Showing 267001 words to 270000 words out of 347556 words

Chapter 90 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8727

barnawa nagani wani takadiri haka naganshi jiya ya shigo suna magana da wasu mutum biyu.
Mostin Nura naji gab da kunnena yana fadin injin baki fadawa kowa inda kayan nan suke ba don da ansani suma ana iya binsu can akai masu hari tunda an kwashe daga nan din.
Na girgiza kai kawai sai ya tashi ya nufi wajensu isa din akaci gaba da maida ba,asi dama hakane sai abu ya faru kowa zaita kawo nasa ba,asin yana fada daga baya.
Hankalina na mayar a wayata sako nagani a ciki daga soja yana fadin yanzun nan zasuzo insha Allahu kada ki motsa daga inda kikefa.
Allah sarki sojana na fada asheko shiya turo min ma,aikatansu suka kawo muna agaji da ba haka ba bansan ya zata kasance muna.
Nima a take na rubuta mashi sakon godiya kan taimakon da yai muna din na tura mashi ba,a jima ba ya mayar min da amsa da sorry Fatima bani kaduna ina Enuguh nazo aiki a nan nakai wata bani kaduna idan na dawo zan shigo insha Allahu.
Allah ya tsare ya kare ya dawo dakai lafiya cikin iyalinka na tura mashi da sakon ya sake turo min da godiya na lumshe idanuna don tunane kan shakuwan mu a baya dashi.
Muryan su hjyn ya habibine ya katseni min tunane a lokacin da suka shigo ana gaisawa dasu din caraf ido mu ya hade dana hjy laraba da alama nayi mata magana tace ta gane itama da kai.
Da zasu tafine nace zan shigo dan anjima ko zan samu barci duk wanan abinda ake ta sintirin yi mama na daki kwance ta gama fadanta ta kwanta.
Fada tayi wai basuci ba basu shaba an jawo masu masifa a gida haka na rana daban na dare daban kamar a kainane farau aure har tayi ta gama ba wanda ya kulata a lokacin do kowa nashi ya isheshi a zuciya lokacin.
Ina wankane na sake jin muryanta tana fada daidai zan fito naji mama uwa ta amsa da fadin bari cewa ga banza kin manta sunan da kuka lakawa Bintuce KARAN DAFI KINFI DAN DAWA ANFANI.
To shine nan sunan kuwa gashi ya bita don ta zamo karan dafi har lefe akazo kwasa Allah bai bada sa,aba lefen wa kika taba ganin anbi dare a unguwar nan ?
Sai Bintu karan dafin gidan mu kai na girgiza na zauna na shafa mai a jikina na shafa da zancen daya bugo min waya yana fadin gamu hanya tafe.
Sai ji nayi ana masu sannu da zuwa suna karbawa har cikin gidan suka shigo amma wai mama bata shedasu ba a gun baba suka tsaya nan yana mayar masu da yadda abin ya faru.
Text message nayiwa Hassana nace ta fito gasu Boss nan sunzo duk su mama basu ganesu ba wai don sun dade basu gansu ba koda akazo zancen aure mazane iyayyensune sukazo wurin baba din tambaya.
Hassana din suka fito ita da Usaina suke fadin baba mazan Bantuce fa baku ganesu bane ikon Allah aiba zan shedashi ba dama duk zuwan da yakeyi nan ba saninsa nayi ba.
Aka kara gaisawa na mutunci dajuna nan Abbas yake fadin kada ku damu da batan kayan ko wani abu zaca turo masu tsaro a unguwar kamar sauran unguwa insha Allahu.
Sun dan zaga cikin gidan sunga irin barnan da akayi muna a gidan ina daki ban fito ba har lokacin da suka fito zasu tafi.
Oga Abbas ne ya kirani a waya gasu sunzo zasu tafi basu ganni ba wallahi ban iya fitowa kunya nake ji na fada sai naji ya kwashe da dariya yana fadin.
Ashe akwai yan mantan arziki haka har yanzu to mukan bama jin kunyanki ki fito da mutane muke suna aon suyi maki jaje akan abinda ya farune.
Nace ka basu hakkuri don Allah nagode kwarai Allah yabar kauna amma gaskiya ba zan iya fitowa ba yanzu ina cikin gida ina kallon ku ai amma gaskiya kuyi hakkuri.
