Showing 189001 words to 192000 words out of 278032 words

Chapter 64 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1035

care idan ma saurayin naki ne, Amma ki sani bazan tab'a bari Kuna soyayyar ku acikin headquarter din nan ba ,idan ma soyayya zakuyi saiki bari idan kin koma gida ya dinga xuwa can Amma ba'a nan ba domin amanarki aka bani"ruky dai ta juyar da kanta gefe tana jinsa ya ce "and lastly karki sake ki K'ara min kuka zan shiga ciki aiki nake Mai muhimmanci" daga haka yay wuce warsa ciki, ya bar ruky ta binsa da harara..bayan shigarsa ciki ciga da Kukan ta tai duk atunanninta idan ta cigaba da Kukan ai zai barta ta koma office dinsu, Amma taji shiru.bayan kusan mintuna goma AA Arab Yana ciki Yana aikinsa dafe kansa yay Jin ta cigaba kukan nata na Rashin mutunci idan ya fahimci ceta so take ta ta kura masa da Kukan Dan taji ya ce bayason kukun, Dan ya ce ta koma office d'inta koh? Take ya mik'e ya Bud'e k'ofar office d'in ya lek'o Yana kallan yadda take ta kuka bil hakk'i da gsky.AA Arab ya ce "ke" Ruky tai banxa ta kyaleshi, ya K'ara K'iranta nan ma ta k'yaleshi,cikin tsawa ya ce" ba magana nake miki ba" ruky ta d'ago da jajayen idanuwanta tana kallan sa, ya ce "wato ni kin rainani koh? ban isa na hanaki Abu ki hanu ba koh? Ruky ta kau da kanta tana tura Baki gaba, ya ce "wlh idan na K'ara Jin muryarki Koda wasa wlh saikin Gane kuranki ,ya ce"silly gurl kawai" daga haka ya koma office din Babu jimawa ya fito ya dire mata wasu File masu bala'in yawa a gabanta ya kalleta ya ce "naga alamar Baki da aikin yine yasa har kika samu damar yin kuka ga wannan files din ki ware min na wannan month din Bai jira cewar ta ba yay shigewar sa office dinsa ya Banko kofar,ruky ihu ne kawai Bata Saba sbd abinda AA Arab yay mata, yanafa kallo itama wasu aikin ne agabanta Amma shine Dan Rashin tausayi irin nasa da San ya musguna mata shine ya kawo mata wannan uban file din ,ya barta ma mana da abinda yay mata ai ya isheta, Amma shine zai lodo mata wannan uban file d'in, a fusace ta ture files din Daya ajiye mata a gabanta tai gefe dasu,ta jawo laptop d'inta ta fara itama nata aikin azuciyarta ta ce "yadda ka kawo su Haka zaka zo ka d'auke su ta cigaba da aikin ta_tanayi tana K'un K'uni......



Haka ruky tana ji tana Gani ta dawo office din AA Arab da zama karfi da yaji,ga yay ta takura Mata da yaga Bata aikin komai saiya d'auko takar du ya ce tai masa copied ko Kuma ya kawo mata files ya ce ta shigar masa dasu computers Bada damar yin musu yanxu zai hau mata fad'a da cewa ta raina shi ko Kuma ya ce "so take ta koma office d'inta DCP ya cigaba da zuwa gunta,to wlh garama ta saki jikinta Dan tadawo kenen".idan ya fadi wannan maganar ji take kamar ya soka mata mashi a K'irji haka take ji sbd yadda take Jin xafin maganar.yau ma Kamar kullum tana zaune bayan ta gama aikinta tana murna yau dai Bai Bata aiki ba,wajen karfe uku na Rana waya suke da Hanan wacce ke ce mata "Amma sis kina Jin Dad'in zama office din ya Ahmad koh? Ruky yya yamutsa fuska ta ce "wani Dad'i Kuma?Abi a takura Maka da aiki bayan aikin Dake kanka sai an qaro Maka Wani ki Rasa shi me yake da baxai Yi aikin saba, sai dai kiga ya tattaro min har nasa aikin ya ce nayi bayan na gama nawa Dan rashin tausayi ,Hanan ta k'yalk'yale da Dariya ta ce "Yo ai maganin ki Kenan da ai bakya yin aikin kamar haka" ruky ta ce "wlh karya kike Dan ba tare muke Dake ba nr shiyasa zakice haka,ke nifa wlh idan naga za'a cigaba da takuramin wlh Babu dole saina bar aikin ma gabadaya wannan Wani Irin xalincine" Hanan ta rufe Baki tana dariya ta ce "ya Ahmad dinne azzalumi? Ruky ta ce "idan muguba mene shi da baya Jin tausayina,shifa baya komai sai ya tattaro min har nasa aikin ya ce "wai nai Masa" Hanan ta qasa sakin dariya ta ce " wai kina Ina kike wannan maganar Babu control haka? ruky ta ce Ina mana inda ya ajiye ni "Hanan ta ce "yanzu idan yaji kifa kina ce masa mugu? ruky ta ce "to yaji mana idan yaji sai me ba shine yake abinda za'a kirashi da mugun ba, bayan aikin da nake Sha saiya hada min da nashi inba mugun taba"......



