Showing 42001 words to 45000 words out of 347556 words

Chapter 15 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8813

muyi magana inji inda take fita kiyi hakkuri va zata sake hakan ba na mike zuwa dakin namu sai ga Samira din ta fito da bucket din wankan mu a hannunta.
Da alama wanka zata alokacin don haka nagusa mata ciki ciki ta kalleni tace ya mutanen gida nace duk sunce a gaidake sako na nan mama tabani na kawo maki ai ta tabe min baki ta nufi wurin randan ruwa tana diba.
Wanka tayi kodata dawo dakin ta samu har na kwanta a lokacin saidai banyi kallo ba ina karatune ni kaina ina mamakin yadda Allah ke ban sa,a ga karatuna duk da ban faye mayar da hankali yadda ya kamata ba amma kuma ina gane komai a ciki.
Mai ta shafa tayi shirin kwanciya kafin ta zauna a bakin katifa tare da jawo wanan ledan data shigo dashi din tana kokarin budewa.
Kamshine ya biyo hancina duk da hakan ban dago ba ko in kalleta naci gaba da abinda nakeyi ina jin yadda take yagan naman ta dauki kwalin five alive ta bude ta kwankwada ta aje a gabanta.
Bissimillah Bintu ki tashi muci nace mefa daga inda nake kwance din tace nama da drinks kwam kwam nace ta cikin bakina sai ta dan kalleni tana fadin ai na manta gida kikaje baki marmarin komai a yanzu ke.
Fadin hakan da tayi yasa na juyo ina fadin kedin dake marmarinsa a gida kikancine ko a gidan mu din an saba muna da cin namane da ruwan zakin kwali ?
Tofa malama abin ai bakai can ba in bakici kawai kice dani bakici ba sai kin fada min magana ba nace ba magana a cikin zancen nan Samira.
In zakiwa kanki fada kiyi don yanzu mutum ake kiyo ba dabba ba kina ganin don muna zama da tsufi basu fahintar komai a yanzu ko to gwaggoma kanta ta fara zargin wanan fitan daren da kikeyi.
Ke ko wani bai fada maki ba keba maiwa kanki fadane ba a yanzu don kawai bamu gaban iyayyen mu shine akace muzo nan don mu bata tarbiyan da iyayyen mu suka doramu akai.
Wata nawa mukeyi gida baba bai sawo muna nama ba anci sai kifin icce fish da ake watsa muna a miya mu tsoci gashi.
Kar ki manta alkawari muka daukarwa baba da mama cewa zamu kula da kan mi tankar muna gaban shi sai gashi tun yanzu kin fara wani dabi,an da bai dace ba dake.
Wai zargina kikeyi da bin maza kome Bintu nace idan ni ban zargeki ba ai duniya zata zargeki Samira tunda sunsan ba haka mukazo masu unguwa ba da farko.
Katseni tayi da fadin indai abin zai zama na zargi sai in koma hostel in zauna bashi ke nan ba ni ban sakawa mutum idoba ya sakamin ko so kike na mutu da yunwa a gidan nan ne ?
Abinci muka rasa a gidan ko a dakin nan idan ma ba a baki ba aizaki iya tashi ki dafa kici wa zai maki magana idan kinyi hakan tsuki naji taja tana fadin nasan abinyiwa kaina ai.
Ban daiyi magana ba na fada zurfin tunane don ba karamin badakala akayi da baba ba ya yarda muzo zarian karatu ba karshe ma da mukace muna wahalan zuwa da dawowa shine ya nema muna alfarma a gidan yar uwanshi mu zauna.
Washe gari mun tashi tunda safe kamar yadda muka saba nikan na dauki abin diban ruwa na shiga makwabtan su gwaggo wurin famfo na dinga debo ruwa na gama naga Samira batayi shara ba na dauki tsintsiya na share gidan tas.
Ruwa na diba na shiga wanka na fito na shiga dakin mu sai na samu Samira ta shirya tsan abinta har tana fesa turare a gyalen ta.
Ciki ciki ta juyo tana fadin ni zan tafi ke nan nace amma baki karya ba ai tace dani idan naje zan karya a school sakon mama din fa baki karba ba.
Ki barshi in mun dawo ki bani tana fadin hakan naga ta fita ba tare datace min komai ba na daiji muryanta a kofan gwaggo tana gayar dasu da kwana.
Na gama a gurguje na fito na gaida gwaggo din nace zamu tafi gwaggo din ta fito tana fadin ina ita yar uwan naki take kuma ta tafi naba gwaggo amsa.
