Showing 339001 words to 342000 words out of 347556 words

Chapter 114 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8721

na fara takawa zuwa gareshi ya kamo hannuna ta yadda na dan fada a rabin jikinshi a cikin kunnuwa yake fadin tunda nake ba wanda ya taba zaunawa dani yai min wanan bayanin haka.
Saike yau dana samu har kika iya kallon idanuwana kika fada min gaskiya irin haka insha Allahu zan duba maganganun nan naki in aikata wasu daga cikinsu don akwai abubuwa da dama dani ya kamata na toshesu garesu amma saboda halin da muke ciki naki yin hakan.
Mun dan jima kafin mu sauka kasa sai sha biyu da wani abu dakin su sister ya fara nufa ya duba jikin jamila kafin mu dawo dinning mu zauna muyi breakfast.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,



HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Sakamakon dan daga bukin da gidan amarya sukayi har yaso ya kawo cecekuce a tsakanin gidajeb biyu inda hjy Laila ta kira dangin amarya tana karanta masu hauka.
Suma sukai fushi suna mayar mata da martani karshe dai sukace sun fasa bada yarsu don su ba,a kawo masu iko da mulki don dai suke da yarsu da alhakin aurar da abinsu don haka sun fasa tunda ba da,a acikin harkan.
Hakan ya jawo cece kuce a tsakanin dangin miji wasu nagoyon bayan hjy laila wasu kuma suna ganin ba,a kyauta ba har suna ikirarin cewa ango ya duba a cikin dangi a aura mashi suba gidan amarya kunya.
Shi kuma yana son matarsa don haka yaki yarda hakan yaso tayarda babban tanzoma a tsakanin su angon da kansa ya kira Boss yana fada mai abinda ke faruwa cewa hjy Laila ta kirasa ta zageshi sai ya nemo mata a cikin dangi ta lissafa mai sunan yan mata a dagin sai hakan ya daga mai hankali.
Ya kira Boss hankali tashe yana sanar masa da abindake faruwa zancena dashine ya fado mashi a rai yace ba zaka nema ba kuma ba zamu takura masu akan date din da suke bukatan aurar da yarsu ba.
Ya nemi iyayyensu maza a waya ya sasanta masu zacen karshe suka yarda da zancen Bashir din suka koma yabon shi don hujjojin daya kawo masu na illan yin hakan.
Kuma sun gamsu dashi bama mijin hjy laila din data shanye baida katabus a wanan karon saida ya motsa yayi ta maza yaciwa matar nasa mutunci akan abinda tayiwa wa yancan aka turo aka kuma bada hakkuri.
Karshe data gane daga wajen Bashir matsala ya fito mata ta dinga zage zage kan cewa don shi ya auri ballagaza wace ba yar kowa ba yake kin dan uwansa ya aure a cikin dagi zasu zuba dashi ta gani.
Sai kuma duk zancen ya dawo masa akunne ya shirya zai nuna mata shine kuwa a cikin hikima ba tare daya fada min ainihin abinda ke faruwa ba yake koyar dani wasu dubarun sarauta da akidodinsu tare da jamin kunne son gudun ya samu matsala wanda nake haddace hakan tare da kiyayyewa.
A bamgaten zancen auren sister kuwa ya turasu gida sunje sunga baba wanda hakan yazowa yan gidan mu a bazata cewa hassana daga zuwa wajena na dan lokaci ta samu mijin har ana zancen aure a yanzu.
Nan tsegumi ya dan fara tashi samira hankalinta ya tashi take jin wani hassadan mu yana bunkasa a ziciyarta itako Usaina ta nuna farin ciki da abin alherin daya samu yar uwarta ta daga waya ta kirani tana min godiya.
Dariya nayi ina fadin sister kinsan ku din masu sa,ane fa komai a cikin sa,ayake zo muna mu kema Allah ya kawo maki naki rabon a hada auren da naki ayisa lokaci daya a rana daya.
Ta amsa da amin sister don nakanso adduan ki saboda na kula yan amin sukan amsa maki adduan ki muka kwashe da dariya munyi hira sosai da ita a karshe muka kashe wayan kan hassana zata koma kaduna din don abubuwa su kankama a gabanta.
Wanann komawa yasani cikin kewarta bayanta ta tafi inda nadanji sanyi jamila tana wurina anbar min ita dasunan jinya nikuma harga Allah na riketa ke nan ba komawa kaduna sai dai idan muje ganinsu don yanzuma kokarin in nema mata gurbin karatu nakeyi a nan Abuja.