AA Arab daya fito daga office dinsa tun dazu Yana jinta ya jin gina da kofar ya harde hannuwansa a kirjinsa Yana kallan yadda take ce masa mugu azzalumi jin jina kai kawai yake axuciyarsa ya ce "lallai wannan yarinyar wlh tayi mugun Raina shi yanxu har mugu take ce masa
,to da wama take waya ttukunna? da har take Bada labarin shi, take cewa shi mugune? ruky ta ce "hello bakya ji nane"daga Daya bangaren Hanan ta ce "aini kinfi k'arfina tunda ya Ahmad kike cewa mugu Allah yasa Kuma ya jiki" Ruky tai dariya ta ce"to idanma ya jinin sai me, me zaimin wlh ko agaban nasa ne saina fada mugu ,idan ba zalinci ba Yay ta bani wahala wlh nikan na gaji idan ya qara kawomin Wani aikin wlh sai dai yazo ya taddasu a inda ya ajiye Dan wlh Allah bazan yiba , duk mamah ce ta jazamin ,Kuma id...kasa qarasawa tai sbd juyawar datai Jin qamshin turaransa ido hudun da sukai dashi yasa take tai saurin kashe wayar tana Jin kamar ta nutse a wajen sbd kunya, shi dai AA kallan ta kawai yake Bai ce komai ba har tsawan Wani lokaci,ya sauke numfashi ya ce "nine mugun Kuma azzalumi koh?ita dai ruky tayi shiru kirjinta na bugawa da karfi ya ce "wa kike fad'awa cewa ni mugune? Ruky tai shiru kanta a qasa, yay kwafa ya ce "xanyi maganin kine yanxu" ya cigaba Ya ce "Kuma bari kawo Miki abinda kike cewar baza kiyi ba idan na kawo mikin ,Dan Allah Kuma karkiyi kinji" daga haka ya koma cikin office d'in, babu dadewa ya fito ya dire mata file d'in Daya dauko ya ajiye mata gabanta ya ce "idan Kinga dama karkiyi d'in kamar yadda kika fad'a,kiga yadda xanyi Dake"daga haka ya bar wurin ya koma cikin office dinsa.,ruky ta dafe kanta batabi ta kan wayarta da take ta vibrate ba Hanan ce me kira ganin ta kashe wayar,jiki asan yaye ta jawo ta files d'in ta fara dubawa.....



*Bayan kwana biyu*


Ya kasance yau saura kwana bakwai a koma shari'ar su Alhaji sunusi ayau Kuma ya kasance xa'ayi Shari'ar lateef da shafa ,kotu ta cika mak'il da mutane Dan saurarar wannan qara, Dan mutanan gari tun lokacin da akai rugun tsumin tonuwar asirin su Alhaji sunusi suka San abinda shima d'ansa ya aikata anan duk wasu abubuwan da lateef yake aikatawa a boye Wanda mutanan gari Basu sani ba ,suka fara fallasuwa anan suka San komai .zaman kotun k'arfe shadaya ne na safe Amma mutane da wurwuri suka fara xuwa kotun.AA Arab Yana office dinsa shidai Ruky ita tana first falor shi Kuma Yana cikin office din,tun kar fe Tara Saura suka shigo office din Amma ya riga ruky shigowa, k'arfe goma da Rabi ya fito first falor inda ruky take,ya tarar da ruky tana aiki a laptop ya qaraso ciki ya tsaya atsakiyar falon Yana kallan ta ,ruky ta d'ago Jin ana kallan ta,ta kalleshi batai magana ta d'auke kanta ta cigaba da aikinta.....