Kallona tayi cikin mamaki kafin tace to Allah ya kyau yarinyar nan kuwa tana son zama abinda ta zama a gidan nan ana haka kuwa ?
KADUNA
Ya habibine tare da ya ibrahim sukai sallama a gidan mu safiyace matan gidan gaba dayansu suna tsakar gida suna aikinsu na safe.
Binsu da kallo sukayi suna amsa masu sallaman sai mama uwace tace wai mahmoud ne tafi sannunku da zuwa kallon mamaki kowa ke masa jin mama uwa ta ambaceshi yasa maman biyu fadawa daki tana jawo hijjab din ta ta sargama a wuyanta.
Dakin baba suka fara shiga suka gaisa dashi baba yake fadin Mahmoud kudu dai ya karbeka ke nan yaushe rabonka da garin nan balle nan gidan.
Ai shi mutuwa ba rabuwa bane koba zuri,a a tsakanin ka da Safiya akwai mutunci babba tsakanin mu da ku ayi hakkuri baba ya fada yana noke kai don kunyan da yaji din a lokacin baba yace hakkuri aiya zama dole musanman daku yaya.
To ance ka kara aure yaya ita iyalin naka take da wajen aikin naka munyi murna kwarai da gaske da jin wanan nasaran da kake samu yanzu a rayuwa.
Nagode baba ya fada nan dai suka taba hira dashi mai kama da nasiha kafin yace zai shiga su gaisa dasu mama ciki amma baba yaushe akayi wana gyaran haka ai wurin kamar ya matse a yanzu ?
Lalai ka dade rabonka da gidan nan saidai muji kazo ka tafi har na dauka ko wani abinne ya faru kuma aishi wanan tun shekaran da matarka ta rasu Fadimatu ta dawo hannuna aka maida wurin nan haka da kake gani.
Ikon Allah lalai na dade rabona da nan din yanzu ina ita bintu din takene baba jin hakan baba ya dan murmusa yace suna zaria suna karatu a jami,a dama shine burin fadimatu kuma ta samu.
Yace ikon Allah yanzu Bantu har takai shiga jami,a to Allah ya bada sa,a yasa a fito da kwali mai kyau suka amsa da amin zai tashine ya ajewa baba din kudi yana fadin ayi hakkuri din Allah donshi mai laifine garesu.
Sun shiga dakin mama sun gaisa inda a can su mama uwa suka sameshi suka gaisa dashi tare da masa murnan auren da yayi din a lokacin.
Ya dan zauna jin yana jin nauyin ita maman biyu din ita kuma tana masa kallon takaici da bacin rai to zamu koma mama ya fada yana aje mata kudi a gaban ta ya kara ciro wasu yana fadin wanan kuma abawasu mama su raba.
Bayan ya fito gidanne kowa ya shiga fadin albarkacin bakinsa ita dai mama cewa tayi in dai amana gaskiyace zai fita ai.
Gidansu suka shiga dakin mahaifinsa ya nufa don basu samu zama dashi ba jiya da dare daya shiga ya samu yasha magani zai kwanta.
Sun gaisa yayi shiru ba kamar yadda ya saba zuwa da iyalinshi ba a baya su zauna ana hira sosai da baba din har kowa.
Jin shirun da Alh din yayi yawa yasa Alh fadin an tono damune akazo ganin mu ko wani aikin ne kuma ya kawo ka nan arewa har kazo gida.
Jin hakan da sauri yace a,a nan dai gida nazo in ganku in koma don aiyuka basu bari nazone ko nayi niyar yin hakan .
Hakan ma ba laifi ai mun gode tunda ka tunamu a yanzu kasan aikin yanzu har hana zumuta yakewa bawa don neman duniya sai yasa mutum ya manta da kowa.
Ayi hakkuri Alh nasan nimai laifine hakan ba zai kara faruwaba insha Allahu a gafarce yace babu komai nidai nasan ko bakazo don mu ba aiya kamata kazo kodon yaran nan ko ?
Yayi shiru Alh ya mike yana fadin shi zai fita don zaije asibiti kafin ya wuce zuwa tasha inda yake zama har yanzu daya tsufa don sun zama sune shugabanni yanzu a wurin.
Baba amma ya kamata ace yanzu kana zama gida ka huta kuma hakan yasa Alh ya jiyo ya dan kalleshi tare da murmushi kafin yace idan na zauna su bayin Allah nan suci me mamuda.
