Showing 48001 words to 51000 words out of 347556 words

Chapter 17 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8802

ko gwaggon kuce ta fada min wallahi zancen haukan da uwarta tazo min dashi na rashin tunane yasa na fara jefa zargina akanki Samira kuma nabi hanya da kowa bai zata ba nagane hakan.
Don hakane na daukoki baki alaikum na dawo dake gidan nan ban kumayi wani zancen komai in ba yau din nan ba don kawai in cirewa kowa zargin a zuciyarshi.
Karatu kuma daga yau din nan kin dainashi ke nan a gidan nan kodana jeka kadawone kuwa sai kije dakin mijinki idan ya yarje maki kya karasa a can ba dai a gidan nan ba kuma yanzu.
Innalillahi baba don Allah kayi hakkuri kuskure aka samu abinda kake zargi ba hakana bane akasi aka samu ko a ranan amma don Allah a yafewa Samira tayi kuskure hakan ba zai sake faruwa ba insha Allah .
Hannu ya dago min nace baba kaiwa Allah ka bata dama na biyu taci gaba da karatunta tunda har mun ketare matakin farko insha Allahu hakan ba zai sake faruwa da kowa ba.
Fadimatu ke kanki wallahi kin munafunceni don kina kallo yar uwarki na shirin jefani a cikin kunya kin kasa tsawata mata ko kuma ki fada min koki samu uwarta ki sanar da ita halinda yarta take.
Kinsa aiwatar dako dayan hakan kinga alama ya nuna cewa dukka kudin yanzu dole in zargeku da aikata ba daidai a rayuwan ku kuje gaba kun fara bude ido kuna son kufi karfina .
Kun watsar da tarbiyan da muka doraku akanshi dole inyi abindaya dace yanzu da rayuwan don a zauna lafiya ke kuma Lanto dan bakida kunya da imani kika nuna bayan yarki kike duk da kinsan abinda take aikatawa a can din ba daidai bane a rayuwanta.
Kuka nakeyi sosai ina sharban hawaye da jan majina hakan ya jawo hankalin yan gidan da ba,a kasa dasuba suna sauraren mu duk da basu jin abinda ake fadi sosai a dakin Abba din amma sun fahinci matsalan tamu babbace sosai.
Da kyat mama Lanto ta iya bude baki tayi magana tana fadin malam ni abinda ta fada min bashi bane ka fada a yanzu don tace dani Bintu da gwaggonsu duka gidan sun hade mata kai basu kaunarta suna hattaranta acikinsu.
Innalillahi na na ambata ina kallon Samira din nace ke samira akwai wani rana da banyi maki magana amma ki shareni karshe ma gaba kika dauki yi da kowa a gidan bakiwa kowan mu magana duk wanan bai dameni ba.
Mama da nake zuwa gidan nan na taba nuna maki akwai matsala iyakadai ina matsa maki cewa sai an bata wani abu inkai mata don muna cikin bukata acan din.
Kuma ki samu abinda kika ban nakai tace najeshi a nan zan mata nasiha tayi banza dani amma ban taba nuna hakan ba ai sannan baba ni nasan ba maza takebi ba ko wani abu kawai dai kila zaman mu gidan gwaggone bai mata ba.
Nifa na gama maganata daku yanzu kunji hukunci dana yanke a zuciyana yanzu game da karatunta don ba za a maisheni mutumin banza ba kuma.
Gaban baba naje ina masa magiya da alkawari har inta sake wani abinda ba daidai ba zanzo gida in fadi da kyat muka samu baba ya yarda ya janye magananshina ba zata komaba din.
Mun fito waje tunda baba yace damu naji ai musulmin banza ake hadawa da Allah yakiji na baki wanan daman in halinkine haka ki koma mungode baba muka fada lokaci guda.
Muka mike muka fito muka barshi tare da mama Lanto a ciki yana fadin kingani kune baku gane alherin yar nan gareku ba har yanzu ke Lanto idan wani yace zaiwa bintu haka agidan nan azato yanzu sai inda karfin ki ya kare ga kareta..
Ba haka ta fada min ba don ta nuna da Bintu aka hada kai a gareta yanzu ai kinji yadda zancen yake dai yarki a zancen gaskiya ta fada hanyar daba daidai ba ba wanan bane zuwa na farko ina zuwa unguwan kuma naga irin rayuwan data dauko boyeta dai yar uwan keyi don tana sonta da karatun.
