Showing 36001 words to 39000 words out of 347556 words

Chapter 13 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8799

alfarma a wurin ki.
Nan muke kasan layin nan bamu dade da dawo ba garin nan to akwai wani yaron mu dayake sayo muna wanan awaran shine muke so da yawa in ba damu muna da buki da zamuyi dashi.
Dan murmushi nayi har duple dina yana dan lutsawa nace zaikai na kwano nawa sai naga sun kalli junan su kamar ta ashirin haka ko fiye ko da sauri nace aikin ashema ba mai yawa bane sosai zamu iya in Allah ya yarda.
Kamar wani rana kuke sonshi ke nan tace zuwa ranan jumma,am nan mai zuwa insha Allah nace to sai ki ban lamban wayan dayanku don muyi communicate daku muji inda za,a kawo maku.
Baida matsala hakan karfe sha biyun rana zamu iya samu nace insha Allahu ok nawa zamu baki dan tunane nayi kafin na fada masu kudin sai naga sunyi dariya kawai abin ma ai ba tsada yadda muka zata.
Na dai raga makune don farkon haduwan mu ke nan daku sukace sun gode manyan yanka za ayi ko kanana mai yawan maganan a ciki tace min kingane zaki munashine irin dai yankan da zai karrama bako din nan don Allah yajin yayi dadi sosai nace baki da matsala suka ciro kudin suka ban mukayi sallama dasu.
Har sun juya dayan tace min son Allah ko kinsan wani gida da aka iya abincin buki mai kyau na gani na alfarma da zai fitar da mutum a kuya.
Nace kwarai kuwa wanan gidan ma sunayi sosai kuwa da cewa gidan mu nace ai sai kowa ya yaba insha Allah suna alala na gwagwani dana leda suna tuwo duk na,uin da kukeso sai fadi kalan miyan da kakeso ka kabar masu zabi suyi ma.
Wai masha Allah wallahi naji dadi har ina tunanen inda zamu je mu samu masu aikin nan nace Allah ya yanke maku wahala to kinga abinda zamuyi shi wanan tuwon na kwana shidane za a dinga muna saidai muzo mu dauka.
Kinga zai fara daga ranan wanan alhamis din ko jumma,a zuwa dai asabar har lahadi kilama amma zamu kawo maku shinkafa da abin miya kullun kuma zamu dinga waya dake sai a fada maki abinda akeso .
Don Allah amana yayi dadi sosai don bakin mu na kunya da zasuzo muna haba hajiya kada ki samu matsala insha Allahu komai zaiyi daidai.
Kudi ta ciro wrapper yan dubu dubu ta miko min tana fadin wanan zaku sai kayan miya abinda babu cikinsa wanan kuma dai sai abawa masu aiki su fara tabawa kafin mu hadu.
Suka tafi suna min godiya ina masu sai da suka bace min da gani na fada cikin gida ina kwalawa su mama kira da mama uwa ku fito yau ta samu fa.
Na dauko maku rigama da rana tsaka kowa ya fito na fara basu labari ina kyalkyatar dariya suma haka wai bintu wanan bakin wayau naki a ina kika gajeshine ?
Ai in batayi ba Allah zai tambayeta kun manta haka malam yake da wanan wayau neman kudin a baya muka juya da mamaki haka maryama take da neman kudi shima kuma malam kun gani abin yasata tsakiya ke nan ai.
Karo na farko da mama ta kira sunan mahaifiyata da sunan kwarai bata aibanta ta agabana ba jin hakan yasa nasan yan arzikin nata suna kusa lokacin.
Nace mama da wanan abin akaishi wani gida a gara a kawo nan ko dan dubu biyar biyar muka samu kan wanan harkan kinga ai mun karu ko gashi kuma ko banza zamuci mu koshi har yan kannena.
Ai kinyi dabara keda tuka tuwone aiki kome a garemu yanzu barin dawo a zauna ai kasafi muji yadda za a tsara abin but hassana ta fito daga dakinsu tace dani a ciki saiga hussai na fadin wa za a bari a baya har ni wallahi dani ciki.
Nace barin gama mu san ya za ayi idan nashigo na fice na barsu suna magana na koma wurin sana,ata mukaci gaba da aiki sai karfe takwas na kwashe kayan muka dawo gida.
Dukkansu suna zaune suna kallo a kofana alwala nayi nayi sallah isha,i kafin na fito da kudi wrapper guda nace yanzu mama yaya za ayi sai a fara lissafi ke Samira dauko littafi ki rubuta.
