Showing 318001 words to 321000 words out of 347556 words

Chapter 107 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8758

ya sake ya shafo kaina yana fadin .
Amma baki nuna min kina bukatan wayanki ba ai na dan dago ina nisawa nace don wanda ya ban waya ya karbi abinsa sai na tambaya don bandata ido kawai dai na dauka baka aon nayi amfani da wayane yanzu ina matsayin matar ka.
Uhumm yace amma tunda na baki wayan baki taba kirana dashi ba ai ya fada ya kara lumshe idonshi nima dan murmushin ciki nayi sai sautin dana sake kafin nace dashi ta ya zan kira mutumin da bai ma san da zamana ba ina dai kiran brother shida ya nuna min kulawa tun farko.
Kice nayi laifi dama brother sin naki kike so ashe hakan yasa na karasa dagawa daga jikinshi ina fadin wallahi sam bata jin sonshi a zuciyana ba illan na yan uwan taka da irin kulawan dashi ma yake nuna min.
A rayuwana nakan nuna damuwa akan duk wanda ya nuna kauna a gareni amma bawai irin yadda kake zato yanzu ba har lokacin idonsa na rufe yake fadin ni a wani matsayi aka daukeni lokacin ke nan ?
Boss din inda aka labani har karatuna ya kammala abokin ogana mai girman kai da tsanan mutane har banson mu hadu dakai don irin kallon da nakan tsinkayo na kiyayyana a kwayan idanun ka.
Murmushi yayi ya dago yana fadin kin min sheri a nan sai kin roki gafarana don duk wani abinda Abbas ke maki da saninane ko waya zai kira ina wajen a tare dashi shi a zatonsa yana kokarinsa yaga ya cusa minke a zuciyana .
Wani kallo nayi masa yace kwarai shi a nasa zaton ke nan ai abinda bai sani ba shine tun ganin farko da nayi maki zuciyana ta kamu da kaunar ki saidai lokacin gaskiya bawai kaunar so bace a,a kaunace ta halin tarbiya da natsuwa dana hango a gareki.
Badon komai ba sai don kalman da kika furta min nine na fito ban kula ba na kabe maki waya har ya fadi ya fashe amma kuma kece mai ban hakkuri a lokacin.
Wanan abinda kikai min yasa zuciyana ta yaba da hankalinki koda muka dawo office nina turasu suje su nemoki su baki hakkuri su kuma kai maki waya har da Laptop a cikin bonus din da mukan bayar a shekara.
Dama kai ka turosu lokacin yace su sun isa su taba kayan company haka idan ba saya maki zasuyi ba su aje kudi ido na lumshe na shiga tunane lokaci guda abinda ya faru lokacin ne yake dawo min a rai.
Kallo daya idan mutum yai min zau daukeni a matsayin miskili amma sam ni ba haka nake ba matsala ta daya dai bani da saurin sakin jiki da mutane sai nayi nazarinka na dan lokaci mai tsawo.
Kada kiga nayi saurin sake maki haka lokaci guda nagama nazarinki ne tun kan auren mu nasan yana da wuya kiyi wani abinda ba daidai na asha a rayuwan ki don hakane nake son ki saki jiki ki daukeni mijinki abokin hurdanki da shawaranki a kaina.
Ni marayane da ban da wa ko ya ko kani ko kanwa hakan yan uwan uba da nake dasu iyayyensu a lokacin sun rabani dasu sun hana yayansu hurdan arziki dani wanda a karshe hakan yabi min jiki ba ruwana da kowan su a rayuwana.
Sai gashi a yanzu kuma su yayan nasu suna aon hurdani ni kuma a yanzu bana iya sakasu jikina ko kadan don na saba rayuwa a ni kadai a baya sai ko su Abbas da suka nuna min kauna basu kyamaceni ba sai ma ince a dalilin Abbas da iyayyensa bakai wanan matsayin a yau.
Wasu hawaye naji suna zubo min a lokaci guda wanda bansan ko hawayen meye yazo min a lokacin ba na dai ajecewa na tausayin kalaminsa na karshe ne game da rayuwanshi.
Muna shiga daki wayan nawa ya ban da hannunsa ba tare dayayi min maganan komai ba na karba a sanyayye na aje gefe saida da karfe shidda suka fita shida Abbas lokacin na dauko wayan ina dubawa.
Sakkoninne barkatai suke shigo min ta ko ina ga miscalled nan ba adadi daga mutane daban daban nasan yakan dan kunna wayan ashe lokaci lokaci.
