Showing 312001 words to 315000 words out of 347556 words

Chapter 105 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8807

mama tace a gaidani bata samun zuwa ta tashi da ciwon kai nace Allah ya bata lafiya suka zaga gidan ko ina suna yabawa kafin aka dawo falo aka zauna nan dai suke ja min kunne kan zaman aure.
Tare da kara kula da zumunci yan uwana da yan uwan miji duk naso kowa a zauna lafiya yadda sukaji shine babba a family dinsu don haka in kama girmana don girman mijina a cikinsu dole a banshi nima idan na kama girma na.
Meye girmana shine kada inyi wanan wasan da zurfi yana kawo raini kada in zamo mai rowa zai jawo min kiyayya a wajensu idan sunzo da bukata wajen mijina suka biyo ta hanya nayi kokari naga ya basu in kuma girmama iyayyensu hakan zaisa nima su girmamani.
Wanan fada nashashi tun kan a kawoni gidan do shiga gidan yawa kuma Royal family sai mutum yayi da gaske don ma nahaifina ya saya min inci a idanuwansu ya kai daurin aurena sokoto an daura a fada shine darajata a idanuwansu yanzu hjy laraba ta fada a karshe.
Su mama suka amsa da fadin aiba karamin dubara bane hakan bashi yasa yaya na fadan wai an fifita Bintu akan sauran yayan ba don nace da dalilin hakan ta mayar da fadan gareni ranan ba kalan tijara da batai min ba gidan nan.
Wai matar nan zatayi hankali kuwa haka ta dauka da zafi zuwan mu bata san Nuratu yanzu ko mijin ku ta wuce saninsa ba don dai nata na wajene kawai aida bata ganta garin nan ba.
Mufa munso akai muna ita can kasan mune tayi bukinta a can saidai ba lokacin hakan da tasha mamaki a rayuwa wallahi Ammi ke fadin hakan.
Abinci na gabatar masu suka hau fada don me zan masu girki haka suda sukazo ganin daki kawai ai yanzu zasu tafi na dan marairarice suka zauna sukaci banda mahaifiya dako ruwa taki tabawa sai hankalinta data mayar kan waya.
Mikewa nayi tsam daga gefen Ammi din na nufi inda take zaune batayi aune ba taji na fado mata a jiki nasa kuka ko sau daya tun zuwanta hakan bai faru a tsakanin mu ba da ita.
Bata hanani ba ta kyaleni har masu saurin hawaye suka fara kwala a cikinsu saida nayi mai isata Ammi ta taso tazo gen kujera tana dagoni tare da fadin hai Fatima ai yanzu ba kuka a gareki ki godewa Allah lokacin kuka ai ya wuce gareki yanzu.
Gaki a dakin auren ki Allah kuma ya baki miji dan albarka dan mutunci ko jiyan nan da kukaje kun tafi kun barmu da mamaki don alherin daya kai muna bai faduwa Fatima.
Ashe hakan ba godiya yakamata kiwa Allah ba inda kin sha wuya yanzu Allah ya duba maki wahalanki ya baki miji dan albarka dan mutunci da zai kula dake da kowa naki matukar kin masa biyayya kun zauna lafiya dashi.
Allah na tuba in ba abinda da mahaifi ba da take gani kamar in ta tafi yanzu ta tafi kuma ke nan ai ke Bintu farin ciki ya kamata kiyi a yanzu Allah ya cika maki gurinki kinyi aure a cikin gata ba yadda akaso ki wullakanta ba.
Lokacin wuya ko kuka ya wuce a gareki yanzu sai dai hamdallah waya taba zaton ko kwatankwacin hakan a gareki sai gashi Allah ya rufa maki asiri ta yadda wani bai taba zato ba hjy balaraba ta fada.
Bintu kan taga duniya Allah kuma ya rufa mata asiri don bata da alhakin kowa a cikin mu kaf gidan nan koka batawa Bintu rai don taji haushi ita lokacin ma take maka alheri kai.
Aimu Nuraru ta haifawa ya ba ita ba tunda mu mukaci gajiyan haihuwa kowa kuma ya sheda hakan Allah dai ya shigewa lamarin ki gaba kiyi hakkuri don Allah ansan akwai zafi hakan amma ko can kike tunda Allah yayi mijin ki na nan sai kun rabu kinzo nan din.
Yanzu ai wata kila ranon ki ya jefo mahaifiyar ki garin nan haka abin hake ga Allah shike tsara komai yadda yaso ga bawansa ki saka imanin hakan a zuciyar ki aiba rabuwa akayi ba.
