Showing 306001 words to 309000 words out of 347556 words

Chapter 103 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8723

tambayan Usaina don tafi dama dama yanzu.
Wai gaskiyane abinda su uwa ke fada Usaina din tace wallahi mama ba kari ciki gaskiyane abinda su abin su ance kamar sihirin gidane in ma mace bata a matsayin mace ba anyi karya ko sihiri suna gane hakan donsu basu bar gargajiya ba har yanzu.
Cabdijam wanan yar shu,umar gaskene yanzu ashe duk abinda mukewa yarinyar nan hasashen ba hakan bane ta da kimar ta da mutuncinta a tare da ita wayewan a iya fuska ya tsaya mata dama ?
Mama kune baku san batu bafa ko wanan mijin nata Allah dai ya nufa shine mijin sai anyi dashi yarinyar nan bayan wanan sojan da samira tayi sanadin rabasu ban taba jin ance ga wani saurayinta ba ni dai kan ban tabaji ba mama.
Ba fadin na wataba kun dai gani yanzu ai ta fada a cikin haushi tana mikewa tare da fadin masu kudin da mulki suke bin yayan tallakawa suna batawa karshe kuma suce tagari sukeso a auro.
Uwar daka tashiga har lokacin tana mita tana fadin yara kuke baku san komai ba ko makiran gwaggon nan naku tana ido kifi kifi tana iya shiga da ficen asirin budurci meye bamu sani bamu anyi dubun hakan muna gani ai.
Cikin dan lokaci na samu sauki zuwa washegari na dan fara komawa normal yakai yanzu haushinsa nakeji bibiyu ga haushin abinda yayi min ga kuma haushin fadawa wanan anty nasu har yan uwa duk sun sani.
Meye na bai yana wanan sirin ai iyamu yakamata zancen ya tsaya basai kowa yaji ba kamar anty larai tasan abindake raina washegarin da tazo take fadin.
Kanwata kada kiji hauahin hakan duk da kuna ganin an daina al,ada a yanzu ba dukane suka daina ba ki godewa Allah daya tsareki daga cikin uwayen dake bata zurian su masu zuwa ta hayar banzatar da kansu tun a waje.
Azo kuma ace ana son haihuwan da mai tarbiya bayan ke uwa ko uba kun riga kun kafawa zurian ku nagaba mashi ta hayar gurbata jininsu da harkan zina.
Ita zina abuce mai nauyi a wajen Allah mutanen yanzune da suke shagala da mutuwa suke manta nauyinta har sukai ga aikata hakan basu san illanta na baya ba tun a nan duniya Allah zai fara jarabtansu kan hakan.
Akan yayayen su akan dan dan uwa akan wani shaki nasu har inya kasance kai koke ba mai haihuwa bace a duniya sai ubangiji ya jarabeka da wani gurbatace a cikin zuria ta hanyar da zaka fara dandana zafin zinar daka aikata a baya.
Don haka ba haushi zakiji ba kamar yadda shima mijinki rashin sani yasa yake fushi da mutane yanzu kan an fadawa duniya halinda kike ciki.
Ya Allah ya tsare ya kare akadarta baki kai budurcin ki ba a zurian nan nasu ya kike ganin makomarki zata kasance a cikinsu tana fadin hakan ta kureni da idanu tana son jin amsana na dukar da kaina kasa sai naji tace.
To in fada maki zasu saka maki alama alama ta tsana a fakaice alama da zai zauna a kanki na tsawon shekaru masu tsayi har zuwan zurian ki.
Idab aun taso acikin tarbiya ace sun gaji hakan udan ko suyi akasin hakan ace aisu aika dama sunyo gadon hakan a wajen uwarsune don su maza basa laifi kin sani mu dai mata mune masu laifin ko yaushe .
Allah yayi maki albarka ya baki zuria masu albarka a rayuwan ku ya tsareku daga duk wani sherin mahassadan ku na fili dana boye kalubi garemu diya mata Allah ka tsarewa kowa zuriansa duniya da lahira amin.
Ta ban nonban wayanta duk abinda ya shige min suhu na kirata bayan wanan na tabatar na dauketa tankar yata da muka fito ciki daya da ita mu dinga zumunci da junan mu.
Nayi mata godiya tare da gamsuwa da duk abinda ta fada min nacewa daga ranan kada in fargaban miji idan yazo min zafin na dan lokaci ne kuma ya tafi ke nan insha Allah sai abinda ba a rasaba kuma.
