Showing 204001 words to 207000 words out of 347556 words

Chapter 69 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8763

a idon wasu koda kuwa yan uwasane idan tace mijinta take kishin hada alaka dani shivdan uwan natafa da tace shima ya nuna yana sona.
Wani maso ya nuna min banda shima kallon kyamar da yake mina idanunshi nani ba yar kowa bace face mai aiki kawai a cikinsu.
Zan iya cewa ga Hjy din da Al,amin nadan ji dadin su a gidan saiko shi ya Aliyu din da kullun yake min wasa don sunan kakarsu da nake dashi shima kuma din yana da aurensa ai.
Ire iren wanan tunanen nakeyi har nakai wani lokaci a dakin ranan ban leka school ba dama karfe biyu zamu dawo gida idan muje ranan sai ban damu da zuwa din ba don bama zan iya ba don wanan kazafin da hjyn saudiya tayi min.
Matar dana dauka kamar uwata ko wata yar uwar mahaifiyata yau ta dawo tana min mumunan zargi haka a kan mijin ta kuma yarage duniya gareni ke nan kuma na tambayi kaina.
Sai dare na iya dan fitowa muka fita da Aliyu zuwa bakin titi wurin masu shagunan unguwan muka danyi sayayya na bashi kudi ya tsalaka titi ya sayo muna nama muka dawo gida.
Gwaggo da mijin ta suna zaune a tsakar gida muka dawo na gaidashi da dawowa daga kasuwa na nufi dakina don ban faye zama waje ba idan yana gida.
Aliyu nasa ya dauko roba a cikin kwandon kwanonin gwaggo na zuba masu nasu ya kai masu da abin sha harda Nura danta daya dawo hutu yana gida lokacin saidai bai dawo daga kasuwa ba tukun shi.
Na dibi nawa na mikawa Aliyu din saura nace ya wuce makaranta yaje yaci ya fita da murnan shi yana zabga godiya dan abinda muka sayo din shi naci na kwanta a ranan don damuwan dake tare dani a lokacin.
Allah kaine Allah buwayi gagara musali Allah kaike daukaka wanda kaso a duk lokacin da kaga daman hakan a bayin ka.
Yanzu Fatima Bintu Bantu ce har hjy ke jifana da zargin cewa ina kokari in sace zuciyan mijinta daga gareta da wani nasaba nawa zan iya aikata hakan gareta ita yar sarki mijinta ma dan sarki kuma mai fada aji a Nageria.
Kai mutane suna aikata abu ba tare da zurfin tunane kan abinda suke kalubalantan ka dashi ta ina zanga mutum kamar Abbu har in kebe dashi muyi wata mu,amula ta daban har nawa nake ga shekaru wai ?
Da hjy ta sani da bata aikata hakan a kaina ba bata furta wanan zancen har ya fito ya dawo kunnena ba don a matsayin uwar data haifoni a duniya nake kallonta.
Tabbas Salima bata fadi karya ba a nan awajen bukin Azawat dinsu ne ta samu kawayen da suka zugata kan hakan har take min wanan mumunan fahintar a zuciyarta yanzu kuma.
Anyway karshen kwadai ke nan dama ga duk wanda bai tsaya a matsayinsa ba yakai kansa inda Allah bai kaisa ba na fadawa kaina hakan a filli.
Zancen yan gidan mune ya fado min a rai in har sukaji wanan labarin sai sun min gwai sau dubu a kaina don sunsha fada min ba gyaran gyaran ba dai,,,,,,
Gashi kuwa tun ba,akai ko ina ba hakan ya fara bullowa a gareni dole inwa kaina kiyaman laini da duk wani mai kudin dake jana a jikinsa tunda hakan baida tabbas .
Haba jama,a kamar ninafi kowa dai bakin jini a cikin al,umma sai wanan ya tafi wanan ya bullo menayi wa jama,ane haka nikan wai alheri dai bai katbeni ba ke nan dai ?
Ko kuma zancen gwaggo ne zai tabbata a gareni da takan fada min cewa in dai kulla da addua da sadaka don mama bata da kyau garama mama ta fitar da nata ansani sauran da nasu ke boye Allah kadai yasan me sukeyi a kaina yanzu haka ?
Don yanzu kowa nasa yasani abar kwanciya wani na maka nasari a kai don in sunga tauraron nan naki dake haskawa haka na tabbatar da bazasu kyaleki ba yar nan.
