Showing 48001 words to 51000 words out of 278032 words

Chapter 17 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1090

da cewa bana ciyar Dake, Ameenah ta sunkuyar da kanta qasa,yace kidoramin rawan xafi xanyi wanka tace to haka ta dauki kwanan da kofin shayin ta fita daga dakin , Kabiru Kuma ya haye gado Yana jiran ruwan yay xafi yafita yay wanka ,...


Haka Ameenah ta fita ta Dora Mai ruwan xafi kamar yadda yace kafin ta koma ta zauna ta fara karyawa Kuma, kamar wata marainiya haka tai lamo da ita,babu dadewa Kabiru ya fito kallo Daya ya mata ya dauke kansa yay hanyar murhu bayan ya dauki bucket,ya juye ruwan xafin ya wuce toilet Ameenah ta bishi da kallo magan ganu fal ranta Amma babu damar magana, tana nan xaune ya fito daga wanka ya shige daki babu dadewa ya fito cikin shigarsa ta koyaushe wato kana nan kaya , Wandanma Wani crazy sai t _shirt baka ya dora wata hula akansa Irin Mai budewar nan,...


Sai ganinsa Ameenah tai yanxuma da jaka ya rataya a kafada,ya Kalleta yace xoki rufe gidan duk Wanda yaxo Nemana kice bana nan,haka ta taso ta nufosa tana Mai gyada masa kai shiko daga haka yasa kansa ya fice daga gidan, Ameenah ta koma ta fashe da Kukan da take ta rikewa, gabadaya duniyar ta mata zafi kwata kwata,ga Kabiru yaki bari taje gida da da dayake barinya duk bayan sati biyu taje gida Amma yanxu kwata kwata ma ya hanata xuwa,ga shi daga gidansuma babu Wanda ya qara xuwa tun xuwan da Nana tai,ta dauka ma umma xataxo tunda dukda da wuya ma taxo amma ganin Nana xai wuya vata fada mata cewa tai jinya ba yasa ta Saka kan kance da xuwan nasu Amma shiru kusan sati uku, gabadaya ta rame ta bushe tasa tunani kawai aranta, Allah Yana Gani ta tsani AURANNAN kamar yadda ta tsani Wanda ya ajetan, babban Damuwarta ma Bai wuce yadda yake tafiya ya bartaba,duk da ita da xaman nasa da rashinsa duk dayane tunda bawai yana mata Wani abune Wanda xai faranta mata ba, Amma Kuma xama da mutum a kusa Yana da Dadi Koba a komai xata dinga Jin motsinsa a kusa da ita,Amma kullum ita kadai take kwana kamar maiya,tun tana tsoron har ta Saba,wlh Wani lokacin ji take kamar ta gudu,saidai Kuma tana tsoron karfa a qara Irinta wancan lokacin da aka saceta ta fada hannun mugayen,badan hakaba wlh da ta tafi gida inyaso komai xa'ayi saidai ayi,sallamar saude ce ta dawo da ita daga tunani da take tana Mai goge hawayen ta tana kokarin saita kanta,....


_______?&


Ruky ce xaune office din DCP duk a tukure take,Dan tunda ya kirata wai taxo office dinsa gabadaya taji Wani ban barakwai,gashi Kuma ya sata a gava sai Wani shirme yake mata,da wani xancen da kwata kwata Bata sanshi ,ya kalleta a karo na babu adadi yace my bakiji me nace bane ta kirkiro murmushi asan ta daidai ta kanta tace naji sir ,ya Wani langwabar da kai yace haba my kullum sir babu Wani sunan soyayya daxa'a dinga Kirana dashi,Ina Jin Dadi Nima, ta Dake tace sir Wani iri kenan , yay murmushi yace nasan Kinsani kawai dai so ake a wahalar Dani ,ruky girgixa kai tace kokadan bansan Wani suna xan fada Maka ba, yace toni bari na xabi sunan itadai ruky ta sunkuyar da kanta Kasa, yace to ki Kirani da Beb mana,ai ruky Batasan lokacin data dago ta kalle shiba , lallai ma wannan qaton mutumin xatacewa Wani Beb tabdijan wayaga girma ya fadi wai raqumi da Shan ruwan akurki,....