Yay gyaran murya kafin ya ce cikin qasa da murya "ki shirya yanxu driver zai kaiki UK hospital xaki biya ku dauki yarinyar nan da maman ta zaku wuce kotu right now,ruky ta kalleshi ta gyad'a masa kai Amma batace komai ba,daga haka taga ya fita daga office din ma agabadaya Ya Kara waya akunnansa alamar kira yake , ruky ta mik'e daga xaunan da take ta gyara xaman abayar jikinta ta dauki hand bag d'inta da wayarta ta nufi bakin kofar office din kicibis saukai Dan Saura kad'an su bangaji juna ruky tai baya da sauri tana sunkuyar da kanta kyasa,ya d'auke Kansa batareda ya kalleta ta ba ya ce "ki fito,ya fito da motar,ya fada Yana bata hanya ta wuce,tana fita ta tarar da motar abakin k'ofar office din nasa ,taga ashema motar sa ce , driver ya fito ya Bude mata back seat ta shiga AA Arab ya Kalli drivern ya ce "idan ka kaisu ka dawo Ina jiranka" driver ya ansa masa cikin girmamawa daga nan Ya Shiga yaja motar suka tafi, AA Arab ya koma cikin dinsa Yana jiran driver ya dawo ......



Ruky sun biya sun d'auko shafa wacce Alhamdulillah jiki Yana sauki babu laifi , saidai har yanxu tana k'ark'ashin kulawar likitocine Dan ba'a gama mata wasu treatment d'in ba , Amma babu laifi ana patan samun sauk'i da yardar Allah,doc Fatima itace agaban motar kusa da driver,ruky da baba lami da shafa suna bayan motar suka d'au hanyar kotun......



___________?&



A cikin kotu kuwa, kotu ta cika mak'il da mutane daban daban Wanda suka zo Dan halartar wannan shari'ar,Hajiya SA'A itama tazo ita da Samira da wata cousin sister din ta,fuskar nan ta_ta tayi jaga jaga da hawaye Dan har Wata rama tai sbd Damuwar da take ciki, tana tsaye ahabar kotun tana dakon jiran shigowar lateef tunda tasan daga prison za'a kawo shi , kota ganshi taji Dad'i aranta,Dan ko bacci Bata iya Yi sbd damuwa ,Babu dad'ewa kuwa motar ta shigo cikin Kotun take Hajiya SA'A ta xabura kamar xatai kan motar yayarta Samira da wata cousin sister dinta suka rirrik'eta Suna rarrashinta, Hajiya SA'A kuwa k'ok'arin kwacewa kawai take kamar wata Mai ciwon hauka ,har motar tai parking aka fito da lateef Wanda ya fita hayyacinta kamar ba Shiba, Hannunsa sanye da handcuff,ga gandurobas sun Sako shi agaba,sukai cikin kotun dashi , Hajiya SA'A ta k'ira sunansa da Wani Irin sauti, lateef ya juya Yana kallan ta saidai bai yi yin kurin xuwa ba ,suka tasa shi agaba sukai cikin kotun dashi, Hajiya SA'A ta kalli Samira cikin Kuka ta ce "Kinga yadda lateef d'ina ya koma koh samira? Kinga yadda suka maidamin da d'ana Samira,wayyo Allah na nashiga uku, wannan wacce Irin jarabawa ce ta sameni"ta fad'a tana kokarin k'wace daga rik'on da suka mata, Samira ta toshe mata Bakinta ta ce "ki daina fad'ar Irin wannan SA'A karkiyi sab'o, Hajiya SA'A ta k'wace bakin ta ta ce "bakisan Mai nake ji bane Samira baza ki Gane ba" cousin sister dinta ta ce "mun sani SA'A Amma idan rai ya b'aci hankali ai baya gushewa,kiyi hkr" Hajiya SA'A ta rufe fuskarta da tafukan Hannunta _ta dinga rusa kuka kamar me,sai Kuma ta fara tafiya cikin kotun suka rik'eta suka bi bayansu.....