Bayan kinsan a jirace ake daku aga tsakaninku tunda dake ta yarda take komai a cikin gidan nan yanzun kin nuna mata haka kuma yarki tafita a wurinki ba daya kika daukesu ba.
Shiru mama lanto tayi tana hawaye baba yace na dauka a yadda kuke ko irin haka ya taso ke mai zaunar dasune kiji tsakaninsu ki tsawata masu har su daina hakan.
Tayi nadama ta gane kurenta karshe ta mike ta shiga bayin baba ta wanko fuskanta muko koda muka fito mu samu kowa cirko cirko suna sauraren abindake faruwa a dakin baba din damu.
Ban tsaya a gida ba bayan fita baba na shirya zuwa gidan hjy Hajjara don in gaida ita mekaratu in baki mantaba hjy hajjara matar data fara ban kwangilan aikin abincinta da tace a saudiya suke zaune mutanen katsina state .
Ko ina school zata kira layina mu gaisa kafin na dawo zamu gaisa yafi sau uku shine naga ai ya kamata naje na gaida ita yanzu din nama fice a gidan namu dai duk da ina son shiga har gidansu hjy mairo in duba su jamal da aka dauki lokaci bamu hadu ba don haran suna raina sosai.
Dan karamin hijjab ne baki a wuyana sai dan flat shoes baki shima mai kyau dana sayo akasuwa tun shigana get din gidan na hango wasu tsala tsalan motoci a fake haraban gidan sukai biyar hakan yana ni wasi,wasin ko dai tana da bakine in koma.
Muryan wanan matashin dashine sanadiyar haduwanmu da ita wanda tace yana sayo mata awara a wurina naji yana fadin kai madalla kai amma naji dadin zuwan nan naki jiyafa muka gama maganan ki a gidan nan da ummi.
Dan murmushi na sake mai kadan nace ina wuni ya amsa yana fadin muje Allah yasa za a raba gardaman nan dake muka fada falon gidan yana magana ina bayansa yace ummi gata ta dawoma ashe koda ake maganan nan.
Duk suka juyo suna kallon mu sun kai su bakawai zaune a falon har hjyn sai naji wani kunya da nauyi ya dira min lokaci guda a cikin jam,i nagaidasu a tare lokaci guda duk suka karba min.
Hjyce tace ikon Allah mamata dama kina garin nan ashe nasan jinya kika shigo ko nace eh ummi ya gida ya aiki kuma aiki kan yanzu yake ga yan hutu nan sun biyomu wai mu koma ni kuma yanzuma nake nan don ban gama abinda ya kawoni ba kasan nan.
Haba dai ku bar muna ita mana muma muna sonta a nan ai Ke ke ke wani ya fada da karfi a cikinsu zata tafine kin zo kina wai wani kuna sonta kuma anan ai.
Yo ga tsiya haka kawai ka dakawa yata tsawa don kajita da sunan umma ko kada ki yarda duk wurin sai wanan kawai zaki dagawa kafa amma dukansu jikokinne a nan.
Dan rabewa nayi saman hannun kujera na dora jikina akai ina masu kallon gefen idanu don ganinsu gaba daya ya firgitani lokaci guda duk sai naji na takura a wurin.
Yafi tsayin mintina goma sunawa mai sunan nawa kakarsu sheri yayin dani kuma a wurin na dukufa a cikin tunanen kosu wayen wayan nan mutanen haka.
Shiru sukayi gaba dayansu ashe wasunsu suka zubo min ido jin shirun nasu kamar basu falon yasa nadago kai ina sakin wani zazzafan ajiyan zuciya.
Wanda a daidai lokacin kuma muryan hjy na tsinkayo ya shigo kunnena tana kiran sunan tare da fadin kingansu baki ganesu ba ko sun tareki da sheri.
Wanan din shine yayan su khairiya wanan ke bi masa wanan din matarshine sai wanan itace autana wanan kuma kinsansa lokaci buki ai wanan kuma na karshen shine uncle dinsu autan dakin mu kenan Mohammad sunece masa Uncle mohammad ko uncle.
Na dago kaina ina kara masa kallo har lokaci bai dago ya kallo inda nake ba sai aikinshi yakeyi a cikin laptop dinshi dake saman jikinshi.
Ma,ana dai dukkansu iyalan wanan matar da nakewa kallon bata kai haka ba ashe gyarace da take samu da kula ya boye yawan shekarunta.
Na gyara zama sosai na dan kallesu ina fadin mama Allah ubangiji ya raya makisu acikin aminci ubangiji yasa gaba dayansu rayuwansu alherine gareki da sauran al,umma.
