Showing 108001 words to 111000 words out of 278032 words

Chapter 37 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1050

ka fadamin wanene kai, shin ku kuke Saka kanku kuke sace 'ya'yan mutane, idan kukaje Kuka kai musu hari, sannan baxa ku bar suba da ciwon dauke musu yara da kukeyi ba,sai Kun hada da kashesu ko kuma ji musu rauni,sbd Rashin imani Irin naku,ko Kuma sakaku akeyi idan sakun akeyi suwaye suke sakun,kodan bayanxu ya dace nai maka tambayar nan ba, first of all menene sunan ka,AA Arab ya fada Yana xuba masa ido, zailani yay shiru kansa harsannan aqasa,AA Arab yace cikin tsawa bana Mai maita mgn, zailani ya dago da kansa ganin babu wasa fuskar AA Arab yace sunana zailani shitu,AA Arab ya jinjina kai ,sai Kuma yace Ina sauran abokan ta addancin naka suke , sannan Ina kuka kai yaran da Kuka shiga kauyan kuka dauka, inaso ka fara bani ansan wannan tambayar kafin wasu tarun tambayoyin su biyu baya,. domin wannan sunake da bukatar sani...



Zailani yay shiru AA Arab yace cikin kakkausar murya bana magana Ina qara maimaita tawa,I Said where are the rest, zailani yace Nima bansan inda suke ba,AA Arab yace ok kana so kacemin kenan kai kadai kake wannan harkar kenan, zailani yay shiru AA Arab yace koka fadamin ko Kuma yanxu nasa ka fadamin ta karfin tsiya, naga alamar jikinka haryanxu baiyi laushi ba,zailani yace,Yana mgn Yana goggoce Baki Irin dai maganar rikakkun Yan iskan nan,yace ni iya gsky ta na fada Maka, AA Arab ya mike yace ok Banda lokacin batawa akanka,naga alamar baka shirya ansamun tamboyin nawa ba,bari idan jikinka ya fada Maka xaka fadi GSKYR abinda nake tambayar ka,daga haka ya fice daga dakin,wasu police ne su biyu suka shigo bayan AA Arab ya Basu umarnin yadda xasuyi dashi,....



Suna shiga babu ko digon imani Suma a tasu fuskar suka hau laftar xailani da kulke idan angama su sa masa wannan abun na shocking a hannunsa, suna Kuma tambayar sa ya shirya fadar GSKY,ko Bai shirya ba,Amma Dan karfin hali Irin na zailani yaki ansa musu saidai yay ta Basu hkr,haka Suma Basu hkr ba,laftarsa Kawai suke,bayan fitar AA Arab office ya wuce direct dan akwai ayyukan da xaiyi,Dan baxai Bata lokacinsa kan wannan jahilin ba, gara yasa Avi dashi ta hanyar da zai Fadi GSKY cikin sauki,....




?&Abangaren gidan mamah kuwa ,har yau babu Wani motsi ,na sanin inda Rukayya take, kullum Yan jaje xuwa suke, su mamah sun Bada kudi wajen bawa malaman addini Dan su tayasu da addu'a , da Kuma rokon Allah ,akan Allah ya bayyana Rukayya idan har tana raye idanko Bata raye Allah yasa su samu koda ganin gawarta ne sugani ko hankinsu ya kwanta,Dan gabadaya sun Kuma mikawa Allah lamuransu, sadaka tunda Rukayya ta Bata kullum acikin yinta suke,ayi girki abawa almajirai da mabukata,abin sadaka dai sunbada unguwa unguwa,gari gari, gabadaya yanxu mamah ta daina kukan fili ta koma na xuci,.Dan ta fawwalawa Allah komai duk abinda ya qaddara akan Rukayya Batada Wani iko akai,. ....



A bangaren Hanan kuwa yau tunda har kwana uku Babu labarin ruky Babu dalilinta, ta yanke hukuncin,zata fadawa AA Arab kawai tai in yaso ko bincikennema akan Alhaji sunusi ya kama sai ayi, yanxu haka ma, tana zaune a office dinsu na government house,Kiran doc Fatima ya shigo wayarta,tai picking,bayan sun gaisa doc Fatima cikin alhini ta shiga yiwa Hanan Jaje akan batan Rukayya da Kuma patan Allah ya bayyana ta,Hanan ta ansa mata cikin karfin hali, sannan doc Fatima tace ga baba lami dukta damu da cewa ita tana so ahadata Dake, Hanan tace ok abata wayar, daga haka doc Fatima ta Mikawa baba lami waya wacce ta fashewa Hanan da Kuka Tama kasa furta Komai, kukan ta kawai take bilhakki da gsky,Dan tunda taji lbrin Batan da ruky tai ta shiga Wani mummunan shock,Hanan gabadaya itama abun saiya dawo mata sabo,....



