Showing 228001 words to 231000 words out of 278032 words

Chapter 77 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1022

ba .


"Please fiancee ki bari ko zanji na samu relief", ya fad'a Yana k'ok'arin jawota jikinsa,ai ganin haka yasa ruky ta sa masa kuka ta ce.


"Please sir Dan Allah kabari",tana fad'a tana k'ok'arin k'wace jikinta Wanda ya had'a ta danashi ya fara k'ok'arin kamo fuskarta da bakin ta zaiyi kissing ta fara tureshi tana masa magiya Amma Ina AA Arab yayi nisa bayajin k'ira Dan Wani Irin fiti nan nan k'amashi ne ke tashi ajikinta,Dan dama tunda ta shigo motar daurewa kawai yake Yi ,ruky tasa ihu Wanda Yay saurin toshe mata Baki,kafin ya dawo hayyacinsa ya sake ta,tai saurin matsawa baya can k'arshen motar jikinta na rawa ta fara k'ok'arin Bud'e murfin motar tana Murd'awa tana kuka ,AA Arab ya dafe kansa kafin ya D'ora kan striarin motar Yana sauke numfashi kamar Wanda yay gudun tsere Yana tunanin meya aikata haka meyasa yay ,wai Meya Kaishi ma yay mata wannan abun.

Ruky ta juyi tana kallansa tana kuka tace.


"Ka Bud'e min na fita ",


AA Arab yana k'ok'arin saita kansa ya d'ago Dak'yar Yana kallan ta yace cikin shak'akk'iyar murya.

"Ki nutsu fiancee saina Bud'e miki",

Ruky tasa Mai kuka tace.


"Nidai ka Bud'e min na fita Dan Allah dare fa yayi ga mamah sai K'irana take", ta fad'a tana k'ok'arin Bud'e murfin motar.


AA Arab yay yay ta tsaya karta shiga gidan a wannan firgicen da take Amma tak'i,babu yadda ya iya ya cire lock d'in ta Bud'e da sauri ta fita ko tsayawa K'iran da AA Arab yake mata batayi ba ta fita da sauri har tana had'awa da gudu ta shiga cikin gate d'in gidan.


AA Arab ya dafe kansa Yana Daya sanin abinda ya aikata mata haka,ya Dad'e acikin motar nan Saida ya gama dawowa hayyacinsa sannan ya tada motar yay reverse ya fara tafiya a hankali yana Jin cikin sa na Murd'a masa.


Ruky kuwa kasa nutsuwa tai saboda firgici,data shiga gidan ma da tai Sa'a babu kowa a falon direct sama ta haura zuwa d'akin ta ,tana Shiga ciki ta rufo k'ofar ta jingina jikin k'ofar tana dafe k'irji Bata tab'a tunanin haka AA Arab yake ba duba da yadda Bai tab'a yi mata Irin haka ba ,Koda suke zama waje D'aya office koda wasa Bai tab'a kwatan kwacin tab'a jikin taba balle harya rungume ta,ta Sauke numfashi ta k'arasa Shiga cikin d'akin ta na k'ok'arin cire kayan jikinta saboda yadda gabad'aya kamshin turaransa ya bayyana cikin nata kayan ta cire ta d'aura towel sannan ta shiga wanka har lokacin Bata dawo dai dai ba,tana tunanin dama shima haka yake dama , to wai haka mazan suke ne ko Kuma su biyune masu Irin halin shida lateef ,take gaban ta ya fad'i Jin wani tunani da tai,take ta dafe k'irji azuciyar ta tace Ina gaskiya bazan K'ara bari mu had'u ba ,sai Kuma tace wajen aikin fa take ta fashe da Kuka sannan ta fara wankan ,Saida ta gama wanke jikinta tas har lokacin Bata daina Jin kamshin turaransa ba haka nan dai ta fito daga wankan ta tsane jikinta da towel ta k'arasa gaban mirror ta fara Shafa lotion d'in ta bayan ta kammala ta k'arasa bakin wardrobe d'inta ta da d'auko kayan da zata Saka, doguwar riga ce marara nauyi ta d'auko sai hula data sa akan ta bayan ta shirya ta k'arasa gaban mirror ta feshe jikinta da turaruka,tana juyawa taga wayar tana kawowa haske Koda ta duba taga AA Arab ne ke K'iran ta , take taji ranta ya B'aci taji gabad'aya ma haushinsa take ji,ta tura Baki gaba tana kallan wayar, Amma tak'i picking ta bar wayar tana ta ringing ta fita zuwa d'akin mamah Dan sanar mata da cewa ta dawo..




