Showing 192001 words to 195000 words out of 347556 words

Chapter 65 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8784

nuna hakan a gareni haka na nufin akwai matsala ke nan a zamana dakai.
Look Fatima ya kirani dashi kai tsaye yace ki bari zan shigo in duba baba zamuyi maganan idan nashigo yanzu ki huta don naga kamar barci kikeyi a yanzu na tayar dake.
Ban kara magana ba na kashe wayan ina jan tsuki na aje wayan na koma na kwanta a rigigine ina kallon tsohon silin din dakin nawa da har ya fara dan canzalaini saboda tsufa.
Na sauke ajiyan zuciya ina kallon kofin da mama din ta shigo min dashi na dan mike zaune na sauko bakin gadon ina daukan kofin na bude na kai a bakina nadan kurma naji dadin kokon don baida yami a baki don haka nasha kusan rabin kofin ina tunane a kasan raina.
Idona na mayar na Lumshe lokaci guda ina mikewa don in nabi ta tunane a yanzu bacin ran zuciyana a lokacin zai dada karuwa min ne a raina.
Don haka na fito zuwa wurin baba na samu har lokacin bai fito daga daki ba ashe nayi mamakin hakan dakin na nufa nan nasamu Nura dashi da dan wurin mama na miji da yazo daga inda yake sana,anshi.
Shiga nayi dakin da sallama ina gaida su kafin nakai kasa na zauna gab da inda baba yake zaune saman katifa a kasa Nurane yake fadin to baba gata nan ma tazo ai kallon baba din nayi nace.
Dama yana nemanane ?
Eh to yace sai a sawo mashi irin abinda kike sayo mashi din nan meke nan nura na tambaya ina kallon nura din nakuma juyo na kalli baba ina tambayan shi ?
Baba mekake sone yace min abu mai sanyi din nan fadimatu cikin kwatace dan wani iri naji ina sakin dan murmushin yake lokaci guda nace barin fita yanzu mu sayoma abin sanyi.
Au dama wai abin sanyi yake so ya kasa fadin hakan tun dazu ya gyada masu kai kawai alaman ehh .
Kinsan fa asibiti soja yana sayo mashi su idan zaizo yanzu ko an kwana biyu bai zoba bai kawo ba ashe yana son abin a ransa kai baba ai wanan mai tsadane sosai.
Nura kaje supermarket din nan na unguwar round about zaka sameshi wurin kasayo mai na mike naje dakina na dauko kudi dubu biyar ya rage min cash a gida ranan na dauko four thousands na kawo mai ya mike ya fita.
Nan na zauna da ya Ahmed muna hira yana bamu hiran Lagos yadda suke sana,ansu a can din muna mamaki a nan hassana ta sameni muka zauna sai kuma ga Usaina.
Saida akai kiran sallah azahar muka gyara baba don yayi sallah har dakin muka fito saboda ranan yace baya fitowa waje babu zafi a dakin.
Nura kuma ya kawo mashi Yought din kuma yasha sosai a cikinsa har yana fadin ba zaici abinci ba a lokacin sallama akayi ana fadin wasu zasu shigo duba baba ya Ahmed ya shigo yana fadi.
A raina nace munyi sa,a mun gyarawa baba dakin kafin mu fito da yanzun haka ko suwaye zasu shigo su samu dakin a bace su raina muna shiyasa gyara muhali ko yaushe yake da dadi gudun ai maka girshi haka.
Lokaci daya gidan ya dauki kamshin turaren maza mai taken one millions years DC wanda company turareb nan na Us suke hadawa mai tsada don ko kwalbanshi abin kallone kasan an kashe kudi ga sayansa.
Har dakina wanan kamshin mai sanyi da ratsa zuciya ya biyo hancina zubur na dago sai gashi na samu kaina da leke ta kafan labule don in tabbatar da zargina a kai ko gaskiyace abinda zuciyana ya fada su Oga Abbas a gidan mu.
Su din ne dai kamshin turaren Oga Bashir yakai har dakina oga Yusuf ne a baya sun cire takalman su a kofan dakin na baba duk da babu ko Capet din leda a dakin balle ties ko carpet na ainihi.
Haka baba ke rayuwan shi a dakin daga shi sai simintin dakin da yai sumul sumul dashi don shafin dana a ciki ba kissa ga masu aikin a lokacin.
