Showing 327001 words to 330000 words out of 347556 words

Chapter 110 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8761

A boye naba hassana kudi sukaita asibiti don baba yayi tsaye in fito mu wuce mu koma gida don kada in saka bakina a cikin zancen dole hakan akayi mukayiwa mutanen gida sallama muka tafi muka barsu cikin wani hali.
A mota ina zaune ni duk kunya da nauyi ya rufeni na nisa nace iya yau kinga draman gidan mu ko ai saidai idan baka zoba zasu haukata muna uba saboda mugun halinsu na banza.
Koda muka isa gida hankalina yana wajen abinda ya samu Samira din duk da nasan tunda taki magana zancene daya shafi aurenta amma tayi kokari data iya biyo hanya haka ta dawo har arewa da raunika haka a jikinta.
Murmushi nayi son tunawa da wakanta na dan maliyo maliyo maliyo dan maliyo nawa gobe da labari jibi da labarai ido na lumshe ina fadin dadina da gobe a yanzu saurin zuwa.
Sakkaya yanzu tunkan aje lahira ubangiji yake fara hisasabinsa don gashi samira ta girbi abinda taso kartan banza yan iska suzo gida suyi min sai gashi ya faru a kanta.
Zuwa magariba hassana ta kirani tana sheda min an kwantar da Samira nan asibiti don Samira ta shiga wani hali bayan fitowan mu gidan dazun hankalina ya tashi sosi da jin abinda ya faru.
Ba daman naje a lokacin don baya gari don haka na shirya abinci na tura iya da driver suka kai masu tare da abubuwan bukata a asibitin nayi kokarin yin waya kuma da mama Lanto na kwantar mata da zuciyanta.
Yan uwanta da suke tare sai Usaina a lokacin wanjen da muka gama wayan mama lanto ta fashe da kuka suke bata baki har iya din dake tsaye Iokacin wajensu.
Data dawone ta samemu falo zaune muna kallo muka zauna a nan muna zancen akan samira din da matsalan aure a yanzu take fada min yadda taji wata yar uwar mama Lanto na fadin cewa duka ya linkida mata kuma ya sakota da wanan uban rauni har da kariya a hannu.
Watau iya duk yadda akayi akwai abinda tayi har ya fusata haka da ita amma ya Mahmud ba mabugin mace baceshi gaskita bansan shi da wanan halin ba na fada tace ai gashi kin fada hakan yake.
Na bata dan kabarunshu da yadda muka zauna a baya dashi har yadda yaso aurena nakiya cikin dadin hira na labartawa iya komai tave na dai fahinci akwai chakwakiya a gidan ku uwar dakina na amsa da sosai iya.
Amma dai mahaifitarki rasuwa tayi koka taso a cikinsu ko don na kula kamar ba mahaifiyarki a gidan na danyi murmushi ina fadin a,a iya rabuwa sukayi da majaifina dai ta koma kasarsu da zama ta barni nan na taso a cikinsu.
Wai ilon Allah wani lokaci muata mukanyi fushin zuciya mu aikata abinda ba daidai akan diyan mu sai daga baya kuma abin yazo ya damemu a rayuwa.
Nace hakane amma ni tawa uwar rabamu akayi da karfi da yaji iya na bata dan labarin don tana da hankali sosai har yadda na taso cikin su mama da irin gwagwalmayan da nasha a hannunsu.
Zuwa baiyanan mahaifiyata loop okacin bukina ta nisa tana fadin ikon Allah dama rayuwa kowa da tasa kalan kaddaran wani yasha wuya daga baya dadi yazo wani kuma dadin zai taso a cikinsa akarshe wahala yataso masa .
Ya Allah ka sadamu da mafificin alherun ka amin muma da sadiya dake kwance gefen kafata muka amsa da amin sai falon yayi shiru na dan lokaci guda inka debe Sadiya dake zaune ta kurawa tv ido don ita tana da sha,awan kallo nake gani.
Tsakanina dasu babu tsangwama ko hattara zama mukeyi na amana basu wuce hurumin na abinda ya kawosu ni kuma ba matsi ko wullakanci a tsakani dasu don sunzo gidan mijina da sunan aiki a,a na daukesu kamar wasu bangare na rayuwana wa yanda zama ya hadamu a rayuwa ban yarda na nuna masu wai muna da bambanci ba .
Iya ina bata girmanta na mtsayin babba a cikin mu ita kuma sadiya ina mata daukan kanwace a gareni in naga ba daidai ba zan tsawata mata cikin hikima da basira sai kiji iya din tace fada mata dai hjy kila ke taji naki ko iya ta kawo karanta a waje zan mata fada a wurin kai tsaye.
