Showing 93001 words to 96000 words out of 347556 words

Chapter 32 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8751

kusa zata fadama koda muke fita tana bin mazan ta ban taba fadawa kowa ba saidai in barwa cikina zancen.
Dakata Fatima ya fada da karfi yace ba zancen wasila nake maki ba yanzu zance nakeyi na tsakanina dake ko ya wasila take Allah ne ya kaddara zata shigo rayuwata a yanzu itama.
Yanzu muna zancen ne na tsakanin nidake na ya zamuyi mu dora sabon rayuwa a tsakanin nidake ki bar dauko min zancen wasila kina kadawa cikin zancen mu idan munayi.
Sannan da kike zancen wasila kina zargina akansu in har kin yarda da rantsuwar da zan maki wallahi Allah ban taba sanin duk abubuwan nan kan wasila ba sai yanzu da kike fada min.
Aurena da ita kuma mukkadarine daga ubangiji don maman baby ta hadani da ita a matsayinta na aminiyar marigayiya ta tausayawa zaman kadaicin da nakeyi ta hadani da wasilan da kike zargin kila tun Safiya nada rai muke tare.
Wallahi ban masan wata wasila ba a lokacin ni in zaki min adalci kema kinsan tun safe in nafita sai yamma lis nake dawowa gida lokacin .
Dakata yaya don Allah fadin hakan da nayi yasa Samira dats shigo dakin take saurarena ta dago kai ta kalleni cikin mamaki.
Da meyasa baka san da hakanba sai yanzu ?
Yanzune igiyan so ya jawoka gareni ko me don Allah kada ka daukeni wata yarinya ko wata bakauya can da zakazo ka ruda da dadin bakin ka namaza kaci bulus .
To don Allah ina rokonka daka tsaya a matsayin da kake a wajena shine mutuncinka dani kada wanan kalaman naka ya kawo abinda mutuncin ka zai ragu a raina don Allah.
Jikinshine ya dauki rawa lokaci guda ya fara fadin nasan zakiyi min wanan borin amma nina riga dana tura Alh ko yaje yaga baba nasan kuma shi baba zai fahinci gaskiyata a wanan zancen ya gane sonki nakeyi tsakani da Allah bada wata manufa ba yadda ke kike zato din.
Nace da sauri wanan kuma ruwanka don ba baba zai zauna min da mijin da zan aura ba ko zanyi aure sai in rasa wanda zan aura a duniya sai kai yaya ?
Don haka ina son ka sani daga rana me kamarta yau bana son ka kara shiga tsabgan rayuwata sabodani Fatima nasan mutuncin kaina ni ba yar iska bace ko mai kwadayin abin duniya ba.
Ina fadin hakan na kashe wayata a cikin takaici ba tare dana tsaya jiran mezai fada ba a lokacjn don sauraronshima wani tashin hankaline agareni lokacin.
Na mike daga inda nake na suri butan zuwa ban daki na kewa na bar wayan a dakin hakan yaba samira daman duba number da nake waya dashi haka saidai ba suna.
Kodana dawo ban shiga dakin don haka na nufi dakin gwaggo a kofa na tsaya ina gaida ita sai gata ta fito tana fadin yauko lafiya kuke koda yake nasan ramuwar baci kukeyi a yau din yasama ban lekaku ba.
Nace wallahi gwaggo ban samu barci bane sosai jiya yasa da safen nan na ramashi don jiya naji tsoron maganan da kika fadane gwaggo.
Tace kai amma yar nan mu garin nan yanzu inda sabo mun saba jin wanan a haura gidan mutum ai masa ta,asa akasheshi ko a kwace mai dukiya a linkida masa duka ko a wullakanta masa iyali a gaban shi sai dai munan unguwar gaskiya da sauki sosai.
Hakafa muke ji ana fada ayi kaza duk a zariyan nan shiyasa da zamuzo baba yace ba zuwan zaria karatu ba saidai muyi jeka ka dawo lokacin mun wahala don muna makara sosai lokacin.
Mun da jima nan da gwaggo muna hira can samira ta fito tana gaida gwaggo din ta koma daki saida wayana yayi karane yasa na koma dakin kunsan waya abokin rayuwace shi a yanzu.
Nurane ya kirani na dauka muke gaisawa bayan mun gaisa yake fadin kina kusa da wanine don abinda zan fada maki banson kowa yaji na fada maki shi.
