Showing 261001 words to 264000 words out of 278032 words

Chapter 88 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1039

yayiwa 'ya'yan ta sai dai 'ya'yan maimuna su yake kulawa wannan Abu Yana matuk'ar taka rawar gani wajen hau hawan jinin ta......





07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y






*____JAMI'AR TSARO____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*____(MRS SARAKIES =؋?)=?1?____*




*Bismillahirrahmanirrahim*



_______season two ep 1?? 0?? 3??




____________?&

Yau dai su ruky,suka tashi da niyyar zasu tafi gidansu AA Arab su gaida su ummi da Abba,da yay dai dai da one week da bikinsu .ruky tayi musu girki Mai Rai da lafiya batare da AA Arab ya sani ba Dan d'azu ya samu k'ira daga government house akan governor Yana son ganin shi ,shine fa ya tafi tun wajen k'arfe 9 na safe.tana kitchen ta har had'a abincin data girka musu a acikin basket bayan ta gama ta ajiye akan cabinet d'in kitchen d'in, ta fito ta shige D'aki danyin wanka,tana shiga d'aki ta Bud'e D'aya daga cikin akwatunan lefenta ,Wanda ya kasance na kayan kwalliya ta d'ibarwa su zuhrah zata kai musu ta zuba a wata babbar Leda ,ta ajiye a gefe ta d'aura towel ta shige cikin toilet D'in. tana fitowa har tazo tsakiyar d'akin Bata kula da AA Arab ba Dake Zaune bakin gadon ya zuba mata ido Yana kallan ta,tana juyowa taga mutum a zaune bakin gado Yana kallanta baya ko k'iftawa har ga Allah ta tsorata Dan ko kadan bataji motsin ya dawo ba , gabad'aya sai kunya ta kamata Dan daga ita sai towel ta fito tana shirin komawa yay Saurin k'arasawa ya rik'ota tasa dariya tana tura Baki gaba tace.

"Dan Allah ka bari Babu kyau tsorata musulmi fa", ta fad'a tana tura Baki gaba,yay murmushin Yana rik'e da ita har lokacin kafin Yay k'asa da murya yace.

"Ni ban tsorata kiba kece dai kika tsorata",ya fad'a Yana mannata da jikins???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a,ganin haka yasa ruky sauya zancen da cewa.


"kaga fa wanka nai kaima kaje kayi lokaci na tafiya zanje na shirya Karna bushe", ta fad'a tana ture Hannun sa daga saman k'irjinta.

Bai fasa ba sai ma ya zuro da kansa ta kafad'ar ta Yana kai mata hot kisses a wuyanta kafin yace cikin shak'akk'iyar murya.

"Sai dai idan zaki tayani muyi tare", ya fad'a Yana K'ara had'a ta da jikinsa.

Ruky ta k'ank'ame jikinta tana cewa.


"Nidai a'a Dan Allah ka sakeni lokaci fa Yana tafiya ta fad'a tana k'ok'arin k'wace jikinta",yay Wani murmushi yana d'aukar ta cak yay hanyar toilet d'in da ita .take ruky tasa masa kuka tana tureshi Dan Allah ya Gani wallahi AA Arab Yana takurawa rayuwar ta, kullum Abu D'aya ko gajiya bayayi,Yana rik'e da ita suka shiga toilet d'in,bayan sun shiga toilet d'in ya direta atsakiyar toilet d'in ganin haka yasa ruky tai yunk'urin gudawa yay saurin sawa k'ofar keyy yana zarewa yasa a aljihunsa Yana mata murmushin mugunta Ganin zata fita daga toilet d'in.tasa masa kuka tana masa magiyar Yayi hak'uri ya barta ta fita Amma Bai kula taba saima fara rage kayan jikinsa da taga Yana k'ok'arin Yi take ta juya masa baya tana rufe fuskarta da tafukan Hannunta tana Wani kukan shagwab'a,shidai AA Arab murmushi kawai yake harya gama ya juyo da ita Yana kallanta tak'i Bud'e idon ta kalleshi ita aka dole kunya take ji ,yay Wani killer smile yakai hannunsa ya kwance towel d'in Yana kallan ta daga sama har k'asa Yana Wani murmushi yana zareshi gabad'aya Ruky ta fad'a jikinsa ta k'ank'ame shi tana cewa Dan Allah ya bari shikuwa Wani Irin shock ne ya shige shi lokaci D'aya Yanayin sa yana sauyawa, Ganin tak'i sakinsa yasa Shima ya k'ank'ame ta Yana Wani numfarfashi, atak'aice dai a toilet d'in ma Saida suka lalace da soyayya kafin ya suka fito Yana d'auke da ita .ya zaunarta gaban mirror Yana tsane mata gashita kafin ya dauk'o handirar Yana tsene busar mata da gashinta,ita dai ruky tana ta kallansa ta mirror tana Wani Jin k'aunar sa na ruruwa a azuciyarta, lokaci bayan lokaci suna had'a Ido shikuma ya Wani kashe mata ido Yana murmushi itadai ruky sai dai ta tura Baki gaba tana masa hararar wasa ita adole fushi take dashi yasa ta wanka biyu.hakan nan dai suka gama shiryawa kafin nan suka fito downstairs bayan sun Rufe ko Ina sun Kuma kashe kayan wutar gidan,AA Arab ya zubawa Ruky ido da mamaki Yana kallanta ganin basket da wata k'atuwar Leda a hannun ta ta sauko downstairs bayan ta k'araso har gabansa ta kalleshi tai masa fari da ido kafin tace.