Shi mamaki na bashi kwarai a lokacin ni kuma iya gaskiyana ke nan bazan iya fita din bane don haka kawai na tsunci kaina da jin wani irin nauyi da kunyansu a zuciyana lokaci guda.
Kallon Abbas din dake waya yana kwasan dariya yayi yace muje mana sai ya kwashe da dariya ina jin yana fadin kai kaji wai kunyan mu ake ji yanzu ba za a fito mu gaisa ba.
Shi kuma sai naji yace ta fito tayi maka me yace ohh hakane tsiyan da zaka fara shukawa ke nan nikan na kashe wayana na kwanta.
Nan yake fadawa abokan tafiyan nasu suma mamaki sukeyi wai akwai yan matan da suka saura da kunya haka a yanzu ashe ?
Ina kwance ina faman tunane a kasan zuciyana Nura ya shigo dakin yace mena fada maki Bantu dadina dake akwai saurin yarda wallahi haka kawai naji zuciyana bai kwanta ba da wanan tarin kayan nan a gidan nan.
Ni namafi kai zuciyata gun mama da kike gani don na ganta tana wani zance a waje suna ganina suka canza magana ita da wanan munafukan yarta din nan maman tudun wada.
Tun lokacin naji zuciyana tana yawan zargin hakan ashe nasu ma kadan ne masu shirin akwashe din gaba daya suna can daban suna nasu shirin.
Amma duk da hakan ai kai zuciyar ka bai baka cewa turosu akayi suzo su kwashe kayan nan ba don yadda suke magana kan kwangilansu fa ba kashi a cikinsa kaga ke nan an turosune suma.
Kai abin nan da daure kai yake daga bangareki ke nan ko daga nasa bangaren nace Allah masani koma waye indai zai barni a raye aimai saukine da badon Allah ya taimaka ba jiyan nan me kake ganin za,ayi a gidan nan .
Tunda sunce in ban fito ba kona gidan zasuyi ga baki daya suga jikin da zai saka kayan ke nan ko nifa abubuwan suna ban tsoro sosai gaskiya a yanzu.
Allah ya fisu kamar yadda yake kareki kullun daga masifun dake bibiyanki ki dubafa haka kawai kina kwance kamar an tadake lokacin.
Shigowan Hassana dakin yasa muka juya wajenta muna fuskantar ta tace Nura nima hakan yaban tsoro da mamaki kamar wace keda aljannu a kai don Allah.
Ke baki ganin yanayinta nina dade da sanin ba ita kadai bace wallahi nasha auna hakan a zuciyana sai kika tana abu hankalinta kwance ba wani damuwa.
Yanzu mama ke fada muna wai yace zai kara turo wani lefen wai ina kayan naki suke ne Bantu har yaushe aka kwashesu daga gidan nan ne wai ?
Ni ban sani ba na bata amsa ina dariya tabi da harara nace tambayi Ammi nikan ban san ya akayi ba idan na fada maki nayi karya gaskiya na yarda tunda kince in tambayi Ammi.
To shime zai turuwa kaya kuma tunda basu sace ba shi mama ke fada a daki wai ta dan juya ta kalli kofa tace kinsan mama da daukarwa kai fitina tana can tana fada a daki wai yana aon ya nunawa mutane riyane kawai bayan wanan da akayi.
Nayi magana shine ta hauni da fada nagodo na bar masu dakin nasan zasuyi daidai da usaina ita don naji ta fara fadin ke mama ina ruwanki ko dankine da zaki bakinciki da zai kawo kaya.
Nura kaji min mama fa harda fadin ya dai haukacene kila har baima san abinda yakeyi da kudi ba amma nan kuma kayan Samira itake zuwa nunawa mutane shi tunda tasan ba,ai abin kwarai a nan ba.
Waini dama har da kaya akai matane na tambaya cikin mamaki don ban taba jin labarin hakan ba ko ga wani a gidan mu hassana din tace kaya kuwa irin gwajon bakin ruwan nan na iyamurai ya kwaso wai sune lefen sai daga bayane nasan sun masa magana aka karo mata dogayen riguna da wasu turame haka gasunan dai ga kamarsu kayan.
To bagashi ya wuce ba yanzu har an manta anyi hakan kuma tana zaune lafiya da mijinta na basu amsa nace ai yawan kaya aure ko wani riya can bashine aure ba gaskiya mamata fada.
Wani gaskiya a nan wanan shine nuna hali ba bakin ciki ko kyashi ka kashewa abinda kakeso kudi tunda Allah ya baka halin yin hakan.