DCP yace ni gashi na xaba ya qasara fada Yana murmushi itadai ruky batace komai ba,yace please say something mana ,ta daga masa kai ya Dan bude ido yace yayi ta daga masa kai yace thanks my please ki fara daga yanxu ,sai Yanxu tai magana tace tunda ka xava it's okay basainace komai ba,yay murmushi yace thanks hakanma,yace yauwa Dama maganan da nakeso muyi shine yau na tura wasu sajen unguwar tareda ASP anas, zasu xauna suyi monitoring gidan ,suga shin ana shiga Koko, zasuyi monitoring gidan sosai har Allah yasa agano waye ma mallakin gidan ,Ruky da harga Allah taji dadin Hakan da yay tace thanks sir ya wani Bata Rai Irin da wasa dinnan ,sai Kuma ta danyi murmushi tace nagode sosai b.... Bata qarasa ba yace ki karasa mana ta girgixa kai tana Mai mikewa tsaye shidai DCP Kallan ta kawai yake, Santa na masa illa axuciyarsa,ta gyara avagar jikinta tace let me go ,yace thanks my ,daga haka tai hanyar kofar fita,Dan wlh Sbd maganar Hanan da tai matace yasa kawai yanxunma ta Dan sakarwa DCP,Amma badan haka hmmm,baridai agama case din shafa,DCP ya bita da kallo har sannan ji yake Inama mafarkin dayake ya kasance wlh da saiyace yafi kowa SA'A arayuwa,danshi wlh Yana San soyayya over ,danshi wlh xai iya cewa yaji dadin wannan case din daya hadasu da ruky na shafa kova komai xai dinga samun ganinta indai ya bukaci Hakan ,Bai Fargaba har ruky ta bar office din, sai Kuma ya sauke ajiyar xuciya Yana Mai Maida hankali kan computer gabansa,.....


________?&

S MaiTama ya naga ka fito kana Wani kyabe Baki lpy, Wanda aka kira da s Mai Tama Yace inako lpy haba waya kawo mana wannan useless dog =?? din gabadaya babu Wani testing tattare dashi shiyasa ni nafi san,na turawa wlh Amma na nan Nigeria kwata kwata basuda Wani testing ya fada Yana Wani kyabe Baki tareda xama a kan kujera,saleem ya dafa kafadar s maitama,yace haba s MaiTama nidai wlh naji Dadinsa Kaine dai bakajiba,s MaiTama yay tsaki ya mike ya fara xura Wandansa da rigarsa yace wlh saleem ka batamin Rai gashi gabadaya a mike nake dole naje na Nemo yarinya Mai xafi Dan wlh saina sauke sha'awata baxan tava iya samun nutsuwa ba akan abinda nakeji dinnan , saleem ya rike haba yace s MaiTama yau Kaine xaka fita Neman yarinya bawai ta kawo kanta ba,s Maitama yay tsaki yace ba duk kaine ka jawo ba ,ya fice bayan ya dauki makullin motarsa,


Bayan tafiyar s MaiTama haka saleem ya mike ya shiga dakin da dog =?? din nan yake yaje ya afka masa,s MaiTama bai zarce ko Inaba sai Wani gidan Yan bariki Wanda anan ne xai samu Mata kala kala,Irin Wanda yakeso yay manage dasu ,Dan wlh saidai yay manage,baya tunanin zai samu Irin yarinyar Daya keso awurin,abinda yasa ma yasan wurin ya tava dauko saleem awurin,inda shi babu ruwansa kowama ya samu dauka kawai xaiyi,yay anfani da ita,ba ruwansa da zabe,Amma shi Ina ba ko wacce mace yake iya anfani da itaba, harsai yaga wacce ta masa,yana xuwa suna zazzaune sun bar barje a kofar gidan,yanayin parking ya leko ta window yagansu , gabadayansu sai suka fara gyaggyara xama ana babban kado wurare shiko s MaiTama gabadaya ma saiyaji Yana kyan kyaminsu,kwata kwata gashi gabadaya a mike yake ,ya matsu yajishi jikin abinda zai Lafa masa abinda yakeji ,Dan haka ya shiga baxa ido yaga wacce xai iya hada jiki da ita,Hakan yasa kowacce mace yin iya bakin kokarinta Dan yace ita svd indai sukaga mace ko namiji a area nan tasu to Sunsan abinda ya kawosu,Dan haka ya kira wata black beauty,ta nufosa cikin sauri ganin ita yake nufi,ganin ta nufeshi yasa sauran hararar ta suna maijin bakin ciki Dan Basu akace ba >?#?,Dan wlh wannan mutumin daga Gani akwai kudi,kodaga yanayin motar xakasan lallai kudi ya xauna,bare Kuma SHikansa din duk ba gabadayansa ya suka ganshi ba, iya kansa kawai suka iya hangowa, tana xuwa ta kwarkwasa glass din motar ya cire lock din ta shiga batareda wata tambaya ba ,kawai yay reverse suka wuce itama Bata Damu da tambayar tasava,Dan haka batai magana ba tunda ai Sunsan kan xancen tunda bayau suka Saba ba,s MaiTama daga nan Bai xarce ko Inaba sai gidansa,.....


