Showing 291001 words to 294000 words out of 347556 words

Chapter 98 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8743

Karfe hudu kowa ya dawo kaduna masu gidaje a nan suna gidansu baki kuma suna masauki suna hutawa sai dare da za a tafi dinner karfe takwas ne na dare don haka iyayyena maza suna dawowa suke fadin karfe shidda na yamma za akai amarya gidanta.
Gidan da banda Abbas ba wani mahalukin dayasan gidan nan sai su biyun kawai suka san hakan har yan uwa nasa sun fara tsegumin kan su ba a kaisu gida sun gani ba ko a wanan gidan nasa zai zaunane suke tambaya.
Ba ansa don duk wanda ya kawo zancen sai ace dashi ba a san gidan ba har wanan rana din Ammi sunso suje suka gidan tun kan aikai saidai hakan bai samu don ko wani lokaci Abbas din zaice ayi hakuri yana busy a lokacin.
Su kuma basa so a samu wani akasi don hakane suke tambaya amma ba,a akaisu ba yasa sukaja baki sukai shiru don sunsan inma an samu akasin zasu gyara kafin su bar kasa.
Sai matan gidan mu suma aun dayi tsegumin gefe daba,a rasa ba dai don mama ke tambayan mama uwa da cewa ke uwar diya kun diba gidan amaryace inda yar taki zata zauna kun shagala da harkan buki haka.
Ai dole mu sani yaya tunda ba daji zasu ajeta ba nasan wanan ba matsala bane kawai dai abinsune a cikin ka,ida akeyinsa don hak namu ido kawai don ko iyayyenta sunyi magana banji komai ba kuma.
Mu dai ai gamu ganin karya kai da ganin karyan nan kasam ba abin kai sake bane wanan dole akwai lauje cikin nadi abune ake yinsa ba bincike kudi ya rufewa mutane ido ana abu a cikin makanta.
Yaro karami yana fidda miliyoyi haka amma don kwadayi an rasa wanda zai zauna yayi nazarin hakan akansa don son abin duniya don kawai ace yarshi matar wanine.
Yaya ke nan ai yanzun kuma ba wanan zancen tunda uwarta tazo ta fansheta ita da nata irin bajinta kinga ai abune na kaiwa kaiwa yanzu kuma balle kinsan halin malam muna ganjn kamar baiyi bincike ba bintuce zai dauka ya bayar hakana ba tare da wani bincike a kaiba ya san komai da kike ganinsa wajen nan mama lanto ta fada.
Sai ga zancen zuwa kai amarya karfe shidda nan mutane kowa ke fadin zai tafi dashi za,a yaga gida nikan tunda labarin hakan yazo min jikina yayi sanyi lokacin na fara tunanen sabon rayuwan da zanshiga inda wasa nake ganinsa a da ayanzu kan ba wasa aure nayi da gaskiya.
Ina nan kuryan dakin dasu Ammi ke aciki baza kasan ina dakin bama don can kuryan gado nake angama mulke min jiki anyi komai daya dace ai min irin yadda al,adansu yake dama na nan din hjy Battulace a tsaye kan komai da Ammi da sauran yan uwa a wajen.
Nayi kuka har nagaji saida suka tsawata min suka kuma dawo lalashi da ban baki suna min nasiha muna hakane mama Lanto da gwaggona sai mama uwa suka shigo wai su baba sunce a kaini suna jirana.
Tare da su Ammi muka dawo mu ukku muna shiga gidan kai tsaye dakin baba suka nufa dani mun samesu a zaune ganin mu yasa su fadin kun iso ko ai sai mu tashi mu tafi kada a makara.
Su uwaye sun dauka wani wajen zasu dani mama uwace tayi karfin halin tambaya wani waje zaku kaitane kanin baba da ake kira da Modibbo yace gidan mijinta mana yanzu meya rage kuma banda fatan alheri a rayuwansu tunda an daura aure.
To ai bamu shirya ba bamu fadawa makwabta sufito a tafi ba yace kinga mun hutar daku mune nan da kanmu zamu kai yarmu dakinta kowa ya huta sai in munje din zaku iya biyomu a baya wanan ba laifi bane.
Haka ko zancen ya kasance a kaina don ko su baba Abdullahine baba mai mota mahaifin ya habibi malam hamza sai mahaifin mu da kansa mota biyu suka daukemu zuwa gidan ina bayan mota tare da babana baba mai mota yana gaban mota sai nasiha suke min na zaman duniya da biyayya ga miji har muka kai wani gida naji karan bude get din gidan motar tashiga.