Nan dai suka shiga suna gaida baba din da yake zaune ya dan kishingida jikinshi babu riga yana shan iska sai dai magana ma da kyat yakeyinsa a lokacin dasu suna gaisawa dashi.
Mamace ta shigo dakin ta samesu suka gaisa har su mama da kowa ana zuwa gaidasu da shigowa saidai har lokacin babu wanda ya iya shedasu ko suwaye su din ?
Ko Fatima tana nan Oga Abbas ya fada yana kallon ya Ahmed din cikin tambaya fatima don ya manta da hakan sunana yake saboda Bantu din ya amshe min sunana nakwarai a yanzu.
Fatima wace Fatima ke nan daga kofa mama uwa ta amsa da Bantu yake tambaya Allah sarki kune na ranan a asibiti ko da kukazo nan aka fara mamare a kai suna tunosu daga nan ta saka min kira na amsa ina fitowa daga dakin.
Wani dogon rigar silkne a jikina rigar yar dubaice haka mai sauki dinkin dogon hannu sai daga kasa yana da adon baki haka zuwa cinya saman kuma duk jace har hannuwanshi sai bakar hula dana dora a kaina da ya dan fitar min da somana dana daure a waje ana iya hango ribon dina.
Ke Bantu zoga sauranyin ki yazo na ranan nan Usaina ta fadi hakan da karfi duk wanda ke cikin dan gidan namu zai iya jin mu a lokacin abinda take fada min .
Haka yasa cikin dakin baba kuma oga Abbas da yusuf suka kalli juna suna noke kai cikin dariyan jin abinda aka fada din game dasu.
Haba dai Ogganninane fa na wirin aiki na fada ina fitowa daga dakina lokacin cikin daure fuska da jin abinda ta fada wanda yai bala,in bata min raina a lokacin.
Haba dai fadi gaskiya madam mun gane wanan ai tana wucewa nima na kasa yi mata magana son takaici dakin na nufa ina dumfara muna hada ido da oga Abbas dake facing din kofan daga inda yake zaune.
Lokaci guda ya sake min murmushi wanda yasa nima na dan sake ina dafa kofan shiga dakin baba din nace sannun ku da zuwa ya hanya.
A cikin muryana da suka hade da yanayin maganana dake bada ma,ana da zaton sallone ko yaukine irin na mata nakeyi wanda halittabane kawai hakan ga wanda ya sanni yasan yanayina.
Fatima ashe kina nan Oga Abbas wanda ke kirana da kanwarshi ya fada yana dan kallona nima kallonsa nakeyi a cikin girmamawa nace ina nan tunda muka samu hutu .
Magana Boss din mu yayi daga ciki wanda ya dauke mashi hankali ya tsaya sauraren shi a lokacin kafin ya juyo ya juya harshe cikin turanci yana tambayana wani cigaba aka samu a jikin baba din yanzu ?
Jin hakan yasa na dan karasa shiga dakin ina jingina jikina da kujeran dake kofa wanda oga Yusuf ya zauna nace akwai cigaba sosai a yanzu don yana dan wasu abubuwa dake motsa jikin nasa ba kamar lokacin da muke asibitin ba dashi.
Idan ba damuwa zamu so zuwa jibi Allah yakaimu za,aje Abuja dashi a dubashi a can ko akwai wani abinda zasu gano game dashi dukar da kai nayi kasa da murya ina fadi a cikin hausa.
Baba kaji abinda sukace wai zasu kaika asibiti Abuja a kara duba lafiyanka zuwa jibi in Allah ya kaimu zaka tafi ko na tambayeshi cikin tausasawa.
Ya dago yana dan alama da kai alaman zai tafi din insha Allahu yana kuma hada hannayenshi wuri daya alaman godiya a garesu No haba baba ka huta ba komai Abbas ya fada.
Turancin ya karawa Abbas din kafin suka mike tsaye lokaci guda suna dan magana ganin hakan yasa na fara fita kafin su ashe sun ajewa baba din kudi bayan fitowana.
Har kofan gida na rakasu a lokacin suna batun shiga motocin su ganina a bayan su yasa oga Abbas dan dakatawa yana fadin zamuyi waya aiki mukazo yi nan garin muka zo duba lafiyan baba tunda mun shigo.