Sun dai ta ban magana kaina yana duke ashe itama mahaifiyar tawa hawaye takeyi lokacin saida naji tana fadin Allah ne shedana hjy Laraba kullun da yarinyar nan a raina.
Nayi sadaka ba adadi a kanta idan tana raye ubangiji ya tsare min ita a duk inda take nayi kuka dare nayi na rana alkawari kawai nayi cewa nasan muddin ta girma zata nemeni idan hakan ya farune zanzo gareta gashi ko Allah ya nufa lokacin hakan yayi garemu.
Shine ya shigo yayi mamakin ganin su yana gaidasu yake fadin bayace idan sun iso na kirashi ba kafin na bashi amsa don kukan da nayi abu ya tokare min zuciya nake ji lokacin.
Ai bamu dade da zuwa ba hjy balaraba ta fada ya sake tambaya idan tafiyan yana nan Ammi take fadin yana nan insha Allahu gobe da safe zamu bar garin nan zuwa kano daga can da asuban washe gari zasu bar kasan nan.
Don daga nan saudiya zasu tafi wani buki daga can zasu koma gida insha Allahu ashe akwai sauran tafiya ke nan Allah ya kaimu lafiya ya fada suka amsa da Amin.
Yayi yi yunkurin tashine tsaye Ammi ke fadin Bashir kayi hakkuri don Allah zaman aure sai an hada da hakkuri a rayuwa don mu mata komai girman mu hakkuri ake damu a zama.
Kai babbane kai kuma keda gidan ka abinda duk baka so kana da daman tsawata mata ta daina ga iyayyenta nan ko mun tafi su suna nan zasu rika lekoku lokaci lokaci ubangiji Allah ya baku zaman lafiya da zuria dayyaba masu albarka.
Ina ji ina gani suka tafi nayi kuka kuka sosai saida ya kamoni ya rugumeni a jikinsa muka koma ciki dakinsa ya wuce dani direct ya zaunar dani saman gado ya dauko ruwa ya ban har lokacin baice min komai ba.
Ban daki ya shiga ya dan jima a ciki ya fito da alwala yana fadin ki tashi kiyi sallah la,asar ya gabato in kin idar ki kwanta ki dan huta gobe kuma zamu bar garin nan zuwa Abuja ina son a duba Visa dinki idan baiyi expiring ba zamu bar kasan nan wani sati insha Allahu .
Haka na mike na koma dakina a can ma bayan na idar da sallah saida nayi kukana mai isata kafin nakai kwance nan inda na idar da sallah din na kwanta.
Barci na danyi kadan na tashi tunda ban saba kwanciya bayan la,asar ba sai hakan ya zamo min daban me zan dauka dayace na shirya don ban san tanadinsa ba can Abuja gashi ba zama zamuyi ba koda munje din .
Allah ya taimakeni sai gasu Nura kamar sun san ina son kiran hassana wayanshi na karba bayan na basu abinci sunaci na koma na kira hassana da maryam din mama Uwa.
Sai da Nura zai tafine nake fada mai zancen tafiyan mu Abuja din nake tambayanshi yaya za ayi da zancen karatun Aliyu ke nan don banson in tafi ban san matsayinsa ba.
Muna kan maganan ne sai ga Boss din ya fito inda nake zaune yazo ya zauna gab dani ashe yaji me muka fada yake fadin kafin mu bar garin nan gobe za a kaishi school insha Allahu.
Amma na kwana da badon yace baison zaria ba can zamu kaishi barewa college zaria inda mukayi karatu nida Abbas amma yanzu za a nema masa wani nan cikin gari na kudi.
Dan murnan farin ciki yasa yana washe baki a raina nace zaka fada saida muryan Boss ta katse mu da yake fadin amma fa sai kayi mi alkawarin zaka dinga cin na daya duk term.
Shigowan su hassana dasu maryaman Ammi ya dakatar damu daga dariyan da mukewa Aliyu din bayan sun gaisane take fadin kai kana nan ga mai mashin can yana ta fada har wajen baba yazo ya kawo karan kafa.
Jin hakan yasa Nura din ya zabura zai fita sai kuma ya tsaya yana fadin to Bantu sai munyi waya ke nan ko nace insha Allah yayi muna Allah ya tsare lokacin ya riga Nura din fita gidan .
Ashe ya tsareshi sunyi magana ya tafi mun dade dasu hassana a gidan su suka zaba min kayan da zan tafi dasu suka shirya min daki nan maryam tazo ta samemu mukasha fira kafin su tafi gaskiya aure ashe wani abune sai mutum yakai zuciyarshi nisa idan yana amarya.
