Showing 99001 words to 102000 words out of 347556 words

Chapter 34 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8748

Yana fadin hakan ya lumshe idanunsa yana tuno da wasu abubuwan da suka faru dashi a bayan kafin ya koma turai lokacin da yake karatun jami,a a nan zarian


ZAINAB IDRIS MAKAWA


KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
3?? 0??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Nidai na fito daga ajin naga ko ina nabi ana bina da kallo sai kuma na nasa hakan kamar tsarguwane danayi nake ganin hakan gareni.
Innuwa na samu na zauna kasancewa ba sallah nakeyi ba a lokacin daga bayana naji an min sallama na juyo don inga maishi wata yar jiji da kaice kemin sallaman tana fadin barka da hutawa yar uwa.
Nasanta farin sani don ko bamu magana muna yawan haduwa amma girman kai bai bari ta gaida ko don haka kowa yasanta duk fadin school din nan saboda ajinta da class.
Tace dani kece Fatima ko na kallota da mamakin inda tasan sunana tana tare da wasu da shigansu zai nunama kosu wayesu.
Eh nice na bata amsa don Allah idan ba damuwa zanso nasan inda kika san Bashir Sa,id ko koma kema yar uwarsace don naji ance kema daga kaduna kike ?
Kallon mamaki nake mata kafin inyi magana mukaji muryan wani yana fadin eh mungata wanan yasa muka juya muna kallonshi.
Ok gata zamuzo tare yanzu Miss Fatima kina da sako daga Mr Sa,id office ko kina da lokaci ki biyo mu na dan juya na kalli yan matan nan nace excuse me don Allah tsaye sukayi suna bina da kallo.
Office din H,O,D muka nufa da mutumin dayazo kirana din naji dayan yace compound yar uwarsace kuwa ga zahiri munji.
A zaune na samu wasu mutum biyu idan ba idona yake min gizo ba wanan mutumin daya miko min waya dazun ne ya dawo a yanzu na fara gaida h,o,d din na juyo garesu muka gaisa .
Hjy Fatima wanan daga Digital global suke sunzo nan don su ganekine kan abinda ya faru dazun dake da safe sunzo a bisa umurnin ogansu da kiyi hakkuri kan wayanki daya samu matsala ta dalilinshi.
Ni fatima na fada a zuciyanata amma a fili cewa nayi ai ba komai sir asalima nice mai laifin ai nida hankalina ya dauku don Allah suyi hakkuri sir kuskure aka samu.
No kada ki damu ga wanan maigida yace a baki kiyi hakkuri don Allah baki na bude kana na dafe da sauri na juya na kalli malam da yau araha yake a gabana ba wani kame kame wajen ganinshi gareni.
Ido ya kada alaman in karba don haka na mika hannaye guda biyu ina karban abinda ke cikin wani
dan jakka mai kyau da yake miko min irin na kasan waje wanda a lokacin ban san komeye a cikinsa.
Sai wani irin faduwa da gabana yake min lokacin guda haka na mika hannu na karbi jakkar ina kara masa godiya kaina yana duke kasa lokacin kuma suke kus kus da junan su ganin hakan cikin yar murya nace ko zan iya tafiya sir ?
Jeki yau kan kin fito a sa,a HOD ya fada da dan murmushi a fuskanshi mutumin da ake fadin bai da sauki ko kadan sai gashini har da murmushi yana min murmushi yau har da yar ba,a.
Na juya a sanyaye ina daga kafa da kyat naji mutumin yana fadin zata iya ai mu gwadata mu gani idan zata iya hakan gabana naji ya fadi amma haka na dake na fita daga office don.
Dan tsayawa naja nayi ina tunane kafin na yanke shawaran komawa gida kawai a lokacin don haka na nufi hanya gadan gadan don fita daga cikin haraban makarantan.
Ina zuwa wurin masu abin hawa na samu na hau tare da fada mai unguwar da zai kaini yace min dubu daya tunda ni kadaice haka nace muje kawai ni dai burina na fice daga makarantar a lokacin.
Gidan shiru na tura kofan dakin mu nasa key na bude na shiga na mayar na rufe har lokacin gabana yana faduwa dan jakar kwalin na aje a gefena na dauki buta na kewaya.
