Showing 156001 words to 159000 words out of 347556 words

Chapter 53 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8754

gareni wanda ba daidai bane mutum farat daya yayiwa dan wani wanan zaton a rayuwanshi ba.
Alhamdullahi tunda mahaifina da wasu sun yarda dani amma shi soja dake kokarin hakan a yanzu gareni meye manufansa nema wai ?
Sai lokacin nake dana sanin rashim gasa masa magana da banyi ba ta yadda zai zargi kanshi duk da wani zancen banza gaskiya bai taba shiga tsakanina dashi ba har yau.
Saidai a yanzu na gano yana da matukar kishi sosai don abinda ya fara hadamu dai shine kan zancen aikin nan da nake danyi da company global da yake zargina akai.
Wanda ni kuma nasan tsakanina dasu ba komai bane da ake zargi illa na dauka wani damane kawai Allah yai min a hakan da zan kara dogara da kaina a yanzu din.
Sai ni kuma da nake masa kallon tuhuman yaudara don kawai bai fada min cewa yana da mata ba tunda farko har ya bari shakuwa mai yawa ya shiga tsakanina dashi ta yarda nake jinshi a cikin raina irin ba wani din nan bayan shi.
Sai gashi daga baya nagane ashe yana da mata duk sa ya fada min da kanshi amma nake ganin hakan yaudarane wanda shi kuma na kula da bai daukeshi komai ba a wajen shi.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
4?? 8??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Wurin nemo caja in makala wayata don dai a cike take da caji ba zancan dauke wuta a wanan garin mai albarka a nan naci karo da abinda mutumin jirgi ya ban wanda ban tsaya dubawa ba a lokacin.
Sai lokacin na zaro takardan ina binshi da kallo ashe rudewane ko tsoro ya hana inwa takardan kallon kyau a lokacin da yake mika minshi a cikin jirgin.
Da sauri sauri nake karanta bayan takardan an rubuta Alh Abbas ibrahim gadon kaya kano state international bussines card.
Sai aka dawo daga gefe kasa da manyan haruffa aka rubuta ABBAS IBRAHIM GADON KAYA EMEPEAIR NAGERIA AIR LINE MANAGER.
Ido na fitar waje waje cikin mamaki ina fadin dama da babban mutum na zauna haka ashe ban sani ba har nake dan mashi kallon ko irin dattijan banzan nan ne ashe ?
Aje katin nayi ina tunane kafin na bude naga abinda ke cikin envelop din a lokacin wanda babu komai a cikinsa sai kudi yan saudiya da ake kira da riyal ba zance ga adadinsu ba a lokacin don bansan kansu ba don haka ba zan iya kiyasata su da kudin Nageria ba na sandai kyautace ta banjinta akai min a wurin nan.
Ina shirin mayarwa in dunkule ne aka turo kofan daidai lokacin dana gama turawa cikin jakata ko na juyo ina kallon maishigowa a lokacin Salima ce tashi tana fadin umma suna kiranki a falo .
Har ta juya zata fita sai kuma ta tsaya tana fadin nazata barci kike ai don banji motsin ki ba tun dazun hijjab na dauko na dora a kaina ina bata amsa da fadin .
Yanzun dai nake shirin kwanciya dama tare muka fito daga dakin nawa najawo kofan kamar yadda naga sauran dakunan sunayi a gidan nima hakan nakeyi yanzu sai ka dawo ka murda ka shiga.
Bamu kai falon tare ba don ta tsaya a dakinta ni kuma na nufi falon kai tsaye inda zan samesu don ban taba shiga part din su mama ba tun zuwana kasan.
Gaba dayan su har kowa na zaune a falon ganin su hakan yai matukar firgitani a lokacin domin kuwa sun masifan yi min kwarjini a yadda nagansu sun hadu lokaci.
Don haka na danja burki nakai minti biyu a tsaye wurin ina binsu da kallo ko kyatawa banayi ban san lokacin dana saki wata zazzafan ajiyan zuciya ba lolaci guda.
Ga wani bangare na zuciyana yana kitsa min dana koma kawai har su bar wajen zaifi a gashi sai hiran su sukeyi gwanin ban sha,awa suna cin abincin su cikin jin dadi da annashuwa.