________?&

Wai zaliha ya naji shiru ne yaufa kusan kwana uku kenan da xancen salisu Amma Banga Wani sauyi ba,kodai kin kuskure kan abinda na fada miki,baba asabe ta fada tana,kallan zaliha Dake linke kayanta, zaliha ta juyo ranta a bace tace babarmu wlh Inayi kingafa ko daxu Saida nabi ta shagonsu Yana ma xaune Amma wlh ko kallona Bai yiba har na shiga shagon na fito bama siyayyar xanyi ba,duk Dan ya kalleni Kuma ya kulani yasa na shiga Shagon nasai cingum,Amma wlh kamar Wanda yaga Kashi wlh babarmu Baikalleniba,....


Baba asabe tai tsaki tace Dan ubanki haka akeyiwa saurayi nace miki kidanga kwarkwasa kina karairaya Taya ZA'Ayi bakya haka zai san da mace a gun, zaliha tace wlh baba duk inayi ,baba asabe cikin harxuka tace dallan rufemin Baki wlh dole ki xage kisa salisu ya soki ko kinki ko kinso,ni bantaba Ganin yarinyar da akeso da arxiki ba kike kawaicewaba saike, Kuma wlh karya kike babu abinda kika aikata na abinda na fada miki,da kinayi wlh namiji ko jikin Dutse ne dashi wlh saiya motsa ballantana Kuma ke da surarki da komai dame Nanan tafiki idanba haskeba da Kuma wannan manyan idanuwan nasu na gado,...


To wlh kinji na fada miki koh ki tabbatar kinjawo hankalin salisu kanki, Nana tace naji baba, baba asabe saikuma ta sassauta ganin zaliha ta karbi xancen nata tace kokefa Mai kashin arxiki,yanxu Kuma tunda uwarta ta saki damarta muba saimu dama ba,ni wlh nasara dame yayan maimuna suka fiku da duk mazan da zasu sosu masu kudine kinafa ganin wancen saurayin Ameenah Wani Mai motaci ,yaxo Neman AURENTA,haka nashiga na fita Dan mardiya ta aureshi ,Amma fafur yaki Niko na hana auran ma gabadaya,saikuma ga wannan Dan albarkar Kabiru muka hadu dashi Aiko nace wlh saiya auri Ameenah Kuma shima Dake yaga farar fata Tuni ya karbi tayin danai masa,....


Zaliha tace wai babarmu dama kece kika hana Yaya Ameenah ta AURI shamsu,baba asabe tace hmmm zaliha kenan Baki sanni ba Ashe ,ai wlh tunda maimuna ta aure min miji wlh baxa ta tava samun kwanciyar hankali ba daga ita har yayanta tunda ta shiga gonata,to kema shiyasa nakeso ki dage har sai salisu ya dawo yace ke yakeso ta karasa fada tana mai murmushi, zaliha ma murmushin tai tace to babarmu in Sha Allah xanyi ,xanyi tunda kema dai so kike na auri Mai kudi kamar yadda Nima nake buri, baba asabe tace yauwa ko kefa gaki da bakinki irin Wanda akeso Mai sheki,tuni xakiji kin sace xuciyarsa,zaliha tai murmushi tana kallan futkarta jikin mudubin dakin ,Jin uwarta da kanta ma ta yabi bakinta, itada har take ganin wannan bakin nata yayi yawa,Amma tunda babarsu ta fada ta yadda,saikuma ta juyo ta dan Bata Rai tace babarmu wannan Alhajinfa shikuma ya xanyi dashi ,baba asabe tajawota kusa da ita ta qara kasa da murya tace shikuma wannan kawai ki bi dashi a zaki aureshi shikenan saimu dinga cin kudinsa,Dan wlh inasan wannan tsiran dayake kawo Miki da lemon kwalbar nan me kama da Zuma, karki koreshi kicigava da Kulashi,zaliha cikin farin ciki tace toh, tace to babarmu Kinga atasha har juyan abincina yakemin,gashi anjima ma yace xaixo,baba asabe ta kwalalo ido waje tace Allah zaliha,zaliha tai murmushi tace wlh , baba asabe tace lallai Mai kudine to svd haka karki Rabu dashi yanxu harsai kin kusa auran salisu zaliha tace to,baba asabe tace Allah yasa idan zaixo yaudin yaxo miki da leman kwalbar, zaliha tace ai kullum ne babarmu,baba asabe tace bari na kaiwa malam kunun nan,zaliha tace to ta cigaba da linke kayanta,baba asabe Kuma ta fice daga dakin ranta fes Dan ta dauki burin duniya ta dorawa zaliha tunda itace auta ,bugu da qarima tafiso ta AURI me kudi tunda kaf yayan ta dataso su auri me kudin Basu auraba Amma zaliha saita auri me kudi tunda ga salisu nan, ....


