Showing 102001 words to 105000 words out of 347556 words

Chapter 35 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8801

ai abin yayi yawa gaskiya kullun abu daya tun yarinyar nan bata san komai ba har yakai yau ta fara baku amsa daidai da abinda kuke fada mata .
Mahmoud dai koshi ya saura a duniya ta fada maku bata auranshi tome kuma yasaura basai a bashi duk wace kuke son bashi ba zancen ya wuce mama uwa ke fadin wanan zancen suma ba kyalewa sukayi ba sai abinda bakinsu ya rage masu a lokacin.
Mama sai cewa take tana kumfan baki mu zuba nida ke a gidan nan bintu aure saidai kiga yan uwa nayi ba dai ke da auruwa ba garin nan.
Assha yaya ke da kanki kike fadan haka kuma na sake lekowa bayan mama uwa tasa na shiga daki na kara lekowa nace wallahi na tabbatar da idan ki zaunar dani gida ke kuma har yayanki kaf kuda aure kuma sai hange .
Wai bintu banace ki bar zancen nan duk wanda ya zalunci wani ai Allah yana kallonsa ke uwa naga kina son ki shigewa zancen nan to bari kiji ko ke kika saya an sayar maki don dama nasan irin munafuncin da ake kullawa a gidan nan .
Dama samira ta fada kin canza yanzu kin famfare da kyau idon ki ya bude da maza gashi kuwa munga hakan dama yarinyar data fara sanin maza ai bata kunya ko shayin kowa.
Basai kin nuna muna idon ki ya bude a yanzu ba indai mamudane ke dashi sai dai lahira idan ana aure ni kuma na amsa da fadin don kawai ban ra,ayinsane a zuciya dakunga tsiya a gidan nan.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
3?? 1??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Mun dauki lokaci muna abu guda dasu kafin nagaji na kyalesu don gidan ya kicime ga baki daya duk wanda yazo sai suce ba komai son kada aji meya kawo fadan a tsakanin mu.
Bayan baba ya dawone tun a waje mutanen unguwa suka fada mai yau gidansa tun safe ba dadi fitana matan gidan keyi da yara su Isah mai shago ke nan suke tseguntawa baba.
Don haka baba din ya shigo gidan da yayi tsit kamar ba kowa a cikinsa sai dan jefi jefi kake jin magana yana tashi idan ya dawo budan kofanshi dake bada kara na daban a gidan ake gane cewa ya shigo gida.
Don da makullin shi yake fita duk inda zai tafi sai ya dawo ya bude kofan nasa ya shiga don haka wanan dawowam da kowa ke dakonshi aka san ya dawo gida.
Malam ka dawo mama Lanto dake tsaye kofanta tana daura dankwali ta fada ya wani juyowa rai bace yace Allah ya dawo dani ya tura kofan ya shiga daidai lokacin mama itama ta fito daga dakinta da sauri ta kafa kujera ta zauna a kofan nata.
Ya dan dade a cikin dakin kafin mama Lanto ta nufi dakin nasa don itace da girki ranan tana shiga mama tace ina nan da bakina inji wata munafuka ta fadi ba daidai ba.
Daidai da mama uwa ta fito tace duk gidan dai munafukai muke harda wace kuke dasawan yanzu ma ba,a barta ba ke nan balle ni indon nice kun fada yarinya ta baku amsa kinga ankai gabar da ba,a son akai ai yanzu.
Mama irin figagun matan nan ne fitananu masu jinini da masifa ga daga harshe kamar ba ajikinta zance ke fitowa ba idan tana masifa har wasu jijiya ke taso mata a wuya suyi rada rada dasu.
Kai kai kai diban albarkan ya isa hakana wanda kukayi a bayana bai isa ba sai kun kara hada min jama,a karo na barkatai yanzu ma a gida.
Tun a hanya jama,a ke tarona suna fada min irin cin mutunci da kukayi yau a gidan nan duk bai ishekuba yanzu ma sai kun tayar a gabana to shege ka fasa gani gaku.
To malam banda hauka daga jin ka dawo ta dauko kujera ta kafa tana fadin gata ga mutum taji munafukin da zai fadi abinda ba daidai ba shine na bata amsa ai da duk gidan mun zama munafukai ke nan akanta.
Wani kallo ya bisu dashi yace au ashe bakison ace kinyi kikeyi wai yaushe ne zaki san kingirma ki kama mutuncin ki na babba a cikin gidan nan ne ?