____________?&


*ZARI'A*


A b'angaren su baba asabe kuwa ta dage saita zubar da cikin zaliha tayi jik'e jik'in ta bawa zaliha Dan cikin ya zube Amma shiru kakeji,har asibiti taje ta karb'o k'wayar zubar da ciki ta bawa zaliha tasha Amma Abu ya gagara babu abinda ya Sauya,yanzu haka tana tsaye a kan zaliha ne Dake kwance acikin falonsu, su Mardiya kuma suna tsakar gidan suna zaune zaman kashe wando ta kalli zaliha tace.


"Tashi Kisha wannan maganin a gabana bansani ba ko idan kika Sha zuwa kike kike zubarwa idan Kinga na bar wajen da tuni ya zube ,shiyasa gashi Tsinan nan cikin nan Yana nan daram yak'i zubewa",ta fad'a tana hararar zaliha,


Zaliha ta mik'e Zaune daga kwancen da take ta karb'i kwanan shan da maganin yake ciki ta kafa a bakin ta Tasha Rabi ta Mik'awa baba asabe sauran tana cewa na k'oshi babarmu kar nai amai",


baba asabe ta kalli kwanan Shan tace .


"Shanyeshi zakiyi tas Dan ubanki Dan so nake a yau wannan cikin ya zube", zaliha ta yamutsa fuska tace Dak'yar.


" na k'oshi babarmu Dan Allah ki bari kar nai amai",

Baba asabe ta harareta tace .


"Kinsan har Inda naje na karb'o maganin nan kuwa , kinsan Irin yawan danai kafin Allah ya had'a ni dame maganin nan kuwa?wallahi sai kin shanye tas Dan atabbatar min indai kika wuni kina Sha daga nan zuwa dare cikin nan duk mun nacinsa saiya zube ,saboda haka ki kafa bakin ki shanye Dan baza ki jamin asara ba , gabad'aya jarin abincin nawa ya k'are a garin nemo maganin zubewar cikin nan saboda haka wallahi saikin Sha, kin San daga fara fita ta zuwa yau kinsan nawa na kashe kan zuwa wajen likitoci da malamai wajen ganin tsinan nan cikin nan ya zube ? To wallahi ko zaki mutu ba k'oshi ba sai kin shanye maganin nan karbi ki shanye", ta fad'a tana k'ok'arin d'ura mata ,babu yadda ta iya zaliha ta karb'i maganin Ta shanye tas tana ya Mutsa fuska,baba asabe ta sauke ajiyar zuciya ganin ta shanye maganin tas Sannan ta karb'i kwana nan shan zata fita dashi,amai ne ya tahowa zaliha ta mik'e da gudu ta fita tsakar gidan tana kwara Rashi kamar me baba asabe tasa Wani ihu tabi bayan zaliha tace .


Yanzu Dan ubanki maganin kika amayar,itadai zaliha amai kawai takeyi bama tajin baba asabe saboda abinda take ji, baba asabe tace.

" kai wallahi kedai Allah yay wadaranki , wallahi zaliha zan iya tsine miki idan har cikin nan Bai zube ba ,ta fad'a tana kuka ...


Malam Auwalu Daya fito daga d'akinsa Yana kallan baba asabe yace .


"Wato Asabe bakiji abinda na fad'a miki ba akan cikin ba koh? , duk fa abinda kike Yi Babu Wanda bansani ba duk Wani motsinki da shiga da ficen da kikeyi dayawan da kikeyi zuwa wajen malamai da likitoci na ganin kin zubar da cikin nan Babu Wanda bansani ba kallanki kawai nake,ke Kinsa isa kiyi jayayya da Allah ne ai abinda kika shuka ne kike girbarsa ,ai tunda har kika ga cikin nan Bai zube ba to ya rantse ne sai yazo duniya kin ganshi,ya taka da k'afar sa,ai duk abinda kika aikata wallahi asabe saikin girbeshi,ya fad'a cikin d'acin rai Dan wallalhi yafi baba asabe Bak'in cikin ganin cikin nan..


Baba asabe ta harareshi kafin tace.


" wallahi Allah mugun bakin ka saidai ya fad'a akan ka ,mugu kawai Wanda baya k'aunata ,ba kuma ya k'aunar 'ya'yana , wallahi malam in Allah ya yarda sai dai mugun bakin ka ya koma kanka kaida 'ya'yan da kake so ta fad'a tana hushi.


malam Auwalu yay murmushin takaici yace .