Baba lami ta kasa furta Komai har lokacin kuka kawai take Dan ita Bata saniba sai jiya da doc Fatima take mata Jaje anan taji,ananma tasan cewar ansace wai Rukayya Kuma bugu da qarima harda Khalil,baba lami jiya harda gudawa da qarin ruwa,Dan take awajen ta fadi tsabar yadda abun ya bugeta, shafa ma tayi kuka kamar ranta xai fita, shine fa sai daxu ta farfado shine ta Dage akan dan Allah Akira mata ko Hanan ne taji daga gareta ya ake ciki,....



Ganin baba lami ta kasa furta Komai sai sheshshekar kuka kawai da take ,yasa Cikin Kuka Hanan tace da baba lami Dan Allah tayi shiru Rukayya da Khalil in Sha Allah xa'a gansu ,baba lami tace cikin gunjin kukan dayaki tsaya mata tace jami'a indai akanmu ne aka dauke su jami'a da Dan jaridar wlh kuce musu ni munyafe mun hkr har agaban Allah mu mun hkr su sakesu,Hanan tana share hawayenta tana jinjina kai tace bamu san ko suwaye ba Amma in Sha Allah xasu fitoma,baba lami cikin Kuka tace wai haryanxu ba'a San inda suke ba,Hanan ta girgixa kai tace baba ki tayamu da addu'a kawai,....



Baba lami ta qara sautin Kukan ta tace innalillahi wainna ilaihi rajiun nashiga uku na lalace ni lami duk nina jawo inama Ban kai kukana gidan TV nan ba,Hanan tace baba karkice haka,haka Allah ya qaddara, babu yadda xamuyi addu'a itace magani baba lami ta qara sautin Kukan ta,Hanan ta kashe wayar ganin yadda baba lami kesan qara karya mata da xuciya, doc Fatima ta karbi wayarta tana qara bawa baba lami hkr Dan itama wlh ta tausaya musu matukar gaya,ta fita daga dakin tana Mai tausaya musu gabadaya,dama ta shigo duba baba lami ne,Hanan ta kifar da kanta kan table din gabanta ta fara xubar da hawaye tayi kusan mintuna 20 tana wannan kukun ganin lokacin tashi yayi yasata mikewa Dan tafiya Dan daganan heardquater xata Dan ta sanar da AA Arab komai akan abinda ta sani......




____________?&


Alhaji sunusi ne tsaye ke waya da CP Wanda ya tabbatar masa da cewa tabbas ankama xailani , Alhaji sunusi cikin tashin hankali yace Dan Allah ya taimaka masa da asaki xailani cikin sauri kafin ya tona musu asiri,CP yace, GSKy wannan maganar tafi qarfinsa, Alhaji sunusi yay Masa tayin makudan kudi masu tsoka CP yaji kudi , Irin kudin da Bai taba jiba take ya rude ,yace da Alhaji sunusi ya kwantar da hankalinsa xai kokarta, Alhaji sunusi yace idanma baxai Yiwu ba, akwai gubar da zai Bada akashe xailani da ita Dan kada ya tona musu asiri, batareda da kowa ya Gane kasheshi akayi ba,cikin rawar jiki CP yace shikenan duk yadda ake ciki xasuyi waya,alhaji sunusi sai Yanxu ya saki ajiyar xuciya sannan sukai sallama, sannan yay shiri shaf dan xuwa inda yasa aka kai su ruky,...




DCP kuwa dayaji lbrin Batan Ruky gabadaya rasa nutsuwarsa yayi,Dan xa'a iya cewa hardan shock ya samu,Dan Allah ya gani ba karamin kaunar Rukayya yake ba, bilhakki da gsky Dan wlh shi Dan aure yake mata,duk Wani binciken inda xa'a samu Rukayya dashi akeyi,har AA Arab Yana jinjina Irin kokarin sa akan aikinsa, Amma Allah ya Gani kullum da abin yake kwana yake tashi Dan shima har gida yaje yayiwa mamah jaje bisa jagorancin Hanan,Dan shi kullum patansa aga Rukayya,....