Yanzu saboda Allah meya hada wanan fitinan hakane yana kallon matan nasa kowa yayi shiru ya kara fadin tambaya nakeyi fa akan me ake fitina hakane tun safe har dare ke Suwaiba yana tambayan mama ?
Shirun da tayine yasa mama uwa fadin akan dai zancen mamuda ne na gidan Alh mijin marigayiya safiya da yanzu yace Binta yake so ?
Sai kuma taja baki tayi shiru yace sai akayi yaya kuma ina dai ita Fadimatu nake jira dama tazo mu yanke hukunci ko idan ta yarda shike nan in kuma tace batayi an zauna lafiya.1
To shine da Altine taji tazo ta shigo da safe bayan fitan ka tana fadan maganan da bai dace ba har yakai Bintu ta fito ta basu amsa shine ya zama fitina tace zataje ta duketa muka hana sai ta mayar da fadan wurin mu mu duka.
Koba yaron nan mamuda ba insha Allahu shida Fadimatu har abada saidai gaisuwa da mutunci na zumuta ke kuma ga yayan ki nan sai ki bashi duk wace yaga tayi masa a cikinsu Allah ya basu zaman lafiya.
Ai bance zan basa ya ko wani abu ba amma dole in fada yadda na tsunci zancen daga sama a tsakar gida wai mamuda zai auri bantu a gidan nan.
Yanzu ma aiko kafin malam ya yanke hukunci kowa yaji abinda binta ta fada ko a kafa aka daura matashi ba zata ja ba don ba shine abindake gabanta ba ta fada kowa yaji yanzu dabara ta ragewa mai shiga rijiya kuma.
Uwa nasan dama a haka zaki kare gidan nan wurin iyayi da kinibibi dama ace kema son Allah da Annabi kike mata da sai mu kyale amma son dolene don abin duniya.
Badai in nabi ina samu ba zasu tayarwa baba da wani fitina a gida ya tsawata masu dole kowa ya shige dakisa yana hadiyan rai tunda basu samu fadawa juna magana a cikin masifa ba.
Washe gari tun da safe nayi wanka na shirya zuwa gidan hjyn saudiya don wanan zuwa ko yaran anty safiya ban nema ba saboda ubansu da kakansu mama data yamutsamin rayuwa dama nasan da zaman hakan amma ban dauka zata fito fili kiri kiri ta nuna min hakan ba a gaban kowa.
Tun daga haraban gidan naji wani iri don ga motocin da su Al,amin suke amfani dasu nan duk an lulubesu a cikin rigan mota hakan ya nuna ba za ai amfani dasu ba kuma maza.
Allah sarki Al,min cikin dan lokaci munyi shakuwan daya zama muna zumuta nidashi har mutum zai dauka a wuri daya muka taso dama dashi yanzu kuma ya manna min sabon shi a zuciyana ya tafi ya barni dashi don a kalla yanzu sunfi wata da komawa.
Iya mai aikice ta bullo ta wani kofan baya dauke da wani roba a hannunta data debo ganyen shuwaka a cikinsa tana ganina ta sake fara,a tare da fadin a,a mutanen zaria yaushe garin ?
Na dan sake fara,a nace shekaran jiya da yamma na iso jiya kuma ban samu shigowa ba ina gida tare muka shiga tana fadin ya karatu nace Alhamdullahi iya .
Hjy na zaune hakince nayi sallama na shigo ta dago tana fadin yar halak ashe kina hanya dazun nan muka gama zancen ki da Aisha fa a waya take tambayana ke.
Allah sarki mamata ashe kina hanya kasa na zube cike da girmamawa na fara gaida ita ta amsa min a cikin fara,a tana fadin dama Al,amin ya fada min zaki dade bakizo ba a yadda yaga kin kwashi kayan mai yawa lokacin da kika tafi na amsa da eh mama.
Na dan kaucewa zuwa gidane don gudun hatsaniya tsakanina dasu mama kuma hakan baiyi wani tasiri ba gareni don jiya da zuwana da fiti suka tareni saida rayuka suka kaiga baci.
Nan na fara bata labarin abinda ya faru kaf tsakanina da mama da yaranta akan ya habibi da kuma irin sherin da Samira tazo bayana tana kulla min .