Nagode na fada tare da dan dukar da kaina yake fadin i will call you letter Allah ya bashi lafiya suka tafi nayi mamaki da farko yadda akayi suka gane gidan mu amma.
Saidai da muka fitone dasu din naga wanan driver da yake kawoni gida sai mamakina ya tsaya a kansa nasan shine wanda ya kawosu gidan namu ke nan a lokacin.
A cikin gidama dana koma bayan wucewansu zance cikin gidan mu gudane shine kan ina kuma na samesu su kuma suke tambaya daga cikin dakin da mama take tsaye take tambaya.
Mama uwa ke bata amsa da fadin budurwa mai farin jini a gari ai ba bace take ba a cikin gari don alaman hakan ke nuna farin jini ga ya mace ai a biyota har gida ba tabi ba .
Yan uwa su sheda su gani shine farin jini don ko mun sheda mu ba fadi a baki ba kawai Usainace ta iya bata amsa a lokacin da fadin mun sheda hakan masu kudi na inda suke .
Don ga sheda mungani a hannun mu dumus mun wataya mun walwala muji dumus ba fade ba mama Lanto dake gefe tace kowa ai rabonsa yakeci.
Ban tsaya ta kansu ba na shige wurin baba na samu mama na kidaya kudin a hannunta Bantu ga kudin da suka bada dari biyune cur ta fada tanagowa daka kidaya kudin tana kalona.
Mama asai abinci a kara zaifi don naga abincin ya kusa karewa dama Allah ya rufa muna wanan asirin saura kuyi cafene ku dan cire na sabulu kuma ga ya Ahmed nan ku bashi ya sayo maku komai zaifi.

Kunyi hakkuri don Allah an min rasuwane kukajini shiru kwana biyun nan


ZAINAB IDRIS MAKAWA


KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
6?? 0??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Zancen duniya baya boyuwa saidai ba,ayishi ba akace ba,ayibama ance anyi balle anyi din don ko a gidan mu muna ganin an rufe zancen ashe bamu sani ba zance yabi unguwa ko.
Don kuwa inda muka san wanan zancen ya faru shine a ranan mama Lanto da yarta sun wuni a dakine saidai muga fitan samira din da waya a hannu ko kuma aji tana waya kus kus kus.
Sai darene mama Uwa ta shigo tana fadin ance in zaka gina ramin mungunta ka ginashi ya zam gajere don bakasani ko kai kafada.
Na gidan mu kan sun gina da zurfi sun fada a cikinsa ko don yau uwa da yarta suna cikin tashin hankali sosai dazun Amira ta shigo tana fada min taga Samira a kofan gida tana waya tana kuka.
Sai yanzu nake ji ashe Mahmuda yazone yaji abinda ya faru tun jiya yana garin yaki daukan wayanta kuma shine ta nemi ibrahim take magana dashi lokacin kuma Nura na kusa wai wallahi kazafi akai mata ba ita ta aikata hakan ba.
Shi kuma yace anface takai dare hannun yan sanda a ranan don haka shikan ya fasa kinji halinda ake ciki in tace ta iya sherine ai yanzu ya cita kuma.
Amma kar yayi muna hakamana don wallahi mama mafi son ma tayi auren ko a huta da wanan fitinan haka nikan idan zan ganshi zan fada mai cewa kazafin akai mata wallahi.
Amma ke kan Bintu zuciyar ki na daban ne nace ba haka bane mama ba zaki gane me nake nufi ba sai idan ta bar gidan nan zaki fahinci maganata a sannu.
Matsala dai yanzu don kawai basa son asan da zancen sai idan ta baci amma kuma waya fitar da wanan zancen har akaji don dai nasan isah mai shago ba zai fadawa kowa ba yadda na rokeshi.
Ke kina ganin yaya zata bar zancen nan a cikine bata fitar dashi ba ko su hassana ai zasu iya fadi a inda zasuji don a yanzu sunfi tsanarsu dake a gidan nan.
Don yanzu ai ke sun sakar maki mara tukunna don ba bari zasuyi ba nasani lafewane kawai irin na dariyan hakori da jini duk dasu yaran da sauki lamarin su gaskiya ba kamar uwar ba dai, da har yanzu nasan na ciki na ciki a kanki gaskiya.
Nasani amma dai wanan matsalan har in su suka fitar basu kyautawa baba ba don hakan zai iya kara jefashi cikin wani hali abinda nakewa gudu ke nan gaskiya.