"Wannan kallan fa", ta fad'a tana Wani tura Baki gaba

Ya shafa kansa kafin yace .

"Meya wannan a hannunki .ya fad'a Yana kallanta


Ta sauke numfashi tana Marai raicewa Tace.

"Basket mana",

Yace .


"Ina zaki dashi Kuma?.

Ta Wani langwab'ar da kai tana kallon sa tace .

"Inda zamu mana",

Ya kalleta yace.

"Yanzu harda Wani special girki kikai Dan kawai ki bawa kanki wahala gida fa zamu bafa Wani wurin ba".

Ta tura Baki gaba tana d'auke kanta daga kallan sa kafin tace.


"Ai Babu Wani abun bawa kai wahala Dan nayiwa su ummi girki Dan Allah Dee mu tafi lokaci na tafiya".

Ya sauke numfashi kafin yace.

Ita Kuma wannan ledar fa ?".

Tace da alamar gajiyawa da tambayar da yake mata abune aciki.

Ya sauke numfashi ganin tak'i fad'a masa yace.


"Daga yau karki K'ara bawa kanki wahala indai zamuje gida kinji ai ko?"ya fad'a in a serious talk.


Ruky ta kalleshi kamar zatai magana sai Kuma ta Sauke numfashi kafin tace .

"Shikenan naji muje", Amma Kuma a zuciyar tasa aranta Bazata fasa yiwa iyayensa hidima ba indai zasu je ko Kuma ita idan zata tana wannan tunanin har ya k'araso zuwa gabanta ya karb'i basket d'in Dake hannunta ya bar mata ledar suka fito daga falon gabad'aya ya danna Wani D'an Abu take k'ofar falon ta rufe ruf, Ruky ta bishi a Baya har inda yay parking motar sa a compound,ya Bud'e mata front seat tashigo bayan ya karb'i ledar hannunta ,ya Bud'e back seat yasa basket d'in da ledar hannunsa itama duk yasa aciki ya rufe ya zaga driver seat ya Bud'e yashigo yay wa motar key gate man ya Bud'e musu gate suka fice daga gidan....


Tunda suka shigo gidansu AA Arab Ruky take kallan girman gidan da had'awarsa harma da yanayin ginin,duk da itama gidan nasu bawai baya bane wajen kyau da had'awarsa, Amma shima gidan su AA Arab kat ne idan nace kat Ina nufin k'arshen kyau,suka shiga har cikin falon gidan AA Arab na rik'e da basket d'in ita Kuma tana rik'e da ledar hannunta Dan da haka yace ma
Duka shi zai d'auka dagewa tai akan ya Bata ledar Dak'yar ya Bata, suka shiga har cikin falon bakinsu d'auke da sallama ,su ukhty suka tadda a falon Dan duk gobe suke shirin zasu wuce gidajensu ,ga yaransu suna wasa a falon,da fara'a duk suka ansa musu sallamar su ukhty Aysha na cewa ah Ashe dai kuna hanya da har mun fara cire Rai da zuwan ku". ta fad'a tana kallan AA Arab.


Ya Wani had'e Rai kafin yace cikin dakiya sai kace shine gaba da ita,


"sai dai idan tun ASuba kike so muzo". ya fad'a Yana zama kan D'aya daga cikin kujerun falon,ukhty Aysha tace.