"Asabe albarkacin Wani dalili kike ci shiyasa har Yanzu ban d'auki mataki a kan kiba, da Kuma ganin kin girbi abinda kika Dad'e kina shukawa naga kin girba, Dan wallahi da ida idonki sai Kinga abinda kike shukawa kina girbarsa,Amma badan haka ba wallahi da tuni kinbar gidan nan", Yana fad'ar haka yay hanyar waje Dan barin gidan.

" baba asabe ta bishi da cin mutuncin tana cewa sai ya shiga wuta idan baiyi wasa ba ,alhakin tama kad'ai ya isa ya kaishi wuta miye miye Haka dai dinga zagi da Rashin mutunci kala kala a tsakar gidan nan,sudai su lawisa Suna jinta suna mata Wani kallo, suna mata addu'ar shiriya ..



A bangaren ummah kuwa itama tana jinta Amma Batai magana ba , Ameenah tana d'aki tana karatun Al'qur'ani,duk Babu Wanda yay magana acikin su ,har baba asabe ta gama fad'an ta ta gaji tai shiru.,sai Kuma ta koma kan 'ya'yan su mardiya wai sun cinye mata abincin saboda tana shiga d'akin ta gansu gabad'aya kusan su bakwai akan Kwanan abincin data ajiye Dan taci, Kuma shika d'ai ya rage Wanda zataci,tana alwashin saita Dake su, lawisa ta tashi tana cewa ita dai gaskiya karta daki 'ya'yan ta ,itama mardiya haka ta Mik'e tace kar adaki 'ya'yan ta ,take baba asabe ta hau tsine musu albarka tana cewa kuma sai sunbar d'akin ta tunda sun Raina mata hankali Kuma basuda kunya, bud'ar bakin mardiya sai cewa tai ai itama yanzu taiwa babansu Rashin kunyar,suka hau Yi mata rashin kunya take baba asabe tasa kuka tana tsine Musu albarka tana cewa Kashe ta suke so suyi wallahi sai sun bar gidan sun koma d'akin mijinah su ko Kuma idan duniya zasu shiga sai dai su shiga haka ta shiga d'aki ta hau jefo musu da bagkonsu tsakar gida tana musu cilli da kayansu tanayi tana tsine musu kamar wata mahaukaciya.....




07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y





*____JAMI'AR TSARO ____*



*____THE WOMEN POLICE____*




*NA*




*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*




*____(MRS SARAKIES =؋?)=?1?____*




*Bismillahirrahmanirrahim*



______season two ep 9?? 0??



__________?&


A tak'aice dai ruky a wanna dare Batai picking call d'in AA Arab ba ,harya hak'ura ya kyaleta ya koma Yi mata text's, shima text's d'in Babu kalar Wanda Bai mata ba, Amma babu Wanda ta Bud'e aciki bare tai reply har ta kwanta daga k'arshe ma kashe wayar ta tai .da safe da ta tashi da bazama taje wajen aiki ba, kawai dai Dan tasan bazai tab'a yiyuwa bane Tak'i zuwa ba,bayan ta gama yin breakfast ta haura sama Dan yiwa mamah sallama, mamah tana d'akinta suna waya ita da anty mufeeda, akan Bak'in da sukazo jiya ,ruky ta shigo d'akin Bakin ta d'auke da sallama, ta k'arasa shigowa cikin d'akin,Saida ta jira Mamah ta gama wayar Sannan ta gaisheta, ta Kuma sanar mata zata tafi.mamah ta kalleta kafin ta ansa mata gaisuwar data mata sannan ta k'ira sunanta da .


"Auta!",


Rukayya ta d'ago tana kallan ta kafin ta ansa mata cikin girmamawa,mamah tace.

"Ki kula da kanki kinji? Kinga dai yanzu ba irin da bane ,yanzu ansa miki ranar AURE,saboda haka ki kama kanki kinji?", ta fad'a tana kallan Ruky.


Ruky ta gyad'a mata kai kafin tace cikin sanyin murya.

"To mamah!",


Mamah tace .

"Yauwa ko kefa Allah ya kiyaye ya dawo Dake lafiyayyan", ruky ta gyad'a mata kai Sannan ta juya ta fita daga d'akin.


Tana shiga office tasan cewa AA Arab yazo tunda tun a parking lot taga motarsa Koda ta k'arasa wurin zamanta Batai gigin zuwa office d'in saba bare ta gaishe shi,hardai ta fara aikin ta sama da mintuna talatin da zuwan ta,Amma bataji motsin Saba, Haka dai tai Jin tsoro da fad'uwar gabar yadda zasu had'u da AA ARAB.


