Showing 279001 words to 282000 words out of 347556 words

Chapter 94 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8739

dai gashi kowa da kalar nasa don wasu sunce set din zinaren ta idan an sayar zaikai na miliyoyin kudi ba kadan ba gaskiya.
Kai ance ance ne kawai fa hjy Naja,atu tayi masa sayayyan a Dubai fa ta kuma fada min ko nawa ya bata ta kashe mai ta dauki kashin miyan ta fara tsotsonshi don dabiantane tsotson kashi dama tana gwigwiya haka take tana son miya mai kashi a rayuwanta ita.
Ummu anya ba Fatima bace Bros Bashir zai aure furrrrrr ta furzo kashin data tara a baki tana gwigwiya tare da kallo inda dan nata yake cikin alaman tambaya sauran dake falon suka tsura masu idanu cikin rashin fahinta abindake faruwa lokacin.
Al,amin kanka daya kuwa Bashir fa ya auri Fatima kace wanan shirin bukin da akeyi haka kaidai kowama zai aura ai zamuji dai tunda munzo amma ai ruwa ba sa,an kwando bane.
Wallahi Ummu abinda nake gani ke nan itace zai aura amma bari mu gani dai yadda kikace don naga motoci a gidan su Fatima din daga wasu state sunzo .
Shiru tayi bata bashi amsa ba don haushi sai zuwa can take fadin ita Fatiman batayi auren bane har yanzu ta tsure shi da ido tana son amsa daga bakinshi.
Ya dago yana fadin ba,ayi ba ya bata amsa yanzu dai ake bukin nata don daga gidansu nake na tambaya akace bukinta akeyi a gidan wai wata fatimace kanwar nata daya ta tambaya.
Shirmen Al,aminne kawai wanan fa ance a sokoto za a daura aurenta Family din sarkin musulmine ita wanan kuma da yake zance diyar wani tallakane a nan Unguwar.
To koni dai haka naji ana fada Fatimace sunan matar nasa wace ta kare nan A B U zaria bara sun gama service ke nan dasu Zahara don sun san yarinyar suma suna mamaki da sukaji.
Amma sunce yarinyar gaskiya ba laifi tana da kyau ga kuma kokari ba zakace ma diyar tallaka bace idan ka ganta komai nata tsab take da ita.
Lokacin hjy Ummu taji wani abu kardai zancen nan ya zamu gaskiya ace Fatima dince da gaske zata auri bashir in ko hakane gaskiya da itace tayi saki na dafe ga yarinyar nan.
To shike nan ma zancen gardama ya kare ga photonsu na free weeding pict ta dora a kai yanzun nan ta dorashi a dp nata tabbas itace ya fada yana dagowa daga inda yake zaune don ya kawo mata wayan ta duba ta gani.
Dam dam dam gabanta ya buga lokaci guda kafin ya iso garesu ta mike wayan ya mika mata ta dauka kallo daya tayiwa photon da sauri ta kawar da kai lokaci daya huduban hjy Laila akan Fatiman ya fado mata a rai.
Inda take fadin kina da sakaci hjy ta ya irin wanan yarinyar zaki daukota ki saka a cikin iyalinki irin wanan yaran basu da wuyan sace zuciyan namiji lokaci guda don ko mijinki kada kiyi mamaki idan yace yana sonta wata rana.
Wanan maganan ya dagawa ummu hankali har yakai tana jin kiyayyan Fatima sosai a zuciyata daya jawo sanadin rabuwarta da yarinya mai sanin ya kamata da kokari da kawar da kai amma ta dauki tsanan duniya ta dora mata ta yadda har bata son ganinta a gabanta.
Yau sai gashi Allah yaiwa wanan yarinyar gata ya bata miji irin Bashir mijin da tasan duk abinda suke fada akansa kakene irin na kishin kiyayya ga juna da sukeyiwa mahaifiyarshi har ya shafeshi.
Shiru tayi duk zancen da akeyi a falon bata tsinka masu ba sai sauraran kowa take rabi da rabi don zuciyarta ta lula tunanen abinda bata taba zato ko tsanmaninsa ba akan fatima din.
Mikewa tayi zuwa dakinta sauran sin fahinci akwai matsala yasa basu matsa mata ba lokacin sai hiransu sukeyi a wajen hankalinsu kwance saidai suna dan tunane hakan kasan zuciyarsu.
Waya ta jawo ta danna kira ana dauka hjy laila bata jira mai Ummu zata fadaba take fadin kin ganmu nan yanzu muke shigowa ko airport bamu bari ba muna lagos.