Ki ba mijinki lokacin ki son yana bukatanki a kusa dashi a wanan halin kada ki nisanta kanki dashi ki nuna kina tsoransa ta kare da fadin ko a daren yau zaki iya maraba dashi.
Zata fita take fadin asha dinner lafiya nikan nagama aikina zan fadawa maman ku mami ta biyani son surukarta ta dawo normal yanzu baki da wani matsalan komai kuma.
Kaina dukar kasa ina dan murmushi ta dauki makulin motanta dake saman table tana min sallama na taso don in rakata take fadin ki zauna ki huta kada mijinki yace banda tausayi kuma.
Nace ina son in dan mika kafana dama har wajan motarta na rakota karo na biyu ke nan dana fito haraban gidan tun ranan da aka kawoni tana kokarin shiga mota mukaji karan budab get wanda hakan yasamu juyawa don ganin waye ya shigo shine da Abbas suma idanu suka zubo muna har suka iso suka taayar da motan nasu.
Suke fadin ahh Anty Larai dama kina nan ashe kallonsu tayi tana fadin ba dolena ba kada kani yace ban damu da maralafiyansa ba ga amaryan ku nan Allah yabada zuria mai albarka ni zan tafi.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
9?? 7??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Bayan tafiyan anty larai da Abbas yagamawa sheri yana kiranta bakanikar mata sai mun zo kawo maki taki la,adan har gida amma dakin tsaya kin taya kanwar taki murna yanzu zai fi.
Kalloshi tayi tana fadin No Bashir duk abinda zakaiwa Fatima ka bari kuyishi a daki ba a gaban wanan shakiyin ba da bai mantuwa duk yabi ya dameka ina kulle dashi shi har ya manta nashi haukan dayaiwa mutane lokacin.
Bashir din yace kyaleshi anty ai tara masa nakeyi yanzun nan fitan ki gidan nan shima zai fita ko insa Samuel ya sako masa karnuka can sai lokacin na kula da karnukan dake gidan a cikin wani keji daure guda uku sunci sun koshi sai harbin iska da sukeyi.
Dariya ta kwashe dashi kafin tace dani kanwata koma gida kinji ki huta barni da wa yan nan shakiyan duniyan na gyada kai cikin yar siririyar murya kamar ina rowan sallamanta a lokacin nake fadin sai anjima anty na juya na tafi dama na matsu in bar wajen don Abbas dana gani saboda bala,in nauyinshi da kunyar shi da nake ji.
Kodana koma ban shiga daki ba a falo na zauna saboda zaman kadaici ya fara takura min duk dana saba da hakan ma na wanan gidan yanzu ya zamo min daban kamar daga sama Aliyu da Nura suka fado min falon.
Cikin fara,a na taresu ina fadin kamar kun san tunanenku nake a yanzu bayan mun gaisa suke fadin daga unguwa suke suka biyo mu gaisa nayi dariya ina fadin baku fito don ni ba ashe sa,ama naci da kuka biyo ta nan na ganku yanzu.
Muna hira da dariya zakice bani bace lokacin ya shigo falon bayan tafiyan Abbas din suka sake gaisawa da Nura din da Aliyu yake fadin ashe su Ammi zasu koma ranan Thursday ?
Eh daga nan kano zasu su shiga jirgi zuwa kasan su ita Ammice da sauran zasu koma gashuwa don sune ma taga tafiyansu ta dakata har wanan lokacin basu tafi ba.
Amma Nura baka fada min hakan ba ai eh dama ai zasuzo ga gobe naji suna fada suyi sallama dake daga nan suga gidan ki naji suna fada yau da safe da muka shiga gidan ko Aliyu ?
Aliyu din ya amsa da ehh dazun da muka shiga sunce gobe zamu kawosu wajenki kuyi sallama daga inda yake tsaye yake fadin zamuzo muma yau din nan da yamma mu gaidasu ai kafin su tafi.
Gwaggo tana nan ke nan naga Aliyu kallon Aliyu din Nura yayi yana dariya kafin yace yaface ba zai koma ba shi yazo ke nan wajen ki ummansa ma ta fadawa baba da zasu koma gida bayan buki.
Amma ai baka gama karatun kaba Aliyu na fada ni anty gaskiya a gurin ku zan zauna na sani Aliyu amma ai ba haka ya isa naji ya fada daga bayana inda yake duke saman makarin kujera ya dan kwanta muna maganan.
