Showing 72001 words to 75000 words out of 347556 words

Chapter 25 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8717

ku yanzu kun girma bakwason gaida mutane ko ya fada aina gaidaku da kuka shigo yace shine gaisuwan na dai danyi murmushin yake mama uwa ke fadin .
Bintu aiko Mahmoud ya wuce gaisuwan mike a gareki shine fa uban gidanki na farko na dan kara murmushi mai kama da dole nace kai mama.
Da zai fita yaja Nura suka fita gidan Nuran ya dade a wurinsa kafin ya dawo yayi wanka ya fita ashe ya karbi layin wayana a hannun Nura din dama kiran ke nan da yaiwa yaron ashe.
Wayata ke kara na dauka hjyce ke fadin kinga tuwon mu nan na jiya angyara muna cin abinmu komai baiyi ba mamata nace kai har yau din nan baku cinye ba mama tace wallahi yana nan da karfinsa kamar yau akayisa.
Nace mama yau ban samun shigowa muna aikin buki yau da gobe sai dai idan mun rarage zaku ganmu ok ta fada dama nayi tunanen hakan amma don Allah kafin ki tafi dan wake mukeso da maida yaji.
Dariya na danyi nace mama wanan aikin Al,amin ne kuma ko tace wallahi a,a uncle dinsu daine yake sonci wai nace bari a kiraki aji ko kina da time kizo ki muna.
Sai banda gobe insha Allahu zanshigo na hada tunda uncle din mu keso ai dolena nazo na hada tace kema kinsan halinsa ke nan nace sosai mama bayan mungama wayan da mamane.
Wani bakon lamba ya kirani ban faye saurin daga kiran da ba sunaba don haka bandaga wanan dinba shima bai kai wani lokaci ba ya katse.
Ranan aiki sosai mukayi sai bayan azahar na samu shiga gidansu hjy mairo koshi don naji shiru basu aiko muna da kayan miya ba har lokacin nashiga.
Dakin hjy mairo naje bata ciki a lokacin tana dakin mijinsu don haka na zauna zaman jiranta harta fito din nadan jima a zaune sai gata ta fito din tana ganina tace yauwa Binta kizo muje falon Alh don Allah.
Nabi bayanta muka shiga yana zaune a kasa ya ishishire kafafunshi ga yan uwansa mata su biyu zaune saman kujera kasa na zube ina gaidashi kafin na juya ina gaida yan uwan nasa.
Suka karba yace a,a Fatima wai kina garin nan dama kodai kinzone nace baba bukin mukazoyi da angama zan koma yace yar albarka.
Kinganta nan hjy yarinyar nan diyace ubanta tun yanzu ya morewa haihuwanta don kullun cikin saka mata albarka yake to bashiba yaya harmu nan makwabta muna sakawa yarinya gata albarka.
Yarinyace mai halin dattako yanzu ki duba duk yaran nan dake shigowa wa kikaga ya gaidamu haka da sauri yar nasa tace wallahi babu babu nima na nasa hakan a raina gaskiya.
Kingani irin yaran nan ya kamata ace Mahmoud ya nema yaran na arewa akwai tarbiya da sanin darajan kai amma yaje ya kwaso wanan abin kamar icce wai mace ?
Banda farin fatan me take dashi nasan farin ne dai ya rudeshi amma in b??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ashi ba meya gani jikin wanan matar daya kwaso .
Alh ga Bintu nan itace me aikin ka kama nakin Aljihu ka kulle yanzuma a bin miyan ta biyo son kada a makara wai yata ya fada na gyada masa kai yace kamar meda dame kuke bukata ?
Na lissafa yaga sun masa sauki don wani ma basu fada mashi ba yace to jeki ki jira hjy a falonta na mike ina fadin to baba na fito da sauri na barsu suna rigiman amsan kudi da hjy din.
Ni kan dakinta na shiga na zauna a saman hannun kujera ina dan dakilan wayata saiga su sun shigo kamar kullun shida Ibrahim ya ibrahim dinne a gaba ya fara fadin hjy Binta kina hutawa fa yanzu.
Na danyi dariya nace kai yaya harda kuma cikin mana sherin jin muryansu yasa wasila shigowa tana fadin har kun dawo ke nan ashe garin baida nisane Nura nagani yana shigowa da kaya dakin nace Nura yace anty Bantu kina nan ashe ?
Kai ina ka shiga mama tana nemanka tundazun yace muna tare dasu yayane kaje gida mama na nemaka ka dauko muna nika yace yanzu zan tafi ai.
