Showing 225001 words to 228000 words out of 347556 words

Chapter 76 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8812

musulunci a zuciyan ki don gudun kota baci Allah ya kyauta.
Tafiyan mota ba dadi tundai akace maka motar ta kasuwace dole kai hakkuri da duk yanayin daka tsunci kanka a cikinsa lokacin hakan nima nake zaune a motan kudu zuwa arewa dana shigo a matse zamu dawo kaduna ban kara kwana ba ranan da muka fito camp daga can gareji na nufo kai tsaye.
Banyi gigin zuwa gidan Samira ba don yamma da nagani haka nayi kundunbalam shiga motan da zata taso a lokacin daga can tazo kaduna don ma wai driver yana da dan nasa kokarin yasan darajan mutane sosai haka kuma yana da addini don ko ina zai tsaya ayi sallah akama hanya.
Shigan asuba mukayiwa kaduna din don haka yace in zauna a nan cikin mota in gari ya waye sai ya saukeni unguwar da zan tafi naji dadin hakan sosai da yayi min na nasa nikan Fatima ina da sa,an mutane wani lokaci.
Gari ya danyi tar an fito daga sallah har mutane sundan fara cuwa cuwan su sai gashi yake tambayan ina zan saukane na fasa masa yace ai unguwar mune ma ashe.
Tafe muke a unguwar saidai abin mamaki shine banga gidan mu ba a wajen sai wani sabom gina na zamani daya fenti ga kofa da dan get irin na zamani.
Abu daya ya ceceni shine shagon isa da nagani yana nan kamar yadda yake shi yasa na dakatar da mai motan a nan ina faman baza ido a kofan wanan gidan gabana ko sai faman faduwa da yakeyi lokaci guda ina .
Ina tunane Allah yasa baba ba saida gidanshi yayi ba a bayana wani mai kudim ya saye ya gyarashi haka ba mutane da saka ido a yanzu su isah mai shago ke nan da tun tsayawan motan idonsu na kanta suga wanda zai fito cikinta a lokacin.
Na bude kofan na fito har lokacin isah din yana tsaye ya rike leda saida na fito ya tabbatar nice yake fadin a,a hjy Binta kece tafe ashe ?
Sannu da zuwa ya kudu ya aka barosu can kuma lafiya kalau isa ya muka sameku kuma na fada ina sauka daga motan wani ya kira cikin yaran dake kofanshi yace don Allah kuzo ku kama mata kayan nan a shiga dashi nan gidan baba.
Shekarata daya sur a kudu ina bauchakwalintan kasa a can duk da zaman garin gashi ga kamar shi amma haka yafi min dake gidan mu a nan kaduna .
Naso na dawo arewa amma tun tasowan zancen Samira a kaina na yankewa kaina shawara zama a can inda aka kaini wani company ina aiki dasu a matsayina na yar bautan kasa a wajensu ga gida ga abin hawan company dan haka komai yazo min da sauki a garin.
Inda naga sun bi sun shiga min da kayan nima ba tare dana tambaya ba nabi na shiga gidan kafin mu karasa muka hade dasu Usaina a guje sun fito tarona .
Nan muka rungume juna dasu a cikin murna da shaukin ganin junan mu muka shiga gidan har su mama uwa da mama Lanto duk sun fito tarona a cikin murna da ganina.
Gaba daya fasalin gidan an canzashi mutum ya godewa Allah idan yana da muhalinsa waddatace mai fili daya bari don ba,asan me gobe zai haifawa mutum ba son sanin gaibu sai Allah dama.
Wanan ya taimaki baba a yanzu filinsa daya rage baya da gaban gidan mu duk a hade anja masu dakuna ciki da falo da makewayi a ko wani daki a yanzu .
An warewa baba nasa part din an fitar masa da falo da daki da bandaki a cikinsa ga kitchen an gina masu babba sabanin da da kwanone aka rufawa madafin wanda a nan suke girki in ana ruwan sama su dinga wahala a cikinsa yanzu duk ba wanan a garesu.
Haka kuma bandaki yanzu nakowa a cikin dakinsa yake an huta da fadan polishing da rashin wanke bayi da wasu basayi ayi ta fada ni dai dama baba ya rabani dasu anyi fitana anyi fada an gaji an kyale hakan.