Ki duba yar uwar nan taki fa yarinya ce amma saboda hassada da kyashi ta hana zuciyarta shakat a kanki bata ko iya boye halinta.
Ga yaran yanzu ko manya basu kaisu ba su suna kai kansu da kansu wajen bokaye da malamai wata yarma tafi uwarta sheri ai.
Ke gaki in an karbo maki ki tsaya kina zilla zilla bakyason sha ko amfani dashi to ki matsa da sadaka da addua don yafi komai amfani ga bawa dama wanan anayinsa daine don kariya .
Niko zancen yaron nan soja ban yarda cewa ba rabaku akayi ba tunda har ta kasa hakkuri da sherin boye ta fitar a fili kowa ya sheda hakan kece dai kawai kikeson boye ta.
Gabanane ya fadi tunawa da yadda mama ta nuna damuwa kara a ranan kan zancen baba da za ace baima san abinda yakeyi ba a lokacin ya furta hakan saboda yana ganin mutuwarsa gabansa ya fadi hakan .
Amma haka mama ta kwana ta tashi tana mitan maganan da danta don ma shi ya Ahmed din ba kallan zuciyarsu daya bane da ace wanine daukan zancen zaiyi.
Na shiga uku na furta sai ga hawaye yana zubo min lokaci guda don sanin halin mama danayi kamar yunwar cikina zata iya aikata min abinda ba daidai ba wajen mutanen nan a bayana.
Zata aika don abin yan gidan mu ya wuce musali ba kunya ko tsoro idan zasu aikata abu ga mutum.wai saboda duniya kawai ba tunanen mutuwa a gabansu.
Dolene ma in kira Nura ko to ince masa me kuma in dai barwa Allah shiya iya da lamarin mu tunda na zame masu karan dafi yanzu a cikinsu.
Watsar da zancen nayi bayan naci kukana da damuwa kan hakan gashi banda abokin shawara sai gwaggo duk data kula kwana biyu ina cikin wani yanayi amma na boye mata hakan.
Sai bata kara tanka min ba ta zuba min ido kawai tana kallona Aliyu mane yakan so ya jani da hira in yayi yayi yaji ba amsa yakan tafi ya barni ya kyaleni.
Anyiwa baba aikin lafiya an fito dashi kuma lafiya saidai fatan alheri gareshi kuma yanzu din wanda labari ya gama zagaye yan uwa da abokan arziki cewa nice nayi sanadin kaishi asibitin Abuja mai tsada.
Tambayan farko da mutum zaiyi shine wani aiki nakeyi kona samu a yanzu da nayi karfi haka har nakai baba wanan wajen ?
Wasu yan arzikin zasu fadi cewa sanadi daina samu wasu kuma suce ai na wuce sanin da akai min a baya don yanzu nagama famfarewa ga baki daya na zama babban yar bariki don har makka naje.
Zakiji ance makka a,a yarinya ta bunkasa ita Bantu din masu hankali kance dama a??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ita iya neman na kanta ta aika in ance taje makkah don akwai zafin nema gareta.
Zakiji yan munafunci na fadin ita tafi kowa zafin nemane da har zataje makkah a wanan shekarun adai bincika kawai.
Irin maganganun dake tashi ke nan a dan takin nan wajen wa yanda suka san mu da wa yanda suka san matan baban mu din sunfi yawa a gari.
Rayuwa akwai daukarwa kai wahala a yanzu har wanda baiji ba bai gani ba yana tofa albarkacin bakinsa dan daukan zunubi kuma a zargawa mutum abinda baiji ba bai gani ba.
Ganin cewa ba wani test a gaba yasa na shirya komawa Abuja in duba su saidai ina son na dan tsaya kaduna in duba gida suma a nan.
Don haka ranan laraba na samu gwaggo da zancen don in samu shawara na dawo bayan karfe biyar shida saura na gaida gwaggo dake tsakar gida na shiga dakina na kwabe kaya na fito na kewaya.
Na fito na aje buta na nufi wajenta ina fadin gwaggo ina son zuwa in duba jikin baba ingani amma ina son in tsaya kaduna in duba su mama kafin na wuce.
Ta dago tana fadin hakan nada kyau gara a dubo muna shi muji lafiyan jikin nasa ai tunda in ba gani kayi da idanunka ba don waya sai aita cewa da sauki da sauki.