Ina zaka ban gama da kai ba lokacin na dan dago kai na kalleshi wani iri kwarjininsa nagani nayi saurin dukar da kaina kasa Nura din ko har ya kara fita da sauri suka shigo dasu tomatoes tattasai alaihu mangyada manja jarka jarka sai nama mai yawa sosai a cikin wani kwandon saka.
Amma kayan nan baiyi yawa ba wasila ta fada tana wani yatsune fuska kowa ya kallota dakin kanwar yaya din tace mu ai wanan ma bai isa a taron gidan nan.
Mikewa nayi ina tsuki nace idan hjy tazo anty hafsat ace na tafi don Allah a aiko min dashi cikin lokaci nasa kai na fice nabar dakin ya dago ya bini da kallo itama tana kallonshi.
Kasa daurewa tayi tace Bantuce manya yanzu a nan kuma girma dai baida wuya yanzu dan kwana biyu sai kaga mutum ya girma anty hafsat tace kinsanta ashe tace wai Bantu sosai makuwa ba tare muke a can dasu ba.
Na shiga gidan banjima ba sai ga Nura yana shigowa da kayan ciki yana tarasu a kofana kallon kayan mukeyi har suka gama shigowa dashi yace to ga kayan nan anbar wanda zasuyi amfani dashi acan wanan ya Mahmoud yace akawo a diba ayi aikin da za ayi saura muci a gidan nan muma.
Allah ya taimaka tun acan anyanka an wakeshi sol don haka mamata karba ta tafi wankewa ni kuma na fara gyaran kayan miya lokacin ne mama Lanto ta fito ta kafa kujera muka fara aikin ma,ana dai tare zamuyi aikin ke nan da ita.
Sai shadaya muka rarage muka kwanta agajiye koshi ma din dai zamu kwantane zuwa uku mu tashi mu fara aikin don idan munce mu bari har safe zamu iya makara azo ba a samu karasashi da wuri ba
Don hakane muke yawan yin aikin a cikin dare amma abinda mukasan zai lalace bamuyi sai mu barshi da rana muyisa don haka yanzun ma fannin miya da mun gama komai saura hadawa.
Wanan aikin yasa mu danyin magana da mama Lanto saidai ni ban yarda na sake jiki saboda yadda ta nuna min tana bayan yartane duk irin mutucin dake tsakanin mu abin ya bata min rai sosai wallahi.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[8/13, 10:45 PM] +234 906 446 1581: KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
2?? 2??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


Washe gari karfe goma sha biyu da rabi mun hada komai an zuba a kuloli don na sayo manyan kula don wanan sana,an na robobi saboda muna shan wahala akan kula yasa na sayo set biyu tunda muna samu acikin sana,an gida kuma na karuwa da wanan girkin don in munyi kowa nacin abinda ransa keso ya koshi.
Wanka nayi na dauko wani less mai ruwan brown buje da riga na saka yayi min cif zakice donni aka dinka shi dama na shirya tsab na kulle dakina gidan bukin naje don su turo a dauka.
Anty hafsat na gani ta fito ta samu mota mukazo tare muka kwashi kayan saura alale dake saman wuta shine bamu karasa ba a lokacin koshi don kada muyisa da wurine ya lalace muke barinsa sai rana ya dan daga mu hadashi akaiwa mutum.
Ni dai nasan muna aikin kwasan kayan nan mama rasawa mama Lanto kira tasameta a dakinta sukai maganan da zasuyi ta fito can mama din ta fito tana cewa kishiyoyin nata zata dan fita.
Ashe gidan hjy Hajjara ta tafi don sabodani suna dan shiga suma ai masu abin arziki lokaci lokaci ita da Al,aminne a falonsu suka gaisa tace wurin hjy din tazo tace lafiya dai ko ?
Tace magana nazo yi dake a gidan nan tana nuna son sai Al,amin din ya tashi dan bamu wuri auta ta fada mai ya dago yace ni mami tace dan shiga daga ciki.
Ya mike ya shige ya basu wuri lokacin ne mama ta soma magana tana fadin hjy dama nace in zo in bincika ko da saninki don yaran yanzu sai a hankali.
A yan kwanakin nan muke ganin canji ga mutumiyar ki Binta shine nace barin zo in bincika naji ko a nan take maki barna baki sani ba don kaya masu tsada dakyau muke ganinta dashi tana amfani dasu.