Na wayace wa Samira da fadin barin fita in duba maka waje ya gane me nake nufi yasa ya kashe wayan ni kuma na saka takalmana na nufi wajen gidan.
Saidana fitane na kirashi ya daga yace wai anty Bantu me kikaiwa maman biyune halan tun jiya take fada a gidan nan wai ke din makirace kin iya yaudara da makirci dama yasa kika shigewa ya Mahmoud.
Ya Mahmoud kuma na fada a fili a zuciyata kuma cewa nayi oh ashe da gaske yake ya fasa maganan kowa yaji zaiko ga tsiya wallahi ni me zanyi da mijin yar uwata yar uwan nawa kuma dakin mama habadai don Allah.
Nura kyaleta haukan banza sukeyi don ni banda lokacin hakan yace ai haka maman mu ta fada mata da take magana nace ka fadawa mama tabar tanka mama idan tana haukanta don Allah ni me zanyi da wanan mutum da baida mutunci ma.
Bayan mun gama wayan da Nura na dawo cikin gidan raina a bace saboda wanan maganganun Allah ya taimakeni weekend ne ba karatu a ranan don dasun caza min kaina da zancen banzansu.
Gyaran dakin na tsiriyi lokaci lokaci ina jan tsuki samira dake kwance tana charting ta dago kai tace wai dake da waye haka sister .
Na girgiza mata kai gami da fadin babu komai naci gaba da aikina ta bini da kallo can naji tace ban yarda ba ta yaya zakice dani ba komai bayan tun cikin dare nake jin kina jan wanan tsukin haka.
Bayanshi duk wani mahaluki mallakin hankali ya dubi yanayinki yau yasan akwai abindake damunki sai dai idan boye min zakiyi baki son nasani na yarda da hakan.
Haba dai ba abinda ya faru wanan dan rainin hankalin ne yakeson ya raina min wayau kawai ita kuma mama tana gida tanawa mutane haukan banzan data saba koshi zaiba mutum tsoro oho ?
Samira tace waye ki fada min kin tsaya kina yi min kwana kwana na kasa fahintar zancen ga baki daya a yanzu.
Kallota nayi da kyau nace watau samira wasu mutanen yan rainin wayaune sosai wallahi a yau na yarda wasu mazan basu da isasshen kunya.
Samira tayi saurin katseni da fadin wai waye wanan da ya shiga inda bai san kaya bace wani wahalalen dan rayuwane wai sai faman shan kwana kike dani.
Ke dai bari samira ya wuce wanan dan rainin hankalin ya dauka ana fadin yayi kudi yanzu ya faso gari shima bari yazo ya raina min hankali tunda yaga wawiya ko makwadaiciya.
Humm ba fada da tsohuwa dama jinini to ki fada mana ni duk na kagu inji ko meye sai turani daji kikeyi ina kara bata.
Nace wai wani tatsuniya ko almara domin kuwa ni a matsayin tatsuniya ko almara na dauki zancen shi wai ya Mahmoud ne fa yazo min da wani zancen banza a yanzu shine ita kuma mama ke nata haukan a gida
Ido Samira ta ware tare da wani irin dagowa tana fadin amma ko yaya baiyi ba wallahi shi ina hakan zaiyuyu don baisan ke baki da lokacin irin soyayyan nan bane ko ?
Nace aini na fada mashi gaskiya ya kama kanshi tun wuri don ni ba shasha bace da zai dauko wahala ya dora min da sunan so yanzu.
Humm maza ho ni dama nasan za,arina wai ansaci zanin mahaukaciya wallahi tunda sukazo din nan na zargi hakan bandaiyi magana bane kawai .
To ita kuma mama haukan me takeyi wai nace na shirme mana inba shirme ba haka kawai daga jin magana zata hau fada tana kirana da makira .
Ke nan ni naje nace ya soni ko me oho ita bata san ni bai gabana ba koma yana gabana me zai hadani hada jiki da wanan yanzu da nake daukanshi a kazami saboda sanin matarshi da nayi a baya.
Ita dai take nata haukan yanzu ta dauki hussai ko hassana mana ta bashi nace ai haka akace ta fada wai saidai ya kara zaba a dakinta badai ni ba.