AA Arab Yana cikin office d'in sa Yana aikinsa Mai muhimmanci, yaji shigowar ta Amma Bai fito ba dama kuma Bai Saka ran zata zo gaidashi ba duba da yadda suka kwashe da ita a daran jiya, shiyasa ma Bai fito ba shima,zai jira idan ya fito Dan zuwa masallaci yay mata magana.


A b'angaren ruky kuwa ba k'aramin Dad'i tajiba da AA Arab Bai fito ba Dan Allah ya Gani Wani Irin kunyar sa take ji kamar me,tana nan zaune ta kwashe a wanni a inda take zaune tana aiki bataga d'uriyar Saba,sai dai taga yaransa police suna shiga office d'in nasa da dukan alamu akwai abinda yake kaisu,ita dai tana zaune tana Fargabar yarda zasu had'u dashi .da lokacin sallahn Azhar yayi AA Arab ya fito Dan Zuwa masallaci ai ruky tana Jin motsin Bud'e k'ofar office d'in nasa ta juyar da kanta gefe gaban ta na fad'uwa har sannan , Kallo D'aya AA Arab yay mata ya wuce Bak'in k'ofar ya Murd'a ya fita , ruky tana ganin ya nufi k'ofar fita ta juya tana kallon sa ,haka kawai taji Wani Abu ya tsikari zuciyarta lallai ma wato ko yay mata magana koh?Shine ya kama hanya ya tafi, haka ta fad'a azuciyarta,kawai sai ta mik'e a fusace tai Hanyar toilet itama Dan ta d'auro alwala.

Tana kan sallayan Bata tashiba tana addu'a har Wani lokacin Bai dawo ba,sannan ta mik'e ta koma kan kujerar ta _ta jawo laptop d'inta zuwa gabanta, har zata cigaba da aikin kuma taji ta kasa tunani kawai take yadda AA Arab ya share ta kamar Bai gantaba, bayan ai shi yayi mata laifin Amma shine zai fita d'aukar zafi da yawa, take taji ranta ya B'aci ta fara k'unk'uni tana magana k'asa k'asa.


AA Arab Bai dawo daga masallaci ba Saida ya D'an fita Wani wuri sannan ya dawo wajen k'arfe karfe biyu da Rabi na rana lokacin ruky ta gama cika tai fam da ita, kamshin turaransa ne ya fara mata iso kafin shi ya shigo,take ta saita kanta ta had'e Rai ,har ya shigo bakinsa d'auke da sallama,ruky ta ansa masa a saman lab'b'anta Batare da ta kalleshi ba,AA Arab ya k'arasa shigowa ya Tako har gaban table d'inta ya zuba mata ido Yana kallan ta da mamakin Yadda tai kicin kicin da fuska ita adole fushi take bayan shiya ka mata yay fushin tunda shi akayiwa laifin k'in d'aga call d'insa ,ya D'an duk'a kad'an har sannan kallan ta yake ya k'ira sunanta cikin k'asa da murya ya ce.


"Fiancee!",


Bata kalleshi ba ta ansa masa a k'asan labb'anta. bai damu ba yace.


"Nasan haushina kika ji akan abinda ya faru jiya koh?,ya fad'a Yana kallan ta kafin ya cigaba yace.

"shiyasa har nai ta K'iran ki bakiyi picking call d'ina ba har text's na tura miki Amma babu reply, why please? Ya fada cikin damuwa.

Ruky tai shiru batai magana ba.yace .

"kinsan Irin halin da kika jefani kuwa Rukayya!", taji ya k'ira full name d'inta ,ya cigaba Yace .

"Meyasa baza kimin uzuri ba , kuma da kinyi picking call d'ina a lokacin da hak'uri fa na k'iraki na Baki, Amma Shine bakiyi picking call d'ina ba daga k'arshe ma kashe min waya kika Yi,haba fiancee , ya fad'a cikin damuwa,ya cigaba yace.


"billah Dan bakiga Irin halin Dana shiga bane a daran jiya shiyasa, wallahi da bakik'i picking call d'ina ba,Amma yanzu ma Bai b'aci ba Bari na Baki hak'uri Bai jira cewar taba yace .


",kiyi hak'uri fiancee! ,in Sha Allah Hakan bazai sake faruwa ba kinji?",ya k'arasa fad'a Yana kallan ta .


Sai a sannan ruky ta d'ago ta kalleshi cikin Jin kunyar abinda ta aikata masa ,Amma sai ta maze tareda D'an shagwab'e fuska tace.