Suma sun kwana biyu basu kira ba kuma na kira Nura shekaran jiya bayajina yace don haka nake son zuwa sai gwaggo tace in ba shirme ba da baya jinki ba sai su sukiraki ba.
Baiyi hakan ba kuma ita Suwaiba tana can har yanzu din ke nan nace mama ba tana can aiba zata dawo wani ya tafi ba indai mamace.
Balle gida sukutun aka bamu acan da suke zama tunda ance ba a zama asibitin da majinyaci saidai kuzo ku dubashi ku tafi haka tsarinsu yake.
Ai kuwa tana can tana cin riba matar da kanta tasani sai yayan ta ai halin Suwaiba baiyi ba wallahi har ta koyawa kowa wanan akidan gaba daya gidan kowa dansa ya sani.
Shiyasa nake tausayinki kullun a cikinsu keda ba uwa ba dan uwa a cikinsu dan ma Allah maji kan bayinsa ya rufa maki asiri yana daukakaki cikinsu.
Shiyasa ake son ka kasance da zuciyan alheri a kullun wanan takin kike zubawa kanki da Allah baiyiki da zuciyarki da keta ba a cikinsu.
Don dai suwaiba kan sanin da nayi mata tun farko ba canzawa zatayi ba muma kannem mijintane amma lokacin da mukazo zama dasu ba akwashe da dadi damu ba a lokacin.
Kan wanan gatan zata iya kulla maki sheri babba kuwa ba Lanto da yarta bane makiyan boye nata tayi a yanzu don wani manufa da take dashi.
Gwaggo nasani don ta fara tun ina can nan na kawo labarin abinda ya faru kaf na fada mata da sauri ta tare da fadin aina sani nasani wanan rayuwace ta yan kasa irin nasu haka suke da bakin ciki da hasssada har basu iya boyewa.
Dolema nasani sai tayi sherin ta a nan sai tayi indai suwaibace wace bata son wani da karuwa ko kadan ita kuma har yau Allah bai karata ba sai baya da takeci Allah mana ragawa yar kawai dama irin su suna tsawon rayuwa su karasa a karshe suyi ta kukan da sunsani.
Kin tabbata KARAN DAFI nan da suke kira maki kuwa don kinfi yayansu amfani ko yanzu balle gaba bama guzace fa ta ya za ayi tayi imani jinin kafircin nan har yanzu a kwaishi.
Abinda bata son gani zata ganshi akanki kuwa don ba aiwa Allah shishigi cikin lamarinsa sune basu gane hakan datana gane da tabar wanan halin.
Yaushe tafiyan naki ta dago tana tambayana nace ranan Jumma,a nake son shiga kaduna in Allah ya kaimu Asabar da safe in wuce zuwa Abujan insha Allahu.
Allah ya kaimu tace kafin ki tafi zan zaga wajen malam na kara tuntubansa a kanki duk da nasan baki son hakan amma ya zama wajibi naje makini don kin nuna ni nakine fiye da kowan ku dolene in tsaya maki kota halin kakakuwa.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
6?? 5??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Zakiji labarina kamar alamara ko labari kawai saidai idan kin natsu zaki fahinceni duk da nasan dayawa labarina zai tuno masu da wani bangare a cikin rayuwansu a wanan lokacin.
Tabbas nasan dayawa zasuyi tunanen cewa ina hakan da nake bada labarin nan zaiyuyu ace ya mace mai shekaru kamar nawa tana gararaba haka a cikin duniya.
Yar uwa ki bari kawai idan naki rayuwan ya tafi a daidai nawani da akasi ya fara tun farko duk da nasan akwaima wace tafini shiga taskun rayuwa a baya.
Don dai a kasan hausa akwai mamaki ya mace ta koma kamar namji a gida tana gararanba a cikin duniya haka don neman dogaro da kai alhalin tanada iyayye a raye to tabbas akwaisu akwasu kuwa sosai a nahiyar nan ta arewa.
Kowa bai isa ya kaucewa kaddaransa na rayuwa ba don nikan tawa kaddaran haka yazo min da kalubali a rayuwana wasu su tausaya min wasu kuma su zaga wasu su yaba su bata haka halin dan adam yake.
Ni daya ke faman wanan tunanem zaune a bayan mota driver sai guda yake kwasa damu da baifi yan mintunaba a ganina sai ganin welcome to kaduna da nayi a gaba haka na nufin mun shigo garin kaduna ke nan lokacin.