Shegen yaro yasamu tasowa ba shiri waishi bukin aure ko ranan daurin auren ne sai mu bata shirin ba wani jan aiki bane wajen mu kin sani duk da wana karon da alama suna da tsauri mutanen ba masu saukin kai bane.
Hjy Laila wai kinsan wa zai aura kuwa tace ina zan sani ina Jamaica zaune zamana kazo bakazo a sakaka a bakin duniya ehh zamuzo din amma don abu biyu.
Tsuki Ummu taja kafin tace wai ina baki kina roko wai kinsan yarinyar nab tawa bashir zai aura ashe wata yarinya kike nufi hjy maryam ?
Yarinyar nan dai tawa da kika sama a gidana saudiya kika gargadeni da ita tun lokacin na matse na rabu da ita tunda ta dawo ban kara kulla ta kanta sai yau nake gani wai ashe itace Bashir din zai aura ashe.
Ehh ehh na gane wanan shone girl din danayi warning dinki a kanta ko ummu din ta amsa da ehh ita fa ashe kin tuno da ita ke nan kwarai kuwa sosai ma natuna aiko don abincinta.
To itace wai Bashir zai aura ashe da sauri tace kiwa Allah ki bari ta sake fadin wallahi ga photo aure yanzu suka sake kiji dan iska da yaki sakewa sai yanzu da abu ya kankama.
Dagowa tayi tana kallon Al,amin din da yashigo yana miko mata waya har bataji abinda abokiyar hiran nata ke fadi ba a lokacin sai hawan Al,amin din da tayi da fada.
Ya zaka shigo min daki haka kai tsaye babu sallama yace haba Ummu sallamata biyu fa kina magana baki jini ba ya mika mata wayan ya juya rai bace don kusan yaji kalaminta na karshe akan Fatima din.
Ke nan zarginsu ya zama gaskiya kan mahaifiyar tasu watace ta zugata kan yarinyar nan ke nan wanda ummu din batayiwa kanta da yarinyar adalci ba gsskiya.
Meye laifin Fatima garesu ya tabbatar ko rantsuwa yayi baya kaffara da cewa Fatima bata aikata mata wani abinda ba daidai ba tsakaninsu.
Daki ya nufa ya bai koma falon wajen bakin nasu ba shima yashige daki yana jin bacin ran nasa yana karuwa don a lokacin guda yake jin hakan gaba daya rasa ya baci masa.
Mun kwasa harni zuwa wana gidan munsha mamaki sosai gidane mai kyau ginan zamani gidan da aka jima anayinsa akazo akace maishi ya mutu lokacin gida biyune tsakanin mu da wanan gidan .
Daga baya aka sayarwa wani shi kuma bai tare ba kuma ba,asaka kowa ciki ba sai wani dansanda daya zauna baifi shekara biyu ba kuma aka rufe gidan ashe angyarashi haka har yafi da kyau sosai shine zamu sauke bakin na gashuwa a ciki da duk wani wanda yazo donni.
Matan su yaya suka kama daki daya muka ajewa su Ammi daki daya sai daya yan mata da yara da akazo dasu a ciki wasu biyu kuma aka barwa maza.
Kowani daki akwai gado da katifa akwai kitchen da gas cooker a hade akwai ruwa available a gidan baida wani matsalan komai.
Ban tsaya ba ganin sun samu masauki muka dawo nida hassana da Fadila gida sun fada min Ammi tace kar nayi kumahi ko wani gyara kai duk saita iso za ayisu .
Mun koma ba a fi minti goma ba mukaji ana masu sannu da zuwa wai motocinsu sun iso mota biyu mayan jeep masu kyau da daukan hankali suka tsaya kofan gidan namu.
Ammi ce a gaba suna bayanta dukkansu nade a cikin lafaya irin nasu keda gani kinsan ba kananan lafaya bane wanan don sunci kudinsu ko a idanu.
Fadila data dauki cup zata debo ruwa tace hayya Ammi yasa hankalinmu ya koma kofan don jin sunan Ammi din data ambata aiko sune tafe daganinsu kaga Larabawa sosai dan banbancinsu kadan dasu don su bakakwne masu shige da shuwa haka.
Kamshi ko ba,a maganarsa don lokaci guda gidan namu ya kaure da kamshin su na daban dake bada ma,ana zaka san cewa su din gaga Arabia suke.
Gida ya kaure da murnan ganin Ammi don zuwanta anyi rabuwar lafiya da kowa a gidan sunkai su goma fa gaskiya idan ba karya nakeyi ba da gudu na fito dagani sai wani dan dogon wando da t,shirt a jikina kaina yana daure da ribon na rugume Ammi din.