Alhaji sunusi ne tsaye adakin da ruky take ciki ,tana xaune baiwar Allah gabadaya ta fita hayyacinta kamar ba ruky ba yar gayu yar kwalisa yanxu gabadaya har Wani duhu tai,sbd tashin hankali da wahala,da damuwa,xancen wanka ko babu shi Dan da gsk Alhaji sunusi kesan cutar da ita,ya fara takowa xuwa gabanta yay kasa da murya yace ,kin amince da sharadin Dana ginda ya miki ko Kuma har yanxu kina kan bakarki, ruky ta kurawa waje Daya ido,Bata ko kiftawa, Alhaji sunusi ya qara Mai Mai ta mata tambayar daya mata,kamar baxatai magana ba saikuma ta fasa,ta juyo ta fuskanceshi , ta nisa tace Ina kan bakata baxan tava bin abinda kakeson nayiba,.....



Alhaji sunusi yay Wani Dan iskan murmushi ya goya hannunsa abayansa ya fara xagaye wurin Yana jinjina kai,saiki Kuma ya tsaya cak da abinda yake ya juyo ya fuskanci Ruky,yace bazaki ansa min abinda na umar cekiba koh, saikuma yace hmm wlh Rukayya har yau bakisan wanene niba shiyasa,da ace kinsan wanene ni da wlh baxa ki tsaya kina exchanging words daniba, Amma babu komai, naga alamar barinki da nai free bansa anfara gana miki axaba Dana tanadar miki bane shiyasa kike da taurin kai, Amma da sannu ni xan sauke miki shi,....



Ya cigaba Yace daga wurin waccan qaramin kwaran Dan jaridan can nake naga alamar duka ku biyun bakinku Daya, Shima naga taurin kai ne dashi kamar fir'auna,Kuma xan sauke masa , Amma naga alamar ya fara saduda Tunda gashi, nasa ana gana masa tasa axabar kala kala,naga alamar kema sai anbi Dake ta haka sannan xamu dai daita Dake,sbd haka kema yanxu xa'a fara gana miki taki kalar azavar daga haka ya juya zai fita , Ruky tace hmm wlh ba azababa yau ko kasheni xakai kana sawa ana dawowa dani wlh Ina kan bakata, baxan tava bin abinda kakeson nayiba,Alhaji sunusi ya juya yay murmushi sai Kuma yace wlh Rukayya saikin fadamin inda kika kai duk Wani evidence dinku,wlh Kuma Rukayya baxaki koma gida da Rankiba,kinji harna fada Miki, ni nan ni xan xama ajalinki Ruky tai murmushi Mai tafe da hawaye tace baxanyi mamaki ba tunda naga kai xuciyar ka kamar Dutse take sbd kekashewa harma tafi dutsi kekashewar, uncle sunusi wai Dan Allah menai makane, Mai muka tare Maka arayuwa,laifine danna kasancewata JAMI'AR TSARO, laifine dannayi aiki da doka xa'a hukunta Mai laifi ,kamar yadda doka ta tanadar,wlh uncle saidai ka kashenin dadai nai maka abunda kakeso din, tunda kai mugune azzalumi ne,Mai xuciyar fir'auna,ta karasa fada tana Mai rushewa da gunjin kuka,Alhaji sunusi ya juya a fusace yay kan ruky ya shako wuyanta Yana zare ido yace ni kike fadawa wannan bakaken magan ganun Dan Kinga Ina kyaleki to shikensn muxuba nida ke mugani waye xai fara janyewa,Kuma wlh ayau ba sai gobeba xansa afara gana miki azavar kamar yadda na fada miki, ruky ta rike hannun Alhaji sunusi Wanda ke shake da wuyanta, tana San kwace kanta ,Amma ta kasa saima Wani Irin numfarfashi da takeyi kamar wacce ke kan gabar rayuwa ko mutuwa, Alhaji sunusi ya qare Shake mata wuyanta kamar xai rabata da ranta,Saida ya tabbatar da ta kusa daina numfashi sannan ya saketa ya jefar ta a tsakiyar dakin da gabadayansa tiles ne, kan ruky ya daki kan tiles dinnan aqasa haka ta fadi sumammiya, awurin...




Alhaji sunusi ajikinsa na rawa Yana huci ya nuna ta da yatsansa yace bayanxu xan kashe kiba, saina gana Kiji azaba tukunna,yace wlh Rukayya bakiga komaiba na Daya daga cikin ukubar Dana tanadar miki matukar Baki bi umarnin abunda nake so kiyi ba, kashe ki baxaimin wahala ba,daga haka ya tsallake ta ya fita daga dakin, guards dinsa sukai qasa da kansu ganin yadda ya fito ransa abace ya nuna wadanda ke gadin Rukayya yace idan ta farka karku kyaleta ku gana mata azaba karku raga mata harsai tace ta yadda zatabi umarnina, suka ansa masa da girmamawa daga haka yay gaba abinsa Yana sakin numfashi sauran guards din suka mara masa baya,......







