Showing 333001 words to 336000 words out of 347556 words

Chapter 112 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8762

watsake a kaina kamar wanda yayi wani dadewa bamu tare ya fara fita office lokacin na samu kaina har na tuna da wayata nasa sadiya ta kwaso min, a dakina nakasa don duk yadda muke dasu ban basu idon hawa sama dakin boss ba inda muke zama.
Na bude wayoyin baifi minti biyar ba saiga kiran hassana ya shigo min na dauka ta fara fada dani kunbi wayoyinkun kashe hankalin mutane ya daga haka.
Baba yana ta son magana dake bai sameki ba hakama layin mijinki bai shiga duk ya daga muna hankali nace don Allah kashe barin kira baba din tace ai gani waje tare dashi nace bari na kira kada mu cinye maki kudi na kashe kan tayi wani magana.
Don nasan abinda baba ke nemana dashi banson kuma ta tsaya taji don yadda za adauki maganan nasan sherin samira zata iya zarga min wani zance na daban kuma akan hakan.
Saida nabada yan mintuna na kira baba ina bashi hakkuri kan hakan kafin nace mashi nadan kashe wayan ne ina son hutu na kwana biyu saboda jikina.
Yace duk na damu fadimatu kinsan jiki da jini yi hakkuri baba na sake fada yace mai mota yazo ya sameni da wani zance dama nake son muyi dake.
Eh baba kai kadaine a wajen na tambaya yace ehh fadimatu ina waje zaune ni kadai nan na kora mai dalilina ya dinga sa min albarka tare da fadin shi Mahmud din yayi gaskiya.
Dayake shi namijine ai kinga yasan abinda ya dace ayi sha,anin kudine ba maganan wasa bane wanan dole ayishi da shedu kuma yadda yayi din yai min dadi sosai da alaman gaskiya a tare da yaron har yanzu.
Ki sanarwa mijinki muji duk abinda ya fada hakan za ayi don ba zamu ketare zancen shi a yanzu ba saboda yafimu iko dake yanzu son haka shawaransa zamu dauka kada ki yarda ki boye min komai daya fada kuma.
Nace to baba insha Allahu zan shawarce shi iji mezai fada nasan insha Allahu ba zai hana bama ya dinga saka min albarka lokacin ne na rokesa kan zancen zuwan hassana nayi sa,a bai hana ba illa cewa da yayi hakan dai ba zai zamo matsala bako ga mijin ki ?
Nacw baba shima ya roka tazo din ta dan huta in samu abokiyar hira kwana biyu yace to babu matsala sai kun aiko din zanyi magana da ita da uwarta insha Allahu.
Muna gama waya dashi na jawo abinci ina ci akai sallama big brother din maman uku ne ya shigo na sheda yaron nake masa wasa da fadin big brother ka zama saurayi haka yana dan dariya cikin jin kunya.
Bayan mun gaisa nayi mai tayin abinci yace yagode a koshe yake yake fada min mamanshi ta aikoshi da driver su suzo za a dauki photo sadiya aje a sayo mata form dashi lokacin na tuna na kira sadiya din akaje daukanta photo.
Baban yaran shiya biya komai daga can basu tambayeni komai ba aka kawo mata form har uniform din islamiyan da cewa da yamma gobe zasu je da ita aimara interview asan ajin da za a sakata.
Da yamma bayan mun kwanta nake fadawa boss niyata ta saka sadiya islamiya din da yadda mukayi da maman uku din har ta aiko aka dauki yarinyar photo.
Nan kuma na sanar dashi sancen ya habibi din ban boye masa komai ba sai aurena da yaya habibi din yaso yi shikan ban fada mai ba wanan na boye masa yace nace yazo nan abuja ya sameshi haka muka aje maganan dashi.



ZAINAB IDRIS MAKAWA

ANCE WANDA BAIJI MAGANAN MANYA BA YAYI HASARA NI DAI NAJI INSHA ALLAHU GASHI NA DAN KARA TSAWON PAGES DIN SU MAMA SU ANTY DA ABOKAINA AYI HAKKURI DANI DON ALLAH YANAYINE HAKAN.

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Iya taji dadin saka mata jika islamiya da nayi tayi min godiya tayiwa mai gidan sai gashi kuma monday an kaita makarantan boko hakan yasa tsohuwan sakamu gaba tana muna kuka wai farinciki saida kyat muka samu ta lafa.