"Amma shine d'azu da zaka fita masallaci bakamin magana ba ",ta fad'a tana Wani tura Baki gaba Wanda ke sawa AA Arab yaji gabad'aya Yana Neman fita hayyacinsa .


Yace .

"Ok,wai d'azu? ai Gani nai kin juyar da fuskar ki bama kyasan ganina shiyasa nace bari na k'yaleki idan kika huce nai miki maganar shiyasa na tafi ban miki magana ba,Amma am so sorry princess",ya fad'a Yana murmushi.


Ruky ta sauke numfashi tace .

"Shikenan, Amma Dan Allah kadaina min abinda kake min bana so",ta fad'a a shagwab'e.


AA Arab ya k'ura mata ido kafin yace .

"Ok am sorry in Sha Allah bazan sake ba ,Nima bansan ya akayi Hakan ta faru ba,Kuma ma kece kikemin duk abinda yasa nake kasa controlling kaina akanki",ya fad'a cikin rad'a


Ruky ta sauke idonta k'asa kafin tace .


"To Nima kayi hak'uri da abinda nai Maka jiya , wallahi Nima tsorata nai",ta fad'a kamar zatai kuka.


AA Arab ya d'ago daga duk'en da yake yace Yana kallan ta.


"Alright wannan Babu komai ya wuce aike bakya laifi a wurina u are special &the best", ya fad'a Yana murmushi.


Ruky itama murmushin tai kafin ta ce .

"Alright thank you, Nima ya wuce",ta fad'a tana kallan sa, ya shafa kansa yace cikin rad'a.

" thank u fiancee,bari naje na cigaba da aiki",


ruky ta ce.

"Ok"


Yace.

" ko zamuje ki tayani",ya fad'a da sigar tsokana Dan yasan dama ai ba zuwan zatai ba ,ta girgiza kai kafin ta rausayar da kai tace.

"Nima ga nawa aikin Yana jirana",ta fad'a tana kallan sa


AA Arab ya Dan Yi murmushi kafin yace.

"Nima da wasa nake miki Nasan ba zuwa zakiyi ba",

Ruky ta sauke kanta k'asa tana murmushi ya D'an Matsa baya kad'an kafin yace .


"bye bye", ruky ta kalleshi tana murmushi daga haka ya shige office d'insa, ta bishi da kallo tana sauke numfashi.



Haka kowa ya cigaba da aikinsa har lokacin tashi yayi ruky ta shiga tai masa sallama,ya mata fatan Sauka lafiya , sannan ta juya ta tafi .


Da da daddare ruky tana kwance akan gadonta suna waya da AA Arab kamar yadda suka Saba,ya k'ira sunan ta yace .


"Fiancee! kinsan siblings d'ina sun dage saina kawo su gunki wai suna so su ganki ,suga wacce Mai sa'ar ce tai wuf da yayansu",ya fad'a Yana murmushi cikin sigar tsokana.

Ruky ta D'an Bud'e ido kafin tace.


"Wai su Ameerah!?",

Yace.

"eh mana sun takuramin akan na kawo su gunki tunda suka ji zancen AURAN nan kullum su burinsu na kawosu gunki, ya fad'a Yana murmushi.


Ruky tai murmushi tace .

"Please ka kawo su mana mu gaisa",

Yace .


"Noo Bayanzu ba "


Ruky tace cikin Damuwa.

" why please?",

AA Arab yace .

"Kawai nafiso sai nan da Wani lokaci tukunna",

Ruky ta D'an Bat'a Rai kamar Yana gabanta tace .


"Haba sir! Dan Allah nidai ka kawo su ",

AA Arab yace .


"Idan har ni zan kawosu sai dai karsu zo Dan bani da lokacin kawo su ",


Ruky tace.


" to ba saikasa a kawo suba",


Yay murmushi yace .

"Bazan sa a kawo subaz kawai Dan san yawo",ya fad'a Yana ya Mutsa fuska.

Ruky ta had'e Rai kamar Yana gabanta cikin damuwa tace "

"Gidan na mune Dan zasuzo wurina shine yawo? kai meyasa kake hakane",ta fad'a cikin damuwa.

AA Arab yay murmushi yace.

"Wannan damuwar da da kikayi fa,kawai Dan nace bazan kawo suba Kuma bazan sa a kawo suba shine zaki damu? naga dai k'arewar Tama AURANKI Zanyi ai zasu ganki ko?",

Ruky ta k'ara B'ata Rai kafin tace.

"Nidai kawai tunda har suna so


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login