Don haka nayi kokarin juyawa in koma daidai lokacin ne kamar an fadawa hjy ina wajen ta juyo ta saki murmushi tana fadin karaso mana mamata kizo ki zauna kin tsaya daga can kuma.
A firgice naga uncle dake kusa da Abbu zaune ya lankwashe kafa yana cin abincin ya dago kai ya kallo inda hjyn ke kallona tana magana sauran ma da basu san ina nan ba suka bini da kallon mamaki lokaci guda.
Ina tsaye ban tako zuwa inda suken ba ta kara fadin kiyi hakkuri nasa an taso dake kina hutawa dolene yasa hakan don nasan bakici komai ba kika kwanta muko gamu sai kwasan gurkin ki mukeyi yanzu.
Daga inda nake din tsaye nayi mutuwan kasko haka na fara takowa zuwa inda suke zaune a kasa a baza wani carpet mai girma a kasan wanda don cin abinci aka ranadeshi kawai a gidan .
Kamar da bi,ansune hakan cin abinci a kasa ba saman table ba don mai karatu in baki manta ba ko a can Nageria da suka tafi nake maki bayani lokacin a kasa suke zama suci abinci ba saman dining table ba duk da ko wani gida nasu akwashi amma basu hawa sai a kasa suke zama suci.
Har lokacin dana karaso din na zauna daga gefe suna min kallon mamaki har kairiya da itama tazo a lokacin sai itane ta bude baki tace umma dama wanan kankanuwar ce tayi wanan abincin don Allah?
Itace mana ki mata da itane tayi ta supply din abinci lokacin bukin ki amma umma kamar tafi nan girma nagani koda yake ba zan gane ba gaskiya din mutane sunyi yawa a lokacin.
Saida nakai zaune nake fadin ya Aliyu ashe kunzo ya anty Aisha kuma ya dago ya kai loman tuwo a baki yace keda umma kunyi surprise din mu da zuwanki don umma bata fada muna zuwan ki ba ai.
Al,amin dake gefe a zaune ya gyara yana fadin watau bakiga uncle ba sai ya Aliyu ko don ya Aliyune, , , , uncle ya dago a fusace ciki halin nan nasa gaba daya yanayin fuskansa ya sauya lokaci guda yace.
Yaron nan ka rainani da yawa duk wurin nan bakakaga kowa ba sai ni da zaka ambata wallahi zanyi maganin ka kwanan nan .
Dariya Al,amin din ya kume a cikinsa yace wai naga bata gai dakai bane farko sai ya Aliyu ina zata fara gaidashi yayi mata wanan halin nasa na zuciya tun yanzu gashi ya fara nuna hakan a gabata ma.
Alhalin nan yazo yana kewan abincinta wata da waranin ya kasa cin abin kwarai a cikinsa sai yau na tabbatar da zancen ka Al,amin tun dazun shi nake kallo yadda yake ta kwasan loman tuwo ai Abbu din ke fadin hakan cikin wasa ga uncle din.
Murmushi ya danyi yana ci gaba da kai abinci a bakin shi kafin ya danyi kamar loma uku ya dago yana wanke hanayenshi yakai kallonshi ga Abbu din yana fadin Abbu zakasa yarinyar nan ta dauka ko gaskiyane hakan ta raina mutum.
Ina abin raini ga abinci kaidai ka matsa matarka ta koya zaifi don haka da kuje Nageria nake matsawa yaran nan akan su koyi wani abu a wurinta suka tsayawa mutane yanga.
Ai ummu gara Aisha don da muka dawo ta gwada dafa muna abinci saidai ace ba dadi kamar na ita wanan din amma tayi kokarin girka munashi gaskiya .
Yata a ina kika koyi girkin gargajiya hakane Abbu din yake tambayana nace kawai dai na iyane kuma na dan shiga wurin koyon girkin zamani a nan kaduna saidI ban dade ba nafita saboda karatun dana fara lokacin.
Tsam ya mike aka bishi da kallo Abbu ya kalleshi yace ina kuma zuwa ana hira yau yace zai shiga daga cikine daga inda Al,amin din yake zaune ya kara fadin gara dai ka zauna uncle.
Wani kallo mai dauke da takaici yayiwa Al,amin din cikin yan dakiku kafin kuma ya koma daure fuska yayi murtuk lokaci guda kamar wanda bai taba yin murmushi.
