Showing 252001 words to 255000 words out of 278032 words

Chapter 85 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1032

part d'in su ya hanaf suka shiga ta k'ofar baya ta zaunar ta kan kujerar Dake falon fuskarta tana rufe har lokacin, kawai ango ya shigo tare da friends d'in sa dama already k'awayen amarya suna ciki ko wacce ta saita Cameran wayar ta harda abokanan Angon kowa rik'e da wayarsa ya saita Camera,da murmushi a fuskarsa ya k'arasa har gaban ta inda ya D'an duk'a ya Bud'e mata furkarta Dake cikin mayafinta take fuskarta ta bayyana ya kamo hannun ta ya mik'ar da ita tsaye yana kallan fuskar ta da kyau cikin wani Irin yanayi na shaukin kasancewa da ita tare haka yake binta da kallo ,Amma itakan bata yadda ta kalleshi ba ta lumshe idonta, baiyi wata wata ba ya rungume ta acikin jikinsa take aka d'au ihu da sowa tare da hasken camera Dake ta tashi ta ko ina a wurin sai d'aukarsu pictures da videos akeyi,ita dai ruky gabad'aya kunya ta kamata k'irjinta sai wani Dokan uku uku yakeyi, shiko AA Arab wata nutsuwa yaji tazo masa ta musamman.ya saketa Yana kallan da murmushi a fuskarsa Yana rik'e da Hannunta D'aya itadai ruky ta sunkuyar da kanta k'asa,haka aka shiga Yi musu pictures ga photographers din da aka dauko na musamman Suma suna yi musu pictures harda vedios Basu Dad'e ba suka tafi,sai Kuma after isha'i prayer Azo d'aukar Amarya. Hanan ta Maida ruky zuwa d'akinta ...



Da Dadad'e wajen k'arfe Tara na Dare manya manyan motocine sukai parking a k'ofar gidan AIG umar MaiTama Dan zuwa d'aukar Amarya iya Motar da za'a d'auki Amarya ce kawai aka shigar da ita har compound d'in gidan.ruky ce d'urkushe agaban mamah wacce take mata nasiha, Kuka kawai take kamar ranta zai fita,daga k'arshe mamah tace cikin ruwar murya wacce itama kad'an ya rage ta saki Kukan saboda tausayin Autar tata ganin zasu rabu, uwa uba kuma zata shiga sabuwar rayuwa tace " tashi kuje Allah ubangiji ya Baku zaman lafiya ta K'arasa fad'a tana Mai goge hawayen fuskarta ruky ta mik'e ta rungume mamah tana sakin Wani marayan kuka ,da k'yar Hajiya Maryam da cousin d'in Mamah Hajiya Zainab suka b'anb'areta daga jikin mamah suka fita da ita har compound inda motar take sai dirzar kuka take kamar wacce ake zare ranta,bayan sun shigar da ita driver yaja motar suka tafi...


A bayan government house gidan ruky yake inda governor ya bawa AA Arab kyauta tun lokacin Daya dawo Kaduna Mai karatu idan zaku tuna to nan ne dai gidan,AA Arab ba da San ransa ma zai zauna agidan ba Dan da shi anasa burin gidansa Daya Gina Dake unguwar GRA Nan yaso zama Dan dai kawai governor yace sai dai renewa yayi bayan haka ya fad'awa ma Abba shine fa Abba da ummi sukace kawai yayi hak'uri ya zauna Agidan, gidane upstairs,komai na gidan luxury ne,su kansu funitures d'in da aka zuba mata Agidan Suma kansu luxury ne kunsan abunka da masu abun ga Kuma itace auta yasa aka kashe mata kud'i bana wasa ba wajen siyan kayan d'akin ,su Hajiya Zainab ne Suke rik'e da Hannunta suka shigar ta har cikin bedroom d'inta,bayan sun zaunarta bakin gadon suka K'ara Yi mata nasiha kafin su fito su tafi, Anty mufeeda ta k'arasa gunta suka rungume juna ruky ta saki Kuka tana cewa "Dan Allah anty karki tafi ki barni",ta k'arasa fad'a tana K'ara sautin Kukan ta ,anty mufeeda ta ringa lallashin ta kafin itama ta kasa daurewa ta saki Kukan haka suka rungumi juna suna ta kuka,da k'yar Ruky ta saki anty mufeeda ta fito daga d'akin tana share hawayen dayak'i tsaya mata, itama Hanan Kukan take ta k'arasa har gaban Ruky ta rungume ta dama already k'awayen duk sun mata sallama sun fita tunda sai cewa ake kowa ya fito za'a maidasu,ya hanaf ne yashigo d'akin Ganin Hanan Bata fito ba ya tsaya Yana kallan su da mamakin yadda suke kuka babu mai lallashin Wani acikinsu ,nan ya k'arasa har gaban su yasa hannunsa ya b'anb'aro Hanan daga jikin ruky wacce sai kuka take Yana kallan Ruky da kyau yay k'asa da murya cikin lallashi yace.