Zaman mu na kaduna na kula har iya din sunfi jin dadin shi a yanzu tunda suna dan fita zuwa unguwa wani lokaci ko wani aike tare da driver da ke zaune don mu a gida.
Maigidan bayanan yayi tafiya zuwa South Africa na sati biyu yasa ya barmu a kadunan zaune tunda banjin dadin jikina ina renon karamin cikin daya baiyana a jikina yanzu dan wata ukku.
Zaune take saman gado tana shan ruwan tea lokacin iya tayi sallama ta shigo da kayan karin safensu suka gaisa tana fadin yau kan jiki yayi kyau gaskiya hjyma tace a gaida ku maigidan ne baya gari kuma kalamin tsoho da yayi nacewa kada tazo idan ba mijintane ya dawoba shiya saka bata zoba.
Aiko hakan wallahi Bintu tayi ta nuna yar uwatake nagari abinci kai dakai haka ga kudin magani wallahi angode kice mata babu komai don Allah tayi zamanta har mijin nata ya dawo aiko hakan tayi namijon kokari wallahi.
Samira din ta lumshe ido tana hadiyan wani bakin ciki da har ya kasa boyuwa a fuskanta ta dago tace dama daga gidan bantu ake kawo wanan abincin kullun.
Sau ukun nan kuwa tunda mukazo asibitin nan ba fashi ga kuma aike a kai akai na alheri kofim hannunta na ruwan shayin ta mikawa mama din ta koma ta kwanta tare da juyawa ta bada baya.
Ganin hakan iya tayi masu sallama ta tafi lokacin data dawo gida ina daki don haka bamu samu ganin juna ba sai yamma bayan sallah la,asar nafito muna zaune falo driver ya dawo yana fada muna an sallamesu shiya kwashesu zuwa gida mukai mata fatan Allah ya bata lafiya.
A karshe dai muka zauna zaman hira kafin magariba yayi nan ta jefo min tambaya da nikan hjy mahaifinku daya da ita wanan mara lafiyan ne ?
Nace uban mu daya mana iya me kika gani mahaifiyarta ce amarya yanzu a gidan mu bayan fitar tawa mahaifiyan daga gidan namu sai naga ta nisa din nan tana fadin cabdi jam na kalleta nace iya da magana ke nan ko ?
Tace babba kuwa don ko na hango kiyayyarki a tsakiyan idonta daga jin ance daga wajenki abinci da komai ke fitowa hatta da kudin asibitin da aka biya nata tun lokacin wani malolon bakin ciki ya rufeta data kasa boyeshi a cikonta.
Mahaifinmu daya wallahi amma na rasa meke damunta ta dauki tsana ta sakamin ita da mahaifitar su hassana nan dai na dan kara bata labari akansu har sunan da suka saka min na karan dafi tace yafi dan dawa amfani ba inji manya.
Ranance karo na biyu da naji wannan karin maganan da farko a bakin gwaggona na zaria sai kuma gashi a ranan bakin iya nake fadin iya meye wanan karan dafin ke nufine wai ?
Murmushi ta danyi kafin ta dan moskuta tana gyara zama tace tau abune kamar a baiyane don sun nuna kin buwayesu kinfin karfin su don shi karan dafi tsirone daga Allah a daji ba,a shukasa ba,a farga dashi har a sare sai ya fito yana nuna alaman sanyi da danshi a waje duk inda ya bayana din.
Wani lokaci kuma don karfin tsiron yakan fito koda wuri ya kasance mai tauri ko da saman dutsene za,a iya samun tsiron a nan ma.
Wace ta saka maki sunan nan tasan komai a kanki kafin ta furta ta buga tagani baki biyu yadda sukeson su ganki ba a idanuwansu shiyasa ta furta hakan akanki ta kiraki da karan dafi.
Nisawa nayi nace iya kada ki gaji dani son Allah meye amfanin wanan tsiron kuma tace amfaninsa shi yafi amfini ga mata don akasari indai hadi daya shafi mahaifane da wuya ba a hada da wanan ganyen da ake kira da KARAN DAFI din .
Mata suna hadashi cikin wanan hadi na kayan mata kadan don faninshi na wanko maihaifa ana asiri dashi na neman tsari daga miyagun abubuwa mutum ko aljan ko wani dabba mai cutarwa.
Ana amfani dashi wajen namijin dake da matsala akan al,auranshi wajen inganta tashin gaban maza haka mace mai neman haihuwa idan ta lakanci dafa wanan tsiron da dan balma kadan tana sha na tsawon wani lokaci da yardan ubangiji akan dace da haihuwa.
