Showing 159001 words to 162000 words out of 347556 words

Chapter 54 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8806

yaji wanda zai dan kama ciki saidai ba mai yawa sosai ba don marmari kawai na hadashi shima saboda yana cikin abin karin hausawa a gida da safe.
Dakina na nufa don ina son yin wanka a lokacin bayan na fito na saka wani riga nawa dogo na atamfa dinkinshi mai kyau yana cikin tsaraban abuja dasu oga Abbas suka saya min zuwana Abuja na farko.
Salimace ta shigo ta samu na gama kitsa kaina dakin kuma a gyare shima sai kamshi yakeyi na turaren dana fesa din a jikina lokacin.
Bin dakin tayi da kallo ko ina tsab ta karaso tana murmushi take fadin kai Fatima kin huta wallahi ke sam na kulla da bakijin nauyin jikinki yanzu har kinyi wanka kin gyara daki haka ?
Murmushi nayi na dago ina kallonta nace nasaba da hakan ne inda na fara tashi ta koya min wanan dana falka tun asuba zan gama komai kafin gari yayi haske.
Gaskiya ta baki training kuma gashi har yanzun baki fasa hakan ba komai naki tsab yake ji dakin nan don Allah yadda kika gyarashi zuwan nan naki.
Meya dace mace tayi tun kan in fita fa dazun na gyara dakin nan aiki gun mace ba komai bane idan ban motsa jikina bama nakan ji ciwo nason kamani wani lokacin.
Kizo muje Ummu da Abbu suna falo mu gaisa ta fada hakan yasa muka jera zuwan falon don mu gaidasu tana gaba ina bayan ta muka fito falon suna zaune.
Hjy na gefe tana zuba dan wake a plate shi kuma Abbu din yana zauna ya mike kafa ga abincin da aka zuba mai a gabanshi yana yaci sai dan koko a cikin dan karamin kofi kadan daga gefenshi.
Ban karaso ba kamar yadda ita salima din taje gaf dasu ta zauna muka gaidasu da kwana suka amsa kusa lokaci guda hjy din ke fadin yau kan zamu tuna gida da kyau mamana sai ga dan wake haddade haka mun sama kinyi.
Ummu dani fa aka hadashi salima ta fada a,a ai ummah hani ta fada min tare kukai komai sai salima din tayi murmushi nuna jin dadi.
Wai ina Mohammed Abbu din ya fada yana aje kofin kokon dayake sha a gaban shi dan wake hjy takai bakinta ta tauna kafin tace dashi.
Cikin tabe baki wata kila yana dakinshi bai tashi ba lamarin Mohammad sai shi ta fada tana kara kai dan wake a bakinta lokaci guda.
Sai Abbu din ya kalli salima dake zaune yace salima jeki dakinshi kice dashi shi fa akw jira a nan da hanzari salima din ta mike zuwa part din maza gidan.
Dakin ta hango a rufe ta karasa tana kwankwasawa sai taji kofan dakin a budema yake ta tura ta shiga da sallama ta hangoshi kwance saman kujera yayi rigingine yana kallon saman dakin.
Gaidashi tayi ya amsa take fadin Abbu yace kafito ayi break ya dan kallota cikin dauriya yace zan fito amma ba yanzu ba.
Don kai ke dan damuna da ciwo ina son indanyi barci yanzun nasha maganine ta kalleshi tace sannu uncle Allah ya baka lafiya ta fita taje ta fadawa Abbu din abinda yace yace Allah ya sauwaka.
Abbu din bai dade ba a wajen ya mike ya shige ciki hjyma data gama ta bishi aka barmu nan dasu ya Aliyu suma a karshe suka fita a wurin salima nake jin cewa ashe matarshi ta haihu tana Nageria tazo ganin gida.
Na nuna jin dadina tare da yiwa jaririya addua lokacin ne anty Khairiya ta fito ta zauna ta karya tace zata dan shiga makwabtan su su gaisa don tunda tazo bata fita ba.
Tana taya muna fitan muka mike muka bita baya azatona da wautana nakance garin ba mazauna a cikinsa ashe ko ina da nagani akwai mutane daga yanayin gina nasune kawai ba zaka gane hakan ba.
Zakiga gida kato ace masaukin bakine masu ziyar ashe matan gidan suna ciki a can sama suke rayuwansu basu fita sai idan ya kama su fito din suke fita.