Don kuwa bayan tafiyansu ne naji gidan ya koma min shiru lokaci guda ni kadai kamar manya a gidan hakan yasa na koma dakina na kulle kain bai dawo ba sai bayan sallah isha,i ya shigo.
Abinci ya nema yaci kafin ya shiga yayi wanka bai fito ba nice na sameshi a dakinsa waya yake saidai bai dade ba naji ya kashe yake fadin akan me kikai kuka dazun Fatima ?
Jin hakan yasa na kallo shi kasa bashi amsa nayi na dukar da kaina sabanin abinda nayi tunane naji lokacin a bakinsa don cewa yayi ko ina takurawa rayuwan kine a dan zaman nan naki.
Da sauri na dago kai na dan kalleshi ina fadin sam baka fahinceni bane karon farko da nasan mahaifiyata a rayuwana ke nan tazo kuma bamu zauna kona sati daya ba a tare zata kara barina ta tafi.
Wanan yasaki kuka bayan kina tare dani kinsan halinda na shiga ganin kina zubar da hawaye kiyi hakkuri haka Allah ya tsarowa rayuwanki tun farko nakima da sauki bisa gani da bazan kara ganinta ba balle in kyautatawa rayuwanta.
Hakan daya fada yasa naji wani iri a zuciyana don gaskiya ya fada da ace ta mutune fa aiko ganinta ba zan saki yiba yadda naganta a yanzu.


ZAINAB IDRIS MAKAWA







[21/12, 9:08 pm] +234 803 159 6352: KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
1?? 0?? 0??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Mun isaz Abuja lafiya gida mai kyau mai tsari a tsakiya Aso gidan yake unguwa mai tsabta da ma,ana a cikin Abuja duk da shigan dare mukayi hakan bai hanani ganin kyau unguwar ba tafiyane mai kama da sada zumunci a tsakanin mu.
Donko ta iyalan aminai akayishi mu uku mata sai yaransu dana yusuf dana Abbas suna ta hiransu a mota nikan kalla ban tofa ba don bakuwa nake a cikinsu lokacin.
Saidai idan suyi dan abin dariya na dan murmusa ko on kinji muryata wani yaro daga yaransu yayi wani abinda da yashi dan kuka a lokacin zan dan lalasheshi.
Sai daga baya na fahinci wanan tafiyan da suka hada amma fa a hasashena nayi wanan din na farko kamar suna son sabo a tsakanin mune don yadda suke.
Sai nabiyu zasu rakani kamar sune matan da zasu kaini dakina sosai don a cikin ba,a sukan jefo min magana mai kamar nasiha Yusuf baya motan wai sai washegari idan ya dawo daga bauchi zai taso don suna kokarin kai branch dinsu a can bauchin na company iPhone yanzu yake wanan zirga zirgan shiga bauchi.
Har Allah ya kaimu lafiya a bakin matar Yusuf naji sunan unguwar da take fadin Oga Bashir ka huta yanzu ka fita cikin hayaniya kana unguwar manya ganin kuma a yanzu ai wahalace garemu.
Kamar yadda ban faye magana ba sai jefi jefi shima hakan ne sai Abbas ne ke kokarin jansa da fira ko yanzu ma kalma daya ya bata amsa dashi shine insha Allahu kuma nan da dan lokaci ai kun bar wanan unguwar da kuke.
Amma zakiya sai naga kamar unguwar naku ai ba matsala Abbas ya fada ta dan tareshi da fadin ni fa bana son yawan hayaniyan nan kuma kabilu sunyi yawa ko don yaran nan nan gaba ina son mu bar wajen nan.
Zakiya ke nan a garin nan yanzu inane ba a cakude ake ba ai Allah ne kadai ke tsare bayinsa a duk inda mutum yake hafsat matar Abbas ta fada don haka suke magana kamar suna challenge din junansu duk na fahinci wanan a dan tafiyan namu.
Da naga saurin kaiwa Abujan da mukayi a ranan don da yamma sosai muka bar kaduna sai gamu cikin Abuja wajajen takwas da rabi na dare mun isa.
Shiga nan fita nan sai gamu a gidan nasa mun tsaya nan suka kuma fara yabon gidan can a bakinsu ni dai ina kallonsu mun fito mun shiga gidan ina rike da yar wajen yusuf karama uwar ta dauki babban don tayi barci shi bashir ya dauki babban yar Abbas da itama tayi barci muka shiga ciki dasu.