Bazance ga unguwar da muke ba a lokacin don kaina yana duke kuma a rufe don haka bansan inda tafiyan namu ya kawo mu ba lokacin.
Shiru sai can sai naji an bude kofan motar baba ya fara fita ta bangarenshi kafin naji muryan Oga Abbas yana fadin sannuku da zuwa baba sannuku da hanya bissimillah ga hanyan shiga gidan ai nan ku shigo baba.
Naji baba din ne ko wani ya bude bangaren da nake zaune muryan baba naji duk da sheshekan kukan da nakeyi a lokacin amma hakan bai hananu gane muryan baba din ba.
Haka na daure na fito ina sheshekan kuka naji baba ya dan rugumuni yana fadin kukan ya isa haka uwata kamar yadda yakan kirani idan wani abu mai muhinmanci ya sameni na tashin hankali.
Ki daure kibar kukan nan ki kama addua a bakinki ki shiga gidanki da kafar dama insha Allahu alherin Allah ya biki a wanan gidan har abadan abada arayuwanki uwata.
Muryan su Abbas ne da wasu ke fadin Ammin baba amin ya Allah a dinga jero muna tagwaye kuma duk shekara inji wani fitsarare a cikinsu sai suka kwashe da dariya gaba dayansu.
Muryan baba Abdullahi naji yana fadin ina surukin namu ne yazo ya karbi matar tasa daga hannun mu a daidai lokacin baba ya dan duku a kunnena yana min rada ki fara karanta bissimillah saiki karanto fallaki da nasa kafa ukku ukku ki gama ki karanto ayyatulkursiyyu kafa daya ki karanto hasbunallahu wani ni,imal wakeel kafa bakwai ki shafa da niyar Allah yazamo tare da rayuwan auren ki yai maki jagora ako wani lokaci cikin gidanki.
Nafara kamar yadda baba din ya umurceni dayi har nakai karshe wajen yayi tsit lokaci guda zakice babu kowa a wajen lokacin sai mu kadai nida babana a wajen.
Saida naji baba yana min addua sun dauki amin amin baba nagane suna kusa muryan mami naji tana fadin wai ina son din nawane yazo mana ya karbi matarsa hannun baba yau nauyi ya rataya a wuyansa baba ya sauke nasa nauyin shi saura yanzun kuma.
Aka kwashe da dariya tace ehh man gaskiya na fada yanzu danane da wanan nauyin sun rabu lafiya da baba yanzu kuma shi ubangiji ya dorawa hakan.
Allah ya zaunar daku lafiya ya baku hakkurin zama da junan ku yakawo zuri,a masu albarka aka amsa da amin lokaci guda.
Har lokacin kaina na kasa kuma rufe da gyalen lafayan jikina can naji wanan kamshin turaren nasa wanda hakan yasa lokaci daya gabana ya fadi rassss can naji muryanshi yana fadin sannuku da zuwa ya fada.
Karbi matarka gata nan na danka maka ita amana duniya da lahira ubangiji Allah ya baka ikon rike wanan amanan ya gama ku da malaikun rahama a rayuwa zamanku amin summa amin.
Aka amsa da amin kafin naji wani murya na fadin gaskiya baba kabada nauyi mai wuyan dauka ga abokin nan namu saidai kagama magana don wanan adduan ai da kayi Allah yayi muna jagora gaba daya aka amsa da Amin.
Hannuna naji an daga wani ya damka lokaci guda naji wani iri don nasan ba hannun babana bane a zatona dai kila mami dince take jan hannun nawa yasa ba mussu nabi bayan mashi kamar yadda ake min jagora alokacin don ba gani nakeyi ba don idona dake rufe a lokacin.
Zaunar dani kasa akayi nidai ina bi sai daga baya wanan mayen kamshin nasa daya gama game min hancina ya sanar dani cewa shidin ne ashe ya rikoni yanzuma mun zaunane a gaban su baba kowa yayi muna dan nasiha kafin suyi muna sallama su tafi abokan nasa suka raka su baba din.
Dauketa ka kaita dakinta naji muryan mami na fadin hakan sai naji yace mami gaki kuma tace yadda aka baka amanan nan ka tabbatar da kayi komai tun yanzu shine rikon amana din.