Wanda saida nayi shawara da mahaifinsu ya yarda in riketa a wajena din nakuma rike na tura jamal tare da bashi hakkurin cewa idan ya gama karatunshi na secondary zai tafi jami,a zan dawo dashi kusa dani mu zauna amma ya rike sirine tsakanina dashi hakan ya yarda a cikin murna.
Ni nasan akwai maraice wajen yaran don basu samu kulan daya dace ba nima da bata haifa ba ina kewanta ballesu data haifa da cikinta suke cikin kadaicin mahaifiya a yanzu don kiri kiri yan uwan uban zasuyiwa yayansu abu su kyalesu acewansu ai mahaifinsu yafisu hali yayi masu mana shima.
Komawan sister gida suka fara samun matsala da samira dakan sake habaici har abin ya zamo fada a garesu wani lokaci sai manyan gida sun shiga sun rabasu.
Allah cikin ikonsa hassana ta hadu da wani dan banki mutumin zamfara suka sasanta kansu akan suna son junansu ta bugo min nace indai tana sonshi tayi abinda hakan baida matsala ai.
A gaban mama mukai wayan bayan mun gama waya mama ke fadin kuna jawo mi zancen aure a yanzu ko na hassana din ina zan iya don kawai ku kunyatani a idon jama,a na nake da abin maku aure a rana daya ku biyu.
Budan bakin hassana a cikin takaici taba uwar amsa da cewa da kika san baki da abin auren mu rana daya mai yasa kika haifomu rana daya lokaci guda don sun fetsara idanuwansu ba kunya a yanzu.
Sai hakan ya zamo masu fitina har gaba baba yayi masu alkalanci aka sasantasu da uwar tasu baba kuma yace aure ba fashi yayi niyar haka kuma bazai fasa ba tunda Allah ya kawo masu mazajen aure.
Hassana take fada mi rikicin mama da Usaina din wanda banji dadin hakan ba gaskiya muyi waya na nuna mata kuskurenta nakuma roketa taba mama hakkuri ta kwantar mata da hankali Allah zai rufa asiri insha Allahu ba zamuyi kunya ba da rufin asirin Allah muke ko yaushe ai Allah keyi ba mutum ba.
Watan haihuwana ya kama muna zaune yake fadin na shirya zan tafi Somalia saida abin ya ban mamaki yace kina mamakine a wurin mama zaki haihu don hakane nayi taja maki lokaci ban kaiki ba ai saboda mama ta samu tayi buki can itama duniya tasan ta haifa naji dadin hakan sosai muyi haka da kwana hudu Ammi ta iso Abuja don itace zatayi min rakiya zuwa Somalia din.
Zan bar Jamila a wajen iya saboda karatu kuma nasan iya zata rike min ita amana don yadda na fahinceta ba matsalan insha Allah.
Nakira baba don in masa bayani yace mijinki yayi min bayanin komai Fadima haka da yayi ya kyauta nima hankali zaifi kwanciya idan kina hannun mahaifiyar ki din.
Yayi min fatan Allah ya saukeni lafiya ya ban addu,oin da zan dingayi a kullun ina shafawa a cikina izza,jaace kafa bakwai da bissimillah zan dinga tofawa in shafe jikina dashi.
Sai Nasarminallah wal fattahul karim shima sau dari da safe da yamma nayi godiya boss da kansa shida Oga Abbas da matansu sai matar mahaifinshi da Ammi ta saka ya dauko dole baiso ba sukayi min rakiya har Somalia din.
Mun samu taro na arziki sosai don ba wanda ya zaci hakan abinda na dan kula kamar sunsan boss a yadda suke masa ashe ko hakanne yazo ban sani ba har sau biyu ina gidanshi.
Na farko barina kaduna da yayi a lokacin sunje shida Oga Abbas wiein taya mijin Ummi sin murnan zaben da sukaci sai nabiyu kuma yaje masu gaisuwan yayan mijinta Abdullah daya rasu.
Sai zuwan nan namu nakeji ai yazoshi yaki fada min ne don laluran cikin da nake dashi din zuwa da matar mahaifinshi yayi rana don suna dawowa duk ta baradawa dangi abinda ta gano acan din har hjy laila uwar daba saida ta samu wanan labarin taja tsuki don bata so jin haka ba tana fadin aikin banza tunda ba a kasan nan take ba ai .
Abin ya bata mata rai don ya kara rusa mata plain dinta karo na barkatai a yadda ta shirya shine babu dan uwa da zaizo idan na haihu tunda ya hanani hurda da kowa nasu a family.