Bakina yana dauke da sallama da adduan tare da fatan samun kariya a zamana cikinsa daga ubangija Allah mahaliccin sama da kassai don hakane ban iya furta komai ba.
A nan hadaden falon muka shimfide yaran ina kokarin tashi nayi alwala naji hafsat ta rigani fadin bari nayo alwala na sauke wanan nauyin ta mike naga ta shiga wani daki dake gefen falon.
Lokacin muryan matar Yusuf ya ziyarceni tana fadin kinga dama ina son number ki don mu dinga waya muna gaisawa ina son mu zama tie dake sosai mu zama aminai a tsakanin mu .
Ayyah ba waya yanzu a hannuna tun ranan dinner wayata tana hannunsa tayi min wani irin kallo kafin tace wai duk kwanakin nan baki da waya well bakina da number a kanki ba bani na saka a nawa naji.
Na dai bata tana fadin zan gwada lokaci lokaci idan zai shiga in ya mayar maki matar Abbas din tana fitowa daga dakin sai na mike na barsu a wajen naje na dauro alwalana nima nazo nayi sallolin dake kaina itama dayan hakane ta shiga tayi.
Abinci aka kawo muna ashe ganin da banyiwa Samuel ba tun safiyan jiya da muka hadu yana nan ya dawo Abuja shi ya riga isowa ke nan Abujan dama.
Mun zauna suna cin abincinsu hankali kwance ana hira ni kuma na dansha ruwan madara na haye kujera na kwanta lokacin matar Abbas din ta kalleni take fadin .
Dama mijinki yana complain bakya son cin abinci sosai kinga ko abin yana damunsa ke nan a,a garafa ki dinga cin abinci dom yanzu ba da bace bakici abinci ba ya gyara maki jiki yaya zakiji dadin kanki har mijinki ya gamsu dake.
Kai amma Zakiya baki da dama tace ai gaskiya na fada ciki da yunwa yaya harka zai yuyu ga mace harta gamsar da mijin ta yadda yake so kingani nan ko yaushe sai naji nayi nak dani don mijina zakine ko wani lokaci zai iya fado min.
Kai ke kan baki da dama wallahi ko yaushe aka hadu sai kin bar mutum da dariyanki ai gaskiya na fada mace bataci ta koshi ba ina zatayi nauyi yadda akeso ke nan ?
Zuwa lokacin naji ta fara fita min rai don wanan zancen sirin data dauko min a zamana cikin manyan mata dana tashi kamar kishiyasu yasa na koyi abubuwa da dama haka nake da wayau kamar tashin kakar uba.
Don kakar uwace mai sagarta jika itako ta uba zakuyi ta kwamawa da ita tana sonka kana kuma saurin laifi a wajenta nan da nan kunyi fada kuma ku shirya.
Amma idan jikokinta na yarta mace suka shigo nan zakaga so zallah ana nunawa jika a rasa inda za a sakashi a aje mata ke nan shi sillar nono akwai karfin zumuci sosai gareshi.
Shigowa Abbas din dashi ya katse masu hiransu da Abbas din ke fadin har kunci abinci suka amsa da gamu muna ci dai bamu karasa ba muna saukewa amarya albarka a gidanta.
Zaune yakai a daidai lokacin nake kokarin tashi zaune don jin muryoyin mazajen da suka shigo lokacin wurina yayo direct yana fadin kin gaji ko Fatima akwai gajiya har yau bamu huta ba yakai zaune shima a gefena daidai inda na tashi din ya dan shafo fuskana cikin taushin murya kamar mai rada yake fadin.
Bakici abincin ba ko kafin na bashi amsa ya daga yana cewa Abbas Samuel ya zo yaje nan kasa ya sayo suya kada ya bata lokaci ina shi
ko yaran nan basuci wani abuba don gasu nan kwance.
Ya juyo yana fadin munyi waya dasu Ammi suna kano sun isa lafiya da safe su mum zasu tashi karfe hudun asuba ya fada yana kallona jin hakan yasa na dan gyara zama ina fadin ubangiji Allah ya kaisu lafiya nasan Ammi sai jibi zata bar kano zuwa gashuwa ita yace hakan tace dama na lumshe idanuna kafin ya mike tsaye ya bar falon don.
Abbas din ya mike shi yafita da kanshi bai dade sosai ba da fita ya dawo lokacin shi ya shiga ciki ledoji biyu ya aje muna yana fadin su taso ya saukesu sai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login