Wanan gidan ma da mukazo makwantan gidan su hjy din mace dayace a ciki sai yayanta suna sama a zaune sai kashiga zaka gane matar ta nuna jin dadin ta sosai nan larabci ya barke a tsakaninsu dasu khairiya .
Nikan ina kallon ikon Allah tun shigan mu na kurawa tv dake aiki ido suko suna faman hira a tsakaninsu kan cewa lokacin da zasu natsu ai yayi don garin zai fara daukan baki yan ziyara don lokacin umurah daya kawo jiki ko ina sai shirye shiryen taron watan ramadana sukeyi a kasan.
Da an gama kuma za,a fara na mahajjata don haka basu da hutu su yanzu abubuwa kanyi masu yawa a lokacin don mazajensu dake zama busy.
Mun jima a gida muka fito daga gidan da kyautan wani abu data bata bansan ko meye ba a lokacin kuma ni karama nice na dauko kyautar zuwa gida.
Nice a gaba don sun tsaya gaisawa da wani makwabcinsu don haka na shigo kai tsaye ina sallama a cikin zazzakan muryana da ke fidda wani sanadarin sauti ga mai sauraro.
hjyce zaune da kaninta a falon su biyu da gani akwai wani muhinmin magana da sukeyi a lokacin tsakaninsu sai gashi kuma nashigo masu gaba gadi falon.
A cikin takon nan nawa nake da sojana kan min sheri dashi wanda ya zama min natural don yadda nake takawa saikace akan kwai nake rafiya ina gudun ya fashe.
Mamana ashe tare kuka fita dasu na fito na samu bakya nan Abbu ma yaso ya ganki kuma kun fita gashi har ya tafi yadai bar sako da komai sai kin huta mu zauna muji ya za ayi ke nan ko ?
Zaune nakai ina aje kayan dake hannuna tare da kallon hjy din nace Allah ya tsare yakaishi lafiya ta amsa da amin tare da fadin ina suka tsaya su nace suna gaisawa a waje na barsu.
Akan karamar kujera mai cin mutum daya na zauna a daidai lokacin wayana dake hannuna ya dauki kara da kira da sauri na duba Oga Abbas na gani a rubuce.
Da sauri na dauka na kara a kunnena tare da rausaya kaina ina dan lumshe idanuna fuskana yana nuna yanayin annuri a tare dani lokaci guda.
Don sai wani dan murmushi nake sakewa a fuskana duk abinda nakeyi ina narkewa jikin kujera idon hjy da kaninta yana kaina amma ban damu da hakan ba don kula da wanda ya kirani din a waya.
Yayin da su kuma lokaci daya suke bin kalan wayan tawa da kallon don sunsan mai tsadace kwarai karfina baikai in riketa ba don sani koni waye a wurinsu.
Sallama nayi mai a ciki zakakan muryana ya amsa tare da fadin mutanen saudiya at list ai zaki kira ki fada muna kin kai lafiya ko dan hankalin mu ya kwanta ai.
Jin abinda ya fada din yasa na dan sake murmushi mai sauti ina mikewa tsaye don in bar falon saboda su hjy dana kula na dakatar masu da abinda suke nace kagane yayana ba haka bane ban natsu bane tunda nazo.
Mikewa yayi yana fadin Ukutee zan fita ina son inyi sallah a masjid Allah ya tsare ta fada ya fice ta bishi da kallo tare da tunane a zuciyar ta wanda ita tasa me take shiryawa.
Nikan mun dade da Oga Abbas muna waya kafin yayi min sallama har ina mamakin saukin kai irin nasa don da farko dukkansu masu girman kai da miskilanci nake daukansu har Boss din namu ga baki daya.
Kodana gama na fito hjy dasu Khariya na samu a falon ta bude wanan abin dana shigo dashi yayan Anabine kilo mai yawa a ciki muka zauna nan muna sha muna hira.
Da dare hjy bata fito ba ta aiko Khariya ta kirani lokacin ina wanka don haka ta koma ta fada mata saidana fitone take sake fada min sakon hjy din ba tsaya ba na nufi wurinta.

FATAKWAL NIGERIA

Kodaya iso gidan nashi kai tsaye ya shigo a daidai kofa yaji mijin maman baby yana fadin baki da hankaline idan bashi mai hakkuri ba waye zai rike maki yarki da kika haifa haka yana kula da duk wani lalura nata kamar shine babanta.