Sai gashi ba a kasan ma zan haihu ba a wajen uwata a can kasansu ya kaini nan take faman kiraye kirayen waya tana sheda masu bacin ranta.
Allah da ikonsa kwana hudu da dawowansu na haifi dana lafiya abisa irin al,adan kasan ba tare da ankaini asibiti kafin wani lokaci labari ya kawo Nigeria ko duk wanda keda alhakin ji yaji cewa na haifu lafiya a lokacin .
Boss yafi kowa farin ciki da wanan albishir din haihuwan da Ammi tayi masu shiya dinga kiran yan uwa da abokan arziki yana fada masu wasu kuma yana tura masu text an haihu masa.
Wanan haihuwan yaja ragin mutuncin hjy laila a idon wasu da yawa ta yadda ta dinga ikirarin cewa bai haihuwa shi ba namiji bane dan luwadine dan shan jinine ya sayar da kololonshi ga tsafi an masa kudi dasu don yafi kowa.
Ashe duk hakan ba gaskiya bane tana batashi kawaine don sun rasa meyayi mata a yanzu da suka fara fahintar gaskiya a wajensu don sun gano ita macece mai yawan son kanta da yawa diyanta kawai ta sani sai ita.
A gaban kowa tana ririta diyan data haifa kuma zata iya aibata dan kowa taci masa mutunci agaban iyayyensa wanan na cikin abinda yasa suka fara gano ko waye hjy laila a yanzu.
Ba laifi yan Nigeria sinzo suna shida abokan shi su Abbas yusuf da hamza su hudu sai yan uwan mahaifinshi biyu maza biyu mata da sukazo.
Anyi suna a bisa al,adan kasan donsu komai nasu a al,adance sukeyinsa a wajensu aka,idan larabawa na tafarkin musulci gaskiya al,adansu yana da kyau dole kafin sati maijego tayi bul bul tagasu tayi kyau tana ci tana sha mai lafiya komai na gargajiya bana bature ba.
Tun ban saba da hakan ba dole na saba sosai don haka Ammi zata sakani gaba sai naci na koshi wai lafiyana dana yaro akewa kada inso kaina in cuci dan dana haifa din.
Anyi komai dasu kusan kwanan su biyar a can suka dawo Nageria har Ammi don iyali data bari a nan din suka barni da mahaifiyata taci gaba da kula dani.
A irin wanan lokacin na samu zama da fahintar ummina mace ce mai saukin kai sosai da fahinta ashe zato nake mata haka halinta yake da sanyi ko yaushe bata da yawan hayaniya bata da girman kai anan na gane ita na biyo.
Na fahinci ashe bata kulanine don idon su Ammi datake gani haka al,adansu yakesu akwaisu da kunya da kawaici akan komai hakama mijinta matashine sosai ba wani tsoho bane can saidai akwai dukiya don mafi yawan arzikinsu shine garken dabbobi.
Akwaisu kuma don Allah ya hore masu wanan gaskiya ba laifi saidai wanda kansa ya waye suke hadawa da gidaje da motoci a yanzu don wayewan kai da yanzu yakai ko ina a duniya shiyasa abubuwa suka dan sauya yanzu sun rage al,ada.
Yanzu kan sosai muka fahinci juna da mahaifiyata take ban shawaran in fara sana,a kada na yarda na dogara da abin miji don yana iya kara aure ko wani lokaci don haka ya zamanto ina da abin kaina nayi.
Itace ta zaba min sana,an shigo da kaya wanda ya danganci mata da yara tace a ko ina yafi shiga da sauri ya zamanto dai ina da wani abinyi a rayuwa.
Gwala gwalaina na hada na mika mata sai wanda tun ina can aka shiga dasu dubai aka cansu zuwa kudi amma suka bar kudin a hannunsu don nace sai nayi shawaran inda zan buda shagon.
Dagani har dana munyi kyau sosai sai shirin dawowa Nageria da muka fara gashi ya bugo min waya cewa sister dinshi ta dawo Nageria cikin murna nake fadin gashi kuma bana gida yace ai tana gidan ta daya saya masu ita da yaranta.
Naji dadin hakan a can kasan raina don dama ina tunanen yadda zamu zauna a gidan da ita da yaranta sai gashi Allah ya kawo muna saukin komai a sauwake.
Saida muka kara kwana goma kafin muka dawo Nageria koshi don zancen bukin su hassana daya tashi nan da sati biyu masu zuwa insha Allahu.