Ya kwasa ya haura gefen da dakunan kwanan su yake yabarmu a wajepin zaune dan shiru ya biyo baya lokacin kafin ya Aliyu ya kawar da shirun .
Ina zaune nayi sororo tamkar bani wajen don ko kai ban daga na kalleshi ba lokacin saidaya bar wajen suna dariyanshi na dago manyan idanuna ina binshi da kallo.
Ya Aliyu ke fadin girki yarinyar nan yafi min girkin tsofin nan dake sallon girki ko yaushe umma hanni ko yadda yarinyar ke girki bata kaita ba sai faman cika baki wa mutane.
Bari sujika aikin saba fada dama wanan dai ba zama zatayi nan har abada na dan lokacine take nan a tare damu don haka ka kama bakink kafin umma hani taji ka ku kwasa yanzun nan.
Yata naji dadin yadda kikeyi din nan don ban dauka baiwan ki yakai hakan nan ba sai dana gani kuma na yaba da dabi,unki sosai.
Da fatan zakiyi hakkuri damu da yaran duk akan komai da zaki gani ba daidai ba a tare damu da sannu zaki saba da kowa a cikin mu don naga yanzuma kamar a takure kike nan zaune ?
Hjy ta kalloni inda nake tana fadin bansan ranan da mamata zata saki jiki dani ba don ko yaushe a cikin kunya take ita bata da sakin jiki hakan take da kowa dan dama idan Al,amin yana kusa shine abokin yinta daman.
Shiko uncle da kyat yakai dakin saboda kafanshi da yake jin baya daukan shi a lokacin saboda nauyin da sukai masa ya shigo bangarensu kai tsaye dakin barcinsa yayiwa tsinke ya fada saman gado ya kwanta ya zubo kafafuwanshi kasa tare da dage fuskanshi yana kallon saman dakin.
Cikin kankanin lokaci ya tsunci kansa a wani matsanacin tashin hankali mara misaltuwa ba tare da wani bata lokaci ba ya fara tambayan kansa tambayan da baida amsa akanshi lokacin.
Tambayan kansa yake meye ya kawo wanan yarinyar saudiya ita dawa tazo kasan nan ke nan a sanin da yayi karatu takeyi lokacin wanda har lokacin nan bai isa ace na karasa wanan karatun ba.
Ya dade yana tunane kafin barci ya daukeshi har ya manta tambayan dake tare a cikin kwakwalwan shi lokacin game da ganina da yayi don ya dade rabonshi da wurin su hjy don haka yake zaton kona dade a nan tare dasu.
Kuma gashi girman kai ba zai barshi ya tambaya yaji ba yana ganin idan yai haka kamar gazawane a gareshi da wanan tarin tunanen ya kwanta dashi kuma ya tashi dasafe a zuciyarshi saidai babu halin tambaya gareshi.
A dakina kuma tunane nake don ni ban gane kome ke faruwa ba suke tsarguwan uncle a kaina don haka na kwanta da tunanen hakan a zuciyana.
A iya fahintata zan dauki wanan uncle din mai girman kai da saurin fushi tare da nisanta kansa daga kowa atakaice dai irin mutanen nan ne masu jida kansu da lokacin su .
Don ganin yadda yakewa diyan gidan tsawa da cicin magani yasa na nasa a raina nayi nisa dashi tun bai disgani wata rana ba a gaba mutane don nasa ba zan iya kyalesa ba har in yai min hakan kuwa.
Da sauri na tintse idanuna da nake jin hawaye na shirin zubo min daga cikin su amma na kasa don wasu zafafan hawayene ke zubo min lokaci guda wanda bansan ko nameye ba a lokacin.
Barcin da ban samu yazo min ba ke nan a lokacin do tunanen dake min yawa azuciyana banda aiki sai na yawan tunane akullun har hakan ya zame min jiki a yanzu.
Gani barci yaki zuwa min yasa na yunkura na tashi zaune tare da jaye bargon dana rufa dashi a jikina lokacin mike na sauko dafa saman gadon da nake kwance.