Jin hakan yasa yaja ya tsaya bai karasa shigowa ba suko idon su ya rufe sai zubasukeyi don maman baby ce ta karba da fadin ai itama ta sani.
Idan bashi ba waye zai yarda kina nufin har wanan lokacin baisan kyauta yarki bace komai yasani yadai zuba maki idone kawai atafi a yadda kikace.
Karasa shigowa yayi ciki ranshi a bace ya kalli kowansu kafin ya samu wuri yakai zaune tare da dukarda kanshi kasa cikin takaici suma din ido suka zuba mai na dan lokaci.
Kafin baban baby yayi karfin halin fadin haji Mahmoud barka da shigowa kazo ka samemu a fusce a gidan ka lokacin ya dago da idanunshi da suka rikide zuwa ja kamar gauta ya kalli baban baby din yace.
Eh ina can naga kiranku na dawo yanzun ma sauri nake zan fita don na bari za a yi min loading kaya zuwa arewa a yau din nan jin hakan yasa baban baby din fadin.
Haji Mahmoud depot ya karbeku fa don kune manya a yanzu wurin OK lafiya gani ya fada don sanin halin shirmen Adamu jos din daya tun suna bakin bunburutu tare suna sana,a dashi a waje daya.
To haji Mahmoud maganan mai dakinkane dama mukazo mubada hakkuri ayi hakkuri tayi kuskure tunda kaga ta nemomu muzo nan yanzu ayi hakkuri don Allah.
A kan me ya tambayi baban baby tare da kura mai idanu shima kallon nasa yakeyi din yadda ya sako mashi maganan a cikin hasala.
Ya habibi ya kara fadin nace a kan me Adam jos akan kun munufunceni kun aura min bazawara da sunan budurwa ko akan naki kula da yarta da take fushi dani tunda ban bar abinda nakeyi nazo nakai yarta asibiti.
A,a baban Jamal bawai hakana bane don Allah ka saurareni hannu ya dagawa maman baby din data fara magana yace look Habiba kada ku daukeni mutumin banza a zaton ku.
Subbahanallahi don Allah kayi hakkuri yaya za ayi mu munafunceka bayan zaman amanan da mukeyi daku ?
Na yaushe kuma habibi ni zan koma na fada maku aiki nakeyi ana min lodin kaya zuwa arewa nabarku lafiya banda lokacin tsayawa wanan maganan yanzu don Allah.
Ya mike ya fara tafiya har yakai kofa sai kuma yaja ya tsaya ya juyo tare da fadin kwanannan zan kara aure za a kawo min mata daga kaduna don haka dabara ya saura gareta yanzu yana fadin hakan ya fice daga gidan ya barsu nan zaune shiru .
Wasila sai hawaye ke zuba tana fadin na shiga uku ban taba fada mai komai ba bai kuma nuna min yasan hakan ba game dani sai yau din nan.
Shiko Allah dai ya gyara don muryan Adam jos ne a kunnuwanshi ke yawo yana maimaita kalamin daya samu yana fadi a falon gidansa din lokacin da zai shigo gidan .
Wanan ne tsanar da yarinyar nan tayi min kan wasila kome watau Fatima tasan da zancen nan ke nan ta boye min kuma ko a gida bata fadawa kowa ba tabarwa cikinta.
Kenan tasan komai take min kallon tsana ta dauka nasani na yarda na auri wasila hakana da yarta dole dole haka ya faru ya fada sai sharara gudu yake Allah ya gyara bai buge kowa ba lokacin don irin gudun da yake sakewa saman titin.
Lokaci daya Wani irin tsanar yarinyar da uwarta ya shiga zuciyar shi lokaci guda ya rasa da uwar da yar wayafi tsana a cikinsu har zuwa su maman baby din da suka munafuceshi yakewa kallon manyan munafukanshi a yanzu.
wanan maganan ya hanashi sukuni haka ya wuni a ranan yana maimaita zance daya a zuciyarshi har yakai da rashin kwana a gidansa yaje hotel ya kama daki ya kwana a nan don bakin ciki dake cin zuciyar shi.
Sai washegari ya shigo ya canza kayan jikinshi tare da daukan wanda zaiyi tafiya dasu ya bar gidan ya rufe kofan shi da key dinsa don kadama ta gane hakan ta nemeshi ta gane cewa yayi tafiyane lokacin.