Kazo ba zaka koma ba umman ka kuma ta fadawa baba haka kai Nura yace kwarai sun zauna da baba ina wajen lokacin ta fadawa baba Aliyu yace shi antyshi zai biyo nan kaduna.
Shine baba yace ya zauna nan gida a tare damu lokaci lokaci zai dinga kawo maki ziyara yana ganin ki din ba komai shine suka tafi wanan yayi baida matsala hakan ai naji ya fada yana mikewa tsaye.
Har ya doshi hanyar shiga daki ya tsaya yana fadin yanzun zaku tafi ke nan yace ehh dama mun biyone mu gaidaku munji ance bata da lafiya bamu samu zuwa dubata ba.
Baiyi magana ba naga ya wuce zuwa ciki kawai na dago kai na kalli Aliyu nace yanzu kai Aley kana ganin ka baro zaria zuwa kaduna baka karasa karatun kaba shi yafima ke nan ?
Don Allah anty ki barni a wajen ki yaron ya fada yana jin yadda mukayi ashe da yaron a lokacin Nurane ya daga yana fadin muje mu mayarwa surajo da mashin dinsa kafin ya kagara damu.
Cas karewa dama har mashin kuka aro don ku fito yawo ashe yau daku da surajone ai idan na manna mashi dari biyar din mai ya rabamu lafiya nace kaiko dai Nura dari biyar fa ina laifin dan dubu wajen nan yace me kice shi nakewa nema .
Ni kudina yanzu sana,a zan fara indinga irin sana,an ki na shiga kauye ina dauko dan abinda ya samu ina rabawa mutane idan sati ya kewayo su hada min kudina in koma wanan zan kama da dan abinda dana samu a sanadin ki.
Na kula girman kai baya kawowa mutum samu ko wani sa,a sai mutum ya mike Allah yake taimakansa na koyi darasi sosai a duniyan nan kan rayuwa yanzu.
Haka na rakosu zuwa bakin kofa saidai ban fita waje ba don tunawa da irin kallon da yai min dazun wanda anty Larai ta gani a lokacin tace in koma ciki .
Na juyo zan shigo daga inda nake tsaye yazo ya wuceni muryan shi naji ya dakatar dasu lokacin ban tsaya ba nashige ciki kai tsaye dakina na shiga na dan gyara duk da ba komai amma haka na kara gyaroshi na fesa kamshi na koma na kwanta ina tunane.
Ba komai nake tunane ba sai yadda rayuwa zata kasance muna saboda na fahinci shi mutum ne mai tsaurin ra,ayi da doka hakan nake hangowa gareshi gaskiya don in natsu in fahinci wayeshi na zahiri wanda zan iya in dauka wanda akwai rainin wayau na saka burki akan hakan ba zan dauka ba.
Jin ana knocking din kofan yasa na dago ina duban kofan cikin mamaki na karasa Samuel ne a tsaye yana wani dan marairaice yana fadin ko zai iya shigowa ya gyara min dakina cikin tsigar tambaya.
Wani kallo nayi masa kafin nace is forbidden in my religion stop coming to my side as from today don addinin mu ya hana hakan ni kuma ina riko da addinina idan ina bukata wani abu a wajen ka zan kira awaya muyi magana.
Ya dan rosunna irin na ban girka yana fadin sorry ma ya juya ya tafi na koma daki a zatona zai fadawa ogansa yadda mukayi yazo ya sameni sai naji shiru har magariba ban jishi ba ashe baya gidan ma ya tafi ganawa da mahaifinshi a lokacin.
Sai wajajen magariba ya shigo gidan dakina ya nufo kai tsaye fitowana daga ban daki ke nan a lokacin ina kokarin daukan hijjab dina naji an shigo dakin yasa na juya naganshi a tsaye kofa.
Sannu da zuwa nayi mai ya amsa gurguje yana fadin sallah zakiyine idan kin idar kada ki manta zamuje muyi sallama dasu mama da an fito sallah Allah ya kaimu na bashi amsa ya juya zai fita sai kuma ya juyo yana fadin daga can zamuje ki gaisa da mahaifina zai koma garinsa gobe insha Allahu.
Allah sarki ashe bai koma ba nima na fada bai ban amsa ba ya fice na bishi da kallo na dawo na tayar da sallah kamar yadda nayi niya dama.
Ina idarwa na tashi na shirya tsab shigar atamfa nayi na kawo lafaya na dora sama sai takalman kalan kayan dana saka jawo yar jakata na rike don sabo da hakan na dauko basket din dana hada tsarabata wa Abba din na dawo falo na zauna ina dakon fitiwanshi.