Muryan Abbas naji yana fadin hakane mami zamu hadu indai nine ai yacewa Abbas din suna raha yajani zuwa sama har dakin da aka ware min a gidan matsayin nawa ya zaunar dani a bakin gado a hankali yana fadin zaki iya bude fuskanki kisha iska ba kowa a dakin can naji fitanshi shima daga dakin ya rufo kofan.
Jin hakan yasa na dan bude fuskana a hankali ina bin dakin da kallo wai aljannan duniya na fada a raina a hankaki cikin second na zagaye dakin da idanuna kafin na mayar da mayafina na rufe fuskan hawaye na zubo min a hankali daga udanuwana.
Wai kiji min mutanen nan wai sun kawo amarya ashe tun dazun basu fadawa kowa zuwansu ba mutanen nan kamar a shirye suke fa suma duk wani plan din mu sai su rusa munashi.
Wai da gaske kikeyi sun kawo yarinyar nan wallahi yanzun yaran nan suka shigo suna fadi daga can suke sunce iyayyenta mazane suka rakota zuwa dakintama ba mata ba.
Shike nan yan iska mayun banza idan ba mayu ba taya zasu gane akwai wani plan da mukayi kan daukar amarya harsuyi muna over taken haka lokaci guda.
Yanzu dai ai aikin gama ya gama shike nan kuma wanan din ma ya rushe ke nan an kashe kudi a banza haka masu yawa kuma ki bari ba kudin ya dameni bani yanzu.
Yadda nake da yakini akan aikin nan wai ace anyi kuskuren samun sa,an hakan shine haushina na yarda yaron nan dan banzane na gaske na bugawa a jarida.
Waya sani ko irin asirin nan ya dauko na turawa naganin har hanjin mutane da kome ake ciki yasani kallon mutane kawai yake wawaye nayi matukar mamakin samun akasin aikin nan don kowa ya sani sai takwas ake kawo amarya a garin nan kowa yasani.
Yanzuma daga an dauko ai wajen dinner ake wucewa direct daga can suke dawowa gidan nasu amma kinga wa yan nan yan iskan kauyen duk sin rusa komai a yanzu.
Hjy Lailace a tsaye take wanan masifan jin cewa ai amarya tana dakinta tuni shine ransu ya baci don plan din da suke dashi na rugaza masa rayuwa da sun samu aiwatarwa muda zaman lafiya tsakanin mu har abada.
Wanda yanzu mutane basa ganewa daga wajen bidi,an aure shedan da shedanun mutane suke samun galaba a kansu a mata masu tsarin na rayuwa har abada Allah ka tsare kare muna rayuwan mu dana yan uwa musulmai amin.
Gidan muma acan an samu cakwali anyi ta cecekuce na ba,a kyauta masu ba tsegumi kala kala anyishi a wajen mama sai masifa takeyi wai abinda ba,a tabayiwa kowa ba shi baba yake tayi da wanan bukin don ya nuna akwai bambanci tsakanina da yan uwana.
Mata dai sun watse bayan mama uwa ta fada masu karfe takwasne kai amarya kamar yadda aka saba a al,adance don Allah su fito daga can kuma za a wuce wurin dinner.
Mata basu raina buki ko banza balle wanan da suke kashe kwarkwatan idanunsu ga kallon bazata a gidan mu da Allah yai nasa ikon kan ajiyan da yayi a tsakaninsu da gidan mu dasu yan unguwa
din.
Su Fadila kawayena suka iso gidan aka bar su Usaina dasu maryama da zasuzo daga baya a cikin tawaga a lokacin mama ta kira Usaina daki ta cacaketa kan cewa taji wai itace zatayi shigan amare akaita a matsayin amaryar boye gidan ango.
Wani mama baki mussun wanan magana nafa san na girmewa Bantu nasan abinda nakeyi fa ni tace atoh naji uwa na fadin waiko ke a luluba akai a matsayin amarya ban yarda da wanan bakin kiran kadaran ba ehh,hee.
Mama kada ki dauka muna bin Bantu mun mayarda kanmu sakarkaru yanzu da mun jaye mun ki saka kanmu cikin sha,anin nan ina zamuga wanan abubuwan da muka wawasa ga bukin nan ki barmu kawai idan kinga munayin abin mu munsan me mukeyi sarai a nan da hankalin mu wallahi.
Ki dai muna fatan mu samu wanda zai laba damu muma mu kama gidajen mu tunda na bayan mu duk sunyi aure sun barmu a gida.