Kwanan mu tara a Abuja muka daga zuwa Chaina wanda harkan business dinsa ya kaimu can din don baida lokaci sai dare sosai yake dawowa masaukin mu.
Taimakona daya shine yanzu da waya da Laptop a hannuna shike debe min kewa idan zaman kadaici ya dameni zan shiga online nayi charting da abokan arzikina muyi hira.
Na kanga Samira wani lokaci a online amma bata taba yi min magana ba ko mu gaisa nima na shareta ko diban status din ta banayi koda hassana tayi gulma in duba abinda Samira ta rubuta kan waya.
Nakan ce banda lokacinta keda kika gani meya karaki dashi don Allah fita zancenta ki bar kula haukan ta bata dai da wanda ya fimu muma kuma haka bamu da yar uwan data wuceta don a wuri daya muka fito dai.
Ni kaina nasan nayi kyau na kara wani fresh dani to ba aiki fara ba shiga rana tun ina gudun sanyin AC da farko har yanzu dole na saba dashi don shi bai iya zama bai kunna AC ba a waje.
Daga Chaina muka nufi US satin mu ukku a can ya kaini yawon shakatawa naga wajajen al,ajabi da dama don gaskiya country din suma suna da abubuwn abin al,ajabi na tarihi masu yawa suma.
Sai lokacin nasan kanin babanshi da iyalinsa suna can don ya kaini gidan na kwana uku a wajensu gaskiya sun min taron arziki don shi yayi tafiya zuwa wani jaha na kasan yasa ya kaini wajensu na zauna dasu.
Matar bata nuna min komai ba tana kokarin kawo sabo a tsakanin mu ta hanyar jana da hira ko wani lokaci saidai ban yarda na sake jikina ba yadda take so saboda bugu daya nayiwa kowa nasa a yadda yake fada min ko wani lokaci.
A wajentama nake ji ashe itace tayi sayayyan lefen aurena har take fada min kan hada lefen nan tasha zagi a wajen yan uwa suna kiranta munafuka.
Ta dan taba min hiran su hjy maryam da hjy Laila sama sama take fadin gara maryam din amma laila ai zaki ganta don yanzu ba zaki shedata ba lokacin buki anyi yawa kuma ke bakuwace a cikin mu a lokacin.
Kila ko je England daga nan son su a can suke zaune amma ai duk mun kusa dawowa gida a taru kamar da can baya lokacin wani sabon zama zai fara a tsakansu ta fada.
Sai naji na kara tsanar wanan matar hjy laila din da kowa bai fadin alherinta sai sheri naji bani kaunar ma haduwa da ita ko kadan don bata da record din kwarai mace kamar iblis ko bai fadin alherinta a bakinsa kowa nada tabonta a zuciyarshi.
Ya dawo sunso mu kara dan kwana biyu a wajensu ya nuna ba haka ba amma abinda na kula iyayyen nasa maza suna nuna masa kauna sosai a fili gaskiya.
Daga can muka nufo landin larabawa inda a nan ma muka fara yada zango a kasar Egypt na dan kwanaki don abinda zaiyi a nan din baida yawa kafin muka nufi kasan Dubai.
A nan kan na sheda waye bashir nagama fahintar rayuwan shi a yanzu don zakice a lokacin aka kawoni gidansa don yadda yake manne dani yana morewa har abin ya fara ban tsoro.
Amma ba yadda na iya hakan na cikin huduban iyayye da kawaye cewa ki zamo mai dauriya ga halaiyan mijinki duk yadda ya kasance dake.
Don hakane nake daurewa ko ban so sai in biye mashi mu shagala sai ya gamsu ya barni don kansa zai dan fita bai hana kuma in ya dawo din yana mane dani a jikinsa dole doliya kuma in biye masa ayi sha,ani hakana ko banso.
Duk da na nuna mashi kayan lefena ban ko taba ko kwata ba amma haka ya jibgo min dogayen riguna kayan shan iska a warwaro su jakka da takalma daya gani ya bashi sha,awa zaice a saka a leda haka ya hada min kayana makuddan kudi duk a matsayin nawa ni kadai.
Nan ya saya min mota da sunana nikan ma gani nayi kamar yayi haukane ko kuma baisan zafin kudi ba nida ban ma da kawayen kirki ko a kaduna ina zanga kawaye a Abuja balle in fita.
Nasan yanayina ya canza amma ban dauki hakan komai a zuciyana watan mu daya a Dubai a ca muka fara azumi wata na rabawa tsakiya muka nufo kasan saudiya.