Na fahince ki yanzu da aina dauka ko tausayinsu kike ji hakane amma yanzu kan na gamsu da zancen ki saidai gaskiya yana da wuya a yanzu kan bai jaye zancen auren nan ba gako lokaci yana kara karasowa kusa.
Don sukan gaskiya ranan da akasa bukin yana nan a wajen su don naga sai shirinsu sukeyi nace dama ai yana nan mama yaro ne ya shigo muryan shi tata yana fadin wai anawa Fatima sallama inji soja.
Shiru mukayi a dakin muna saurarensa ya sake fadin wai ance anawa Fatima sallama a waje inji soja naji mama Lanto tace kaje dakin can ka fada a kofa.
Mama uwa ta fito tace kaje kace tana zuwa yanzu daga nan bata kara shigowa ba ta fita saidana shirya na sameshi zaune a motanshi ya kafawa kofan gidan mu ido daga can nisa kadan da gidan namu .
Na karasa na sameshi ya bude kofan motan ya fito muka gaisa kamar yadda babu walwala a fuskana haka shima fuskan nasa a ranan ba walwala a cikinsa.
Fatima bansan laifin da nayi maki ba da baki son daga wayana na dago kai na dan kalleshi kafin na mayar da niyar bashi amsa a daidai lokacin motan take gangarowa a hankali zata nufi cikin unguwa yayin da wanda suke ciki suka kuro muna ido.
Karaf idon mu ya hadu da nasa ya habibine gefe ya Ibrahim yana jansa idonsa na a kanmu da soja gashi muna tsayene gaf da junanmu dashi .
Dan murmushi na sake a fuskana zaka dauka wani hiran jin dadi mukeyi dashi lokacin gashi nayi kyau a lokacin waye da jan aji yazo min na zama yan matan kaduna da kyau ba inda zaka kalla a jikina kiga kasawana tako ina abin burgewane ga mutum .
Don na koma kamar wata half Cass dani kallo daya zakai min ki gano ni din ruwa biyuce a idonki yanzu gashi yawan rashinnson maganana a yanzu ya karu min sosai don damuwan da nake ciki kan ciwon baba a yanzu din.
Horn ya Ibrahim ya danyi muna nayi kamar banji shi ba lokacin nace amma dai kamar ka zargi kankane ko don nidai nasan bakai min laifi ba tunda bakai ka turo matarka taci muna mutunci ba ai.
Ke nan don ki wahal da zuciyana kikaki daukan wayata ko nace kasan abinda ya zaunar dani a garin nan kan mahaifina ko yauahe ina kusa dashi don yana bukatan a mutum a tare dashi ko yaushe yanzu.
Gaskiyane nayi maki uzurin wanan to ya jikin baba din nace da sauki jibi insha Allahu zamu kaishi Abuja a kara dubashi a can .
Take naga ya kalleni ya dan canza yanayin fuskanshi lokaci guda yace nan din kuna ganin ba improment ne ko me nace Boss din mu na Digital ya dauki nauyi hakan gareshi.
Kai ya girgiza cikin gamsuwa kafin yace anywhere dama nazo inji ya jikin baba din ya kasance sai kuma zancen kudin nan da zamu bayar don nasan in ankai wa hukuma rabi kawai zaku samu don haka naje na janye case din a kotu.
Nazo naji gyaran zan saka ayi ko kuma mune zamu gyara maku komai da kan mu ya dago yana kallona idona na lumshe lokaci guda ina sauke ajitan zuciya tare da fadin .
Azatona zaka sulhunta ba sai haka ya faru ba sai a dauki abin a matsayin kaddara a garemu irin dawainiyar da kayi da mahaifina koshi ya isa ladan hakan ai a garemu basai ankai ga biyan wani kudin ba can.
Kafi karafin wanan garemu koda kuwa baka aureni ba ni kayi min komai ga hakan don mutunci madarane shima ido naga ya lumshe lokacin dana fadi hakan ya kurawa kasa ido yayi shiru na dan lokaci .
Kafin ya dago kai yace dani nagode da wanan tunanen naki fatima amma kuma hakkin kune wanan zan baku don wanda akaiwa barna idan basu yafe ba fa ya za ayi da alhakin su kuma ?
Shiru nayi don nasan gaskiya ya fada duk da dai robobin sharunne na ruwa da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login