Bayan na dawone na zauna na bude jakar ina zaro abinda ke ciki kwalin Laptop din na fara jawowa baki mai kyau dashi company Apple don ga tambarinsu nan baro baro a sama.
Ban tsaya budewa ba na tura hannu na jawo dayan kwalin shima da nasa tambarin iri daya da dayan kwalin da sauri na bude wayace sabuwa dal kiran IPhone.
Das das das gabana keyi ni kadai a daki saida na sake dan ihu lokaci guda haka na tasa kayan a gaba ina kallo kafin can na mike ina cire kayan jikina lokaci guda tare da mamakin wanan irin kyauta na bajinta dayazo min lokaci guda haka.
Ni wacece mena taka har ya jawo min wanan nasaran a cikin rayuwata akalla da ace saya zanyi a shago zancen daruruwane a nan da ba a maganan su gareni anya kuwa zan iya rikesu na tambayi kaina ?
Zaki iya mana wata zuciya ta fada min me zan fadawa mutane kan hakan ban san mutum ba ban taba ganinsa ba amma sun min kyauta haka na gwadawa a jarida.
Zancen yan matan nan ne ya fado min a rai nace aiga irinta tun ba aje ko ina ba na fara samun challenge kan hakan ni sai lokacin ma na tuno da wanda suke tambayana a kai lokacin.
Sunan da yarinyar ta fada nake kokarin tunowa na samu da kyar na tuna ina maimaita sunan a fili zancen a gwadata din da suka fada ya fado min me zan iya suke nufi ?
Kodai irin wa yan nan mutanen ne masu amfani da daman mutum su yaudareshi su bata mashi rayuwa ni kadai a dakin nake ta faman fassara kalman na kasa gano manufar hakan.
Kayan na zubawa ido a karshe na yanke shawarsn ajesu har sai abinda hali yayi kwance nakai ni kadai a daki ina faman tunane har Samira ta shigo naji suna gaisawa sama sama da gwaggon mu take fasin Bantu bata dawo bane ?
Gwaggo tace anya banga shigowan ta ba son tun dazun ina wajen nan tana tura kofan ta jishi a bude nan ta hangoni kwamce ta juya tana fadin tana nan ciki kwance ai gwaggo.
Ikon Allah yaushe ta shigo gidan nan ban sani ba don tun dana rarage sallah ina wajen nan dakin ta shigo tana fadin ashe kin dawone ke ?
Na dawo na fada ba tare da dagowa ba don dan zazabi zazzani nake ji kamar yana son kamani lokacin tana aje jakanta ta jiyo da nufin magana idonta ya sauka a kayan.
What ta fada me kuma kika samu a nan din soja yazo ke nan tana kallona cikon mamaki wani soja kuma don Allah ki barni waya kawo wana kayan kuma ?
Takai zaune tana mika hannu ta dauko tare da fadin wai meye a cikin nan din ki kalla wanan kawar tawa ta ajin mune ta ban ajiyansu har muka fito ban ganta ba na wuto dashi dama tace in wuto mata dashi gidane.
Kallon irin ban yarda din nan tayi min taci gaba da kallon kayan nace zatazo aiko gani hakan ne ya rabamu karshe ta fita tana fita gidan na dauka nakaiwa gwaggo ta boye watace taban ajiyansu.
Hakan yasa na samu saukin tambayan samira don tana dawowa take tambayan ina suke nace tazo da mijinta ta karba ai sai ta share zancen.
Da dare baba da kansa ya kira yana muna ya karatu bayan mun gama gaisawane yake fadin Fadimatu ko da gaskene kinyi fushi da gida ?
Da sauri nace a,a baba ba hakana bane idan mun hada muna nan tafe to kizo gida, ko kowa baison ganinki ai ni ina raye ina son ganin ki fadimatu .
Jikinane ya mutu nace baba ina nan zuwa insha Allahu muka gama magana na sauke ajiyan zuciya lokaci guda ina bin yar dakilar wayata da sai ka duba dakyau zaka gane rubutu saboda tarwatsewa a lokacin.
Washegari haka na shiga makarantar kamar munafuka sai dai kallon ranan yafi tsananta gareni don har nunani sukeyi wasu na samu na shige department din mu
Idone a kaina caaaa na rasa me mutane suke nufi a kaina malami ya shigo bayan mun gama daukan darasi kafin wani ya shigone wanan kawartawa yar kabilan tibi tazo tana fadin.