Acikin kotun kuwa AA Arab suna zaune da ruky waje Daya Saidai su mazan suna gabansu,su kuma matan Suna bayan su ,da Shafa da baba lami sai doc Fatima wacce take matsayin Mai kula da shafa, barrister shamsu Yana cikin kotun Dan shine lauyan me qara , sai Wani barrister Wanda Hajiya SA'A ta dauke shi ne shine barristern Wanda ake karewa wato Lateef.duk Kansu sun tashi suna gabatarwa da kotu kansu, sannan aka fara Karanto qara,sai Kuma aka fara shari'a ,kowanni bangare ya gabatarwa da kotu hujjojinsa, barrister shamsu ya kawo manya manyan hujjojin da kotu xata yarda da abinda ya fad'a mata,kuma da dukan alamu kotu tana gamsuwa da abinda yake gabatar mata .ank'ira shafa da lateef suka tsaya a inda ake tsayawa anyiwa kowa tambaya Kuma duka sun bada Ansa, tambayar da aka yiwa lateef da cewa yasan shafa dagewa yay akan bai San taba,baima taba ganin taba, ba'a tilasta masa ba aka kyaleshi akan Hakan, aka cigaba da jero masa tambayoyi ,wasu ya amsa wasu Kuma yay shiru.anjima ana fafa tawa tsakanin barristers d'in nan guda biyu kowa ya fardadi hujjojinsa ,kafin daga karshe su AA Arab sukai nasara, alk'ali ya yankewa lateef hukuncin xaman gidan yari na tsawan shekaru 25 da tarar kudi Million 15 ,ai take hajiya SA'A ta mike ta saki Wani wawan ihu ,ta fita daga inda take zaune ta nufi gaban kotu , alkali ya ce ' ariketa afitar da ita waje ,take Samira tai saurin qarasowa wajen ta ta riketa ita da d'ayar , shi kansa lateef Wani Irin marayan Kuka ya saki Yana Dan Allah ayi masa Rai kar a kaishi prison ,ya Kalli shafa ya ce ki yafemin nasan ni na miki fyade Dan Allah kiyi hkr Babu Wanda ya Kulashi, Yana ji Yana Gani haka gandurobas d'in nan suka mik'ar dashi tsaye aka Bada damar kowa ya fita ,suka fitar dashi daga kotun, mutane suka fara fitowa daga cikin kotun ruky da baba lami da doc Fatima suka fito daga cikin kotun sukai wajen motar da suka zo da ita,suka tsaya ruky taji wayar ta Yana ringing ta d'auko tai picking ganin Hanan ce ,daga Daya bangaren Hanan ta ce "ya angama kuwa? Ruky tai murmushi ta ce "wlh yanxu muka fito" Hanan ta ce "ya kunyi nasara kuwa? Ruky ta ce "munyi wining Hanan"Hanan ta ce nayi missing wlh inama Ina nan akai wannan shari'ar nayi kallo gsky wannan gidan gomnatin wlh na gaji dashi gsky headquater xan dawo ace kusan kullum mu a tafiye tafiye muke" ruky tai dariya ta ce " wlh ni Kuma wlh da nice ke baxan tayba damuwa ba tunda inma tafiye tafiyen ne ai ba'a k'afa kuje yiba sai dai jirgi" Hanan ta ce "ke wlh ni arayuwa ta banason tafiya ko yaya take "ruky ta ce "aishikenan" Hanan ta ce "Ina xuwa xan k'iraki daga haka ta kashe wayar......