Nan kan na samu sarari don ko yaushe yana bakin ibada don sosai ya mayar da hankalinsa kan ibada sai can ba a rasa bama zai nemeni.
Anyi sallah lafiya muka fara haraman dawowa gida don abubuwan da suka taso daga wajen aikinsu na gaga na zata zamu wajensu Abbu amma sai naga sabanin hakan don direct jidda muka nufo sai Nageria sallah da kwana uku muka dira Nageria Abuja garin Naira da yan boko duk wani dan fashin boko yana Abuja zaune su akewa lakani da Abuja's


ZAINAB IDRIS MAKAWA

@KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI
ZAINAB IDRIS MAKAWA ?
????????
1?? 0?? 0??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

Surutun mutane a kaina shiya fara sani tunane don tun a airport brother ya kasa danne zuciyarshi saida ya furta wai mutumina inji kasa min kanwata ko kuma wanka aikai mata na ruwan gishiri.
Kasan fa ruwan gishiri shiyayi muna maganin Ibola ya tsaya dakatar Nageria bai karasa shigowa kasan ba a lokacin don karfin gishirin da muka dirkawa cikinmu muka kuma goga ruwansa a kawunan mu.
Shiru yayi bai bashi amsa ba saima kamo hannuna dayayi ya rike a cikin nasa ke hafsat bakiga wani sauyi a wajen kanwar nan tawa ba son Allah ni dai nasan da walaki goro cikin miya.
Don Allah fada muna ko zankai hafsatuna nima ya fada cikin zolaya dan gyara zama yayi daga bayan mota yana fadin ai gaka gata ka tambayeta abinda nakaita akai mata ta koma hakan ta barni da dan karamin kai ni .
Dariya sosai suka kwashe dashi lokaci guda yace don ma baka ganta bane lokacin da muka baro Dubai yanzu ai ta dan fada ta dushe kadan nima kaina a lokacin inna kalleta sai naga ta koma min matan larabawa sak wallahi bata da bambanci dasu tako ina.
Hafsat din tace aiko yanzu bata wani dushe ba gaskiya tubarkallah masha Allah wata kila dai alherine ya samu ta koma hakan tunda tana cikin galihunta.
Hannunshi naji saman cikina yana dan shafa kafin yace in hakan ya tabbata Hafsat nayi maki alkawarin goron wanan albishir din insha Allahu.
Kala ban furta ba saboda wani yanayin da nake ji a yanzu kwana biyun nan bana son kamshin abubuwa da dama take nake jin zuciyana yana tashi ko yanzu ma din kamshin turaren dollop da Abbas din ya shafa shine ya ishi hancina nake jin wuri yana juya min sukaci gaba da hiransu cikin shakiyanci ina gum na kasa magana.
Daidai zamu shiga get Abbas din ke fadin wanan matar da Mami ta turo na kawota tun jiya tana cikin gidan nan fa shi kuma Samuel din mun mai dashi office yanzu kamar yadda kace.
Mami na ke nan ashe zancen yana ranta motan ya tsaya kafin Abbas yace nina isa tunda nasha worning kan da zaran naji kun saka rana in fada a kawo maku mai aiki kasan Mami da kai sai Allah su biyu aka turo maku da yar yarinya karama wai mai goge goge da yan aiyuka ta hado maku.
Hannuna na fisge a cikin nasa na bude motan da sauri na fita da dan gudu na nufi dan wani waje na duka sai amai dama ba komai a cikina sai dan ruwan zafin dana sha a cikin jirgi shine kawai a cikina lokacin.
Fitowa yayi ya kura min ido gaba dayansu ni suke kallo a cikin mamaki sai hafsat data mikawa Abbas din yarta ta karaso inda nake tana min sannu kafin ta juya tana tambayan mijinta akwai ruwa a cikin motan nan kuwa ?
Ya dauko goran ruwa ya miko mata zuwa lokacin shima ya tako zuwa inda nake hafsat din itace ta zuba min ruwa na kurkure baki na wanko fuskana kamar yadda tace dani inyi din.
Riko hannuna naji anyi yasa na dan juyo shine a tsaye a bayana a gaban kowa ga yan aikin gidan dake murnan mun dawo sun firfito don taron mu gasu Abbas da matarshi tsaye.
Amma haka bawan Allah nan ya rugumoni yana kokarin yi min kiss na noke saman kirjinshi yakaiwa kaina sakon abinda yai niyar yi a bakina gaban mutane.