"A'a ni ban ce haka ba sarkin Rashin kunya". ta fad'a tana masa hararar wasa,ya had'e Rai yace.


" to yaushe kike so muzo d'in idan Bamu zo yanzu ba?".


Ukty hameeda ta mik'e ta nufi ruky tai mata side huge kafin ta sake ta tana kallan ta da murmushi a furkarta tace.

"Well come antynmu", ruky ta Maida mata da Martanin murmushin datai mata kafin tace"nagode ta risina ta gaida ukty Aysha da Zainab duk suka ansa mata da fara'a a fuskartsu kafin ta zauna kan D'aya daga cikin kotun falon.hameeda ta gaida AA Arab ya ansa Yana kallan ta kafin yace da hameeda.


"Ummi fa"Bai rufe Baki ba ummi ta sauko downstairs d'in zuhrah na biye da ita har suka k'arasa saukowa tana zuwa tai kan ruky da sauri tana murmushi ta rungumeta tare da cewa.

" well come Antynmu,ta fad'a da fara'arta.ruky ta ansa mata kafin ta zamo daga kan kujerar har k'asa tana gaida ummi.ummi ta ansa mata da fara'a sosai tana zama kan D'aya daga cikin kujerun falon kafin tace.

" a'a Rukayya tashi ki koma kan kujerar ki zauna mana", ruky ta girgiza mata kai cikin Jin kunya tace.

" nan ma yayi ummi",.

Ummi tace.

"a'a zaman a k'asa Babu Dad'i maza tashi ki zauna kinji Babu komai".

Babu yadda Ruky ta iya cikin Jin kunya ta koma ta zauna tana wasa da yatsun hannun ta.AA Arab ya gaida ummi cikin girmamawa.ummi ta ansa masa da kulawa tana tambayar sa iyali ya ansa a kunyace kafin yace .

"Abba fa?,

ummi tace .

"Ya fita ya samu urgent call a company Amma nasan zuwa anjima ai zai dawo",ya jinjina kai kafin ya Kalli zuhra yace.

"gashi ki Mik'awa ummi Rukayya ce ta kawo muku". zuhrah ta taso ta d'auki basket d'in da ledar da ruky ta Mik'a mata ta risina ta karb'a tana Yi mata godiya, ummi ta kalli kayan kafin tace.

"A'a Rukayya harda wahalar haka , a'a gaskiya ki daina wahalar da kanki indai zaki zo nan gidan kinji? aike yanzu ba bak'uwa bace ke 'yata ce kidaina kinji? mungode sosai shukran , itadai ruky murmushi kawai take, Ameerah ce ta sauko falon daga sama take Dan tana can tana assignment shiyasa Bata sauko ba Saida ta gama ta k'araso har cikin falon tana kallan Ruky da murmushi a fuskarta tace.

"Ah!! Anty kune kuka zo sannu da zuwa". ta fad'a tana murmushi.
Ruky ta Ansa mata da kulawa,ta gaida AA Arab ya ansa Batare da ya kalleta ba Dan hankalinsa Yana kan twins d'in ukhty Aysha da suka k'araso wurinsa suka mak'ale masa suna masa surutu suda sauran yaran.


Hameeda da zuhra suka kawo musu ruwa da drink's suka ajiye musu a center table d'in Dake gabansu da snacks.


AA Arab ya Kalli ummi yace.

" Bari naje na dawo".

ummi tace.

"A'a! baza kasha ko ruwa bane" .


Yace ."a'a banajin to k'ishi".


Ummi tace."to Shikenan saika dawo Amma ai Batare zaku tafi ba ko?,


Yace.

"A'a tace ai wuni zatayi".

Ummi ta Jin jina kai tace masha Allah mun gode".

AA Arab yay musu sallama.daga haka ya fita daga falon... Haka nan Ruky ta wuni agidan nan Dan ta zama compotable sosai agidan Dan harta fara sabawa da siblings din AA Arab har dasu ukhty Dan Basu da wata matsala Suma suna yinta sosai sun d'auke ta tamkar k'annunsu Suma,ga ummi itama yadda take k'aunar ta komai tace Rukayya,haka suka Wani Agidan cikin farin ciki ga Yaran yadda suka mak'ale mata har dai suka D'an Saba da ita Suma, dayake itama ruky akwai ta da San Yara haka suka Wani cikin farin ciki...da daddare Abba ya dawo suka gaisa da ruky,shima bashida da wata matsala ya karb'e ta da kulawa sosai har sukai sallama suka tafi kamar karsu rabu haka suka ji bayan ummi ta had'o mata abin arzik'i , ruky tai ta mata godiya,duk sun karb'i contact din juna zasuna waya....