Mata masu matsalan ciwon mara a da zamanin ba asibiti sai birni haka ana amfani dashi wajen hada maganin matsalan ciwon mara din nan a dafa ko a jika ya kwana da dan tazargade da kayan yaji sai a dinga sha wanan ba matsalan mahaifa ba kawai har wajen maza yana da amfanin ga macen da take amfani dashi.
Iya dan abinda nasan Karan Dafi nayi ke nan a wajen mu amma nasan wasu nahiyar suma suna da yadda suke sarafa wanan dan tsiron a wajen su wajen amfani dashi ta hanyar magani.
Dan murmushi na kwashe dashi ina fadin ashe sunan nawa mai amfanine ga jama,a dama aiko naji dadin hakan tunda ba wani suna ba ibilisanci ta saka min ba.
Har nakoma daki daki ina fassara wanan sunan da maman tudun wada ta bani mai ma,anoni haka da yawa ina son in gano dalilinta na rada min wanan sunan.
Bayan sati daya Boss ya dawo daga tafiyan da yaje ya shigo kaduna da yamma lis yana fadin zamu koma Abuja next tomorrow zuwa jibi ke nan insha Allahu.
Hakan yasa washe gari muka je duba Aliyu muka kai masa provisions masu yawa naji dadin ganin yadda yaron ya koma girma yazo masa ya zama wani naysatse dashi yayi kyau ainun kamar ba Aliyu almajirin gwaggo ba a yanzu zakace dan wani mai kudine shi.
Shima Aliyun yayi farin ciki da ganin mu cikin murna yake tambayana yaushe muka dawo na fada mai mun kwana biyu da dawo ai muna nan kaduna kusan sati uku ke nan yanzu.
Ya dan bata rai yace shine bakuzo ba naganku antu babu mai zuwa wajena sai Nura idan ya kawo min visiting kayi hakkuri Aliyu haka karatu ya gada wata rana sai labari.
Munyi sallama dashi don ba lokacin visting bane andai bamu lokacine muka gansa a lokacin daga nan muka nufo gari.
Gidan mami muka nufa a nan muka wuni da yamma muka dawo muka fara shirin komawa abuja don yace tafiyan safe zamuyi ranan yana da aiki.
Da kyat na samu ya biya dani gidan mu don in sallamesu in kuma gaida samira data kwanta asibiti ban samu zuwa na ganta ba lokacin don baya gari.
A nan gidan namu kowa na fitowa muna gaisawa dashi har da dan abin tsaraban da mama uwa ta hada min irin abinda uwa ke hadawa yar ta idan tazo ganin gida haka mamana mama uwa ta dan zage karfinta ta hada muna abin amfanin gida irin na tallaka da zamu dashi bayan a can wajen mama din ma ta bamu.
Samira ko kiri kiri taki fitowa daga dakin mugaisa wai tana barci bata tashi ba yasa baba ya fara fada Boss bashir yace a barta mana tunda bata da lafiya kada a bata mata barcin ta yai masu alheri muka fito su hassana dasu mama har wajen mota suka rakomu.
Nan yake fadin zai turo mota next month a kwashesu zasu zo Abuja suyi muna kara wani dan uwansu zaiyi auren yar gidan minister nan abuja din a nan za ayi bukin.
Nan suka fara fadin Allah ya kaimu lokaci lafiya yace amma ita sister kafin nan zaki zo ko kivdan muna kwana biyu a wajen mu da cewa hassana kafin ya mayar da hankali wajen isa mai shago suna magana dashi.
Duk abin nan dake faruwa a gidan mu lokacin a idon samira dake labe bayan labulen falon mama tana kallon mu sai bayan mun fitane ta dawo dakin nasu ta zauna cikin wani yanayi mai nuna damuwa.
Haka uwar ta shigo ta sameta a zaune ta bita da kallon mamaki kafin tace yanzu ke kina jin yar uwarki dama kika ki fitowa ku gaisa harta tafi ?
Nime zance mata mama dama ai ba don ni tazo gidan nan ba gunku tazo ni meye nawa da saina fito mun gaisa da ita don neman isa kome don tana ganin ita tafi kowa yanzu kome ?
Kallon mamaki uwar ta kara yimata kafin tace ashe ko kina da aiki zaki ko halaka kanki da bakin ciki wa yandama suka fiki tsiyataku da shekaru da komai sun ganta sun barta nan balle ke .