Ikon Allah wa iyazu billahi riban me matan nan zata samu a wanan rayuwan har da takeyi hakane shin mutane basu tunanen rayuwan duniyan ba wani zama mai tsawo bane a acikin da dan Adam zai shagala yana abinda ransa keso .
Yanzu in akwai rabon haihuwa a tsakanin ku da mutumin nan wanan kadai ya isa ya kasheta kuma ayi auren bayanta ko bata mutu ba a nakasata tana kallo kuma ayi auren ba yadda zata iya.
Mutane suna son ja da hukuncin ubangijisu sai su dinga izgili da shishigi alamarin ubangiji kamar rayuwansu a hannunsu yake ita tasan abinda gobe zai haifar a gareki .
Harma dama ita din baki daya da take wanan rayuwa cikin izigli anya matan nan tana tuna mutuwa zai iya zo mata a ko wano lokaci ?
Mama bana fatan hakan ma ya kasance gareni don gaba daya na tsani duk wani abinda ya shafi wanan mutumin a yanzu balle aurensa kawai haukanta takeyi a kaina kawai.
Ki bar fadin hakan don mutum ne shima Allah na iya ikonsa duk lokacin dayaga dama ga bayinsa idan bakyason hakan ki barwa cikinki ki dinga addua Allah yana tare da ko wani bawansa koda kuwa kafirine Allah yana jin rokon bayinsa.
Haka kuma ya biya masa bukatunsa daidai kwatankwacin abin daka roko har fiyema da hakan Allah naba bawansa ko kuma akasin hakan.
Hawayene ke zuba min a fuskana shar ta barni ba tare data hanani zubar dasu ba a lokacin don tasa rayuwace ta kawo min hakan a cikin kaddarata.
Sai bayan dan wani lokaci take fadin jiyan nan mutanen ki suka bugo waya suna tambayana ki kuwa nasan sun tuna da girkin kine mai dadi.
Kaina dago da Idonuna da sukai ja don kuka nace sun isa lafiya ya Al,amin ya isa tace lafiya kalau shi yana Riyadh yanzu ya koma school don zaici gaba da karatune dama.
Allah ya bada sa,a nace ta amsa da amin saidai gashi nima zan koma na dan lokaci don Alh ya nuna bai yarda da zamana a nan ba shi yana can saidai lokacin da zamu dawo kasan in yayi mu dawo ga baki dayan mu yace.
Nisawa nayi na sake dan kallonta nace yanzu mama zaki tafi ke nan kema a rufe gidan tace towa za,a bari natafi ko zaki dawo nan ne ki zauna sai inyi magana da Alh ?
Da sauri nace a,a wallahi gidan mu ya isa idan nazo don dama sabodake da babana nazo garin nan gashi kuma ni zan tafi don yanzu baifi sati biyu na bar kasan nan ba.
Koda na koma zan dawo ke nan idan zaki tafi ta tareni da fadin ina hutu kukeyi yanzu akan me zaki koma zaria ki zauna kuma idan dai ba wani babban dalili zai kaiki ba ai mu zauna nan din tunda mahaifinki in yasan kina nan kina tayani hada gida kan na tafi ba zaiyi fadan hakan ba don ni da kaina zan je har gidan in rokeshi ya banike zaki tayani shiryawa.
Aiko hakan na dinga zuwa na wunin zan tayaki mama ba sai na kwana a gidan nan ba au kema bakya son zama nan ke nan ina guje maki fitinarsuce ai .
Ba damuwa mama na saba da wanan ai ba a dakin kowa nake zaune ba dakina daban da baba ya gyara min nan dai na bata labari harta tausaya min sosai.
Anan na wuni gidan hankalina kwance sai wajajen karfe biyar nayi mata sallama zan dawo gida na fito ke nan banyi nisa da gidan ba naga wata bakar mota ta wuceni da gudu can kuna sai na hango motar yana dawowa baya har zuwa inda nake.
Ban dago kai naga ko waye ba a motob din hakan ba dabi,ata bace yawan kallon mota idan ta gittani inda nasa kai kawai nake duba idan ina tafiyani.
Hjy fatima daga ina haka da kafa da yamman nan jin muryan ya Ibrahim yasa na dago kai ina kallon su cikin dan murmushi ganinsa da ya Mahmoud yasa na daure fuskata da sauri.
Ya kara fadin wai yaushe garin nan ne amma yau din nan kikazo ko don ko shekaran jiya na tambaya akace min baki dawo ba.