Bayan anfito da lateef haka hajiya SA'A ta tafi da gudu tai kansa xataje gunsa aka tareta Amma duk da haka Saida ta isa wajensa ta rungume shi ta hau Yin kuka kamar zatai hauka ,shima kansa lateef d'in kukan yake Yana cewa mommy ki rok'armin yarinyar ta yafemin, Hajiya SA'A tana kuka ta ce babu inda xaka muna tare lateef, lateef ya rungume ta Shima k'am_k'am da k'yar da k'yar aka Raba su suka ja lateef suka shigar dashi motar da k'yar Yana tirjewa Yana komai , Hajiya SA'A tana ji tana Gani aka tafi da lateef,su ruky suna tsaye abakin motar da suka xo har lokacin ,AA Arab Kuma Yana tare da barrister shamsu sai magana suke,ita duk ta k'agu ta bar kotun nan haka kawai taji Wani Irin tausayin Hajiya SA'A ya kamata lokaci D'aya sbd Babu mijin sannan babu D'an Shima ,suna tsaye AA Arab suka qaraso shida barrister shamsu, barrister shamsu suka gaisa da ruky sannan suka gaisa ma dasu baba lami wacce ke tai Masa godiya Yana ce Mata Babu komai ,AA Arab ya ce "Baaba xa'a kaiku awannan motar ya fada Yana nuna musu wata bakar mota dake can gefe, baba lami ta ce "to Babu komai yallab'ai mungode sosai Allah ya qara girma,AA Arab ya ansa mata da Ameen , ruky taiwa baba lami sallama itama nanma baba lami ta dinga Yi mata godiya kamar ta Ari Baki ,daga haka sukai sallama ya Kalli Ruky ya ce "muje" ruky tai gaba wajen motar da yake nuna mata wato motar sa wacce suka xo tare ta shiga back seat,tana jiransa kusan mintuna biyar taga baixo ba juyawar da xatayi ta hangoshi tare da doc Fatima suna magana adai lokacin da taga ya d'anyi murmushi kadan take taji Wani iri aranta,sai Kuma ta tuno da kalaman Hanan da take fad'a a kan doc Fatima akan Abinda take yiwa AA Arab yanxu ma abinda ta gani kenan, sai Yanxu ta tabbatar da abinda hanan take fad'a,ta tab'e Baki kawai ta kawar da kanta gefe harya shigo motar Bata yarda sun Hada ido ba.....



Driver yaja suka fara tafiya Haka motar nan tai shiru har sunyi nisa AA Arab Yana ansa waya jefi jefi,bayan Wani lokaci ya juyo ya Kalli Ruky jin kamar Babu ita acikin motar ganin yadda ta Wani had'e Rai tana kallan gefen hanya yasa yay shiru,kamar baxai magana ba sai Kuma yay qasa da murya yadda ita kad'ai zataji abinda yake cewa ya ce "ko dai Bakiji dad'in hukuncin da aka Yan ke masa bane? Ya fad'a Yana kallan ta,ruky ta juyo ta kalleshi ta ce "wa" ya ce "Saurayinki mana" naji Ance shima saurayin kine Kinga me yiwuwa bakiji dad'in hukuncin ake yanke masa ba"alhalin keda kanki kika shige gava wajen ganin Kinga an gurfanar dashi" ruky taji Wani Irin takaici ya rufe kamar ta saki Kuka haka takeji Aran ta taji itako me xatai wa AA Arab Wanda zata rama abinda yake mata?wai meyasa AA Arab yayi mugun Raina mata hankali ne,kodan ba laifinsa bane duk mamah ce ta bada ita,Batasan lokacin da ta juyo a fusace ta ce "idan ma saurayin nawane sai me, ai ba laifi bane Dan banji dadyin hukuncin da aka yanke masa ba, aiba wani abun bane Dan ka samu da Wanda ya damu da kai ba,kamar yadda kaima naga kana tare da taka budurwar har kana Yi mata murmushi ,akwai Wanda ya isa yace Dan me kake mata murmushi" ta fada tana tsayar da idon ta kan AA Arab Wanda ya zaro ido waje Yana kallan ta da mamaki ,ganin Irin kallon dayake mata yasa ruky ta juyar da kai tana tura Baki gaba, AA Arab ya jinjina kansa Yana tunanin maganarta me take nufi da Yaywa budurwasa murmushi shi Kuma, itako Ruky atunanninta rama WA tai koya k'yaleta ,taga alamar wannan kukan da take masa shiyasa yake mata duk abinda yaga dama,har sukaje office babu Wanda ya qara magana acikinsu.......






07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y





*____JAMI'AR TSARO ____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*____(MRS SARAKIES =؋?)=?1?____*



*('TAURARI


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login