"ya isa haka Auta daina kuka kinji?", ruky tak'i yin shiru saima sautin Kukan ta data K'ara, ganin tak'i yin shiru yasa ya saki Hanan ya rungumeta Yana lallashin ta , Amma Ina Mai makon tai shiru sai ma K'ara sautin Kukan nata da takeyi haka ya daure Yana jin shima wani rauni azuciyar n rabuwa da 'yar uwarsa ya cigaba da lallashin ta da kalamai masu Dad'i da k'yar ta d'an tsagaita da kukun ya sake ta Yana Kallan Hanan wacce keta durza kuka itama yay k'asa da murya yace.


"Kidaina kuka wifey kinji?I'm sorry kiyi hak'uri muje", Bai jira cewar taba ya kama Hannun ta suka fito daga cikin d'akin Ruky ta bisu Amma ina ya rufo k'ofar take ta koma ta zube akan gadon tana ta rusa kuka.....




07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD?mode=ems_share_t



*____JAMI'AR TSARO____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*Bismillahirrahmanirrahim*



______season two ep 1?? 0?? 0??



____________?&


Kuka kawai ruky take tunda su ya hanaf suka tafi suka barta kamar ranta zai fita Bata San tsawan lokacin data d'auka ahaka ba, Bud'e k'ofar d'akin da akayi Hakan baisa ta saurara da kukun da take ba harya rufe k'ofar ya k'araso har gaban gadon inda take kwance ya zauna a bakin gadon kusa da ita yana kallan yadda take ta dirzar kuka tsakaninta da Allah yay k'asa da murya ya k'ira sunan da .


"Fiancee!",

Bata ansa ba saidai Ta saurara da kukun da take taba sheshk'ar kukan ahankali Amma Kuma bata d'ago ba ya kai hannunsa ya d'ago ta zuwa jikinsa Yana kallan ta da kyau,ganin haka yasa ta zaro ido tana kallan sa tana k'ok'arin k'wace jikinta, shidai ido Kawai ya zuba mata Yana kallan ta yace cikin cool voice d'insa.

"Sai kin fad'a min kukan me kike?",ya fad'a Yana tsareta idanuwansa.ta juyar da kanta gefe hawaye na zuba a idonta ya kai hannunsa yana share mata hawayen kafin yace .


"I'm sorry my bride ok,idan ma kukan rabuwa kike da 'yan gidanku baganiba".ya fad'a Yana mata Wani Irin kallo,ta girgiza masa kai tana K'ara sakin Wani kukan tace.

"Nidai mamah,Dan Allah ka kaini wajen mamah", ta fad'a tana sheshshek'ar kuka".AA Arab ya saki Wani murmushi kafin yace.

"Wajen mamah Kuma?",

Ta gyad'a masa kai hawaye na zubowa daga fuskarta har lokacin, yace .


"Idan kika tafi kika barni ni Kuma nayi Yaya?",ya fad'a Yana kallan fuskar ta ,ta wani kalleshi kafin ta d'auke kanta ta tura Baki gaba tace.

"Kaima saika tafi gida", ta fad'a tana d'an yin murmushin abinda ta fad'a d'in",

AA Arab ya jinjina kai kafin yace.

"Dole kiyi murmushi Saboda kema kinsan bamai yiyuwa bane, Kuma nasan kinsan komai, ya fad'a Yana ruk'o hab'arta Yana k'ok'arin juyo da fuskar ta zuwa tashi fuskar,ta cire hannunsa daga hab'ar tata tana matsawa baya yay Wani murmushi yana shafa kansa kafin ya mik'e yace .

"sauko muje falor kiga Wani Abu,ta nok'e masa kafad'a tana kallan sa ta girgiza masa kai alamar a'a.ya sauke numfashi yace.