Shigowan su Hassana a lokacin yai mun dadi sunzo da mai kwaliya kuma kai jama,a ina idar da sallah aka hau kwaliyan dinner kuma nikan nasha wanka kamar agwagwa nagaji nagaji kamar nace wayyo Allah na a lokacin.
Amma ba yadda na iya dole haka na shirya zuwa wanan dinner din wanda a nan kowa zai kure adakanshi don tarone na maza da mata musanman yan mata suna son wanan event din don a nan wata ke gamuwa da nata rabon.
Karfe tara mun gama shiri adaidai lokacin da yan tawagan kawo amarya sukazo da guda da shewa da komai suka kewaya suna ganin gida komai masha Allah suke fada.
Nan kuma aka fara kwasan mutane zuwa wajen event din taro yayi taro duk wani mai danjin kansa shine yaje wajen nan don ba karanin cika akayi wajen ba mota har ba inda za a faka saboda cika .
Wasu sunzo suyi kallon karya wasu kuma suga waye matashin da sunanshi yai fice zai aura yar gari kuma ba,a santa ba tallan ma danayi masu yasa angoge komai bashi a yanzu balle a nuna wani ya ganeni sai goma saura nuka shigo wajen.
Mun dan jima kafin a samu hanyar da zamu shiga zuwa cikin wurin tunda ya kalla sau daya naji daga gefena yace hummm ban kara jin yace wani abu ba kuma.
Abbas yazo yana fadin kunna masu AC Hamza kada zafi ya damesu don Allah mai wancan motar ne yayi wrong packing a haya sai kuma ya juya ya tafi wajen motar ba,a dade ba sai gashi ya dawo yana fadin.
Wai ashe motar dan iskan nan ne Teri shiya fakata haka da gangan a wajen yana wajen nan ne yace har sokoto muke tare dashi ai baku gaisa bane muryan daba zan taba mantawa da itaba naji yana fadin.
Wani dan iska yasa ai cigiyata a cikin taro da gangan na aje motar nan a nan ya za a sace min budurwa ace kuma ba zanyi fushi ko kadan ba mai hali baya barin halin sa.
Da kowa sai yayi wanan zolayar tashi ashe bankai karshen tunanena ba naji yana fadin ashe da gaske ne zazzagawa sun iya kwacen mata don nikan an min kwace wallahi.
Ya zagayo gefen Bashir din yana fadin ka nuna min kai gifted ne har ka dauke min kawata banda ko labari saidai nagani haka gatsau kanwar tawace kawarka ya kwashe da dariya yace.
Kun dai min wayau wallahi Abbas yace inka isa kaje ka fadi haka a gaban Basma mana matsoracin mata kawai an fadama kowa irinkane me tsoron mace ?
Sun dai gama rahansu ya wuce yabada umurnin a jaye motar a daidai lokacin naji muryan shi a bazata yana fadin kinsan Muhammad ne dama shiru nayi ban iya bashi amsa ba sai wanda ke jan motar yace wanan dan iskan baka san halinsa bane wai ?
Mun shiga nan kowa ya bazo ido yana sauke muna kayan mu sky color ce mai dan konewa nasa shadace ba sai an fada ba inda nawa tsararen lace ne dayasha jinin ko wata mace a wajen.
An fara program a cikin dadi inda Yusuf yabada dan takaitattacen labarin ango maryam kuma tabada na amarya a takaice aka fara shagali ka,in dana in wajen.
Inda nagodewa Allah basu kiramu a fili ba sai wasu ake ta kira suna cashewa can sai mai sanarwa yake fadin anason ango da amarya su sauko a fili.
Shiya rike min hannu muka sauko tsakiyan fili tunda naji kida nasan uwayenane tafe aiko bankai ba na hango hjy Battula ta ashi mic din ta fara jero zance kida aka saka sosai suna fitowa harda mmazansu ashe da mazanjensu da sukazo wajen.
Gaskiya sun kayatar an kuma sha kallon budiri anyi barin kudin waje mai tsadan gani labari yakai ko ina ya bazu wajen abokai da yan uwa don sun zuba kudi bana wasa ba kamar yadda abokansa sukai masa kara dangi kuma sai kalilan ne suka fito sukai nasu bajintar iyayyensa maza na dolesa.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
9?? 3??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Buki bidiri birede anyi buki an bar tarihi da record aciki da waje karfe daya saura muna zaune naji ya kira Abbas a waya yana fadin kazo ka kaini gida don Allah kasan bana tsayi haka har wanan lokacin a waje.
Banji me Abbas din yace ba can sai gashi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login