Hana me arziki arziki sai Allah saidai ki sani ba zan taba yarda a yanzu ki hadani da Bintu ba kamar yadda kikayi da farko kika hadani da yarinya ta daina ganin girmana bayan a yanzu na samu mun sasanta da ita.
Keda kika dorawa zuciyarki mugun abu sai kije kiyi ta bakin halinki ke kadai nidai nasan har abada bintu ta wuceki ga komai ga ilimi ko da kanta tana iya dogaro haka kuma ga miji ga kuma mahaifiyarta da yanzu ta zama hamshakiya kowa ya gama sani hakan ni meke gareni yar ?.
Kune dai yanzu zan sa rai agareku dama ruwan ido kuma ya hanaki tsaya kiwa kanki fadan abinda ya dace yanzu ki fada min riban da kikaci na wanan bakin auren naki kin guntule karatun ki kince aure yanzu gashi baki ga karatun bakiga aure anyi biyu babu ko daya.
Don haka duk tsiyan da kika dawo gidan nan ki shuka kada ki yarda ki sak???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ani a cikinsa idan ba hakaba sai na shayar dake mamaki kwarai da gaske a gidan nan.
Umman mu akan Bantu kike fada min haka kwarai kuwa duk abinda babu gaskiya a cikinsa kinsan tun farko ba bin hakan nakeyi ba dama kece kika so ki juyar dani yanzu kuma nagane gaskiya ta yaro kyau take baya karko.
Karki koma ki sake ki kara jefa kowa nawa cikin harkan yarinyar nan donni ba butulu bace yau ki duba inda alherin yarinyar nan ya kai mu a gidan nan ni sakaraine da zan maida kaina baya a yanzu don ki.
Ko ita yaya datafi kowa tsanarta a gidan nan a yanzu ta san abin yafi karfin ta gashi tajawa kanta ciwo a banza yana batun kaita kwance kowa kuma yasan bakin cikinta a gidan nan bakomai bane sai ciwon hassada da bakin ciki.
Yaran ta da Allah ya tsame gasu can da yake suna da wayau da hankali sun shige ana komai dasu dumu dumu a yanzu bamai cewa yayace ta haifesu kuma suke tare da Bantu ayanzu haka.
Kuka ta soma tana fadin yanzu dai nagane umman mu akan Bantu har kike kokarin min baki akanta ke nan kin debe rai ni ba zan taba zama wani abuba da zan kaita ko infita.
Addua na ke nan gareku tun ranan dana haifeku har gobe kuma idan nayi sallah ina binku da adduan samun shiryuwa tunda ke din nan da naga rayuwan ki ya gurba a yanzu da wani akida na banza can.
Kuka sosai takeyi da har ya jawo hankalin mutanen gida a kansu har mama uwa ta karaso tana tambayan meke faruwa uwar bata bada amsa ba sai cewa da tayi tambayar ta aigata nan ta fada maki da bakinta don ni ba zan dauki wanan mugun halin ba a yanzu na fada mata gaskiya shine take min kukan munafunci a daki.
Ai gaskiya ta fada maki Bintu bata dace da haka ba gareki Samira duk abinda kowa zai mata a gidan nan na muzance yarinyar nan tana kawar da kai a kansa ta nunawa mutum bata masan yana mata shiba.
Shi maiyin baida hankalin ne da kullun yana ganin yar uwarshi naci gaba shi yana ci baya ga harkan shi aiya kamata mutum yaiwa kansa fada idan yana da hankali tun wani bai masa hakan ba.
A cikin kuka take fadin yanzu nime nayi umman mu ta shigo daki kawai ta hauni da fada da bansan hawa ba bansan sauka ba akan Bantu ita Bantu din ta fini gareta ne in sani ?
Samira samira kisan abinda kike fadi da aka kawoki garin nan idan badon Bintu din ba ya zamuyi dake agidan nan da kudin magani tunda mahaifasa sunce ba matsalansu bane a kira mijin ki shida yayi ko akai karansa.
Bata san da wanan zancen ba ita sai alokacin amma mama uwa ta fasa mata shi a lokacin kukan da takeyi ta tsagaita tana fadin sukace babu ruwansu fa maman Amira tace kwarai.
Ko kina musun hakane kinga wani daga gidansu asibitin da kika kwanta wanan abin bai isheki ba hae zaki tada wani hasumi ki tayarwa mahaifiyar ki da wani hawan jini yanzu kuma bayan bintu ta raba wanan gardaman a tsakanin mu dasu.
Wake da dubu dari da wani abin bayarwa a yanzu gidan nan kaf kinsan ko a kwashi babu mai bayarwa ma


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login