Kai wanan yar abin ta iya jero muna wanan adduan haka ashe ba karama bace halindai nasu na tsofi don sunan ta kusan fa irin adduan hjyce tayi muna wallahi.
Yayin da hjyn ke fadin amin mamata ya zarian ya karatu ina dai ana mayar da hankali wurin karatun nace insha Allahu mama nagode.
Sai lokacin wanda ya ke zaune kamar dutsen ko kyata ido baiyi ya dago kai yana fadin da tayi maku adduan ba gashi ya biku ba kuna ganin haske a rayuwanku.
Bai tsaya yaji abinda zasu fada ya mike yana daukan computer shi zai shige ciki sai mama din tace dashi awara din zata soya maka ko harda kunun ayyah za ta hado maka dashi ?
Sai lokacin ya kallo inda nake ya kuma kawar da kai da sauri tare da fadin anty bana son irin abubuwan nan kinsani don bansan inda aka hadashi ba gaskiya.
Kai last born ta yaya zan baka abinda nasan baka so ai nasan halinka don hakane na zabi tayi maka din da kanta ita baice komai ba daga hakan ya shige ciki ya barmu a wurin.
Zo nan uwata zoki zauna kinji hjyn tana nuna min inda zan zauna gurin da wanan ya tashi nace barshi mama nan din ma yayi min dama nazo in gaida kene na kwana biyu ban shigo ba.
Ina fadin hakan na mike tsaye ta sake fadin yauwa mamata don Allah kin iya danbu kafin ki koma kizo gidan nan ki gwadawa wanan tana nuna min matar dan nata.
Na iya mama yaushe za,ayi don ba zan dadeba zan koma ko sai na dawo wani lokaci zamuyi tace zai yuyu kuyishi jibin nan banda gobe nace Allah ya kaimu mama ina mikewa.
To kizo ki karbi kudin komai da za a bukata din dana wara din da kunun ayyah hakan yasa na taka zuwa inda take zaune din ta tura hannu a cikin jakkarta na hannu ta debo kudi masu yawa ta miko min na karba .
Nayi masu sallama na bar gidan da sauri don na takura da irin kallon da gaba dayansu suke min din har na fice daga gidan.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[8/9, 10:27 PM] KYAUTA: KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
1?? 5??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,

INNALILLAHI WA,INNA ALAIHIM RAJ,UN INNALILLAHI WA,INNA ALAIHIM RAJ,UN YA ALLAH KA JI KAN MAMA AISHA COROFEE DA RAHAMANKA YA ALLAH KA KARBI BAKUNCIN TA A CIKIN RAHAMANKA YA ALLAH KASA ANNABI YA ZAMA CETON BAYINSA SALIHAI BAKI DAYA YA ALLAH KASA ALBARKA GA DUKKAN ZURI,AN BAYIN ALLAH DA SUKAYI SHAHADA KASA ALJANNA MAKOMACE A GARESU AMIN MUNYI RASHI MACE TA GARI A CIKIN MU ALLAH YASA JINYAR TA YA SAMO KAFFARA AGARETA AMIN, , ,


Har kullun ina kara godewa Allah daya bar min baba da rayuwanshi haka kuma duk da halin rashin baba na talauci hakan bai hana yazama jajircecen namiji ba a cikin iyalinshi.
Don baba ba mutum bane da zaisa doka a gidansa a ketara masa kai tsaye kowa na gidan mu kuma yasan yadda zai zauna dashi ya basa hakkinsa daidai gwagwardo.
Baba irin mutanen nan maza da basu daukan rainin iyali don haka bai bada kafan da mace ko yaro zai kawo wargi a wurinsa ba don ko babu sai ya matsa ya samu abinda ya kawo iyali su sarrafa a ci don bai dauki mace ta tallafa masa da wani abinta ba har raini da fin karfi yazo ya shiga tsakaninsu a karshe irin yadda da yawan mazan yanzu suke yawan yi a rayuwansu.
Zakiga mace itace komai a gida a hakan sai namiji ya mayar da kansa lusari a wurin iyalinshi ta yadda ko yayi magana ba a daukansa wani abu don zubarda girmansa da yayi ya kwanta mace tana juya gida.
Irin wanan lusurancen da mazan yanzu suka dauka a zaton su taimakone shike kawo muna koma baya yanzu sosai a cikin al,umma wanda mafi yawan gidaje da magidanta haka suka koma a yanzu.