Tasha muka sauka na dauki drop da zai kaini gidan mu a kofan gidan mu mai Nape ya tsaya dani na fito da yar jakata karama dana saya don irin tafiyan nan na kwana biyu idan ya kamani.
Ina sallaman mai adaidaita din ne naji muryan isah maishago a bayana yana fadin hjy Fadimace yau garin na juyo na dan sauke murmushi karona farko tun fitowa daga gidan gwaggo ina fadin malam isa mun sameku lafiya.
Yace alhamdullahi daga Abuja ko zarian nace daga zarian nake zanje Abujane in dubo baba nabiyo nan in gaidaau kan na wuce naji yace ai gara da kikazo Fadima don kuwa kamar baba bai bar kowa ba a gidan nan zakice ma baya raye wallahi.
Amma dai karna katse ki karasa ki shiga amma don Allah ku taimakawa yarinyan nan ladidi kada ta halaka don naga kamar uwar abin bai dametaba ita.
Ladidi kuma na dan juyo ina tambaya a cikin mamaki yace kwarai kinsan ta kare tun tafiyan ku da kwana hudu ba,a fada maki bane wai dama ?
Nace wallahi banji ba isa yace ta kare mana can sukayi faduwan adaidaita wai sun tafi buki aka kawota nan raga raga saida mukayi tarbace aka samu mai dori ya dorata na gargajiya ashw baiyi ba.
Ina zuwa isa na fada ina kokarin shiga gidan namu nace idan na fito zamuyi magana yanzu barin shiga mugani dai yace Allah ya hutar da gajiya yana bina da kallo na nufi cikin gidan.
Babu kowa a tsakar gidan saidai gidan daya koma kaca kaca sai kaji dake kiwo a tsakar gidan sallama nayi ba wanda ya amsa haka yasa na nufi dakina dake rufe ina kokarin budewa lokacinne mama ta fito tana fadin waye.
Na waigo ina fadin nice mama mun sameku lafiya tace wai Binta kina hanya ashe daga Zaria ko Abujan nace daga zaria mama zan daije Abuja din ne na biyo ta nan in duba ku.
Allah sarki sannu da zuwa yarinyar mama Lanto din Ladidi da isah mai shago ke kwarmata min ce ta firo tallabe da hannu tana fadin sannu da zuwa Anty na kallota nace yawwa sannu ladidi har zan juya sai kuma na juyo ina fadin ke kuma meya sameki haka hannu a daure.
Gata nan ta fada maki ai mama Uwa ta fada tana karasa fitowa daga dakin da dan kwali a hannunta na kalli yarinyar tayi min narai narai da ido kamar zatayi kuka tace.
Wallahi kaddarane ya jani zanbi su yar chakwai wurin buki munyi yawa na fado a adaidai na kara hannu na an dora kuma wai baiyi kyau ba sai an kara bada dubu goma sha biyar ankaini kauye ayi ga hannun sai kumburi yake min yanzu.
Ita kuma Antyn mu dacewa Samira an kirata tace wai bata da kudi itama ta kanta takeyi maman mu tace ko nawane don Allah ta taimaka muna tace wai wallahi ita bata da kudi a hannunta.
Shine baku kira kun fadi ba daga inda mama uwa take tsaye tace aidama na fadi sukiraki tunda har yanzu su basu san Annabi ya faku ba suna kayan nuku nuku a zuciya.
Jiyan nan tace min da Nura yana gari zata karbi wayanshi ta kiraki ta fada maki bata barci ihu take damun mu dashi idan dare yayi kin ganta nan ana fama da kai ta daukowa mutane wani wahala kuma.
Allah ya sauwaka nace ina karasa bude dakin na shiga haka na daure don dakin baya shakuwa nasan Nura ya zauna a ciki ke nan dan tafiyanan da bana gidan .
Gyaran dakin nayi ina jin shigowan mama Lanto amma bata lekoni ba harsaida nagama na fito zubar da shara muka hade da ita take min anzo lafiya na amsa bayabo ba fallasa ban kara ba.
Saidai a yadda na kula sun raba girkinsu don mama Uwa yayi min tayi abinci taliya data dafa ita kuma yanzu sai gashi naga tana firan dankali dan hausa sallah nayi bayan na idarne na fito ina kulle dakina na leka dakin mama uwa ina fadin ina su hassana ne wai ?
Tace suna gidan yayan Tudun wada kila yau su dawo don tun jiya suka tafi ladidi fito muje asibiti na fada na sake fadin mama zan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login