Washegari da safe bayan tafiyan shi office ban fito ba sai karfe goma sha biyu na safe na fito don in karya babu kowa a falon lokacin gidan yayi tsit na nufi dining table din mu.
Ina tsaye ina tsiyaya ruwan zafi a cup iya ta fito gani yasa ta dan washe tana fadin hjy kin fito sannu da tashi ya karfin jiki kuma nace jiki da sauki iya an tashi lafiya ?
Lafiya kalau uwar dakina sadiya dai bata makara ba yai ko na tambaya ina zama tace a,a ha saima data dan tsaya jiran yaran suka fito kafin sutafi.
Ta juya zata tafi nake fadi iya kin karya kumallo kuwa jin hakan yasa tadakata ta juyo tana fadin na karya tun dazun aida sadiya zata tafi muka dan sha ruwan zafi.
Haba haba iya sau nawa zan fada maki duk abinda kika dafa a gidan nan ki tabbatar da rabon ku a acikinsa amma iya bakya hakan saiki dafa ki kwaso muna duka ki girke.
Iya nan gidan D's akinne ina fada maki ko yaushe ki saki jiki ba,a matsayin yar aiki da kike daukan kanki kike ba a wajen mu to hjy ai naga kamar hakan ya zama ha,incine .
Iya kizo ki zauna don Allah sai mu karya maigidan da kike jin kunya bayanan kin sani ya fita sai yamma ko dare zai dawo don Allah kada kice min ba zaki karya ba iya ki zaina mu karya don Allah na fada ta zauna tsotso kamar za a tsura da ita a lokacin.
Muna ci ina dan janta da hira har muka gama nan falo na zauna na bude wayana ina duban sako kafin na na sake turawa ya habibi da sakon gaiyatan Boss zuwa Abuja wajenshi.
Ba,a jima ba naga ya amsa min yana fadin zan shigo insha Allahu wanan satin zanshigo Fatima ki bashi hakkuri wani abu ya tsayar dani nan din yanzu.
Mukayi sallama ya kashe wayan sai lokacin hankalina ya kwanta don na dauka yana ganin zuwa yaga boss din kamar kasawane a wajensa shiyazo din ya sameshi zai dauka faduwa ne gareshi hakan.
Bansan meke faruwa ba nikan ashe ana nan anata faman shirin buki dan hjy Halima matar wani kanin baban Bashir din da suke zaune a Manchester city.
Nasan hakane lokacin da ya shigo da katunan bukin ya zubesu a gabana inda nake zaune hakan yasa na mika hannu nakai na zari daya ina dubawa naga sunan yan family din nasune a ciki.
Mayarwa nayi na aje a daidai lokacin da yake zama a kusa dani bayan ya gama wayan da yakeyi lokacin na samu yi masa sannu da dawowa ina mikewa tsaye don inhar ya sameni a falo har ya zauna hakan ya zama min al,ada in kawo masa ruwa in kuma zare masa takalamsa da saffan kafansa da sauran tarkacen daya shigo dasu inkai dakin shi a sama.
Bayan na mika masa ruwan ne ya karba ya soma sha na zagaya na duka ina cire takalman da safan a santala santalan kafafuwanshi ina shirin mikewa naji ya jawoni zuwa jikinshi yana min inkiya da hannu ma,ana in zauna a kusa dashi din.
Banki ba na aje kayan a gefena na zauna a kusa dashi din hannunshi yakai ya dan shafo cikina da yanzu ya taso zaki iya hangosa ba zancen boyon ko tambaban ina da ciki ko banda shi.
Hakan yasani murmushi don ko da safe bai fita ba saida yayi hakan kamar me awon cikin ko wani lokaci yanzu ya koma zancen da yakeyi a wayan yasa na fahinci da wani nasa yake magana lokacin.
Don maganace data shafi gida ahali da kuma nuna bacin rai akan wani a family din nasu shiru nayi ina tunane a raina nace watau su dai sarakunan nan suna kokarin ganin sun gina kowa nasu ya zamo wani abin kwantace ba a damu da dan tallaka ya samu ba.
Don na fahinci kowa na family din dan business ne ko wani kusan gwaunati can da yakewa kasa wani babban hidima hakan yasa har ya dakatar da wayan ina cikin zurfin tunane ban san da hakan ba a lokacin saida.
Naji ya furo min iska da bakinsa yana fadin hey me kike tunane hakane na dan nisa tare da sauke gwauron ajiyan zuciya ina fadin abinci fa ?
