wani Irin fari kwana biyun nan , Amma Batai magana ba ,kawai ta kawo Ido ne ta zuba musu......


Da daddare jikin zaliha yay week sosai ga aman da take ta xubawa kamar Me ,ga batacin abinci ga tashin zuciya da take Yi ,ga batason taji kamshin miyar kuka sai amai,yanzu haka ta fito da gudu Jin kamshin miyar kukan, Dan su lawisa ne suke cin tuwo a falon nasu, tana uwar d'akan Amma tun daga nan ta juyo kamshin miyar shine ta fito da gudu xuwa tsakar gidan tana ta kwarara amai.malam Auwalu Yana d'akinsa Yana jinsu , Amma Bai nuna ma yaji ba,ummah ta kai masa abincinsa Dan yau itace da girki ,ganin Bai ko nuna ya damu ba yasa ummah ta dubi malam Auwalu cikin ladabi ta ce " malam Bai kamata kadinga watsi da yaran nan haka ba, ai baxa ka biye halin asabe ba tunda kasan halinta , tunda har kai hakurin zama da ita na shekaru Bai kamata Kuma yanzu da girma yaxo ba ka kasa hakuri da ita ba" Malam Auwalu ya ce " hmm maimuna kenan ,wai ba kina ji Ranar abinda ta fad'a min akan 'ya'yan taba "wai kar na Kara shiga sabgar su akan duk abinda suke ba"shiyasa na kawo Ido na xuba mata ai akwai ranar k'in dillanci" ummah ta ce "naji" Amma malam hakuri xakayi tunda wannan ai Rashin lpy ne ,Dan Allah kaje ka tambayeta me yake damun zaliha ai idan kai haka zataji Dad'i akan baka kula suba"malam Auwalu ya ce "maimuna baxani ba ,so nake na nunawa asabe cewa ni nake auran ta ba ita take AURENAH ba, ummah ta girgixa kai ta ce"naji malam" Amma Dan Allah kamin wannan Alfarmar "Dak'yar Dak'yar ummah ta shawo kan malam Auwalu ya yarda zai je,badan yaso ba ya fito daga d'akin nasa ,ya Tarar da zaliha sai amai take kamar me, malam Auwalu ya qarasa har Inda suke yana kallan zaliha ya ce "zaliha" zaliha kasa dagowa tai sbd yadda cikin yake juya mata, malam Auwalu ya Kalli baba asabe Dake Wani girgixa tana had'e Rai kamar Bata ganshi ba ya ce " kishiryata ku fito mu kaita asibiti daga haka ya bar wajen ya koma d'akinsa......



Baba asabe ta ce "toh", sannan ta bishi da harara,jiki a Sanyaye ta kama zaliha wacce Bata iya tsayuwa da kanta sbd yadda ta galabaita suka wuce d'akinta,ta shirya zaliha tsaf, itama ta Sako hijab d'inta suka fito daga d'akin, su mardiya suna yiwa zaliha Allah ya sawake,bayan Baba asabe sun fito tsakar gidan ta tsaya tana jiran malam Auwalu, babu dad'ewa ya fito daga d'akin sa , ummah na biye dashi,ya ce "muje" Baba asabe tai gaba har lokacin zaliha tana jikinta , ummah ta ce "sannu Zaliha Allah ya sawake"Baba asabe ta juyo ta Maka mata wata muguwar Harara sannan tai gaba, itadai ummah batace komai ba ta girgixa kai tana mamakin asabe da Halin wato matar nan baxata taba saiyawa ba,ta sauke numfashi tai shigewar ta falon ta,bayan sunje bakin titi malam Auwalu ya tare musu napep suka shiga sannan suka nufi wani private hospital mai D'an saukin kud'i Dake nan kusa da unguwar ta su.....



Sunje asibitin, yanzu haka suna cikin OPD zaune a gaban wata nurse,bayan nurse d'in ta tambayi zaliha abunda ke damunta zaliha ta fad'a mata da k'yar, nurse d'in tai rubuce rubucen ta , sannan ta kalli zaliha Dake jikin Baba tana sauke numfashin wahala,ta ce"kina da AURENE baba asabe tai saurin cewa a'a Bata da aure,nurse d'in ta Maida dubanta kan takardar gabanta, sannan ta yagi wata paper tai rubuce rubucen ta sannan ta Mik'awa baba asabe ta ce "kuje lap akwai gwajin da xa'a mata idan kun gama sai ku dawo nan" Babu musu baba asabe ta karb'i takar dar, sannan ta kamo zaliha suka fito daga d'akin, malam Auwalu Dake tsaye a gefe daga waje Yana jiransu,ganin sun fito yasa ya nufosu Yana tambayar baba asabe sun gamane? baaba asabe tana kallansa ta ce "sun turamu d'akin gwajine ,malam Auwalu ya ce "to muje" Bayan sunje aka karb'i takar dar,akace su su jira awaje, zaliha Kuma ta Shiga ciki,Babu musu su kayi hakan....