To sanin halin dan yau yasa nace barin taso muji in naku ne take kwasa bada sanin ku ba ko kuma bata kukayi indai ji jam jam subbahanallahi.
Haba dai keko kina wanan fatan ga yarki saboda Allah Binta yarkicefa ta cikinki ina wanan tunanen ya fito maki haka keko ?
Mama ta gyara zama tace yatace don tana yar mijina amma nasan baki sani bane Bantu karan dafine sosai duk wanda ta zauna dashi sai ta shashi kota yageshi.
Zaki ganta tana abu kamar na Allah amma sululun bonice cuta zallah yasa na taso kada tayi maki barna bada sanin ku ba don wanan kayan nasan ba batasu akayi ba debosu tayi maku.
Allahu Akbar gaskiya bai dace aji wanan zacen hakan ba a bakinki kan Fadimatu ba ina kema uwace kema kina da yaya mata idan aka fadi haka a kansu yaya zakiji.
Shifa sheri ko zargi kayisa akan wani sai ubangiji ya jerabeka ta kwatankwacin wanan abin dakaiwa dan uwaka sheri a kansa don Allah kubar hakan ba kyau.
Yarinyar nan Saboda kirkinta da irin rayuwanta yasa nakejin tankar nice na haifeta don ko dan dan uwanace Fadimatu yadda nake jinta ya tsaya nan.
Kaya dai a nan din ta samrshi tabbas kuma nice nan na bata su da hannuna kayan yatace da tayi aure ta dinka tayi amfani dasu idan munzo Nageria batayi ba kayan suna nan aje.
Nace ta kwashe taje tayi amfani dasu kuma ai naga ba ita kadai ta sakasu ba don naga photon ta da yan uwanta da sukayi shekaranji kowansu ya saka ko ?
To to to dama ai bincikene kinga mahaifinta ya turo nayi to haka yana da kyau amma ki fadawa ubanta cewa yayi dacen haihuwar ya irin fadimatu gaskiya yarinya ce mai mutunci da sanin ya kamata Allah ya kara shirya muna ita amin din ciki ciki ta amsa zata tafi mama ta bata dubu biyu tana godiya ta tafi.
Don lokacin uncle ya fito ya gama exercise ya nufo falo ya huta shine ya iske mama da bakuwa hakan baisa ya koma ba ya zauna dan nisa dasu kadan.
Al,amin ma ya dauka ta tafi ya dawo tana kulewa zata fita yace na dauka ta tafine tace zauna abinka ba alheri ya kawota ba dama sheri tazoyiwa yar mutane tazo nan don ta kullawa mamata sherine a wurin mu ta dauko wayanta data dannawa recording tana kashewa.
Ita din wacece Uncle ya fada ba tare daya dago kai ya kalli yar tasa ba yana ci gaba da taba wayanshi dake hannunsa sanin halinsa ta dago tana kallonshi tace.
Matar uban wanan yarinyar mamatace mai zuwa gidan nan jin hakan yasa ya dago kai yace meya kawota yanzu tace wai tazo ta fada muna muyi hankali da ita don ita din karan dafi ce.
What hakan take kuma Ukuthee haba dai Mohammad kaima ai kasan sherine irin namu na mata kishiyar uwace fa yanzu ta nuna a fili bakin ciki takeyi da yarinyar ta mamemu a jiki haka.
Shine tazo ta kulla mata sheri garemu muga bakinta mu koreta a jikin mu bayan wanan karka kara sherine kawai wallahi shiyasa kaga ina tausayin yarinyar nan gata da kokari da kwazo a rayuwanta.
Amma ai batai kama da irin hakaba gaskiya shi nake fada maka ai sherine kawai don suga rayuwan yarinyar ya lalace ba taci gaba ba shine kawai burinsu mata da yawa haka suke basu kyaunar diyan kishiya kamar su kashesu sukeji a rayuwansu.
Kai mami matar nan babban munafukace wai shine tazo ta binciki Al,amin dake sauraren recording din mama a wayanta ya fada yana kara makala wayar a kunnensa.
Kumafa ka duba Mohammad kayan nan har yayanta naga tabawa ba ita kadai tayi amfani dashi ba fa wasu kayane wai nan gidan ta debesu ne ?
Nan ta bashi labarin komai daya faru yace she is cryzy totally cryzy in ba hauka ba ai yarta ma tasaka kaya kikace daga hakan yayi shiru yana jin wani iri a zuciyarshi.