Ban daki na nufa na dauro alwala nazo na shinfida abin sallah na fara jero nafilfili daga bisani kuma naci gaba da karatun kur,ani saida na samu natsuwa na dakatar nakai kukana ga mahalicina Allah.
Saidana raba dare ina budaya sannan na samu natsuwa a tare dani sai karfe uku na samu barci ya dan daukeni na runtsa .

FATAKWAL NAGERIA
Daga kasuwa yake tafe wayan shi ya dauki kara bai faye daukan waya ba idan yana tafiya do haka wanan din ma bai dauka ba ya barshi har ya katse.
Baifi second ba kuma wani kiran ya sake shigowa lokaci guda hakan yasa ya dan ja tsuki yana mika hannu ya dauko wayan nasa daga inda ya jonata caji a motan nasa.
Matarshi ce wasila a layin don hakan ya danna dauka yana kara waya a daidai kunnensa yaji tana fadin amma dai ai kaga kirana tun dazun kana ignored dinsa.
Yaushe kika kira idan ba yanzun ba tace ni ba wana ba kana ina yanzu don ina son kazo mukai baby asibiti tunda safe aka dawo min da ita gida ba lafiya.
Gashi kuma har yanzu baka dawo ba cikin dan mamaki yace kina zaune tun dazun baki kaita asibiti ba sai yanzu da yamman nan.
Amma ai kasan motana yana da matsala kwanan nan ba zai shigu ba ya tare ta da fadin sai akace kuma ba a daukan ku a motar haya ko ?
Mahmoud kaima kasan yanzu ba zan iya fita na nemo motar haya ba ai yace sai ki jira har lokacin dana dawo gida sai mu kaita.
Don baka damu ita ba zaka fadi hakan cikin mamaki ya kira sunan ta yana fadin wasila duk kokarin da nikewa yarinyar nan bakya gani.
Don kawai yau nace ina da uzuri shine zaki fadi hakan ke wata iri mace ce mara godiyan Allah wasila an fada ta kashe wayan a hasale tana jan tsoki.
Gyalenta ta figa ta dauki yarinyar zuwa waje tana rufe gidan zuwa inda zasu samu mota zuwa asibitin har lokacin ranta a bace yake da kin zuwanshi ya kaisu asibitin da yayi kan wani uzuri nasa can na daban.
Shima dai a bangarenshi mamakine ya kamashi yarasa irin hankali na matar nasa don a yanzu zama kawai suke na yar tsama a tsakanin su don ba wani jin dadin juna sukeyi ba.
Bai dawo gidan ba sai goma na dare ya dade a kofa yana bugawa sai can dataga dama tazo ta bude mashi tana juyawa kai tsaye bata tsaya bin ta kansa ba lokacin.
Ya karasa shigowa cikin mamaki suna zaune falo tana ba yarta abinci a baki ke nan tamaji bugun kofan nasa bataga daman budewa bane kawai lokacin.
Kamar yadda batayi mai magana ba haka shima ya sharesu ya shige part dinshi kai tsaye tun wanan ranan suke zaman yar tsama a tsakanin su koda yana gida babu ruwan kowa da dan uwansa.
Ganin itace zata sha wahala ga hakan yasa ta sauko tana neman shiri dashi lokacin shi kuma yaki ya nunama baisan tana yi ba.
Har yakai ranan ta rutsa dashi yana hira da samira data makale masa tun yana gudu har ya dan fara biye mata suna bata lokaci a waya don ya dade baizo kaduna ba yanzu.
Gane hakan ne da tayi ya kaisu ga tash????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? in hankali har takai karansa wurin yayanta maman baby da a yanzu ba wani shirin kirki ke tsakanin su ba don kirikiri wasila tayi watsi dasu bata taimaka masu da komai dan dama in sun samu shi Mahmoud din kai tsaye zasu samu biyan bukata a wajen shi.
Duk da hakan maman baby din da mijjnta basuyi fushi ba suka samesu a gidan nasu don su shiryasu sai da kyat ya yarda ya dawo gida bayan sun sanar mashi da zuwan su din gidan.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
4?? 9??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Karfe takwas da wasu yan mintoci muna kitchen da salima wace ta tayar dani daga barci tare da wanan dattijuwa ummah hani muna hada abin karyawan safe .
Yau ma koko da kosai na kara hada masu sai dan waken filawa da mai da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login