Aiko banfi kamar minti biyar da zama ba sai gashi falon yashigo shima yasaka kayan maza na yadi mai kyau dinkin iya gwiwa irin na matasan yanzu da suke sakawa na Abuja guys a yanzu .
Kallonsa nayi araina nace wai wanda zaije gaida sarakai kene yayi wanan shigar gayun kamar zaije gun tsaransa lalai wanan zamanin baiyi ba kam shiko ko ajikinsa haka muka fita sai Samuel din dai muna fitowa yazo ya karbi basket din a hannuna ya saka a mota.
Shike jan mu a motan yayinda mu biyune kadai a cikin motan har mun danyi nisa ba wanda yai magana a cikin mu sai can yake fadin na rasa me zamu saya masu a matsayin tsaraba da zasu dashi gadai wanan ya dan kalli bayan motan kadan ko zasushi ban gane meye a cikin motan ba amma haka na dan bude baki ina fadin Allah ya saka da alherinsa.
Bai amsa ba nace kyaluwa na cikin halin bawan Allah nan amma nasan yadda zan masa nima nan gaba yaji ko hakan nada dadi gidansu muka fara zuwa don mu gaida mahaifisa mun samu sun fito sallah ke nan na dauko wanan basket din muka fito ya kalleni yana fadin wanan fa nayi shiru ban bashi amsa ba akai muna iso a falonsa muka shiga.
Kasa muka zube muna gaidashi dattijone dogo mai dan jiki don ba a kiransa mara jiki ya dan aje farin saje a fuskanshi yana da dan kama da dan nasa don ba,a kiransu fara ba,a kuma kiransu bakake suna tsaka tsakiya ne dai.
Ikon Allah amaryace ta taso da kanta gaidani aiko nagode Allah yayi maku albarka yake fada na sone kaina kasa tunda na gaishe shi ban kara dago kai ba kuma.
Nasiha ya dan muna kafin suka shiga hira da dan nasa firane akan wani dan uwa nasu da bansan ko waye ba sai daga baya na fahinci Abbu mijin maman saudiya suke zance ashe.
Suna fadin yace da yamman nan zasu shiga jirgi su koma ya kusa dawowa nan gida Nageria ga baki daya saboda karatun yarane suke can a zaune ita hjy tace yanzu kuma bata son dawowa don yaran duk a can suke rayuwa.
Wata kila son abar zancen ya fitowa mahaifin nasa da wani zance sun dan jima suna magana kafin yace zamu tafi Abba Allah ya tsare hanya a fadawa galadima zamuyi waya dashi kan zancen.
Lokacin na jawo basket din dake gefena ina fadin Abba ga wanan ba yawa bansan da zancen tafiyanka ba sai da yamman nan dana hadama cake.
Yata har wani dawainiya kika dauko haba dai yaushe yaushe zaki fara wanan dawainiyar haka kuma ya kalli dan nasa yana fadin ina dai ba ka bari har ta fara shiga kitchen bane tana bakuwar amarya haka.
Bana jin tana shiga tukun amma tace aiki da kanta shine ra,ayinta ita ya fada ya mike tsaya yana dan gyara rigar jikinshi daya dan yi sequizy don zaman da yayi din.
Karbi wanan ka rika mata nagode nagode ubangiji yayi maku albarka aita hakkuri da juna banda saurin fushi da iyali kana dai ji ina fada maka hakan mata hakkuri ake dasu ko yaushe don haka kazamo cikin masu hakkuri da iyalinka.
Mukai masa sallama muka fito na dauka zamu shiga cikin gidan nasu mu gaida iyayyensa mata amma sai naga sabanin hakan don kai tsaye mota muka nufa zuwa shiga.
Nayi mamakin hakan kwarai don ko muna jiyo hayaniyarsu a falon muryansu yana isowa nan gare mu saidai ba wanda ya shigo inda mahaifin nasa yake damu har muka bar gidan.
Kai tsaye unguwarmu ya shigo saidai wanan karon ta bayan layinmu yabi ya isa gidan da suke din sai ganin mu nayi a kofan gidan bayan mun saukane muka shiga ciki kusan tare dashi ya tsaya daga kofa saidana karasa nayi sallama nashiga suka dauki murnan ganina kafin Ammi tace daga ina haka keda aka kai shekaran jiyan nan gidanki ina mijin naki yake ?
Nace gashi nan tsaye a kofa tare muke


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login