Nan suka fara lissafo abinda za a saya duk na dangin miya dana amfani zamu kashe wurin dubu sittin akalla don muna son ayisa yayi kyau don gobe.
Ku ban yin malmalan tuwo mukaji maman biyu ta fada a bayan mu nace mama da wahala fa zaki iya ke kadai kuwa tace ai dole wani ya kama min amma ku barni a duba yanzu dai mama kece zaki kula da komai keda mama uwa mu sai muyi aikim ku duba mana ko ?
Ina magana ina kirgan kudi na cire goma na fara bawa mama na kirgo wasu goman muka ba mama uwa hakama mama Lanto.
Su kuma yan matan na basu biyar biyar yara kuma na bisu da dubu dubu har kananan sai samarin danabawa dubu biyu biyu nan gida ya dauki murna sosai.
Washegari wanan aikin ya dauke muna hankali sai masu aikina suka tsaya sukai sana,a din ni saida yamma sosai muka dawo gida kamar jiran mu sukeyi su masu bukin sai gasu sun iso muna da kayan abincin irin shinkafa fara dana dahuwa da bag din semo masu yawa sai da aka gama shigowa da kayan matan suka shigo har cikin gida aka gaisa dasu mama suka kumayi masu alheri suka tafi na rakosu zuwa bakin motar su nidasu samira sukai ta zuba muna godiya zakice kyautane zamuyi masu aikin.
Babane ya fito yana fadin wai meke faruwa sai kowa yayi shiru maman biyuce take fadin mallam alherine fa yarka ta dauko muna muna zaune nan dai ta fada mai yadda na labarta masu komai.
Saida baba ya gama saurare yace to nidai gaskiya rikicine bani son amma ai wanan hanyar samune da kuma karuwa da hadin kai in za a tsaya ai masu shi babu hayaniya ko ha,inci walillahi hamdu.
Tsegumine banso ya biyo baya don Allah a kula ya juya ya shiga daki koda muka dawo mun samu har ya gama ya shiga dakin shi yasaya.
Komai mun shirya mun kuma tanadi abubuwan amfani har tukwane hassana taje da mota ta aro lokaci kawai muke jira Allah ya kaimu.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
[7/30, 2:36 PM] Maman Aslam: KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
1?? 1??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,

Abinci muka girka masu mai kyau ga dadi ga daukan ido abu daya na manta shine kulan da zamu saka a cikin idan mungama din don gaskiya ba wani riba da zance na sayi kuloli a wanan harkan.
Don haka na daga waya na kira matar wace nakecewa hjy tana ganin nombata ta dauki wayan tana fadin ya akayine sister yanzun nake zancen ki a raina nace ko kun dora don ga bakin mu sun fara isowa.
Nace hjy har angama komai yanzu ma na kirakine don inda za a zuba akawo abincin tace ikon Allah ashe har an kammala komai nace mata eh.
To yanzun yaya zamuyi don Allah ko zaki taimaka min sai kizo ki karbi kudi a sayo warmers shaf na manta da wanan gamu kuma jiya a kasuwa.
Baida matsala hjy bara muyi sauri muzo nan dai tayi min kwatancen gidan nasu samira da hussaina sai yar mayashinyan yarinyar mama uwa kuburah don mama uwa yaranta mazane ukku jere daga baya tayi mace bayan su macen ta farko bata tsaya ba ta rasu.
Ta kara yin namiji sai ita wanan din mai sunan wata gwaggon mu munace mata anty kuburah tace anty Bantu kije dani don Allah nace tazo mu tafi muka shirya gaba dayan mu zuwa gidan.
Munko ga gida gida na fada a ciki kaduna don filine babba aka diba aka gineshi a yadda hussaina ke fada muna suma sun taso sun samu ana aikin gidan nan anacewa ba,a san me itaba ashe masushi sun tare a cikinsa.
Tun daga haraban gidan muka fara cin karo da manyan motoci da kuma manyan yayan masu kudi duk sai muka dan shiga tsarguwa muna dan rabe rabe ta waya tayi muna kwatancen inda zamu ganta mukabi wanan kwatancen da tambaya a can sama muka sameta.
Da fara,anta take fadin ku shigo daga ciki su ukune a zaune a dakin daganinsu shawara sukeyi kan wani abu gaisuwa ta ban girma mukai mata ta fara magana tana fadin kinga sam na manta da zancen warmers din nan inba yanzu da kika kirani ba.