Fatima how lucky u are ashe kin hadu da wanan guy din egent na company iPhone jiya har kunyi magana ashe dama kinsan dashi ke nan baki taba nuna hakan ba.
Jiya duk maganan da akeyi ke nan kin hadu dashi kunyi magana ance guy din yana da tsadan gani da wuyan sha,ani sosai dama kunsan juna dashi ashe ?
Eh kawai nace mata na fuske a raina ko tambayan kaina nakeyi dama egent ne shi ashe amma zanyi bincike a kai in gano ko waye.
Ko fita banyi ba na zauna a bina aji dama sallah ke yawan fitar dani gashi ina fashin sallah don haka na share a cikin aji duk da rashin karyawan da banyi ba kuwa.
Haka rayuwa ya shude ban samu zuwa gida ba ni kan sai bayan da muka gama jerabawan mu da sati daya na nufi kaduna ban dauki komai ba a lokacin don banje da niyar zama ba dama.
Tun sallamana a gidan yanayin da aka amsa min sallaman nawa nagane akwai wata a kasa gashi na samu mama uwa ta fita unguwa ga kuma hadari ka,in dana,in ya hade gari.
Amma haka na daure na gyara dakina don nasamu dakin Nura ya batashi duk da yana dan gyara irin nasu na maza iya gaban dakin makewayin ko zarninsa bai bari mutum ya zauna a dakin.
Na wanke tas na saka turare nayi mopping din tsakar dakin sanan na iya zama a cikinsa haka mama ta dawo cikin ruwan tsamo tsamo saida ta gyara ta shigo ta sameni a kwance tana fadin yanzu yara ke fada min kinzo ashe ?
Muka gaisa take fadin barin fita in samu abinda zamuci don yanzu gidan nan in malam baida hali saidai kowa yayi dabaransa nace ruwa yayi yawa mama ki bari idan an hada mu sayo bread da shayi kowa yaci ya kwanta.
Ko kuma taliyar hausa nan gidan mai taliya yafi saukin dahuwa shayi kan ai bintu kudin zaiyi yawa gaskiya na gane ita din dai suke so don haka na bada dubu daya suka sayo ina daki aka kawo min nawa kason .
A cikin ruwan nan daya dawo baba ya dawo da dan cefanensa haka na fita naje na gaidashi da dawowa yana jin muryana ya fadada fara,anshi yana fadin Fadimatu badai ruwan nan kika biyo ba kema ?
A,a baba tun kan ruwa ya sauko na iso to to madallah ya jerabawan kuma ita samira ta dawo tace ku baku hada ba ashe karatun naku ba iri daya bane danasu ?
Ance nata yafi wuya ko to Allah dai ya taimaka murmushi nayi a raina nace wata sabuwa kuma kona tsaya bayani baba ba ganewa zaiyi ba don haka bayanin baida amfani a yanzu.
Daki na koma na zauna naci taliyan kadan na dauki kwano na mayarwa mama a nan na zauna muna hira take fadin kaiya Bintu banji dadin da kika iso bani gidan nan ba wallahi.
Don nasan yaya da yarata marasa mutunci zasu hattareki don yadda suke fadi idan kin dawo zasu maki ba gaskiya bane abin ga mai saurare.
Gashiko gaisawa kawai mukayi basuce min komai ba saboda Allah nace kwarai amma mutanen nan sukai munafukai na bugawa ko samira kinganta munafukace ta bugawa itama.
Don duk abinda kukayi a can dasu saita bugo waya ta shedawa uwarta karya da gaskiya harda cewa tayi yanzu ko karatun baki tsayawa sosai kiyi sojoji ke kwasan ki a mota baku can baku nan dasu.
Allah nagodema idan uwar ta gane rayuwanta ta fada mata itace mai wanan halin mama ni nasan abinda nakeyi Allahne sheda dasu gwaggoce da muke zama a wajan su .
Tace yanzu kan idon ki ya bude sosai da maza ashe dama duk munafuncine rashin samun wajene yasa kike nuna keta Allahce a gaban idon mu ashe.
Dan dariya na kwashe dashi kadan nace aniya makomiya inji hausawa insha Allahu mama basu ganin wanan gareni saidai a cikin diyansu.
Ni zancen ya Mahmoud da suke magana tun farko baiga fuskan hakan ba ga bukatanshi don haka ko ya bugo waya ban dauka haka kuma ko massagen ya rubuto ban amsa mashi.