Gaskiya fasalin yayi kyau sosai ga irin gidan yawa irin namu dakuna bibiyu suna kallon juna sai dan filin tsakiyan gida da aka shuka dan icce daya dan fara tasawa a wajen but still yana a cikin basket har lokacin wanda nasan nan gaba zai bada innuwa a gidan ga baki daya.
To wayayi aikin nan kuma yaushe akayi duk ban sani ba nake tambaya kaina a kasan zuciyana dayan dakin dake makwabtaka da mama uwa aka bude min ma,ana shine dakina na baya ke nan a yanzu dana bari.
Muka shiga yan matasan kannena suna ta jido min kayana zuwa cikin dakin ruwa mai sanyi mama uwa ta kawo min take fadin duk da bansa kinci wani abu ba a yanzu tunda yanzu safiyace sosai a gaskiya.
Karban ruwan nayi ina mata godiya muryan mama ya katseni lokacin da nake kokarin aje ruwan a gefena tana fadin mutanen kudu kunsha fama sai kuma kika dawo kika samemu haja haja mun zama amare ?
Dan dariya nayi kafin nace wallahi kuwa mama gashi sai ido nake faman rarabawa wuri ya koma min sabo har nake ganin kamar ba gidanmu dana sani bane
Shine dai din bamu canza gida ba satin mu hudu da kwanaki a cikin wanan daula ga famka idan ka kwanta kamar kada ka tashi daga barci mukan mun sheda ranan haihuwa ai a gidan nan gaskiya.
Mama uwace daga gefenta takarasa fadin hakan na juyo na kalleta tace hausawa sunyi gaskiya da suke fadin da da arzikinsa yafiva mutu abarmai gado mukan ba ajira gadon ba gidan nan gadon aka gyara munama.
Ba abinda zamuce sai Allah ya barki tare mutumin nan dan albarka dan tofon lada wanda bai mutuwa tun a duniya sai ya ga Annabi Binta Allah ya hadaki da mahaifiyan ki itama ta sheda hakan na amsa da amin .
Amin mama Lanto ta fada da tazo ta tsaya daga kofa ta fada ta kara da fadin in har ko wace uwa zata haifi diya mace mai kashin arziki haka aisaika haifi goma lokaci guda baka sani ba.
Ni duk sin daure min kai amma kuma zancen su ya haskamin koma waye yayi wanan aikin ta dalilina yayi hakan towaye ke nan da wanan aikin na tambayi kaina.
Abu na farko dayazo min a zuciya shine maman saudiya don su nake hurda dasu masu arzikin da sai suyiwa mutum goman hakan idan sunso basu san suyi hakan ba cikin arzikinsu.
Bantu fa ajiyan Allahce na fada a cikin mu na dade da gane hakan shiyasa ban tsaya wahal da kaina kan abinda baka iya jayaya da ubangiji a kansa .
Wallahi dai mama ni tun da naga muna sana,a nata yafi yawa ta sayar muna nan da namu saita karba a take zai kare wajenta iri dayane fa dana gaban mu amma haka za ace nata dai akeso nagane baiwane kawai daga Allah.
Sai gashi kuma naga ita bama irin namu takeyi ba komai ta samu akanmu gidan nan zai kare wallahi tun lokacin na saduda da Bantu gidan nan Usaina dake zaune rashe rashe kasa saman ties ta fada.
Mukan ai inaga anyi auren nan mun samu gidan hutawa wallahi yanzu kan saidai mu nunawa wasu badai a nuna muna ba kuma kaf unguwar nan wani kallo nayiwa hassana dake wanan zance.
Ganin hakan tace wallahi kuwa Allah ya kawo muna hutu ta hanyar ki me mutum zai tsaya jira kuma daga inda mama take tsaye sororo tace ku kuma zaman ku ke nan fadanci ba zakuyi auren ba ko ?
Mama ke nan idan muka lake a can din kika sani ko Allah ya hadamu muma da rabon mu tunda gidan sarautane kinga gidan manya ke nan fa .
Shigowan babane dake dogara wani sanda mai kyau a hannunsa irin wanan sandan da ake sayawa manya black colour me dan kai kamar bakin aku yana tafiya dashi ya tsaya a kofa yana fadin.
Fadimatu ashe kina hanya, hanya ke nan kuka kwana ko nace eh baba don bamu taso a cikin lokaci ba saboda ba fasinja yamma tayi lokacin.