07066598376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD?mode=ac_t






*_____JAMI'AR TSARO _____*



*_____THE WOMEN POLICE _____*



*NA*




*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*____(MRS SARAKIES)____*




*=?1?QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION (QOWA) =?1?*




*Bismillahirrahmanirrahim*




_________season one ep 4?? 7??



____________?&


Hanan ce zaune office din AA Arab,wajen karfe 9 :30 na safe Dan jiyan Bata samu ganin saba,ta sunkuyar da kanta tana share hawayenta,bayan ta gama zayyane masa komai tundaga yadda komai ya faro har xuwa yanxu,akan yadda Babar shafa ta fara kaiwa gidan TV kokenta akan ataimaka mata abiwa shafa'atu kadinta,na zalintarta da akayi,da Kuma yadda Rukayya ta Shiga case din, har xuwa lokacin data bawa DCP case da yadda aka kama lateef da yadda CP yay ruwa yay tsaki shida Alhaji sunusi aka saki lateef harxuwa yadda ta qara karban case din ta kai qara kotu ,da yadda aka sace Khalil da Kuma yadda sukai da Rukayya ranar da xa'a sacetan,ta qarasa fada masa da cewa itama tana zargin Alhaji sunusi Yana da sa hannu wajen sace Rukayya da Khalil ko Kuma shiya sace su Rukayya,ta qarasa fada tana share hawayen fuskarta,.....



AA Arab ya fara xagaye office dinsa,Yama kasa furta Komai Yana San ya hada tunaninsa waje Daya,can u imagine ace women police ce tai wannan gwagwar mayar,saida yay kusan 2 minutes baiyi magana ba, saikuma can ya tsaya a inda yake tsayen ya harde hannayensa a kirjinsa, Yana kallan direction daban,ya nisa yace meyasa tun farko Hanan Baki fadamin wannan maganar ba, gashi mun bata lokaci muna bulayin nemanta babu Wani suspect tsawan kwanakin nan,Hanan da take goge hawayen furkarta tace am sorry sir, Bada gangan naiba,Ganin banda tabbaci akai shiyasa,nai shiru,AA Arab ya furxar da huci me xafi,yace itama na farko tayi ganganci meyasa lokacin Baku fadamin ba ai alokacin na dawo, idan dai dai ne abin ya faru alokacin,Hanan tana goge hawayen fuskarta ta jinjina kai,tace sorry sir,AA Arab yace yanxu Ina yarinyar take da maman nata, Hanan tace suna asibitin haryanxu,AA Arab yace haryanxu suna qarqashin kulawar likitocin ko yaya,Hanan tace eh,....



Yace Kuma haryanxu kudin data biya na kula da yarinyar Bai qareba,har yanxu,Hanan tace sir ai kudi ta Bada masu yawa dan idan har zasukai shekara a asibitin bana tunanin xai kare da wuri,AA Arab ya jinjina kai, sai Kuma yace idan xancen ki ya kasance gsky dole Suma aBasu jami'an tsaron da zasu dinga kulawa dasu,Dan babu shakka xai iya xuwa Suma ya daukesun,sbd haka anjima xan tura jami'an tsaron xuwa hospital din Dan kula dasu,Hanan ta qara sunkuyar da kanta kasa tace thank u very hugely sir,AA Arab ya jinjina kai yace in Sha Allah daga yanxu xansa a fara bibiyar duk Wani movement dinsa batareda ya saniba ba, Amma yanxu ki fara samomin number sa yadda xamuyi tracking dinsa cikin sauki.., Hanan tace in Sha Allah..