Hassana hasana kinko san matsala auren me kudi da kike wanan maganan haka bafa hakan na nufin kayi bankwana da matsalolin rayuwam duniya bane ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA
KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
8?? 5??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Don tsoro ysnzu gaba daya na daina kwana dakina dakin mama uwa nake shigewa na kwanta koshi a tsorace muke kwana dukan mu duk da mutane sun fada muna cewa ba zasu dawo bai saidai wanda ya turosu su kwashi kayan ya canza sallo kuma.
Canza sallon nan da ake fada shike tayar min da hankalina sosai dalilin hakan na dauko wani rama na ba gaira ba dalili ko abincin da nikan dan tsankwara yanzu sam na daina cima saidai abu mai dan ruwa zan samu na durawa cikina shike nan.
Sai hakan yasa ina ramewa a tsaye rashin uwar da zan budewa cikina taji damuwana yasa abu nacina a zuciya banda ainin yardadden da zan amayewa zancen inji sanyi yasa nabarwa cikina komai.
Ban kawo zargin kowa a raina kan hakan ba in ma wani zargine zuciyana yafi tsaya min ga yan gidan angon nawa da suka farayi masa bita da kullin irin halin nasu akanshi.
Me yuyuwa su din suka fito muna ta nan kuma don sunga alaman rashin yardan kalaminsu a gun iyayyena sai su juya zancen su mayar dashi wani abu irin haka nan tunane ya tsaya akan abinda ya faru din dani a ranan.
Ganin raman da nakeyi ranan baba ya kirani har dakinshi bayan mun gaisa ya jefo min tambaya Fadimatu meke damunkine kwana biyun nan duk kin canza kin koma wata kala dake haka shiru shiru fa rama da kika dauko yi kuma ?
In wani abin ke damun ki ki fadamin baki da wanda zaki fadawa damuwanki a yanzu bayan ni saiko Ammi a yanzu ita kuma bata kusa damu nasan da zaki iya fadawa wani dakin fadawa Uwa amma kila zance ne da baki son wani yaji kila.
Ko kuma zancen barayin nan ne ya tsaya maki a zuciya har yau din nan wanan da gani dama sherin makiyane ture akai muna dasu suzo gidan nan su kwashe kayan don bakin ciki.
Hakan kuma shi mijin naki bai nuna komai ba a kai tunda ya nuna dama an basu sai a kawo wani indai zasu barmu da lafiyan mu yanzu kuma ga yan kwana kwana duk sun zagaye muna unguwa dare da rana duk a sanadinki.
Jin yayi shiru yasa na sauke numfashina ta yadda har yana iya jini alokacin da akwai wani abindake damunki ko yanzu kin nuna hakan a gaba meke damuwan rayuwanki don Allah ?
Jin ya ambaci Allah yasa dole in fada mai a yanzu na dago da sauri na kalleshi ina fadin dama baba ba komai bane sai kuma nayi shiru can na dago nasake fadin baba dama ba komai bane sai irin yadda komai nawa yakanzo da akasi a rayuwa.
Baba ina tunane yanzu a kullun wasu irin mutane zan tafi nayi rayuwa dasu kuma bayan na nan gidanmu dana taso a cikinsa baba kasa badon Allah yayi min tsaye kaima kana tsaye a kaina ba da bansan irin abinda zai faru dani ba gidan nan.
Ya dan murmusa yace Fadimatu tunda kinsan da hakan nan saiki kara godewa Allah dake kareki a kullun cikin rigigimun duniya.
Ina gode masa kullun baba yace to ki kara a wanda kike masa Allah yana tare dake a kullin insha Allah ko can inda zaki yanzu haka ubangiji zai maki jagora a kansu ki natsu ki daina wani tunane a zuciyarki.
Ki barwa Allah almarinki yai maki jagora akan komai fadimatu kedai ki shiga da zuciya daya ki zauna da kowa lafiya nace to baba ya danyi min nasiha kafin nafito daga wajenshi din zuwa dakina.
Na samu hassana a dakin kwance nace ashe kikana nan yayin da ita kuma ke fadin na dauka kina bayine fa nace ina gun baba tace ya kirakine kan auren da akace an kara matsowa dashi kusa kuma yanzu .
Kusa kumafa kikace kamar ya kusa ban gane ba don baba bai min wanan bayanin ba tace ba ance gidan shi angon naki bane suka kara roka hakan tunda sunce su basu son akai maki komai daga nan gida a dai daura auren ki tare dakinki saboda abubuwan dake faru a nan yanzu.