__A bangaren ummah kan ,duk abinda baba asabe take ciki itada da zaliha na bangaren Alhajinnan tasan dashi , maganar salisu cedai Bata sani ba,Dan haka xakiga idan Alhajin nan ya kawowa zaliha leman kwalba yogurt,gurasa,tsire da sauransu,haka xakiga idan da daddare ya kawo,baba asabe baxata tashi Shaba sai washe gari ,saitaga umma tana tsakar gidan Malam Auwalu ya fita sannan ta fito da gayya ma takeyi tana daga kwalbar leman tana saukewa daga bakinta bayan ta xuka tana Kuma kaiwa tsire bakinta tanayiwa umma habaaici,tanacewa yarta Mai farin jini, kullum sai ankawo musu kaza da kaza,su wacce Kuna akace Boko xa'ayi sai bokon ta kawo musu su Gani...



Ita ummah wlh abinma dariya yake bata meye Wani abin alfahari Dan danka ana bashi Abu awaje Yana karba Yana kawo Maka,tasan dayaya suke Bata abin, maimakon ta hanata Amma sai Wani alfahari take da Hakan wlh ita tausayi ma suke Bata daga ita har zaliha din,wlh tana tausayawa baba asabe akwai ranar kin dillanci bawai fata take musu ba,Amma wannan xamanin Daya tabar bare da samari basa Maka kyakkyawar kyauta svd Allah,saidan Wani Abu da suke bukata daga wajenka,bawai duka ba Amma wlh na garin kadan ne,Wanda xasu Maka kyauta sbd Allah,...


Ita yanxu damumarta Ameenah,Bata wuce yadda takesan taga yarta ba,tasan halin da take cikiba Amma gabadaya malam da Yaya sabi'u sun hanata,tayi Kuma duk yadda zatai ta samu yadda xataje gidan Ameenah Amma kwata kwata babu wata hanyar, Amma yanxu abinda xata fara kawai shine xata aiki Nana gidanne ta gano mata ita,tasan halin da take ciki,Dan ita harga Allah haryau Bata gamsu da auran Ameenah da wannan yaran ba,duk da ita bawai ta qare masa kallo bane har yau Amma daga Jin muryarsama tasan cewa ba nagari bane, har yau tana Jin ciwon yadda aka aurawa Kabiru Ameenah,ga yaran dayaxo har gida Dan mutunci Yana Santa Amma kwata kwata abin ya wargaje,ta rasa Tayaya,Abu Daya ta sani shine wai adole sai an hada auransu da mardiya Dan dai kawai suna sa'anni shikuma malam ya hau kai ya zauna,wlh anyi na farko anyi na karshe akan Nana kan wlh Basu isaba,itama na Ameenah Dan dai kawai lokacin Batasan haka abin xai kasance ba,Amma ko yanxu tana kan bakarta,babu Wanda ya isa ya mata dole,Kiran sallah ne yasata mikewa Dan taje tayi,.....





07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD



*____JAMI'AR TSARO ____*


*____THE WOMEN POLICE ____*


*NA*


*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ____*



*____(MRS SARAKIES)____*


*QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION (QUWA) =?1?*



*Bismillahirrahmanirrahim*


_____season one ep 2?? 2??



_______?&

Hello jabir wai har yau babu Wani motsin ne ,naji shiru har Yanxu babu Wani lvr DCP ya fada yana waya da police din daya aika hayin rigasa Dan suyi monitoring gidan da akai raping din shafa, daga Daya bangaren jabir yace Ranka ya Dade yanxu fa mukaga wata mota tai parking a kofar gidan ,so naga dai mutumin Bai shiga gidanba gate din yaje zai Bude ya shiga sai ya duba aljihunsa zai dauko key din gidan da alama baiga mokullin gidanba, sai kawai mukaga ya juya ya koma mota,sai ya bar wajen,DCP ya Dan Mike daga kishingidan dayake yace kana nufin anxo gidan ,sajen jabir yace yes sir, DCP yace kunbi mutumin,jabir yace a'a, cikin bacin Rai yace meyasa baku bishiva ba, kunga Ina xashi Daya fasa shiga gidan nasa,....