Daga wurin aiki ya samu ticket din jirgi ya nufo kaduna kai tsaye wanan tafiyan yazone da shirin kota kwana duk yadda za ayi za ayi don yana son ya hora wasila da kyau a cikin gidansa.
Sallama nayi kofan dakin tare da dan nocking hakan yasa hjy dake cikin dakin taji ta amsa min daga cikin dakin tana fadin shigo mana don haka na tura kofan nashiga kai tsaye.
Zaune take a kasa da alaman sallah ta idar ta zauna wajen na shigo ina kara gaida ita ta amsa kafin tace dani dazun nace zamuyi magana idan an natsu nace ehh mama ina kaiwa tsugune a gefen ta kasan.
Tace dama dalilin zuwankin nan da Alh yace agaiyatokine kizo shi nake son yanzu in fada maki mu tatauna don kada ai maki girshi
Dago kai nayi na kalli hjyn a ciki mama kafin na mayar da kan na sada kasa ina saurarenta inji abinda zata fada min don zuciyana ya fara min dan sake sake a kan abinda take fada.
Kamar yadda na fara fada maki bayani a baya shine,a duk shekara muna da wani , alada a nan da mu keyi ko wani shakara shine.
Za,a taruo a gidan mutum daya a cikin su shi za ciyar da ko wani mutum da tazo wanan taron don shine yasa aka gaiyotoki kan irin girki da fatan zaki bamu hadin kai mamana hjy din ta kare da fadi hakan cikin sanyi murna
Kada ki dauki hakan wani manufane damu a kanki a,a ga Khariya da Salima dama su Ummah hani har ni din nan duk a tare zamuyi komai naki shine jagora yadda zakiga komai ya kammala da kyau.
Dan gyara zama nayi tare da fadin mama wanan ba komai bane ai don babu zancen ganin gazawa ko takura a gareni cikin haka saboda a matsayin iyayye kuka daukeni insha Allah zanyi da zuciya daya kamar yadda kuma kuke zaune dani da zuciya daya.
Khairiyace ta shigo dakin a daidai wanan lokacin lokacin ne kuma hjyn ke fadin wallahi Fatima nasan Allah ne ya jefoki a cikin rayuwan mu ta sanadin wanan abin.
Don haka ki saki ranki da kowa ki nuna kamar a gidan mahaifinki kike don ko Alh ya yaba kwarai da hankali na tabbatar kuma ba zakiyi wani abin asha a tare damu ba a nan na amsa da insha Allahu mama.
Mama mama kowa mama khariya ke fadin hakan a cikin shakiyanci tana kaiwa zaune tace Ummu naga uncle ya fita ranshi a bace ina mai magana baiko tsaya ya kulamu ba.
Kyaleshi Khariya so yake yaga bacin raina a gidan nan kinsan shi wani kalan mutumne mai baudadaden zuciya da rashin fahinta sai munkai ga yadda ba,a so dashi a gidan nan zai natsu.
Yadda hjy ke maganan yana nuna ranta a bace yake lokacin hakan yasa nayi niyar tashi in bar wajen sai naji tace min ina kuma zaki zanso ki tsaya ki lissafa min abinda ya dace muyi da wanda muma a nan din zamu iya yinsa.
Hakan yasa na koma na zauna tare da tunane a zuciyana jin yadda ta fara lissafo min abubuwan da ya kamata ace sunyi ne yasa nagane ashe ba karamin bukine dasu ba da zasuyi.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
5?? 0??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

A zatona wasane abin kama dan kwarya kwaryan walimane za ayi da baifi mutum goma ba ashe abin yafi gaban yadda nake zato wani irin al,adace ta larabawa.
Mai kama da sada zumunci a tsakanin kabilu sama wanda kake makwabtaka dashi atakaice dai zan iya kiran wanan taron a matsayin walima aci asha mata daban maza kuma daban suma.
Za,ayi ta gabatar da hadisai masu ma,ana dake kashe jikin bawa akan dan uwa musulmi ayi raha ayi dan ba,a a tsakani tare da tatauna wasu muhiman maganganu daya shafi ci gaban al,umma.
Wanda Allah yabawa ikon zuwa zai bada wani abu kamar dai gudun mawa ga maishi ko taimakone hakan ke nufi ni dai ban fahinta ba gaskiya anci ansha an godewa Allah taro yayi kyau sosai a wajen duk da ina ciki nagaji sosai do kwana biyu ke nan bana hutu nakai iyakar aiki don gaskiya na gaji sosai.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login