Don Allah kibar zancen nan sai kace ance masu gidan namu sun gaji danine da za,a korani zuwa wajensu kome ke yar iska ta fada sai na kallota don inji abinda zata fada.
Ke yanzu ba abin fariciki bane hakan ya sameki da har wanan guy din ya matsa haka a kanki ke kanki kinsan yafi karfinki wallahi shi rabo daine inya rantse sai maishi.
Mamaki taban yasa nake binta da kallo tace kwarai tsakanin ki da Allah kin taba mafalkin kai wanan matsayin a rayuwanki ko kwatankwacin hakan ma don Allah ?
Dan dariya na sake mata don ni ta gama danima nake ji a yanzu tace ai tsakani da Allah zamu fada nace nakai har na wuce tunda ba mutum ke tsarawa kansa rayuwaba ai.
Bayan haka kin dai san na hadu da wasu kilama sunfishi komai wanan kuma na daban ne ai baki dai son zancen nan to mu barshi muyi zancen anko kada ai muna girshi.
Usainace ta shigo tana fadin kunyi zancen anko din ne tace gashi dai mun far don bata dakin kodana shigo gara dai ayi ki aikawa kawayen ki da wuri suma su sheda hakan.
Wanan mai wasa da dollars din ai kamata yayi yaiwa yan mata anko gaskiya ki bamu lambashi muji iya abinda zamu iya tsarawa ta bangaren mu.
Don kada ai muna busasshen buki irin na Samira data sha cika baki karshe akazo ko dan waliman nan a lalace akazo akayisa babu komi ba kuma wani taron kirki.
Usaina Usaina daji bai gama cin wuta ba akace ba aiwa kututure barka ita samira ta kama dakinta ga kuma Bantu yanzu itama aurenta zatayi ta huta mu kuma bamu san makomar muba har yanzu.
Karki manta daga Samira har Bantu din duk mune a gabansu wajen haihuwa har zaki tsaya kinawa auren wani sherin baiyi kyau ba nifa irin wanan tunanen yasa kikaga sam yanzu na bar biyawa shagala da duniya koba gaskiya ba ta kalloni.
Nace hakane amma abin daga Allah ne ai wani lokaci koda daki dayane sai kiga kanwa ta riga yaya aure ana haka da yawa ai yanzu.
Balle insha Allahu kuma naku mazajen na nan zuwa nan bada dadewa ba in Allah ya yarda ido ta lumshe dagani abin na damunta tace min amin kedai Bantu .
Shiyasa nake sonki a raina don fadin gaskiya to gaka da abu kaje gulman nawani gara da Samira koba komai dai a ace tana gidan mijinta zaune ai.
Kuma insha Allahu nakun yana tafe da yardan ubangiji mutum dai ya kama kansa Allah ya sanar masa yanzu bagani ba wallahi ban taba sakawa raina aure a yanzu ba da Allah ya tashi ikonshi a kaina sai gashi kin gani auren yazo min kowa bai zata abu kamar almara don Allah.
Munkai wani lokaci suna nuna min damuwansu har yadda mama take shige shige a kansu da damuwan mama tunda taji zancen aurena yadda tasawa kanta damuwa ashe.
Duk saida suka labarta min har hassana tana kuka tana fada min yadda mama ke aiwatar da wani abin bata sonshi ko kadan nidai hakuri na basu kan hakan nace suyi ta fadawa Allah damuwansu da kansu sukuma yawaita sadaka ko yaushe.
Nan zancen anko din ya wuce ba,ayisa ba kuma don yadda suka shagala da hira a lokacin har yanzu uwar ta fara zarginsu a kaina sukace wai in sunyi siri a daki sai suzo su fada min don na shanyesu sai bina sukeyi suna yannena ga haihuwa kuma.
Nasan wanan da dadewa do ko wani lokaci idan rajimu daki shiru zatayi ta kwala masu kira su fito in sunyi nawa wajen fitowa nan zata fara zagi tana fadin.
Kanwar uwarku ta hanaku fitowa zuwa wurina ko sai kaga sun fito suna fadin haba mama wanan ai baiyi ba don kawai bamuji ba haka zata shiga daki dasu tana jinini a kai.
A bakin Ammi na samu labarin date din bukina a ranan kuma shima Oga Abbas ya kirani yana min sheri


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login