Shi baba bai dauki wanan dabi,anba kamar yadda da can baya iyayye maza da kakanin mu basu yarda da wanan akidan ba na mazan yazu komai na gida namijine zai sawowa iyalisa daidai karfinsa iyalin kuma su karba a cikin dadin rai tare da godiya da yiwa maigida fatan alheri.
Amma a yanzu komai ya koma hannun mata mace ce zatayo cefanai itace ke kula da duk wani laluran diya kai dama duk wani power na namiji ada can baya.
Yanzun ma ban taba kudin da hjy Hajjara ta ban ba saida baba ya dawo nayi masa bayanin komai har yadda naje gidan nata don in gaida ita don dama yasan tsakanin mu da ita.
Saida na gama masa bayani baba ya dago kai yana fadin to Fadimatu ba zan hanaki zuwa inda ake sonki da alheri ba don nasan ke me bukatan wurin zuwane inda aka nuna maki fuskana in nayi duba ga rashin uwa da baki da ita akusa balle yan uwan uwarki da zakije su debe maki kewa a garin nan.
Shiyasa nakan dan daga maki kafa fiye da sauran yan uwanki nake bari ki wasu abin wani lokaci duba ga yadda nasan rayuwan ki ta natsuwa don da wuya ki aikata abinda za ace dani assha daga baya.
Don kinga kamar sana,an nan da kukeyi har yau banji wani abin tir da Allah waddai a bakin mutane ba game da ke sai na sa albarka.
Amma kinsan irin takon da zakiyi da mutanen nan dubaga yanayin mu na masu karamin karfi a cikinsu kada kiga ta baki fuska har yakai kin koyo wasu dabi,un da ba daidai ba daga baya idan kinyi hakan za aji tsakanin mu don zan saba maki sosao fiye da tsamanina kindai san halina basai an fada maki ba.
Baba idan kace kada naje ko yanzu ba zan tafi ba da safe sai in mayar mata da kudinta in mata bayani yadda zata gamsu.
A,a ai yadda yasa ta yadda dake din haka fada nake maki na ki kama kanki don kinsan halin wasu masu kudin nan basu son ka wuce masu gona da iri don bansan alherin dake bibiyan ki a zaman ku na tare dasu ba.
Nagode baba na dan fada ina mikewa na fito mama dake zaune ta bini da kallo don ita ta tsani yadda take ganin ina hurda da baba din sai ta dauka wani siri muke kullawa da mahaifina din wanda su basu sani ba.
Ban fadawa kowa ba washegari na shirya naje kasuwa na sayo duk wani abin bukatana sai bayan na dawone mama uwa take fada min cewa an kawo min shimkafa daga gidan hjy wai wanda zanyi damu dashi.
Nan nake mata bayani don yanzu ita kadaine muke dan hurdan arziki a gidan tunda mama lanto samira ta bata tsakanina da ita ta goyi bayan yarta kuma.
Don haka muke yar tsama dasu sama sama na jeye jikina ga lamarinsu tunda suma ba sake min sukeyi ba sun nuna min bambanci a tsakanin mu.
Ina shiga daki naga kullin shikafan ya kusa rabin buhu ina kallon shikafan ne sai ga mama uwa ta fado dakin na juya gareta ina fadin mama mutanen nan sunce kadan zan koya masu ga kuma wanan shimkafa zaikai kusan mudu ashirin ai.
Au na dauka ai wani buki zasuyi dashi a gidan a,a tace kadan amma bari ina gama hada masu awara da kunun ayyah su zanje gidan da kaina sai in tambayesu.
Kin daiji zancen bukin zainab ko nace wata zainab mama tace zainab dai ta hjy laraba sun kowowa su yan biyu anko din sunce su fada maki idan kin dawo tun lokacin naji uwar tace babu maiyi a gidan nan don haka karma su nuna maki shi.
Aiki banza ke nan ina shiga gidan ai nuna min zasuyi wanan matsalansuce ai mu bai shafemu ba tace yau ma naji suna zancen yasa na tuna don tana a bankanta babu mai zuwa a gidan nan .
Ta dai tsaya a diyanta nikan yanzu ai na wuce wanan kuma na fada ina dauko kulin ayyah dana sayo a kasuwa karba tayi daga hannuna ta fita dashi don ta wanke don ita duk abinda mama zata fada bata damuwa dashi idan dai tasan zata samu.
Mun hada komai ni da mama don ko awaran nan cikin gida mama ta soyashi nina zauna na yanka kayan hadi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login