Sai kuka bayana take dan bubugawa kafin naji muryan mama uwa sarkin kwakwa tana fadin wai Nuratune don Allah ko kamace hakan ya jawo hankalin kowa zuwa ga wace take kallon tana kira Nuratu.
Itace Ammi taba da amsa jin hakan yasa na dago daga jikinta hawaye shabe shebe a fuskana ina kallon wace aka kira da mahaifiyata din a lokacin .
Wallahi Nuratuce kuwa su gwaggo ke fadi tana salati tare da tafa hannu take su hjy laraba suka karba Nuratu Nuratu suna rungume juna a dago a sake rungume juna ana murna.
Yare wata garsaka doguwar mace mai kyau ga kitso ta dan sako gaba kadan tayi yasa naji Ammi tace hayyah ku basu wuri su zauna sun gaji sosai wallahi.
Da sauri mama uwa ta kwashesu zuwa dakinta har lokacin ina rike a hannun Ammi nan falo suka zazauna banda mahaifiyata din dakw gaisawa da matan unguwa da suka cika gida don kara a kaina saboda zaman mutunci dani da mukeyi dasu din.
Don inada wata akida duk da nake yarinya ina da kula don da wuya dan takin unguwarmu dai kasamu wanda ban shaku dashi ba ko ciwo ko haihuwa ko wani abu ya samu mace sai na leka kuma in samu dan abinda nabada kafin in fito.
Wanan yaja min farin jini sosai a mutanen shiyan namu hakan yasa suka taru don su ramawa kura aniyarta ranan a wajen bukina kuma aiki sukeyi sosai duk mama uwa ta aika masu da alawa na gaiyata din ita take tsaye da mama Lanto ga sha,anin ba laifi ko kadan gaskiya garesu don sun jajirce yadda ya dace.
Nan kallo ya koma sama don Nuratu ta shiga daki tabar matan unguwa da mamaki a kanta abinci na alfarma mai kyau aka gabatar masu yayinda wasunsu ke sallan dake kansu wasu kuma sun kwanta a kasa sun mike don gajiya.
Har lokacin ina jikin Ammi din don ban kara kallon mahaifiyan tawa ba saidai mukan hada ido lokaci lokaci muna satan kallon juna dani da ita amma ba wanda yaiwa juna magana cikin mu baya da gaisuwan dana bisu nayi dasu daya bayan daya bayan sun huta din.
Rashin zuwansu Ammi da wuri yasa ba,a fara min gyaran jiki ba sai wajajen yamma haka mai kitso nayi mai turare na turara min jiki haka dai suka sakani tsakiya suna canza min halita irin na al,adansu.
Tun wanan lokacin banda lokacin kaina saina bar kawayena nake tare da wa yan nan matan masu gyaran jiki din kamshi kan tun kaina na daukan zafi saboda ban saba ba har ya daina jin komai.
Sai dare sosai suka gama min gyara a nan dakin mama Uwa din dole na kwana na barwa yan mata kawayena da sukazo dasu hassana dakina suka kwa ni kuma na kwanta a nan dakin ranan.
Su Ammi sun koma masauki a can gidan suka sauka suma don basu yarda ko kayansu an,sauke masu a gidan mu ba shiko gulma kuma mutane sun rasa ma wanda zasu kama a gidan mu.
Sai tarihin rayuwan gidan mune ya dawo baya a ranan da kuma mama da tafito da kyar ta tari su Ammi taga kuma Nuratu din data san a yanzu tayi mata nisa ta ko ina don irin yadda ta hango ban girma da daukakan da mutanen kaf suke mata zaka gane irace a gabansu da komai a yanzu.
Ranan kan gaskiya anyi kallon kallo a gidan mu suna kallonta tana kallonsu kowa yanawa juna kallon mamaki mama kan baki ya mutu murus sai bakin cikin zuciya.
Don ko sarkan wuyan mahaifiyata abin kallone don gulma ya koma a wajen matan unguwa balle mata ba,a iya samun tsegumi ba ko banza balle an samu din a yanzu .


ZAINAB IDRIS MAKAWA
KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
8?? 9??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Wurine babba don irin haka aka bude wajen ku kama kuyi event din da zakuyi ku gama ku tafi su kulle wajen su wanda a ranama ana samun shagali kusan biyu ukku a wajen don girmansa.