Bayan wasu mintuna zaliha ta fito daga cikin lap din suka zauna suna jiran Saka mako kamar yadda akace musu, ba'a haura mintuna 30 ba wata lap ta fito daga d'akin gwajin rik'e da takarda a hannun ta da murmushi a fuskarta ta qaraso har Inda su Baaba asabe ke zaune ta ce Zaliha Auwalu, zaliha ta d'aga kai tana kallon ta,baba asabe ta ce gamu "nurse d'in ta ce "congratulations Allah ya Raba lpy" ta qasara fad'a tana murmushi, baba asabe cikin d'aurewar kai ta ce "bangane ba dacta ? Kamar ya Allah ya Raba lpy? Nurse d'in ta ce "eh mana cikine da ita harna tsawan wata uku da kwana ki"ta fad'a tana Mik'a musu takardar, malam Auwalu ne ya karb'i takardar Yana dubawa, Baba asabe Dake zare ido waje tabi takardar da malam Auwalu ya karb'a da kallo gaban ta na fad'uwa,sai Kuma ta kalli zaliha wacce itama sobada firgici ta mik'e daga xaunan da take sai gata Dan gwar gwar akan kafafuwanta, tana kallan lap d'in ta ce "ciki kuma likita? wlh nidai bani da Komai"ta fad'a tana kallan Baba asabe jikinta na rawa, Baba asabe ta kalli zaliha kafin ta kalli likitar ta ce "malama kodai Kun manta Saka makon Wani kuka bamu ,ita fa wannan yarinya ce Bata tab'a aure ba" nurse d'in tana girgixa kai ta ce cikin Rashin fahimta "a'a ya Muda aikinmu Amma kice wai results d'in wata Muka Bata ,natane Baga sunan ta nan akai ba" ta fad'a tana nuna takar dar Dake hannun malam Auwalu....



Baba asabe ta fashe da Kuka ta ce "wlh k'arya ne, zaliha Bata da cikin Komai, malam Auwalu da sai Alokacin ya d'ago da kansa daga kallan ta kardar da yake baya ko kiftawa, Dan shi tsabagen shock d'in daya shigane yasa Yama kasa magana Amma da za'a Bude xuciyar sa wlh tafi ma ta baba asabe shiga Damuwa da k'unci, ya kalli lap d'in ya ce "kije likita ai baxa kiyi qarya ba, babu komai mangode" nurse d'in ta juya ta tafi tana wai gensu da mamakinsu , Malam Auwalu ya juya ya dakawa Baba asabe tsawa Dake kuka tana rantsuwar karya akeyiwa zaliha Bata da ciki,Ida nuwansa sun kad'a sunyi jajur ya ce "suda aikinsu ne, Amma kice wai qarya suke asabe?zasu miki k'arya ne? aikema kinsan wasa kike baza su tab'a mata qarya ba, na tabbata kema kinsan zaliha tana da ciki sbd duk Mai hankali ya kalleta zai san da Hakan" ya qarasa fada cikin b'acin Rai,sai alokacin Baba asabe ta juya tana kallan zaliha yadda tai fari fat da ita, take ta gas gata xancen malam Auwalu ta kalli zaliha Dake rera kuka ta ce "waya miki wannan cikin zaliha? Ta fad'a tana ta shako ta, zaliha taki magana sai kuka ,baba asabe ta ce "wlh malam xubar da cikin nan xa'a Yi "malam Auwalu yay mata wani kallo ya ce "wlh Baki isa ba, yadda kika sa taiyo cikin nan wlh saita haife cikin nan Kinga jikanki, tunda duk waya jawo idan ba keba,ko kin d'auka duk abinda kuke bansani ba,duk Wani motsin zaliha babu Wanda bansani ba,dama jiran Irin wannan ranar nake sai gashi tazo cikin sauk'i, lokacin da nake hana zaliha shiga motar saurayi me kika cemin naga k'arya tani kukai daga ke har ita,ai dama na fad'a miki bazan qara shiga harkar 'ya'yan kiba duk abinda xasuyi sbd ke da bakinki kika Fad'i haka"meye abun Damuwa naga har kayan kwad'ayi ake kawo muku kushige d'aki kucinye ke da 'ya'yanki ko kin d'auka duk ban sani bane ,to ga Saka makon kwad'ayin Kunan , aidama duk Wanda ya hau motar kwad'ayi zai sauka a tashar wulak'anci" malam Auwalu ya fad'a kamar zai saka ihu Dan wlh yafi Baba asabe shiga tashin hankali,ta ita ko baba asabe kuka tasa ta ce "wlh ni ban Fad'i haka ba,Kuma wlh sai anzubar da cikin nan wato so kake mak'iya suyi mana dariya koh?, malam Auwalu ya ce cikin b'acin Rai "wlh asabe Baki isa axubar ba dole sai zaliha ta haife cikin nan Kinga abinda kika shuka" Kuma Kuma wlh idan kika xubar ko bansani ba wlh abakin AURANKI ,ya Kalli zaliha Dake kuka ya ce"kema idan kika bari aka xubar da cikin nan wlh sai na tsine miki albarka ,sannan na koreki daga gidana"daga ya daka musu wata tsawar da saida suka tsorata ya ce" ku wuce mu tafi" baba asabe tana ji tana Gani malam Auwalu ya sakosu agaba ya ce su tafi gida, Baba asabe a zuciyarta kuwa ta kudiri aniyar wlh sai an xubar da cikin nan,ko malam Auwalu Bai sani ba,zaliha ko sai kuka take , kamar ranta zai fita Dan wlh Bata d'auka ciki zai shiga ba,ba Kuma cikin kowa bane itadai tasan na Alhaji tanko ne,tunda shi kad'ai take kulawa,Baba asabe ta Daka mata tsawa tana zagin zaliha ta ce "Kuma koki fad'i Wanda yay miki cikin nan ko Kuma na yanka ki"zaliha ta qara sautin Kukan ta,shidai malam Auwalu Yana jinsu wlh ji yake kamar xuciyar sa zatai bindi ga Dan duk wannan abun da yake dauriya kawai yake Amma ya fisu shiga tashin hankali, cikin shege agidan sa innalillahi wainna ilaihi raji'un haka yay ta Mai Mai tawa......