Aiko yana garin nan don ace zai bude gidan mai suna aikin budawa shida yan uwanshi ganin yayi arziki haka yanzu wanab ne ya haukata yaya a yanzu harta manta da cewan datayi da jinin yarta daya bayar yanzu arzikinshi ke bunkasa.
Ke bari muna ji muna kuma kallon drama a gidan nan haka Altine ke shigowa su karaci haukan su wai suna sake min habaici don na fada maki.
Mama kibar kulasu don Allah nifa basune a gabana ba yanzu ni hanyar da zan bi inga karatuna ya tafi daidai in gina rayuwata shine burina kawai.
Ubangiji Allah ya cika maki burin ki na Alheri fatima Allah yasa a gano inda mahaifiyarki take kuci arzikin tare da ita na amsa da amin idanuwana suna ciko da hawaye.
Ban kara magana ba don tuno min da abinda yake damun rayuwata na mahaifiyata da mama uwa tayi a lokacin.
Don wani lokacin nakanyi tunane ince wani irin zuciyane da mahaifiyata da zata tafi ko jiyowa taga halinda nake ciki bata taba yi ba haka ?
Ranan haka na kwana da wanan tunanen don haka ban samu barci sosai ba saida safe bayan nayi sallah na rama barcin nawa har baba ya leko mu gaisa ya samu ina barci sosai ya fita.
Can cikin barcin dana samu mai dadi wajajen sha daya naji muryan Anty Altine tana fadin munafukace Allah dai ya tona mata asiri mama har kukaji da sai abu yayi nisa a sani ba yadda za ayi.
Yan matan jami,a da iya yaudaran kwatan maza waye baisan abinda ake koyowa a jami,an ba yanzu don ubanta ga Mahmoud nan taje ta aura inta isa ?
Jin wanan yasa na mike da sauri na fito wajen dagani sai riga da wandon barci mai kalar light blue sai kasan hannun da kasan wandon da akaiwa kwaliyan da dark blue din yadinsa kaina a banye yake na daure da ribbon na fito hakana nayi tsaye daga kofana ina saurarenta.
Ita kuma tabada baya tana fuskantar kofan mahaifiyarta inda uwar ke tsaye ta rike kyauren kofa suna zance mai kama da tsokana tunda sunsan ba wanda zai basu amsa suke abinda sukaga dama.
Ina jin wata daga cikin kannen dake zaune a kofa take mata signal da gani nan na fito fa jin hakan naji tace tafito mana tsoron Bantu kuma nakeyi munafukan banza da wofi kawai ita ta iya cin dadi ba dole yanzu ta nuna ita kanwar Safiya bace ya maida ita dakin safiya don bata da kunya wani irin sherine batayi masu ba a baya.
Ba dai ni fatima ba Altine in zaki fadi abu ki tsaya ki fadi gaskiya kan abinda kika sani ni kananan maganganun naku kada ki jefani a cikinsa.
Waye Mahmoud da har zan tsaya bata lokacina akan mijin yar uwata ni bansan na samo nawa ba sai ragowa zan dauko ragowan ma na fanin ku.
Bankai lalacewan hakan ba din banga abin da zai rudeni har in fada halaka idona bude ba aje can gaba na fada mai kada ya raina min wayau ya mayar dani baya kan tafiyana.
Burina shine in nemo mayaifiyata da kuka kora ke da uwarki in dawo da ita gidan nan ta zauna a cikin ku yanzu inga uban da zai korata kuma ?
Ohh shegiya yar kunama lalai kin cika kARAN DAFI KIKE dama wanan ne burin ki akan mu nace yau din nan da kuke nuna min wariya na yanke hakan kuma insha Allahu sai hakan ya faru mu zuba daku mu gani.
Anty Altine tayo kaina tana fadin lalai yau zan nuna maki baki cika yar karuwa ba karuwancin da dandin uwarki karyane ita karuwa bata iya hauhuwan shedaniya ba.
A,a,a Altine kada ki tabata don Allah zancen nan dai gudane kullun sai ya tafi ya dawo yau dai kunji da kunnuwan ku yarinyar nan tace bada ita ba zancen hadin nan yau gashi har ankai ga inda ba,a son kai gidan nan.
Wanan irin tonon asirin fa haka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login