Nace shekaran jiyan nazo kafin ruwan nan ya sauko gaskiya baki kyauta ba tun shekaran jiya kina garin nan kuma bamu sani ba.
Tafiyana nake inda suke dan bina da mota a hankali har lokacin kuma shi ya habibi sin baiyi magana ba sai tuki yake da ya ibrahim kawai muke zance.
Shigo mu saukeki a gidamana ya fada jin hakan yasa na dan sake murmushi nace haba dai nan da gidane zan tsaya shiga mota yaya aina karaso ko baifi tako uku ba na shiga gida ba fa ?
Dan jan motan yayi da karfi suka kai kofan gidan mu suka tsaya kafin na iso har sun fito daga motar dauke kai nayi kamar ban gansu ba muka tsaya gaisawa da isah mai shago.
Sama sama muka gaisa ban tsaya ba nazo shiga gida lokacin naji muryan ya habibi yace ke fatima jin hakan yasa na juyo ina kallonshi fuska daure.
Amma kinsan don ki muka tsaya wurin nan ai yana tsaye ya rike marfin motarsa da hannu daya ya dora kafanshi daya saman motan daga kasa yana kallona fuska da yanayin dan damuwa .
Ni kuma na fada cikin mamaki nayi niyar juyawa in shige gida na sake jin muryanshi yana fadin kina daiyiwa Allah to don Allah ki tsaya ki saurareni kada ki biyewa zancen wasu can ki wahalal damu fatima.
Nasan kinkine don wani dalilin da a yanzu bai shafemu ba ra,ayine kawai irin na al,ada bawai Allah yace hakan ba a shari,ance So, ki tsaya muyi magana ta fahinta mukare wanan wasan a tsakanin mu kedai yanzu ba yarinya bace ai ko ?.
Motsin tafiya naji alaman wani zai fito daga cikin gidan mu a lokacin yasa na juya hassanace ganin hakan yasa na tsaya kamar wani magana mukeyi dashi a lokacin.
Tsaye tayi wuri daya bata karaso tafitan da tayi niyar yiba a lokacin ita kuma bata koma cikin gida ba sai kallon mamaki da take min wurin da take din tsaye.
Da sauri na dubeshi ina mamakin abinda ya fada lokacin zakice ba ya habibin dana sani bane dan gayu maiji da kansa da izza da takama ko a cikin gidansa.
Shine yau a gabana yake furta wanan maganan babu ko kunya ko nauyi a idanunsa ganin har lokacin hassana na wajen nace ban gane me kake nufi ba wai yaya ?
Ya dan gyara tsayi sosai har lokacin yana rike da kofan motan yace wato fatima tunda nake rayuwa ban taba fadawa tarkon so ba haka sai a kanki .
Don son da nake maki yanzu a zuciyana bakina ba zai iya furta irin tsananin son da nake maki ba a halin yanzu rasaki a yanzu fatima wani babban gine a rayuwata.
Jin hakan daga bakinshi da sauri naga hassana ta dafe kirji ta juya ta koma cikin gida a fusace ni kuma dan murmushi na sake na kalleshi da kyau nace.
Ya habibi ka manta koni wacece wai a gareka da kake kokarin daba min wani sabon kiyayya a cikin rayuwata a yanzune ?
Tsayuwa yayi da kyau yana sake marfin motan yace sanin da nayi koke wacece yasa zuciyana ya kwadaitu da sonki a yanzu don nasan ke alherice gareni.
Wani dan murmushi nayi mai dauke da takaici cikin dan dakiku ina girgiza kai kafin na koma na daure fuska ina fadin kana da mantuwa yaya.
Idan har kana son hakane don gyara halakan gidan nan da naku kamata yayi ace ka koma dakin maman biyu a yanzu ka zabi wata haka zaisa a san manufanka a kan hakan .
Amma zuwa wurina ba shine mafita ba a zuciyarka saidai kara jefa rayuwa a cikin wani sabon cakwakiya a yanzu don Allah ina me rokon ka yaya ka bar wanan zancen ka bari mu zauna lafiya a tsakanin mu don kaddaran dake cikin hakan yafi alherinsa yawa.
Tsaye yayi sororo ya zama tankar wani wawa a lokacin yana bina da kallo nace don haka ka sani tsakanina dakai har abada ba wanan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login