Zan fita yaushene zaka koma din ina nan zanyi sati gudane a gida Allah ya taimaka mahaifin yace ya amsa da amin.
Daya fitone ya shigo dakin mahaifiyarsa nan ya zauna suna dan hira sama sama da ita kafin shigowan Usman ya kwasheshi suka fice gidan.


Ubangiji Allah yayiwa mama carofee sauki ya Allah ka saukaka mata laluran da take ciki ubangiji Allah kasa hakan kaffarane a gareta ita da sauran musulman duniya ga baki daya amin Allah ya baki lafiya mama carofee ki dawo cikin mu lafiya amin ya Allahu.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
1?? 3??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,

Mun dawo gida a gajiye na riga Samira dawowa gidan don haka na samu gwaggo tana girki tuwo takeyi zata hada talgi na jan masara surfafa don hakan jan masaran ya dan rage ja a idanu.
Daki na shiga bayan mun gaisa na kwabe kayan jikina na fito wurin aikin nata ganyen miya na samu tana gyara na ayoyo na karba nan da nan na gyara ta dauko gari zata tuka tuwo na karbe na tuka lumui.
Na kwashe a kwanoni gwaggo tana nuna min yadda zan zuba har muka gama komai tare ina gyara wurin ne Samira ta shigo wanda dawowanta ke nan a lokacin.
Da yar ledanta a hannunta ta gaidamu tsatsaye wai ita tana fushi ta shige daki kai tsaye bayan kallona na gwaggo tayi tana fadin yar nan da lafiyanta kuwa kalau take gwaggo gajiya dai ta debo.
Har mun gama na gyaran wajene na kawar da kayan aiki sai albarka gwaggo ke samin na shigo na sameta a kwance ledan dana dawo dashi na dauko na bude.
Sakon ta da mahaifiyarta ta bani na kawo mata na dan miko mata ina fadin gashi mama tace na kawo maki kiyi hakkuri da wanan .
Sai lokacin ta kallone shekeke tare da yatsune fuska tana fadin ajeshi nan don nasan ba wani abin kwarai zan samu a ciki ba nace ai tayi kokari don yanzun daminane cinikin komai ya kwanta a garin.
Nima kiran da Isah yayi min ke nan nazo mu bude ajiyan mu don lokacin fiddasu yayi Allah ya taimakeni ajiyan yayi kyau sosai don ba abinda ya tabasu.
Shine na saka wasu akasuwa na dibawasu mama wanda zasu juya abindai sai a hankali wallahi jin ta barni ni kadai ina magana yasa naja bakina nayi shiru.
Nama na fiddo na jawo wani roba na zuba na mike na fita dashi waje jin kamshin yasa ta kallo ledan da roban dana dauka din taga abindake kamshi a ciki.
Gwaggo nakaiwa ta dora saman abincinsu nace gwaggo na manta tun jiya dana dawo wanan wata makwabciyance da muke mutunci naji bata da lafiya na shiga shine ta debo min nazo dashi mu dinga amfani dashi donta dauka a school muke zama.
Ikon Allah har haka da yawa wanan wace irin matace kuwa nasan irin gidajen nan ne na manyan mutane duk da ai sune suka cika kaduna tallakawa kadanne saidai suma din akwaisu .
Ai wanan kan bana dora duka saman abinci ba saidai a dan tsankwara a ije sauran har wani lokacin kuma dakina juya na koma na fara cire ringan dana saka nayi aiki dashi.
Bucket din mu na amfani dama a dakin muke ajeshi shina dauka na fita na debi ruwa na watsa a jikina kana na fito nayi alwala na koma dakin don magariba da akafara kira a lokacin.
Bayan na idarne can naga Samira din ta mike ta fita ta dauki buta tayi alwala ta dawo wuri na bata ta gabatar da sallah can mutanen gidan suka fara dawowa daga wurin harkokinsu.
Dare yayi ke nan a lokacin duk wani mahaluki yana nufo gida wurin iyalinshi don cin abinci ko yadawo ke nan yabawa iyali nasu lokacin da hakkinsu haka al,adan maza yake na ko wani kabila.
Inka debe irin mazajen nan da sana,ansu shine na dare sune kadai baka samu a gida sai ko irin mazajen da sukasawa rayuwan su sharholiyar duniya.