____________?&



Da daddare AA Arab Yana falonsa a Kwance ,wajen k'arfe goma da Rabi na dare,Dan gabad'aya agajiye yake , yau da wuri ya dawo daga office,ya lumshe idonsa Amma ba bacci yake ba,take aikin da zaiyi ya fad'o masa a ransa, Hakan yasa ya mik'e daga kwancen da yake xuwa bedroom d'insa,ya dauk'o laptop dinshi ya zauna gefenta gadon sa Yana dubawa, ya shiga email d'insa Yana Neman aikin da Yabawa ruky d'azu a office,Dan ya ce "ta tura masa" ya shiga yaga ko ruky ta tura masa da abinda ya ce ta tura masan ,saidai Bai Gani ba sannan Bata turo masa ba,take ransa ya B'aci lallai yarinyar nan ta Raina masa hankali,ya mik'e a fusace ya koma falor ya d'auko wayarsa ya lallumo contact d'in ta yay darling, Yana Jin yadda take ringing Amma Batai picking ba,sai da yay mata miss call 2 ana uku yaji wata kasa lalliyar murya tai magana.ruky Dake ta bacci tun wajen k'arfe 9 na dare ta kwanta sbd yau gabadaya ma agajiye take,tun da ta dawo gida tai aikin da AA Arab ya Bata ta ,taji tayi mugun gajiya,Hakan yasa tanayin sallan isha'i ta kwanta ,taji wayarta na ta vibrate Dake a gefenta saman kanta ta ajiye shiyasa taji ta, ta lalumo ta cikin yanayin barci batama duba Mai K'iran ba tai picking ta kai kunne da wata kasa lallali yar murya tai sallama,AA Arab Dake jinta , yaji Wani Abu ya soki Xuciyar sa , Amma sai yay saurin kawarwa cikin husky voice dinsa ya ce "ke"take ruky ta tashi daga kwancen da take tana murza idon ta Jin muryar Wanda ta Doki kunnenta ,kafin tai Wani yunk'uri taji muryar sa ta qara dukan Dodon kunnenta ya ce "Mai yasa Baki turamin abinda nace kituromin ba dazu? ruky ta shagwab'e Baki kamar Yana gabanta cikin wata iriyar murya wacce bacci Bai gama sakin taba ta ce "sir mantawa nai Amma nayi tun dayzu Dana dawo gida" Yana danne abinda yakeji akan yadda take masa magana ya ce "ok"raini ne yasa Baki turamin alokacin da kika gama ba? Ruky ta saki Wani numfashin da yasa AA Arab d'auke wayar daga kunnansa,sbd Irin abunda yaji,yafi 30 seconds Bai iya Gane Wani yanayi yake cikiba,sai ji yay da muryar dake Kashe masa jiki tana "hello,hello sir baka jine?cikin dauriya AA Arab ya Maida wayar kunne yace"ok kituromin yanxu "ruky ta ce naface kayi hakuri"AA Arab ya runtse ido ya ce"ok,alright naji kituromin yanxu"ruky ta ce sir bacci fa nake" AA Arab ya runtse ido yana Jin zata


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login