Ai dama wanan ce zasuyi maki abincin tace eh sune fa muka samu kai amma dai hjy kina da Abu wallahi ai da kin fada min sai in hadaki da wani gidan abinci sun iya aiki sosai wa yan nan ai irin na hausawan mu na gida zasuyi maki karshema kizo kizo kiji kunya.
Amma ai mama da gwaji akansan na kwarai ko ki bari a kawo abincin ki gani idan baiyi ba sai a karba a hannun mu na fada haba dai kawai abar zancem aibaka hanawa mutum abincinsa ba .
Zo mu shiga muyi magana ta mike nabi bayanta ashe bayan mun shiga matar nan ta fara aibanta aikin da zamuyi din tana faman cika baki gaskiya ita data sani wallahi da bata yarda an bamu aikin nan ba don ba zamu iya yinsa yadda akeso ba.
A dakin kuma ni kallon kaiyanci nakewa dakin naji hjy tace kinganmu ko na fada maki mu bakine wanan bukin ya kawomu shekarata goma sha tara rabona da Nigeria muna saudiya zaune a can muke tare da yaran mu.
Yar muce zatayi aure a nan shine muka dawo gida yanzu haka autana tana can ita tana da jerabawane bata samun zuwa yarona dake sayo muna wanan abin da kuke suya yaji muna maganan abinci yayi muna kwatancen wurinku.
Ta miko min kudi na sa hannu na karba tace kadafa zancen hjy ummah ya dameki su mutane haka suke wani lokaci sai hankuri nace babu komai hjy .
Allah yasa wurin zamantane yayiwa aure kuma albarka amin ke dai yar nan tashi kuje kada na tsayar dake waima meye sunan ki nace Bintu au sunan mahaifiyatace gareki ai muka fito zuwa wanan falon.
Har mun daga naji tace mamata dakata ga wanan katin don Allah kiyi min alfarma ki rabawa matan unguwan nan don Allah kada suji komai suzo muna maraba dasu.
Nasa hannu na karba masu yawa sosai mukayi masu sallama muka tafi muna fita hussaina tace masu kudi kan sunji dadin su wanan gidan kamar su sukai kansu.
Nan muka nufi kasuwa zancen su kawai mukeyi manyan kula hudu ko wani set haka muka hadosu muka kwaso zuwa gida .
Sun rigani shiga da kayan gida nice na shigo daga baya dauke dasu ludayan motsa miya miya manya dana tsaman abu gaba daya yan gidan suna waje suna faman aiki wijiga wijiga.
Hussai sai labari take bayarwa ita da samira mama Ladice a zaune mukai arba ta watso min mugun kallon nan nata da take minshi a kullun idan mun hadu.
Ban damu ba na gayar da ita na fara bayanin akan. kayan ga yadda za ayi dasu kallon mamaki kawai take min kafin tace na fada maku ai wanan yar taku Karan dafi ce Allah ya tsiro a gidan nan.
Yanzun banda sanabe da iyawa wanan yar ta iya dauko maku wanan babban aikin haka a duk fadin garin nan su hussai da basu gane me mama Ladi take nufi ba sai cewa sukayi.
Ai da kinga gida ne mama badon dalilin Bantu ba ko get din gidan wa zai barmu mu shiga kai yau kan munga inda arziki ke magana wai akwai kudi a duniya gaskiya.
Amma matar gidan in kinga yadda takeyi damu zakice mu din yan uwantane na jini don a take ta gwale matar data fara sukan mu wai aikin mu ba zaiyi kyau ba.
To ni dai zan tafi dama daga asibiti nake na biyo nan mama Ladi ta fada tana mikewa tou yaya zan leka idan na samu lokaci nima na gaidasu insha Allahu.
Da wanan aikin wahalan da kuka saka kankune har zaki samu zuwa asibitin dubiya aikun daure kanku da wanan wahalan wai aiki to banda abinki tallaka ina yaga hutu mama uwa ta fada
Mukan ai gaba ya kaimu don munsan abinda muka dafa inji mama Lanto dane sai a zuga ka kayarda ka hau ka zauna yanzu kan ina zan yarda da wanan nan ni ko gobe aka samu wani dani a cikinsa.