Hjy larabace ta aiko kirana don haka nake sauri don naje naji me take nemana dashi ina kawowa kofan su na hangoshi tsaye bakin motarshi yana waya saidai kamar hankalinshi yana kaina.
Ban kalli wajen don tunda na tunkaro naga irin kallon da yake min babu ko kyata ido ina karasowane ya saki wani zazzafan ajiyan zuciya inda can kasan zuciyarshi ke azazzalanshi da yayi min magana don damace a yanzu gareshi.
Yaso matuka ya kaucewa duk wata turassawan da zuciyarshi ke masa kan hakan amma wanan lokacin sai yaji ya kasa hakan saboda yadda yake ji kasan zuciyan nasa game da yarinyar a yanzu.
Don haka ya kashe wayan cike da kwarin gwiwa gadan gadan ya furta ke Fatima cikin daga murya a yadda ya saba kirana a baya lokacin ina zaune a wurinsu shida marigayiya anty Safiya.
Daga sama na tsikayo wanan muryan dana dade banji kira haka ba don ko a lokacin inyana son abu haka yake kirana da ke Fatima din .
A dan firgice cikin faduwan gaba na juyo inda yake yana tsaye har lokacin a jikin motarshi yadda na sameshi gami da zuba min idanunshi a kaina.
Tsayawa nayi cak tare da kallonshi naji yace kiraki nakeyi fa duk da naga kamar kina saurine a yanzu da kyat na hade duk wani haushinsa da tskaicinsa da nakeji na dan bude baki nace eh ina saurine hjyce ke kirana.
Sai naga ya dan tako zuwa inda nake din tsaya yana fadin ai naga saurin da kikeyi dinne na gane hakan nima takawan nayi na karasa cin masa.
Dan shiru yayi baice komai ba na dan lokaci yana tura sako a cikin wayanshi nima ina tsaye a gefenshi babu ko motsi kamar wata gunki sai can ya dago yana kokarin budan baki da kyar yace .
Fatima don Allah don Annabi ina son ki tsaya ki saurareni domin kiji abinda zan fada maki duk da a yan kwanakin nan ina hago wani abu kamar tsanata a cikin kwayan idanun ki.
Da sauri na dago kai na dubeshi lokaci guda don maganar tazo min a bazata ta kuma ban tsoro da mamaki na yadda ya gane ina masa kallon banza a yanzu din.
Na kokarta cikin karfin hali nace a firgice bangane ba ya habibi akan me zan maka kallon tsana kuma yanzu ni ina ruwana dakai meka tsare min da har zan yima rashin kunya ?
Ya gyara tsayuwanshi yace kina nufin yanzu ban sanki ba ke nan ma,ana ba fatiman dana sani bane a baya take gabana yanzu kin tashi a wacan kin koma wata me nayi maki kika tsaneni hakane ?
Duk da nasan ba zai wuce kan diyan antyki bane kike min wanan kallon banzan kome ne kuma bayan wanan din ya fada yana mai kura min idanunshi a kaina.
Baki na tabe na dan kalleshi nace inma hakanne hakane ya habibi sai naga ya lumshe idanunshi nace eh donko a yanzu nake ganin dakai aka hada kai ashe aka kashe min anty na a baya.
What ya fada da karfi saida naji tsoro ya nuna kanshi lokacin jikinshi yayi sanyi yake fadin Fatima sheri zaki min kuma yanzu akan mutuwar yar uwarki a baya ?
Cikin dakewa ina murmushin takaici nace yes haka din ne mana inba haka ba ya akayi daga mutuwanta ka auri Wasila ?
Wanan ne kawai hujjanki dama har kike kokarin bata min suna ?
Uhum lalai na yarda kun maida kowa baisam me yakeyi ba duk da nake yarinya na fahinci komai a yanzu cinkin kwantar da murya da nuna rashin fahintana yace me kika fahinta da hakan fatima don ni ban gane ba har yanzu.
Mayafin kaina na cire na mayar a saman kafadana shidai yana tsaye sororo yana kallona nace amma kasan zaman maman baby da anty ko ?
Nasani kawartane mana sosai nace hakane ka kuma san irin korafin da anty keyi na kishinta da take yawan yi a lokacin jikinshi naga ya kara sanyi lokaci guda yake kallona .
Ya dago ya kalli fuskana sosai fuskanshi dauke da alamomin tambayoyi a kaina bila,adadin haka zalika nima manyan idanuna na kura mashi wanda suke matukar firgita mutum idan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login