_____________?&


Washe gari Kuma gidansu ruky suka tafi,AA Arab ya siya musu kayan Tsaraba Batare da ruky ta sani ba tunda shi baiga ta musu girki ba kamar yadda tai lokacin da zata gidansu bare ta kawo musu Wani abun,Saida suka sauka sannan ta ga ya Bud'e boots yaywa masu aikin gidan magana akan suzo ,bayan sunzo suka gaida shi cikin girmamawa ya ansa musu da kulawa,ya nuna musu boots d'in suka shiga fito da kayan suna shiga cikin falon Dashi,ita dai ruky kallan sa kawai take har masu aikin suka gama shigar da kayan ciki ya Basu kud'i da Batasan nawa bane kafin ya k'araso har kusa da ita yana kallan ta ganin yadda ta zuba masa ido tai masa godiya yay mata alamar baya so,Bata sake magana ba har suka jera suka shiga cikin falon babu kowa sai k'arar fan da AC baba hasiya ce ta fito daga kitchen Jin motsi tana kallansu kafin tace.

"A'a sannunku da zuwa sannan da zuwa,kune kuke tafe bari ayiwa su Hajiya magana, ta fad'a tana k'ok'arin juyawa zata haura sama.ruky ta kalleta da murmushi a fuskarta tace.


"A'a baba jeki cigaba da aikinki bari naje da kaina", ta fad'a tana tambayarta ayina maman take? baba hasiya tace.


"tana sama Bata Dad'e da hawa ba", ruky tace.

"shikenan,anty mufeeda fa?.

Nan ma Baba tace .


" Ina ga itama tana saman kinsan shirin tafiya take gobe zata tafi suna ma tare da matar Tahir shima kinsan duk goben zasu tafi tazo yiwa Hajiya sallama ne".

Ruky ta Jinjina kai kafin ta haye saman sai a sannan AA Arab ya samu damar gaida baba hasiya ta ansa masa da fara'a tana tambayar sa aiki da kuma mutanan gida duk ya ansa mata da lafiya lau,baba hasiya tace.

"Allah ya taimaka", AA Arab ya ansa da Ameen kafin ta koma kitchen d'in ta kawo musu ruwa da drink's,anty mufeeda ce ta fara saukowa bayan ruky ta shiga ta gansu ita da Khadija amaryar ya Tahir,su mimie da moha sukai kan AA Arab da gudu suna masa sannu da zuwa ya rungume su Yana kallan su da murmushi a saman fuskarsa suka shiga gaidashi,ya Ansa musu da kulawa,har su anty mufeeda suka k'araso falon da fara'a a saman fuskarsu Suka shiga gaisawa, cikin girmamawa.mamah ta sauko ruky na mak'ale da ita kamar wata k'aramar yarinya da sallama mamah ta k'arasa saukowa abakinta,AA Arab ya zamo daga kan kujerar da yake ya shiga gaida mamah .

Mamah ta zauna ta Ansa masa da fara'a da tambayarsa su ummi ,yace .


"Duk suna lafiya ,anty mufeeda ta nunawa Mamah kayan da AA Arab ya kawo musu,mamah tai masa godiya sosai shidai murmushi kawai yake bai ce komai ba,Bai jima ba yace zai tafi da daddare zaizo ya d'auki ruky, suka masa fatan dawowa lafiya.saida Rukayya ta wuni agidan su , suna ta hirar yaushe Gamo ga matar ya Tahir itama babu ruwanta,suna ta hira abinsu har suka k'ira Hanan awaya, Nan fa Hanan tai kamar zatai kuka tace meyasa Ruky Bata ce mata zatazo ba ai da tazo sun Had'u anyi zumuncin da ita duk da itama tana yawan zuwa gidan mamah gaida ta.ita dai ruky Dariya kawai take mata kafin tace mata zato mata in Sha Allah, ko zuwa jibi ne,nan dai suke ta hirar kafin suyi sallama. sai dare AA Arab yazo ya d'auki ruky lokacin har ya Tahir yazo ya d'auki matar sa, tamkar Kada ruky ta tafi haka taji Dan harda kukunta Babu yadda ta iya suka tafi...