Abbas ne ya taba hanayesa yana fadin dakya sharpshooter mutumina shine kabarni ina zuba haka watau ita hafsat da yake yar garice tayi saurin harbo jirgin don gashi ta samu goron albishir a sauwake.
Lokacin na dan dago daga kirjinshi ina fadin kai yayana ba hakana bane itama bata canka daidai ba gajitace kawai da tarin wahala dana debo yake damuna naji yace Allah ko na gyada mai kai ina murmushi na fada kafadan mijina.
Muryan boyar Allah nan da Mami ta turo ya katsesu tana fadin masha Allah sannuku da zuwa sannuku da hanya lale marhabin.
Iya sannu da gida naji hafsat ta fada taci gaba da fadin ya bakunta da sabon waje tace Alhamdullahi yayan nawane nan ashe tafiyan safe zasuyo haka sai gata kasa ta zube wai tana muna sannu da zuwa.
Haba iya ki tashi a shekarun mu mu yakamata mu tsuguna ai mu gaisheki ya fada ta mike tana fadin masha Allah aiko nagode tun yanzu duk ta rude ta juya sai kuma ta sake juyowa tana fadin ku shaga ciki mana kun tsaya a waje kuma.
Jeki iya zamu shigo ai yanzun nan muna tare da dan farin cikine anan kan mu shigo ciki ta juya tana fadin masha Allah ta shiga ciki lokacin sauran yan aikin maza suke mika muna gaisuwan sannu da zuwa kafin muka dun,guma zuwa ciki muma kai tsaye.
Kayan da muka dan riko aka fara shigo muna dashi ciki a falo muka zube su kuma suna waje ya tsaya da Abbas ana sauke muna kaya take fadin da alama matan nan nada mutunci kiyi hakkuri dasu don Allah kinji Fatima.
A yadda ta fada min ita din yar uwar mamice daga kauye mijinta ya kare sai wanan yar jikan nata da yarta ta haifa ta rasu ta reneta suke rayuwansu a cikin tsanani saiga Mami ta aika mata da tayin aikatau bata tsaya ba ta karba sukazo.
Zama da mitum tundai bagidaje sai kayi hakkuri sosai kakai zuciyar ka nisa sanan zaku fahinci juna a dan zamanta kwana biyu dani na fahinci matar nada tsabta da kula yadda kika ganta din nan haka take da ban girma.
Nasan zakuji dadin juna da ita sosai nan gaba don kina da hakkuri da sanin yakamata yadda na nazarce ki nima sannu a hankali ki koyar dasu komai don Allah banda haufi akanki dadai haliman yusufce gaskiya nasan nan za a samu matsala amma ke kan ko Abbas ya fadi baki da matsala gaskiya.
Karki damu anty hafsat nima don jin yar uwar mamice wallahi matar ta kwanta min arai ni wacece da zan kyamaci tallaka dan uwana da zama lafiya lau zamu zauna insha Allahu.
Sai ga iya din da ruwa ta hado da kofuna ta kawo ta aje muna tana yarinyar kuma ta dan gurfana tana gaidamu itama iyan ta zube kasa tana fadin hjy nace me zamu dafa maku kuci nasan baku karya ba ko ?
Dan ruwan zafima ya isa tunda suna da gajiya yanzu ba wani abincin kirki zasuci ba saidai zuwa anjima a girka abincin don rana hafsat ta fada.
Shigowansu yasa muka mayar da hankalin mu a kansu zama sukayi suna cigaba da hira iya din tazo tana fadin hjy ina za,a kai kayan nan nace bari na taso na bude kofan ashiga dasu.
No ta bari kawai ya fada ta juya ta dan kalleshi sai kuma batai magana ba ta shige Abbas ya mike yana fadin zamu tafi munbar little sister a gida cewa yar shi ta farko dataci sunan Anty larai Asmau.
Bayan tafiyansune na samu na mike zuwa sama dama karfin hali nakeyi da suke nan amai na shega sosai lokacin bayan na gama na watsawa jikina ruwan na canza kaya na kwanta sai barci ban kara sanin inda nake ba kuma.
Na galabaita ranan sosai wasa wasa har ruwa aka daura min washegari sanan na samu dan karfin dana sauko kasa zuwa yamma don nagji da kwanciya a lokacin .
Iya tazo muna gaisawa nan nake tambayanta wani daki suke zaune take fadin a kitchen suke kwana tukun don ance sai mun dawo mu basu waje salati na saka nace kitchen kuma iya ga dakuna a gida.
To


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login