Wai mama an zubawa mama abincin kuwa na dago ina tambayan maman biyu tace ai yanzu ta shigo nace haba dai aiko yaro yazo a zuba mashi dauko leda kuburah ki debo nama a dakin mama ki hada mata da abinci.
Tsayawa tayi tana kallona kamar zatayi magana sai kuma tayi shiru niko muna can munata aikin abincin namu hankali kwance saidai a fakaice nake kallonta.
Bayan kubura ta hada mata abincin ta bata mama ta taka mata tace ke kinga yadda ya ta koma a cikin lokaci kadan ku kuna zaune aina fada maki yar nan bala,i ce gareku wata rana a gidan nan.
Nan dai muka shirya komai sai can mama ta dawo yanayinta ya canza a lokacin oho koda sunce ba zasuyi ba wanan bai dameni ba ni na fada a zuciyana.
Wanan karon banje kai abincin ba Samirace da hussaina da hassana suka tafi kaiwa a motan hilux da matar ta kawo sun dan jima basu dawo ba.
Ina mamaki a raina kome ya tsayar dasu haka sai gasu sun dawo da murna suna fadin kowa ya yaba da kyau abincin maza da mata saici suke suna karawa suna fadin yayi dadi sosai wallahi.
Haka muma munci munsha a cikin wanan aikin kuma mun samu karin daukaka sosai duk da gun wani kamar gazawane irin wanan neman kudin da mukeyi a yanzu ga kuma hadin kai da muka samu sosai don hakan ya jawo ko yaushe ka shigo a tare zaka ganmu kowa da aikin da yakeyi har yara a gidan.
Jumma,a za ai walima don haka ranan mutanen unguwan mu da aka gaiyata zasu sun kuma je sunga buki na alfarma na fada don har su mama dukansu sunje wurin waliman .
Munga manyan mata zakice bukin dangin mune akeyi saboda yadda mukai dumu dumu ana sha,ani damu a gidan duk wani abinda za a sayo a bukin mune ke zuwa idan canji ya rage mun bata tace kai haba dai haba rabonkine ki rike kawai.
Sai a lokacin muka dan san tarihin su wai ashe mutanen katsinane masu gidan amma zamansu a saudiya yake mijin daga zuwa ambasador a can ya zauna yana bussines dinsa.
Yanzu kuma suna shirin dawowa Nigeria da zama shine suka fara zuwa yin bukin yarsu datayi aure a yanzu din muke shan didiman mu ta arzikinsu gashi kullun aka kai abinci sai tace kunci kun ba makwabta kuma suci.
Akai buki aka kare kafiya labari kaf ya kewaye unguwa kowa da irin abinda yake fadi a kanmu idan mutum baisawa kansa girman kai ba sai ya samu ta inda bai zata ba.
Donko munji dadi sosai hakan kuma farawa da iyawan mu sunan mu ya daukaka ga alheri sosai da kowan mu ya samu a wanan harkan .
Mama ma dataso ta dauki hudubar yar uwanta Allah ya taimaka bata biba don yaranta da suka nuna su basu yarda da hakan idan batayi su zasuyine.
GIDAN YA MAHMOUD
Yansun zaman ya danyi dadi a tsakanin su tun lokacin daya nuna rashin yardanshi kan halaiyarta na banza maman biyu kuma tazo ta sameta.
Tayi mata tas tare da kara dorata a hanya tana fadin an fada maki samun wuri haukane ko anfada maki a hakan cikin garaje matan da suka rike sunan mata sukai labari ?
Ko wace mace da kike gani da rarafe ta fara a gidan mijinta ke wacece da zakizo daga zuwanki ki nuna masa ke yar gadarace dolle yanzu zaki mike kiyi kokarin kafa masa gwaunatinki a zuciyarshi ta yadda in bake ba bai ganin kowa a mace.
Amma kinzo da naki rawan kai ke a dole ga macen data samu wuri zaki nuna masa rashin tarbiyanki tun yanzu ko har kin manta ta yadda muka samo kansane ko kina son komawa rayuwan da Allah ya tsamoki a cikinsa ne ?
Ya zama dole ki kiyayye duk wani doka nasa a yanzu kiyi duk abinda akeso ke kuma a lokacin ne zakiji dadinshi sosai amma wanan halin da kikai saurin baiyana masa ai sunan ki sorry a wurin maza yanzun nan zaki zama expiera gareshi.
In bandama abinki keda akeson ki fara lalabashi a yanzu mu sanu ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login