Mekike tunane haka ya kara maimaita min tambayan nasa nace duniya kai tsaye ya danyi murmushi yana kaiwa kwance ya dora kansa saman cinyana yana fadin .
Duniya gidan kashe ahu ko kowa yakashe taro yayi barna to yanzu ba taron ba ba ahun ba miliyoyi ake kashewa akan duniya kawai don zamani .
Uncle Abubakar ne waiya sa a turo min da kudin da zan masu abubuwa a nan kan buki amma su baba Adamu sun hana yace dansa zaizo ya tsara komai shine kikaji ya kira yana min bayani yanzu.
Shi uncle Adamu yana kokarin gani dansa ya zamo kamar kowa baisan abin daga Allah bane shi kuma uncle Abubakar yasan zan masa har abinda yafi karfin kudin da ya turo din.
Shine yanzu yake min korafi a kai yaso tun farko in bari a hada bukin mu dana dan nasu nace ni lokacin nake son bukina kinga kuwa gara danace hakan inba haka ba da yanzu ina zamu kai alhakin bawan Allah nan ko boyar Allah dake cikin ki tunda lokacin zuwan shi duniya yayi kuma a datse masa zuwa don kaddaran wani ai kinga mun dauki alhakin maishi.
Dan harara na jefa mai nace aka fadama haka abin yake ko yace kwarai kuwa ai in da yaso fitowa duniya to kaf zurian su basu da sukuni sai yazo balle da irin nawa ko ince nami mai karfin jini da baki yaiwa yawa kinsan in zasuzo da karfin Allah suke baiyana duniya ai.
Na tabbatar da yawa basu gaskanta cewa kina da ciki ba don ni ban fadawa kowa ba hakama nasan mami a wajenta bata fada ba saidai idan sunzo zasu gani da idanuwansu susheda hakan tunda sunce ni guy ne bana haihuwa tunda maza yan uwana nake bi.
Wa,iyazu billahi har abin yakai can wanan wani irin kiyayyane haka wai akan dan uwansu yace shi ake kira da kiyayyan asali tun a ciki aka dasawa yan uwana kiyayyana Fatima.
Shiyasa ni kuma na nuna masu dasu da babu su duk dayane a wajena shine kikaga yanzu suna nemana ina bultsewa ga harkansu don ba zan taba yarda dasu ba a rayuwana ba.
Sun dauki kiyayyan tun na kakanni sun dora a kaina sun mayar dashi kamar abin bauta sun saka min bakin jini gun mutane a lokacin da nake bukatan wani a kusa dani.
Sun mayar damu da mahaifinmu mun zama makiya shiya haifemu amma ya koma a lokacin baya kaunan mu nida kanwata Zainab har yakai an dauki zainab saboda kiyayya an kaita kauye lokacin.
Kallon mamaki nake masa dama yana da kanwa mace da suka fito ciki daya bai taba ban labarinta ba ko wani ya fada min nace kuma wani wa can zai fada min nida har yau bamu taba haduwa da kowa nasa ba ko irin kawo amaryan nan dangi miji suzo ganin amarya nikan ai basuyi min shi ba da aka kawoni.
Bakinane ya furta yanzu ina zainab din take don baka taba min magana a kanta ba tunda aka kawoni murmushi naga yayi kafin yace tana Niger wajen yan uwan mahaifiyan mu a can ta taso amma yanzu na turata Cyprus tana karatu a can bayan mutuwan aurenta da akai mata na kauye ya mutu har ta haihu biyu a can din.
Yanzu haka ba wanda yasan tana can tana karatu sai ke dana fadawa ko mahaifin mu ban yarda yasan da zancen ba zata shigo kwanan nan don ta gama karatu tare da yaranta.
Allah ya kawosu lafiya na fada ya amsa da amin sai kuma shiru ya biyu baya a tsakanin mu na dan lokaci kowa da abinda yake tunane a lokacin.
Fuskana naji ya shafo yana fadin matar Bashir me kike tunane jin hakan yasa na nisa nace ba komai ya dan jawo kaina yana fadin da komai mana gimbiyata matar yarima mai jiran gado kinsan daga wanan rawanin sai mu .
Wani kallo nayi masa na mamaki ya kwanto da fuskana daidai nasa yana fadin kinsan abin daga jini yake ai abinda kowa kewa kenan dama yanzu sarautan.