AA Arab yace zamu Saka Masa ido sosai,aduk Wani motsinsa,abinda nakeso Dake Hanan shine kema saikin kula ,na tabbata idan har shine ya sace su to na tabbata next target dinsa kece,daga nan Kuma kila sai su ita wacce kuke karewar,sbd haka Yanxu xamuyi duk yadda xanyi wajen ganin munbi diddiginsa,Hanan tace Allah ya qara Maka girma, Allah yasa kafi haka sir AA Arab yace, abinda nakeso Dake shine ki kula kema idan kinji Wani motsi ta bangarenki, let me know, hanan tace in Sha Allah sir,sai Kuma ta mike ganin ya gama magana tace bari naje sir,AA Arab ya jinjina mata kai,daga haka ta fice daga office din,taja masa kofar,bayan ta fita ta jingina jikin kofar office din dafe da kirjinta tana sauke ajiyar xuciyar salama,wlh sai Yanxu taji Wani sanyi aranta, sai Yanxu taji kamar nauyin Dake dan kare a xuciyarta ya sauka,saida ta Dan samu relief sannan tai gaba abinta,farin ciki fal ranta, kamar Wanda akace mata anga Ruky,bayan fitar Hanan AA Arab Saida ya kusan 2 minutes a tsaye sannan ya samu waje ya xauna,ya dauki wayarsa yay darling number ya sanar da abinda yakeson ai masa sannan ya aje wayar ,yay baya da kansa ya jinginar da kansa kan kujerar dayake xaune akai, Yana mamakin karfin halin Rukayya da Kuma Rashin imani Irin nasu Alhaji sunusi da lateef,da Kuma tunanin yadda xai bullo masa ta qarqashin qasa,.....



____________?&



Ataikaice dai zailani baiyi magana ba har xuwa wayewar gari duk mun axabar da ake ta gana masa sbd taurin kai Irin nasa, Amma yaki fada,da Bai fada ba Suma Basu fasa Yi masa abinda aka umarcesu dayiba, zailani ya galabaita kamar me, yanxu haka AA Arab ne tsaye akansa bayan an fito dashi daga inda ake ajiyeshi, yayi laushi sosai AA Arab ya xuba masa ido,sai Kuma ya kauda kansa ya fara Dan takawa acikin wurin yace cikin bacin Rai,yau yaxamto last words na karshe da xa'a tambayeka,Ina Yan uwanka suke wadanda kuke aikin tare, zailani ya dago da kansa da kyar yace Nima ban saniba,AA Arab ya karbi shocking din hannun police din Dake kula zailani afusace ,yasa suka Dora masa shi akan kujera yasa suka daure masa hannunsa,kan hannayen both kujerar ya fara Dora masa shocking a hannunsa da jikinsa,take zailani ya banqare ya saki ihun azaba Yana cije lebensa Yana yiwa AA Arab magiya , akan yayi hkr,Amma AA Arab ko Kulashi baiyiba ya cigaba da Abinda,yake ,da zailani yaga dai wahala xaisha kawai saiya ce xan fada xan fada Dan Allah kadaina zan fada Maka gsky yallabai,AA Arab ya Wani kalleshi on a serious note har lokacin fuskarsa a murtuke take yace kashirya fadar GSKY ko baka shirya ba, kasan baxan fasa abinda nake makaba daga nan har Wani lokacin, don't wasting my time,zailani yace wlh na shirya fadar GSKY yallabai,AA Arab ya kyaleshi yace Ina Jinka,shin ku kuke sa kanku kuke kai musu harin Kuma ku sace musu yara ko Kuma sakaku akeyi, karka bari na qara Mai Mai ta Maka tambayar nan,.....



zailani da sai sauke numfarfashi yake na azaba gashi angama sauya masa kamanninsa,Ya Dan dago da kyar ya Kalli AA Arab da idansa Wanda ya kankance da kyar yace sakamu akeyi yallabai,AA Arab ya xauna kan kujeran Dake wajen Yana kallan zailani yace go ahead, zailani yace Wani ne oganmu mesuna goga shiyake sakamu shima Kuma sashi akeyi Amma ni dai bansan sunan wadanda suke sakashin ba,sbd Bandamu da sanin sunan Wanda suke sakashin ba, nidai kawai abani kudi shine,idan aka bashi aikin mu yake samu mukeyi musu hardashi tunda mudai kudi kawai ake bamu idan munyi din Kuma a biyamu,AA Arab yace karya kakeyi kasan sunan wadanda suke Saka kun, Raina mana wayo xakayi,zailani da kamar xaiyi kuka yace wlh yallabai bansaniba,ka yarda Dani iya gskyr abinda na sani na fada Maka ,AA Arab yace banyarda ba,aiku ba'a bun yarda bane, zailani ya saki Kuka yace na rantse da assamadu bansani ba yallabai,ko al'qur'ani ka kawo saina dafa Maka idanma baka yarda da rantsuwar tawa ba.....




AA Arab ya sauke numfashi,sai Kuma ya mike ya juya baya yace inasu sauran Yan uwanka naka suke , sannan Ina kuke kai yaran da Kuke daukar, Zailani ya sunkuyar da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login