Kam tayi arziki bani yace yana so ba wallahi dataga tsiya da iya shege arzikinta ke nan hakan bai faruba wallahi da ba ragowa toke me zai hana ki soshine guy din ya hadu fa Bantu.
Tsuki mai karfi naja tare da fadin baki ganewane yar uwa rabu da kyalkyal banza kawai inda kika ganshi tace haba dai wallahi za a hutafa kema kin sani.
Hutu da wahala don Allah mu bar wanan zancen kada ki kara bata min rai don naga yama yi bala,in raina min hankali wallahi wai ya Mahmoud fa haba dai don Allah.
Daga wanan maganan ban kara wani zance ba a kai na fita na bar samira kwance wanka naje nayi dana dawone sai ban sameta a dakin ba har na gama shiri na fito na tambayi gwaggo ko za a dafa abincin ranane a gidan.
Take fadin wai taga mu kadaine bamu rasa abinda zamu dan taba a dakin yasa tace saida yamma a girka bansa aljihunta ba yasa nace Allah ya kaimu na juya na koma daki.
Kwanciya nayi da niyar inyi karatu amma kuma sai hakan ya gagareni don tunane da bacin rai dayafi karfina a lokacin can saiga samira din ta dawo take fadin ai ta danje nemo muna abin karyawa ne.
Kallon ledan nayi a take nagane ba sayayyanta bane wanan zama tayi tana fadin ina sauri in dawo ai kada ku dora girki don doyan nan yayi yawa gaskiya.
Ke baki san zaiyi yawa bane da kika sayo haka hmm wai ke kin yarda ni zan iya sayen wanan haka malam nayiwa waya shine ya kwaso min shi hakan nan da yawa.
Amma gaskiya samira wanan halin da kika dauko baiyi ba wallahi shinke baki tunanen hakan kina zubarwa kanki da kimane ai wanan kamar tozarcine kikejawa baban gidan nan.
Don me daba zakiyi hakkuri da abinda sukeci ba inyaso in zakici kwalam dinki sai ki tsaya can kici abin ki idan mun fita school.
Yin hakan kuma laifine nifa gaskiya kinsan ba zan iya cin abincinsu ba ko yaushe din me kuwa zan tauye kaina a yanzu ta fada a dan hasale ?
Ki daiyiwa kanki fada acan gida abincin gidan namu yafi wanan ne dadi ina dai shimkafane sai tuwo a nan ma kuma shi din daine mukeci ko ?
Bata kulani ba naga dai ta mike ta fita sai gata da plate guda uku ta dibawa gwaggo ta zuba min ta juye saura a plate din gabanta.
Ta turo min wanda ta zuba min tare da fadin nasan da kyat kici don kina dauka kamar ta hanyan banza yake biyana da hakan niko nasan abinda nakeyi Bantu wallahi na sani sarai.
Don hakan da kike tunane yasa kona samo abu na baki yanzu bakyaci tunda kin fassara abin a wani tsigar na daban jin hakan yasa na dan mika hannu na jawo plate din gabana da kyau na dauki doyan na dan fara ci dama yunwa nake ji a lokacin .
Sai da mukaci ta mike takaiwa gwaggo dakin tana barci don haka ta ijiye mata a dakin idan ta tashi zata gani.
Maratane yake dan yankawa sanin alaman period zaizo min gashi kuma banda pad a lokacin yasa nace mata zan dan fita in sayo pad kafin yamma ya karasa.
Ki bari nayi wanka mu fita tare ta fada hakan yasa na tsaya jiranta harta shirya muka rufo dakin mukaiwa gwaggo dake motsi dakinta sai mun dawo zamu dan sayo auduga a shago ma fada.
Da kafa muke tafiya don wajen ba nisa sosai naga wani shagi nace muje budan bakin samira sai cewa tayi haba dai wanan shagon kada ki zubar muna da lebus mana.
Dole haka na taka muka isa wani babban shago da mutane ke zirga zirga a cikinsa ga motoci nan bila,adadin an jera nan ta nufa dani mamakin yadda tasan wajen nayi nace ke yanzu saboda wanan kika jawo mu har nan.
Nasan baki san wanan wajen ba ai idan kin shiga sau daya zakiji kina son wajen muka tura kofa muka shiga wajene hadade ya tsaro ga kayan nan kala kala a jere kowa na daukan abinda ya kawoshi.