"ok,to zo muje kiga gidan naki", ya fad'a Yana kallanta ta sunkuyar da kanta k'asa tai shiru tana tunani yace ."please fiancee ko saina zo ka d'auke ki "sai a sannan ta wani kalleshi kafin ta zamo daga kan gadon ta zuro da k'afafuwanta k'asan tiles d'in d'akin Wanda suka Sha Jan lalle sai d'aukar ido suke ,yana kallan ta ya k'araso har gabanta ya kamo hannun ta ya mik'ar ta tsaye yana rik'e da hannun suka fito tana gyara mayafin jikinta ita dai kunya duk ta kamata ahaka suka fito tana kallon corridor Dake tsakanin d'akunan Dake sama ga Wani babban falor Dake nan saman shima,haka ta dinga bin kujerun da kallo komai yayi mata kyau yadda take so,bayan sunagama shiga duka d'akunan Dake sama downstairs suka sauko nan ma wata sabuwar duniyarce Dan babu Abinda ba'a Saba na kayan furnitures komai anyi shi luxury yadda ya kamata,gida dai yayi Masha Allah,AA Arab ya dinga nuna mata komai na gidan daga k'arshe suka Shiga kitchen nan ma dai Komai luxury akamata kayay yakinta masu bala'in kyau da tsada suka fito daga kitchen suka koma falon sama inda anan ne kazar da abokansa suka Siyo musu da drink's Daya shigo Dasu ya ajiye akan center table d'in Dake falon ya zaunarta kusa dashi ita dai ruky sai kunya takeji tana k'ok'arin matsawa daga kusa dashi Amma ya hana Hakan,ya jawo plate d'in da ya d'auko da cup da suka shiga kitchen ya juye musu kazar acikin ya tsiyaya musu drinks Yana kallan ta yace"oya eat"ta girgiza masa tana ya Mutsa fuska tace.

"I'm okay",ya Bat'a Rai yace .

"Sai kinci ai Hanan ta fad'a min tunda aka fara bikin nan bakyacin abinci har yau da ZA'A kawoki Bakiciba", ya fad'a Yana kallan ta.

Ta kalleshi da mamakin abinda ya fad'a yanzu Hanan ce ta fad'a masa Wani Bata cin abinci ya dauk'o cinyar kazar ya kai mata Bakinta kafin yace."Bud'e bakin kice",

Ta gimtse Bakin ta tana girgiza masa kai tana matsawa baya tace .

"Nifa na k'oshi ai naci abinci kafin mu taho,kuma ma ni bacci nakeji zanje na kwanta", ta fad'a tana tura Baki gaba.


Bai yadda ba ya girgiza kai ya jawota jikinsa Yana kallan ta yace cikin k'asa da murya.

"Naji zaki kwanta Amma sai kinci abincin first tukunna",ta girgiza masa kai, Yana kallan ta yace.

"Ok,Ashe ko baza kiyi kwanta kiyi baccin ba indai Bakici abincin nan ba, ya fad'a in a serious talk,ganin ya dage saita ci yasa tace .

"Ok,naji Amma ka bari zanci da kaina ba saika bani ba",ya saketa yace.

"Ok eated",ya fad'a Yana matso da plate d'in zuwa gabanta ,tasa yatsun ta biyu ta d'auko cinyar kazar ta kai bakinta ta kalleshi ta gefen ido ganin shidai cin kazar kawai yakeyi ita ko tunda ta d'auki cinyar kazar nan take fama da ita bata k'ara d'aukar Wani ba ya kalleta suka had'a ido tai saurin d'auke idon ta ta Maida side daban,sai Jin muryarsa da tai yana cewa .


"Meyasa bakya ci?",

Ta kalleshi tace." Ina ci mana",ya girgiza kai yace.


"Ina kallo naga Tunda kika d'auki na hannunki Baki K'ara d'aukar wani ba",tace cikin shagwab'a.


"Ai ya isheni",ya dauk'o Wani naman ya Mik'a mata yace.

"Sai kin cinye wannan sannan ki K'ara da Wani",kamar zatai kuka tace.

"Ya isheni fa ",ya tab'e Baki kafin yace.

"Ashe ko baza ki kwanta ba,idan kinga Kin tafi kin kwanta to kinci naman nan ne", ya fad'a Yana tura mata cup d'in milk da drink's zuwa gabanta Yana kallan ta.ruky ta tura Baki gaba Kamar zatai kuka babu yadda ta iya ta fara cin kazar, Yana kallan yadda tanaci tana gyan gyad'i yasa yace.

"Kije kiyi alwala zamuyi sallah idan na shigo bari nai parking kayan nakai kitchen", ya fad'a Yana kallan ta ta d'auke idonta daga kallan sa gaban ta na fad'uwa ta gyad'a masa kai tana mik'ewa jiki a Sanyaye ta shige bedroom d'in da aka kaita d'azu tana shiga toilet ta shiga direct tai brush ta d'auro alwala ta fito tazo ta haye gado ta kwanta tana jiran sa Amma ita kanta tasan baza ta iya baccin ba.