Don haka kodana dawo kwanan mu hudu Abuja muka rankayo zuwa Abuja dasu iya ga baki daya don komai ba a shirya ba sai fada da ake faman yi tsakanin baba da mama ana tonon asiri bukin yara ya tashi mama tace ita ko spoon bata aje ba.
Gori da zagi mama tacishi ga mutanem unguwa kowa yana zunden ta kan haka don tace saidai a fasa auren don rashin basira irin nata shi kuma baba yace ba zai fasa aure ba ranan daya saka meya hana ta tara tun farko da sai yanzu zata fara tarawa yaba kansa amsa da bokaye baki da abin yi suwaiba sai bin bokaye da malamai Altine ce kafanki wajen mugun abu.
Ire iren fadan nan yasa su hassana din suke bugo min waya suna kuka kan abindake faruwa tsakanin iyayyen namu biyu yasa na matsaya baban Abdallah muka taso zuwa kaduna ko hutu bamu samu ba duk yace baba ya kwantar da hankalinsa hakan ba matsala bane.
Dole inzo don inga komai ya kammala don kudaden daya bamu din ga kuma rikici kullun a tsakaninsu da Samira da yanzu ta famfare tana fitsara son ranta a gidan.
Muna dirowa garin suka dawo gidan mu komai a nan ake tsarawa ina wuta ya Altine dasu mama su sakasu sunce na asaricesu saboda kwadayi makiyarsu ta koma abokiyar shawaransu.
Duk su mama uwa sunzo gidan ganin Abdallah amma mama taki zuwa wai kafa yana damunta ta aiko su mama da zasuzo su gaidamu a cikin fara nace ina amsawa amma miji kan yana fushi da ita .
Don bata bishi zuwa Somalia ba aka kwashe da dariya nan aka dauko hiran rashin lafiyan mama din mukai mata Allah ya sauwaka.
Nikan ba laifi gaskiya saidai ince Alhamdullahi bini ,imatihi Alhamdullahi Alah kulli halin ga ubangijina daya bani ni,ima da daula na duniya da nakewa fatan mu dace da fiye da hakan a lahiran mu Amin.
Abinda yasa nace hakan don kiran da ya Ahmed din mu yai min yana min godiya kan abinda nida maigidana mukayiwa su yan biyu yayi tayi min addua tare da fatan gamawa da duniya lafiya.
A karshe yace don Allah hjy Binta ina rokonki sai naji kaina yayi wani girma da abinda ya fada wai hjy Binta kiyi hakkuri da duk wani haukan dasu mama keyi akan abin nan bakomai bane kin sani mama bata amfani da shawaranta saina maman tudun wada.
Wanda yanzu mun gane wallahi bake kadaice mama bata so ba har damu har damu mun fahinci cewa maman tudun wada mamace dai bata so itace dai bata gane ba mukan muna rokonki don Allah ki yafe muna abubuwan da mukayi maki a baya kurciyane da rashin sani.
Haba yaya nikan ba komai wallahi a zuciyana kiyi hakkuri dai nasan da hakan amma wallahi hjy dole mu baki hakkuri kan abubuwan da suka faru.
Don yanzu gashi kin sakar muna kunyan mu kin barmu da halin mu don Allah hjy ki gafarce mu sai naji kuka ya rikeshi sai abin ya daga min hankali sosai.
Shine na zauna ina wanan tunanen ni kadai da dare bayan kowa ya watse ni bintu abin tausayi a gidan mu yau nice Allah yaiwa daukaka da kowa a gidan mu yake son yin hurda dani.
Ni kuma ina rokon ubangiji Allah ya hore min nida mijina dake taimaka min abubuwa suke tafiya ya Allah ka hore mu da abinda zan ci gaba da dubasu suma ina masu fatan ya Allah ka buda masu hanyar alheri su samu walwala da wadata irin nasu rabon.
Don nikan yanzu Alhamdullahi Allah sai budawa mijina yake tun bayan auren mu shida kansa ya bude baki yana fadin fatima ke alherice a gareni tun shigowanki gidana nake kara ganin haske daga ubangiji ga al,amurana.
Shine kwangila yanzu a gwaunati shine businesses na abubuwa da dama dake daga mutun lokaci guda wanda yanzu sunan shi ke tashi a cikin matasa masu fada aji a kasa.
Buki kan ya kan kama lokacin samira ta yarda na fita har abada kan yanzu yadda taga na tsara komai kuma masu jere sun dawo suna fadin yadda gidajen nasu ya kasance.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login