Wanan karon su kadai suka kama wanan wajen duka bangarorin da don ko wani program da sashen da za,ayi a cikin wajen yau ya kama ranan kamu don haka yan uwa da abokanan arziki na kowani bangare suke harta ansan ko wani aure bangare kusan shidda ke gudanar dashi mafi yawan aure haka ke kasancewa dama.
Bangaren dangin ango ta uwa ta uba da kuma shi kansa angon kansa da nasa gaiyan suma suna tayashi shagalinsa tare ake gudanarwa dasu.
Haka gefen amarya da nata bangarorin itama kamar na angon gefen uwa da uba da nata kawayen da abokan arzkin ta tare dasu ake gudanarwa.
Shima wanan bukin haka ake saka ranzuwanshi saidai duk cikan da wurin yayi zuwa dan lokaci sun gama fahintar amaryan ba dagin uwarta ai don uwarta ta barta ta tafi har yau bata waiwaiyeta ba yan gulma sun yada wanan labarin ko.
An cika sosai an cika makil a wajen cikan zuwan amarya kawai ake jira wanda a wajen wasu na jirane suga matar da Bashir dinsu zai aura haka.
Inda wasu kuma kallon kallo irin na taron buki ya kaqosu don kawai su nunawa mutane sudin ne sun isa kafarsu yakama kasa dakyau
Inda wasu kuma suna son suga ya abin zai kasancene wai don ance yarinyar yar tallakawane futus wanan yasa ma ta yarda ta aureshi hakanan yadda yake don yayiwa mutane rufa rufa saboda ya batarwa mutane lissafi a kansa na kin aure..
Shigowan hamshakan mata su hjy Laila dasu hjy Maryam su Batula su hjy hanne nan kallo ya koma wajensu kuma sai gulman su ana bayani kan kowa sun samu waje sun hakkince sun shigo da tasu kalan iskancin din basu san girma ya kamasu ba.
DJ yayi sanarwa cewa iyayyen ango sun iso zasu shigo yanzu aka saka masu wakar wani mawakin yarbawa suna rawan iskanci har zuwa inda aka tanada masu wurin zaman su.
Sai yatsune yatsunem fuska ko wace keyi kamar suna jin warin mutanen waje a lokocin kowa sai tafiyan takama takeyi cikinsu har suka kai gefen da zasu zauna suka nuna dayan gefen da aka rubutawa uwayen amarya wai can sukeso amma masu shirya wajen sukace haka tsarinsu yake a wajen dole sukai shiru.
Har mukarrabansu sundan fara fisge fisge saida wata a cikin su tayi masu bayanin haka tsarin wajen nan yake hjy Batula taja tsuki tace kuzo mu zauna hakana meye a ciki tunda yanzu zamu tafi.
Sanar da shigowan armarya tare da iyayyenta tunda tarone na mata zallah a ranan hankalin kowa ya koma ka amarya suga kwamacallah gidan mu da yadda za a kare damu din a wajen don sun daukemu abin dariya.
Ni kaina a ranan jin kaina nakeyi tankar bani bace don har banson kallon madubi a lokacin komai na al,adansu sukai min tundaga kumshi har kitso.
Gani an lailaiyeni cikin lafaya abinda ban taba sakawa ba a jikina nikan har ban san yardama zanyi ba a lokacin haka dai nake binsu kawai a wajen.
Mota har bakin inda kowa ke ganin mu ta faka kowa ya kurawa motar idanu na dan lokaci kafin kawayena suka fara dirowa sukazo suka jeru kamar yadda akeyi a event.
Gudan da Ammi khadija ta karbi speaker tayine ya dan firgita wasu don tabbas ba gudan muna nan da aka saba ji bane wanan harshen larabawane sak ke sake gudan shi yasa hankalin kowa ya koma gunda suke jin yana fita din mata sai daga wuya sukeyi a wajen.
Sannu a hankali wani busa ya fara fitowa wanda yaja hankalinsu Ummu da sauran tawagansu da suka san wanan busan a baya kuma suka san a ina akeyinsa nan dan magana kasa kasa ya tashi a tsakaninsu.
Lokacin ne me gudan ta fito fili lailaiye a cikin lafaya dinta ta fara magana a cikin yarensu tana nuna inda muke tafe din guda yafi wakan tashi nan kowa ya zubo muna idanu yana kallon ikon Allah.
Don ba wanda ya zaci abinda yake gani a filin hakama shigarsu yaja hankalin kowa don ansan ba kwakwayon hakan sukayi ba dabiansune.
Wakane ya sauya zuwa na Ali jita inda


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login