To sannnuku da zuwa kin karya ko kafin na bada amsa mama ta karbe da fadin yanzu ta shigo ai sallah ma nake sonyi baba na bashi amsa ina fadi a raina Allah sarki uba ke nan shi ya iya tambayana wanan.
Jin banyi sallah ba yasa suka watse ko lokacin dana dawo daga saudiya ban samu wanan tarbon arzikin da haba haba a wajensu ba kamar na yau inka debe mama uwa dasu yan biyu din.
Na kewaya har nafito nayi sallah su yan biyu na zaune suna hiransu a dakin nawa gashi a lokacin akwai wutan nepa sun sake iskan fanka sai gudu yakeyi sosai yana bada iska a dakin.
Mai na fitar cikin jakkar hannuna son in shafa daga can hassana ta kyala ido takw fadin wai har yanzu man coco kike amfani dashi nace shinafi ganewa yafi karban jikinane.
Muna hira har nagama na shirya lokacin Usaina ke fadin wai meyema sunan guy din nan nakine na kallota da sauri nace wani guy kuma tace wanan da zai aureki mana wanda ya gyara muna gidan nan.
Oga yake ko Boss meye sunansa na gaskiya wai oga Abbas ko wa tace ke baki san shiba koni kuma zaki zolaya nace ban fahinci me kike fadi bane wai dama su suka gyara gidan nan kike nufi nima na tambayeta cikin al,adan dan Africa.
Shi zakaiwa tambaya ya kara tambayanka the same things haka turawa suka shedi bakar fata da wanan halin na atambayeka ka tambayi maishi kuma.
Humm,umm wai ita yar duniya yanzu kan wa zaki boyewa kowa ya gama sanin ai inda kika dosa gidan sarauta yaro mai tashen Naira ga kudi ga mulki ga ilimi ke aikin gama more miji saura mu.
Karshen zancenta ya sakani tunane don haka bankoji meta karasa dashi ba Oga Abbas ko Boss su suka gyara gida akan wani dalili hakan ya faru har ake kira min zancen aure dasu.
Bread da kwai da ruwan zafi su mama uwa ta shigo dakin dasu har da kosai a cikin leda daure ta aje min tana fadin bari na dauko kofi da cukali sannu mama na fada tace haba dai.
Tare muka karya dasu suna faman zuba wanda alokacin nake jinsa kamar damuwa suke kara min a zuciyana kawai da zasu barni in zauna ni kadai da zaifi mun dadi a lokacin saboda inji dadin tunane.
Abin mamaki wai ashe Oga Abbas ya kwabe bakin Nura shi kuma ya kwabe bakin kowa na gidan mu do kada a fada min zancen wai kada in kawo matsala saboda yasan halin mu mata.
Shine har aka kare wanan aikin ba tare dana sani ba sai wanan lokacin dana dawo na samu wanan abin mamakin na gyaran gidan mu din da akayi banyi wani mamaki ba sosai don nasan kwaruru ba sa,ar wake bane .
Saboda su Oga Abbas sunfi karfi kawai dai daga cikin irin aiyukansune na sadakatul,jariya da sukewa mubukata rabon mu ya fado a hannunsu har muka samu shiga ciki.
Barci nayi sosai a ranan don tun goma da rabi dana kwanta ban falkaba sai biyu da wani abu na rana na tashi nayi sallah har lokacin akwai dan gajiya a jikina.
Haka na daure nabi su mama daki daki muna gaisawa dasu kafin nayada zango a falin baba da aka gyara shi tsab harda kujeru irin leda cushion din nan bakake set da table duk a falo.
Mun gaisa munyi hiran wurin bautan kasa dashi kafin ya jefo min tambaya kam Samira dacewa kina ko leka wurin su samira da mamaki na kalloshi don banyi tsamanin yasan da zancen kazafin da tayi min ba akan mijinta.
Kafin nayi magana sai naji yace nasan dai ba zaki biyewa haukanta ba tunda kinfita hankali irin wanan yana kawo rauni a zumunci na kirata naci mata mutunci a waya tunda bata da tunane.
A,a baba aida baka kirata ba indai mun hadu nan gida wata kila mu gaisa amma samira kan gaskiya baba ba zan boye maka ba nagama zumunci da ita tunda takai ga min sheri haka.