Yanzu ke ina zamu gane inda pad yake a wurin nan tace mu zagaya mana idan mun gani basai mu dauka ba a hada dako sweet ne ai dai munga wuri.
Zagayawa muka farayi inda samira har da tsayawa duban turare kai amma wanan turaren zaiyi kamshi lokacin na kallo naga abinda take magana a kai.
Gidan turaren kawai abin kallone kwalinsa mai dan fadi gefe daya rubutun arbiyane dayan gefe acikin boko aka rubutu da manyan haruffa a cikin staly.
WHITE MUSK OUD na dan juya na mayar na aje na dan gusa saiga pad nagani iri iri hannu na mika na dauko wanda nake amfani dashi always.
Na juyo don na dauka samira din tana bayana amma sai na ganta a can wurin turaren dana baro tare da wani a tsaye suna magana.
Juyawa nayi zuwa wajen ina fadin kinga na dauko zo fita don Allah yi tayi kamar bata jini ba a lokacin naga an miko mata wani dan kati tace zaka jini.
Mamakin hakan ne karara a fuskana amma na hade na fara tafiya zuwa inda zan bada kudi na aje dan ledan pad din saman table saurayin dake zaune a wajen ya duba kudinsa ya cika min dan takarda ya miko min.
Da sauri na ciro kudi dan dubu daya ya miko min canji na juya na fita don hakan nake idan na shiga wurin da mutane suke da yawa sai inji kamar ni kadai ake kallo a wurin.
Wayata na fitar ina duban lokaci naji wani murya a bayana yana fadin ga wanan kin manta baki dauko ba kai na dago da sauri na kalli mai maganan.
Wani matashin mutum ne gabana a tsaye yana saye da yadin maza fari kal mai dan zanen layi a tsaye har kana iya gono far singlet daya saka daga ciki sai jar hulan dara a kansa dan karami mai ga wani kamshi da yakeyi mai dadi a jikinsa yana dukan hancina.
Kaina daga na kalleshi kafin na kara kai kallona ga dan ledan da yake miko min a lokacin na bude baki da kyar nace ni wanan kan ba nawa bane ai.
Ki karba mana ya fada cikin hausanshi da kamar bata zauna mai sosai ba a,a ni ba zan karba ba don ko ba tawa bace na fada ina kokarin daga kafa in bar wajen.
Zuwa lokacin nagama kulewa da Samira ko, don bansan abinda ta tsaya jira a cikin shagon nan ba gashi duk wanda zai shiga ko zai fita sai ya dan waigoni kamar mara gaskiya.
Amma ai ke tsaya ki duba tunda nace nakine kika manta a cikin shagon sai ki duba ki gani malam don Allah kayi hakkuri na fadama ba nawa bane ko menene.
Murmushi yayi yace so cute idan kinyi fushin kin kara kyau inaga idan kina fara,a kuma fa nasan ba naki bane amma naga kin nuna ra,ayi a kansane na dauko Mk maki shi.
Ki karba don Allah don in baki karba ba bansan ya zanyi dashi ba tunda na matane bana maza ba lokacin na kai ido akan dan ledan karami mai launin purple dauke da tambarin shagon dake hannunsa.
Malam bance dakai ina so bafa yace ni kuma sai naga ya dace dake yasa na dauko maki shi ya kara miko min yana fadin ki karba don Allah ba don ni ba nasan baki aikeni ba amma ki karba.
Ganin wasu mutum biyu da suka wuce mu suna kallon mu dayan har dan waige na dawo da kallona wurinshi na karbi ledan ina fadin nagode.
Don't mention that tunda kin karba don Allah is ok wani iri naji nabisa da kallo ya gyara tsayuwa yana fadin iam Mohammed Mansur ibn Abu sufiyan zaki iya kirana da Ltn Mohammed mansur.
Ya tareni da fadin saboda wanan abin kikazo shagon nan kawai kafin na gama mai kallon mamakin abinda ya fada kallon ledan dake hannuna nayi nagane yaga abinda na saya ke nan yasa yace hakan.
Banyi magana ba sai juyawa da nayi na fara tafiya don bansan me zance dashi ba a lokaci in akwai abinda mace budurwa ta tsana namiji yasan zancen period din ta nidai a wurina.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
2?? 9??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Ban juyaba tunda na fara tafiya saida na


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login