Jabir cikin girmamawa yace sir wlh mu bamuyi tunanin haka ba,DCP yay tsaki yace Kun Gane fuskarsa, jabir yace a'a ranka ya Dade ya juya mana bayane bamuga fuskar Saba,Kuma glass din motar ma tinted windows ne, DCP yay tsaki yace jabir abinda nakeso da kai shine ku tsaya ku Kula kuyi aikinnan yadda ya kamata tunda har yaxo yau na tabbatar zai sake dawowa nan Bada dadewa ba ,sbd haka ku tsaya kusa ido sosai,Kuna ganin an shiga gidan ku Kirani,jabir yace in Sha Allah sir ,daga haka DCP ya yanke wayar Yana fatan komai yaxo karshe,....


________?&


Ruky ce tsaye tareda da Khalil bayan sun fito daga office din doc Fatima ,ta musu bayanin komai,na yadda results din kasance idan ya fito ,tace Khalil Allah yasa results din nan ya fito kamar yadda muke fata Khalil ya gyara tsayuwarsa yace Ameen ranki dade, yace har yanxu babu Wani motsin daga bangaren su DCP,ruky ta yamutsa fuska tace yace dai ya aika police suyi monitoring gidan Amma haryanxu banajin Wani bayani daga gunshiba,nifa gabadaya ma yanxu sai naji dama ban bashi case dinba, Khalil da tunda ta fara magana yake kallanta Yana sauraran ta yace ki kwantar da hankalinki, ranki dade kinsan Irin wannan case din dole sai ana binsa a hankali in Sha Allah xamuyi nasara ruky ta dago da kanta ta kalleshi tai murmushi tace Allah yasa,inasan wannan kwarin gwaiwar da kake bani, Khalil yay murmushi yace Nima haka ranki dade,....

Sai Kuma can yace meyasa haryanxu baki fadawa DCP cewa Nima nasan da case dinba, ruky tace inada dalili,yay murmushi yace shikenan tunda kina da Dalili na fahimceki, yanxu fa yau saura one week results dinnan ya fito koh Ruky ta gyada masa kai yace Allah yasa Muji alkhairi ruky ta ce Ameen ,daga nan suka cigaba da hira kafin daga bisani su wuce dakin da shafa ke kwance,.....


________?&


CP ne xaune a office dinsa sai DCP Dake xaune shima kan kujeran Dake passing din ta DCP,Yana kallan wata tagarda ,bayan ya karanta ya ajiye ya dauki tab din Dak??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????e gaban CP, yana karanta sakon Dake ciki again Wanda IG ya sake turowa,bayan ya karanta ya ajiye,ya Kalli CP Wanda ke kallansa yace tofa Aliyu Ahmad Arab Kuma,CP ya jinjina kai , DCP yace ya akai Kuma komai ya canxa daga yadda aka tsara ,CP yace Nima haka na gani bayan anturo da sakon,wai idan sukai Hakan xaisa kamar xa'a ga su sun gazane,Kuma abin kunyane ace sai wasu yan wata qasa sunxo sun yakar musu Yan ta'adda a qasa ,wai mu me mukeyi,Kuma Muda muke da jami'i jajirtacce,akawo shimana Aiko xai iya dasu ,inji minister tsaro ,bayan sunyi xama na musamman tsakanin shugaban kasa da Kuma Minister tsaro da Kuma IG na qasa da sauran masu ruwa da tsaki da akan harkar tsaro ,....


DCP yace yanxu dai anbar xancen kawo wasu daga wata kasar kenan,CP yace gashi dai a rubuce ,yace wai Aliyu Ahmad Arab dai na nan jihar Kaduna shine dai xai dawo daga labanin din ,waidama Yana nan , CP yace kasan Aliyu Ahmad hatsabibin mutum ne , Yanxu dai Aiki ya kamashi,xai dawo kasar sa,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login