Ita ana tausayinta bata tausayawa mutane banjin ita da anty Altine zan iya cigaba da zumunci dasu yadda kake so baba don har kasan zuciyarsu mutanen nan biyu basu kaunata a gidan nan.
Nan na kwashe kaf yadda mukayi da ita lokacin dana isa amma baba wai daga baya na fara jin maganganu marasa dadi a kaina suna tashi.
Duk da haka hakkuri zakiyi fadimatu yanzu waye akasa na kalleshi don ban gane me yakw nufi ba yace min ita don zaman nasu babu dadi sam ita dashi.
Dama abinda nake mata gudu ke nan tun farko sukaki ganewa ita da uwarta don tun a lokacin nasan itace ta nemoshi bashi ya nemota ba yanzu gashi nan zaman yaki dadi a tsakaninsu.
Ita kuma Altinen da kike magana wanan kowa yasani bakin halin uwarsuce takwaso don bata raga halin uwarsu ba ko kadan ita dai Suwaiba dince ma yanzu ko girmane naga tana rage dan wani abu cikin halinta.
Naso masa zancen mahaifiyata a lokacin amma naga rashin dacewan hakan don da zuman hakan na dawo wanan karon saboda abin ya tsaya min arai hakan namin ciwo ko banza insan halinda take ciki ko tana taye ko a mace ?
Duk dai in sani insan kuma yan uwanta suma su sanni ko da ba zasu karbeni don na fahinci kamar basu kaunar baba da itane balle ni yar da suka haifa a tsakaninsu.
Wanan yasa baba bai kaunar in kusancesu a yanzu yake min kwana kwana don kada inje ayi min wullakanci niko ko yayane ina son insan wanan sirin da kowa yake boye min a yanzu tunda bata hanyar haram aka haifeni ba kota shine kuma ina dai son insan mahaifiyata ko wasu dangi nata.
A yanzu kam na gama yanke shawara a raina koda sanin baba ko ba saninsa muddin nasan wani abu akanta saidai yaji na wuce kasan da take kawai.
Kwana biyu ina hutu a gida ban leka ko wajen gidan mu gashi tun a hanya wayana yake kashe har kwana biyun nan kuma ban kunnata ba tana lashe din.
Ranan dai na saka caji na dauko na kunna don ina son mu gaisa da gwaggo takoyi cajin na dauko ina kunnawa a daidai lokacin naji muryan maman tudun wada ta shigo gidan mu.
Maman tudun wada in baki manta ba mai karatu itace yar maman biyu wace ta saka min sunan Karan Dafi kinfi dan dawa amfani itace ta shigo ina jin suna gaisawa dasu mama.
Hakan baisa na fito ba son yanzu hankali da wayau ya zo min idan ka nuna baka kaunata nima yanzu kallon da zan ma ke nan bani kaunar taka aje a hakan.
Banji me aka fada ba amma kunnena yaji lokacin da take fadin kice min Karan Dafin gidan ku mana itace ta dawo ashe kai yaya aiko sunan nan naki yaci karan dafin nata alheri ya zamo muna a gidan nan don batai gamin banza ba.
Duniya da bakinku yau kuke fadan haka yaya ko mu fada ko kada mu fada haihuwan Nuratu ya zamo muna alheri don haske ya haifi walkiya a duhu.
Da ansan abinda Nuratu ta bari gidan nan na tabbatar da a lokacin an bari ta tafi da yarta amma ba wanda yasan tsarin ubangiji balle ya shige masa gaba.
Au da haka kika yarda ke amma kuna bani mamaki diya mace ai baiwa dayane gareta tunda ba aurene da ita kifin naku diyan tafi suda basu da wanan sa,an ?
Haba yaya yau da ace yarinyar nan aikin banza take a garin nan idan wani baiji ba wani zaiji hakan ya kamata mu kyautata zaton mu akan yarinyar nan yanzu ai hakana.
Lalai kuwa kan mage yaji gishiri sosai to yaya ba dole ba danwa cikin mu zai tsaya yayi hakan garenu duk da babu uwarta gidan yau mune masu cin dadin yarta.
An kori Nuratu data fara shigo muna da haskenta gidan nan ana barka ashe tabar walkiyan nata a baya ba,a sani ba Allah dai ka yafe muna abubuwan da akayi a baya amin.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
7?? 2??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Kamar an rikeni gurin nakasa motsawa in fita a lokacin har taga sukaje dakin yar uwarta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login