Yanzun kuma an koma ana tsoron sarautan gani suke duk wanda ya hau za a kashesane yasa suka koma zoyalata da yarima mai jiran gado duk ko da iyayyen namu wasu na raye basu son su gaji abin a yanzu don tsoro.
Da sauri nace kaida baka da tsoro shine zasu laka maka ka dauka ko idan ya fadin ya kwashe da dariya nace ai gaskiyane in basa sonka mu muna sonka kana da masu sonka dayawa yanzu.
Dariya sosai yakeyi yana manna min kiss a goshina kafin ya dago zaune yana fadin yau dan uwanki din nan yazo ya sameni a office munyi magana.
Na kalloshi kafin in tuna ina fadin wai yaya habibi ai ba dan uwan mu bane mijin yayatace daya tayar dani ya sakani a boko can fatakwal a hannusa na tashi sai bayan rasuwan yayata na dawo hannun babana da zama.
Kallona yake kafin yace na dauka shine babban yayanku ai nace a,a makwabtaka ya hadamu dasu a unguwa daya muka taso dasu sai dai shiya auri yayan mu data rasu yanzu kuma yake auren sister na guda Samira tana gida yanzu hakama baka santa ba ita.
Ashe dai ke yarinyace karama Fatima wanan din shiya tayar dake fa kikace nace kwarai kuwa shiya sakani bokoma ya dan murmusa tare da mikewa tsaye yana fadin gaskiya ke yarinyace karama nace aina sani na auri tsoho ba.
Nine tsohon while ba laifi idan kin kirani da tsoho a yanzu wanda ya dauke yarinya kamarki ba na danyi murmushi ina mikewa tsaye nace ya kukayi da ya habibi din ?
Yace muyi magana ta fahinta kuma ya gamsu basai ya karbi kudin ki ba ko wani abu zaici gaba da business dinsa yadda ya saba zai kuma karbi gidan mansa daya bada jingina nace gaskiya Boss kana burgeni wajen sanin ya kamata.
Ya danyi murmushi yana kokarin jawoni jikinshi na zille na nufi dakinshi da kayan daya cire din don in na biye masa ba zai zauna cin abinci ba har dare yayi.
Bayana ya biyo ya sameni a dakin ina hada masa ruwan wanka ya tsaya yana rage tufafin jikinshi na fito yake fadin yarinya kona dan sauke maki tsufane kafin ki fita da sauri na fice a dakin yana min dariya na barshi a dakin.
Na samu iya ta kwashe kwanonin abincin ranan da baici ba ana aje na dare wanda wani lokaci zanga iya din tana faman shanyawa takance zaiyi amfani wata rana ga wani.
Ban hanata hakan ba don nasan tafini sanin ya kamata da hangen nisa don hakane komai tayi nake sa ido ban yarda ina mata musu ba akan abinda duk naga tayi din.
Bayan wasu yan kwanaki hassana ta bugo min waya gasu zasu shigo da yarana naji dadin hakan don haka na fara nazarin yadda zata kasance idan sunzo din ga kuma zancen yar uwarshi da zata zo don haka zan bar mata dakin danake amfani dashi a matsayin nawa duk da bansan lokacin zuwan nata ba.
Don shi mutum ne da bai tsayawa wani lokaci ya fada maka magana kai tsaye yadda zaka fahinceshi sai dai ya fadama a dunkule tun ban gane halinsa bane hakan har nazo na fahinceshi.
Kafin hassana ta bar gida anyi jidali sosai da har mama taso ta hanata zuwa saida baba ya rufe ido yace ta tafi don samira taso bata zancen wajen sake haibaici data saba sakewa mutane.
Sun iso lafiya nayi murna da ganinsu har jamal da Aliyu nan hassana ta tsunke da ganin inda Allah ya zabamin a rayuwa tayi addua irin wanda ake son musulmi dashi da fadin Allah yasa wajen zamanane nan har abada.
Itama Allah ya zaba mata mafificin alheri agareta amin sunci abinci mun dan zauna munyi hir??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a nake fadin watau dai ku malam Audi yaje kwasowa dama da akace yaje kaduna jiya.
Tace bai fada maki bane dama nace ai kinsan halinsa da katse zance saidai kaga ya aikata kawai hukuma ke nan sai lalashi ta fada muna dariya.
Na barsu don sun huta najena kwanta don in danyi barcin rana da yanzu na saba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login