Muryan dan gwaggo Nura ne naji yana tambayan gwaggo din da ina yan matanki naga dakin da duhu ko sun fara hiran darene wai hasken wayata na kunna don yasan muna ciki.
Gwaggo din dakewa mijinta shimfida tace ga alama nan yanzu sunna ma cewa suna jinka ai nan ya leko yana fadin yan makaranta ya karatun muka amsa da lafiya kalau Nura an dawo ya kasuwan yace kasuwa Alhamdullahi.
Aina dauka kuna waje wurin samarin kune don naga ita wanan ta fara fitan dare na gane da samira yakeyi don ko kai bata dago ta kalleshi ba tunda ya tsaya a wajen yana muna ba,a don duk cikin yayan gwaggon mu din shine mai yawan kula harkan mu donshi kamar sa,an mune a wajen haihuwa.
Jin hakan yasa ta dago mai kai tana fadin kai kan Nura namiji dakai da sa idon tsiya har da yaushe da yaushe kaga na fita din ni wallahi bani son yawan sa ido ga mutum nan sukaitayi da ita shi yana fada mata ba,a ita kuma ta mayar da abin kamar fada.
Can naji muryan uwar tana kiranshi kamar a hasale ya tafi dai yana muna sheri bayan tafiyanshine na kalleta nace gaskiya hakan baidace ba kina fada mashi magana kuma kinsan shi wasa yake maki.
Sai cewa tayi wai Bintu mekike daukan kakene dani ko kina tunanen kin girmenine ko don dan abinda baikai ya taka karanda kike dashiba kike ganin yanzu daidai kike da kowa ?
Da ace bamu san asalin ungulu ba dasai yace daga masar yake to ki kama kanki dani wallahi idan zaman baiyi tare aiba dole bane zama a wuri daya.
Hakane lalai ba dole amma ga wanda yaga ya matsu koda ace kinsan asalin nawa ba,adai canzawa tuwo suna don mahaifemun daya daku da kuke ganin wata tsiya kuke.
Haba yaran nan haba dai wanan abin baku kyautawa kanku ba kuwa kunzo garin nan dadi dadi kanku a hade amma yanzu kuna kokarin raba kawunan ku kuma muddin kukace haka zakuyi min zan kira mahaikun in sheda masa.
Gwaggo kiyi hakkuri don Allah na fada tace na lura da hakan tun safe gareku ba zan dauki wanan ba don kunsan ina da hawan jini a jikina hakkuri na kara bata ita kuma Samira din sai tsuki taja.
Ganin mu hakan kwana biyu gashi yanzu Samira ta tsiro sai dare sosai zata dawo gidan ta kwanta da gari ya waye kuma tafice abinta ta daina duk wani aikin taimako da mukewa gwaggon din a gida.
MAHMOUD
A takure yayi kwana biyar yace an kirashi zai koma fatakwal inda yake sukai sallama da yan gida ya tafi jirgi yabi don a yanzu bai iya tafiyan mota saida jirgi.
Kodaya isa ya dauki shatan taxi zuwa gidansa saidai yayi rashin sa,a matar nasa bata gida a waje ya zauna ga unguwar nasu sabon unguwane yakai awa uku wajen zaune sai tsuki yakeyi ga yunwa da yakeji kuma a lokacin.
Don haka ya juya yaje ya samu abinci yaci daga can ya wuce wurin abokinsa sun dade tare karfe shida ya dawo gida har lokacin bata dawo ba ranshi ya baci sosai a lokacin.
Baison kiran maman baby don yana son ya fahinci wani abu a gareta haka ya zauna a wullakance sai goma da wani abu yaga wata mota ta sauketa saida ta dade bata fito motan ba zuwa can ta fito kuma ta dade a tsaye suna magana.
Kafin motan ta wuce ita kuma ta nufo gidan kai tsaye ganin shi tayi bakin get a tsaye sai gabanta ya fadi dan juyawa tayi kamar me neman wani abu sai kuma ta juyo tana fadin dama honey yau zaka dawo baka sanar dani ba.
Wallahi gidansu ,,,,, hannu ya mika mata alaman ta bashi key ganin hakan ya hanata karasa fadin abinda tayi niyar fadi a lokacin ta shiga lalaben key din ta miko masa hannu na rawa.
Ya karba yasa ya bude gidan ya fara shiga dakin shi ya nufa kai tsaye ta biyoshi kodata biyoshi har ya shiga bandaki ya dade bai fito ba ganin hakan yasa ta juya itama.
Sauri tayi taje dakinta ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login