Washe gari Kuma government house sukaje gaida governor,bayan sun gaisa da governor suka je suka gaisa da first lady kafin AA Arab ya barta acan shi Kuma ya koma wurin governor suna ta hira kafin ya governor ya tambayi AA Arab yaushe ne komawa zaman kotun su Alhaji sunusi, AA ya sauke numfashi yace.

"Your Excellency nan da one week ne in Sha Allah".

Governor ya jinjina kai kafin yace .

"Allah ya kaimu ".

AA Arab ya ansa da Ameen.haka nan suka cigaba da hira,itako Ruky tana can ta zama 'yar gidan first lady Dan faran faran haka ta dinga hira da ruky kamar dama sun San juna Dayake itama first lady Babu ruwanta, macece Mai fara'a da son mutane,Kuma kawai jitai lokaci D'aya ruky ta Shiga ranta kusan awarsu biyu sukai kafin AA Arab yace zasu tafi, first lady Bata so tafiyar su ba haka tasa aka kawo wa ruky kayayyakin sawa masu bala'in kyau da tsada irinsu atamfofi lesis da dogayen riguna Wanda bama a k'asar nan ta siya ba da turaruka tuli guda duk ta bawa Ruky itadai ruky godiya kawai take mata .ta karb'i contact d'in ruky tace zasu dinga waya Sannan Kuma idan ruky ta samu lokaci tunda ba nisa garesu ba ta dinga zuwa mata please, Ruky ta ansa mata da in Sha Allah.haka suka rabu bayan ta koma taiwa Excellency sallama shima yay musu shatara na arzik'i daga haka suka Shiga mota suka tafi gida.....




07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y






*____JAMI'AR TSARO ____*


*____THE WOMEN POLICE ____*




*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*____(MRS SARAKIES =؋?)=?1?____*



*Bismillahirrahmanirrahim*



_______season two ep 1?? 0?? 4??



___________?&

*Bayan Kwana biyu*


Daya kasance weekend da Yay dai dai da Ranar asabar , Ruky suka shirya zasu je gidan Hanan ita da AA Arab dan dashi zasu je zasu kai musu ziyara.bayan sun gama shiryawa tsaf suka sauko downstairs cikin shirin fita, bayan AA Arab ya kashe duka kayan wutar gidan suka fito suka rufe falon kafin su fito zuwa compound har Inda yay parking motar sa,AA Arab ya bud'ewa ruky front seat ta shiga sannan shima ya zaga ya shiga driver seat yaywa motar key gate man ya Bud'e musu gate suka fita Yana musu adawo lafiya.bayan sun isa gidan Hanan suka fito daga cikin motar,AA Arab ya zagayo ta side d'in da ruky take tsaye tana jiransa ya tsaya yana kallan ta bayan ya jingina da jikin motar ruky ta kalleshi ganin baida niyyar shiga gidan tace.


"Kashigo mana".

Yay murmushi yace .

"kije kimin iso tukunna". ruky ta saki Baki tana kallan sa kafin ta sauke numfashi Dan tama kasa cewa komai haka nan Ruky ta nufi cikn gidan .da sukai Sa'a sun tadda ya Hanaf agidan dan tunda yaji labarin zasuzo Bai fita ko Ina ba Yana nan Dan Yana so su gaisa da AA Arab.da farin ciki Hanan ta taso ta rungume ruky bayan ta shigo falon ta saki ruky tana kallanta kafin tace.


" Ina ya Ahmad d'in?.ta fad'a tana dube duben bayan ruky ko zata ga AA Arab d'in.

Ruky ta juya tana kallan Bakin k'ofar falon tace.

" Yana waje Mana yace sai an bashi iznin shigowa tukunna sai shigo".ta fad'a tana murmushi.

Hanan ta zaro ido waje Jin abinda ruky tace kafin tace.


"Kai Kiji ya Ahmad to kiyi sauri kije kice ya shigo".ta fad'a tana sakin hannun ruky.

Babu musu ruky ta juya ta fito daga falon ita kuma Hanan ta haura sama Dan sanarwa da ya hanaf zuwan su ruky.

Ruky tana fita ta tarar da AA Arab jingine jikin motar sa har sannan Yana latsa wayar sa ta k'araso har gabansa ya d'ago da kansa Yana kallan ta langwab'ar da kai kafin tace.


"Ance Kashigo",ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login