AA Arab ya shigo d'akin Yana kallan ta da mamakin kodai bacci take ne,ya d'auke kansa daga kallanta ya shige toilet d'in bayan ya d'auro alwala ya fito ya k'araso har gaban gadon Yana kallan beauty face d'inta yadda take sauke numfashi ya kai hannunsa ya shafa fuskarta take ta Bud'e idonta tana kallan sa Bata d'auka zatai baccinba Dan wallahi kwanciya kawai tai tai likimo ashe har baccin ma ya d'auke ta ,ta zuba masa idonta tana kallan sa da sleeping face d'inta ganinsa gabanta yasa ta D'an tsaro ta Dan Allah ya Gani Tama manta ayina take Dan duk d'aukarta agida take cikin d'akinta akan gadonta Yana kallan ta yace cikin Kulawa.


"Fiancee!tashi muyi sallah",ya fad'a Yana mata murmushi.ta Mik'e Dak'yar ta sauko daga saman gadon ta ratsa ta gefensa ta wuce toilet ta d'auro wata sabuwar alwalar , bayan ta fito ta tarar dashi kan sallaya Yana jiranta ta Rab'a ta gefensa ta wuce gaban akwatunan ta Bud'e D'aya ta d'auko hijab d'inta ta dawo ta tsaya a bayansa ya juya suka ta-da sallah sukai raka'a biyu kamar yadda aka koyar damu.

Bayan sun idar ya juyo yana kallan ta tai saurin sunkuyar da kanta k'asa gabanta na fad'uwa,yay murmushi Yana kallanta kafin ya dafa kanta ya fara kwararo musu addu'a bayan ya gama ya kalleta yace.


"Are you feeling sleeping until know",

Ta gyad'a masa kai ya Sauke numfashi kafin yace.

" ok ,but bazakiyi wanka ba?",

Ta girgiza masa kai tace cikin rawar murya.

"Nayi kafin muzo", yay murmushi ganin yadda jikinta yake ta rawa ya s'auke numfashi yace.

"Ok to jeki kwanta",Bata bari ya k'arasa ba ta Mik'e da sauri jiki ba k'wari ta haye saman gadon ta matsa can k'arshen gadon ta kwanta batare da ta cire hijab d'in jikinta ba,ya bita da kallo kafin shima ya mik'e ya linke sallayan ya fita daga d'akin .

Ruky ta sauke ajiyar zuciya d'aukarta ba'a d'akin zai kwanta ba , Amma duk da haka jikinta Bai daina rawa ba ,bayan few minutes ya dawo d'akin sanye da jallabiya bakinsa d'auke da sallama daga Gani wanka Yayi Dan sai Wani tashin k'amshi yake ,take gabanta ya Fad'i ganin ya dawo d'akin,ta runtse idonta gaban ta na fad'uwa dif dif,har taji ya kashe switch din da'kin ya hawo saman gadon, ruky ta k'ara matsawa baya kafin ta Ankara taji ya jawota jikinsa tare da k'ank'ame ta Yana hamdala,ai tuni ruky ta zaro ido tace cikin rawar murya .

"Dan Allah ka tafi D'aya dakin ka kwanta mana ",


Yay murmushi sai shak'ar k'amshin jikinta yake Wanda tun d'azu ya cika masa hanci daurewa kawai yake yace .

"Uhmm!Ina da matar zan tafi Wani d'akin na kwana?to ke Kuma fa idan na tafi na barki dawa zaki kwana?",ya fad'a yana k'ok'arin juyo da ita gabanshi.

Ta k'ank'ame jikinta tace Cikin tashin hankalin abinda yake mata.

"Ni ni ai zan iya kwanciya ni kad'ai",

Ya saki Wani killer smile yana kai bakinsa dai dai kunnenta ya rad'a mata cewa.

" Noo!!Cikin wata iriyar murya ",

Ruky ta shagwab'e fuska tace .

"please Dan Allah ka daina",ta fad'a tana k'ok'arin tureshi.ya kai hannunsa kan hijab d'in jikinta yana k'ok'arin cirewa tare da cewa cikin wata iriyar murya.

"Ki cire hijab d'in nan",ta k'ank'ame tana salati tace.

"A'a ni dashi zan kwanta"ya fara k'ok'arin cire mata, take tasa masa kuka Amma Ina Bai fasa ba haka yasa hannunsa ya zare hijab d'in duka Yana jefar dashi kan bed d'in.ruky ta dinga Masa magiya Amma Ina Bata ita yake ba ta abinda zuciyar take ta raya masa yakeyi tanaji tana Gani ya fara k'ok'arin zuge zip d'in rigar ta Yana fitar da Wani irin huci kamar Wani mawiyacin zaki,itadai ruky sai kuka take tana masa magiya Amma ko kula ta baiyiba saida ya cire mata kayan jikinta, ya rage daga ita sai inners Wears d'in ta ,saboda kwata kwata taki bari yayi abinda ransa yakeso sai kokowa kawai suke da ita, Amma duk da haka k'arfin mace dana namiji na D'aya ba,haka ya D'an jagwal gwalata ganin tak'i bashi had'in kai kamar Kuma zata sume masa ya matsa baya yay rubda ciki Yana Sauke numfashi Yana Jin kamar kunnashi akeyi Ruky ta jawo hijab d'inta ta rufe jikanta dashi tai baya tana yin kuka k'asa k'asa ,ya kai hannunsa ya jawota jikinsa ya rungumota d'aukar ta cigaba zaiyi tasa masa Wani kukan tana rok'arsa ,yace cikin shak'akk'iyar muryarsa da Batasan shi da itaba,


"Shiii!!,Babu abinda zan miki kawai so nake na samu relief ahaka",ya fad'a Yana san sanar jikinta Yana shakar kamshin jikinta Yana sauke numfashi,Babu yadda ta iya haka ya rungume ta har bacci ya d'auke su ahaka....washe gari sai wajen 10am suka tashi shima Dan abincin da aka kawo musu ne daga gidan ummi zuhra da Ameerah ne suka kawo driver ne ya kawo su bayan sunzo suka masa waya shine ya fita yaje ya karb'o Bai bari sun shigo gidan ba daga Bakin gate suka juya,shi Kuma ya koma cikin gidan. wajen k'arfe Shibiyu na Rana Bak'i suka fara zuwa haka ruky tai wanka tana tarb'ar Baki cikin girmamawa,Dangin AA Arab ne ma suke ta zuwa ganin amarya tunda duk a ranar zasu tafi, ruky tun tana Saka ran zuwan 'yan gidan su harta sare har k'arfe biyu na rana Basu zoba sai wasu 'yan uwansu ne da zasu tafi suka zo ganin gida dayi mata sallama,Hakan yasa ta kasa hak'uri bayan Bak'in sun D'an tsagaita da zuwa ta zauna a falon ta d'auki wayarta ta k'ira anty mufeeda,bayan anty mufeeda tayi picking Ruky tasa mata kuka anty mufeeda tai dariya kafin tace .

"Lafiya meye haka Kuma Auta?", ruky tace cikin Kuka .


"Anty shine babu Wanda yazo acikin ku ta fad'a tana shashshekar Kuka,anty mufeeda tai murmushi tace.


"Kiyi hak'uri sai gobe zamu zo in Sha Allah"ta fad'a tana dariya.


take ruky tasa mata wani kukan hadda sheshshek'a, Anty mufeeda tai murmushi tace ."haba Auta kiyi hak'uri kefa kin girma yanzu goben dai zamuzo in Sha Allah",ta tura Baki gaba tai shiru tana tambayar anty mufeeda mamah, anty mufeeda tace tana tare da Bak'i,nan dai ta cigaba da kwantar mata da hankali.bayan ta sauke wayar Hanan ta k'ira Amma Batai picking ba saida tai mata miss call har biyar Batai picking ba, ran ruky ya gama B'aci wato ita Hanan zataiwa haka koh?,ta mik'e ta shige D'aki tana share hawayen dayak'i tsaya mata, wato itama Hanan d'in bazata zoba kenan Amma ita taje mata babu komai haka take ta fad'a a ranta.


Sai wajen k'arfe biyar da Rabi na yamman Ranar Hanan ta K'irata,da kamar ruky bazatai picking ba sai Kuma kawai dai tayi ,tai shiru batai magana ba.Muryar hanance ta ratso wayar da .

"Amarya bakya laifi ya gajiya",ta fad'a da sigar tsokana.ruky tace afusace .


"ban saniba,wato shine kema ko ki zo ko Hanan?"ta fad'a kamar zatai kuka.

Hanan ta rik'e hab'a Tana gimtse dariyar ta tace .

"Ni inzo gidanku na K'one",ta fad'a tana dariya.

Ruky had'e Rai tace .

"sai dai abinda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login