Showing 285001 words to 288000 words out of 347556 words

Chapter 96 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8746

Ni wallahi dadi nakeji daka auri yar twenty two danya sharaf duk tafi wa yancan sauran daka bari da farko kurciya kyau ilimi dakuma hankali ya dan juyo ya kalli abokin nasa sai yaga bashi yake kallo ba yasan dai yana saurarensa baidai da lokacin bashi amsane kawai.
Tsuki yaja yana fadin mutum kamar dutsi ba nuna wani feeling shiya suke jin dadin maka sheri ai sun gwadaka yafi a kirka kana abu kamar wanda akaiwa taure dakai.
Sai lokacin ya juyo ya sauke idanunsa kan nasa yace nine taure yace meye marabinka da taure din fada min naso wallahi kasamu yar bariki irin yan duniyan nan da idanunsu ya bude bata da digon kunya kokadan da sai ka raina kanka gareta.
Murmushi yayi masa kawai don baida amsan da zai bashi a yanzu zama ya gyara yana lumshe idanuwanshi kamar ba zaiyi magana can Abbas din yaji yace dashi.
Kai baka san Kakana Aliyu yai min taure ba tun ina karamina don haka banga wata diya mace da zata firgitani ba komai shedancinta kuwa shiyasa lokacin da hjy Atika tayi min kazafi ya fito tsakar gida yace.
Ita din shedaniyace don badai zina ba ko makamancin hakan saidai sunna akan yaron nan kazafin ki baici ba Atika don yaron nan yana tare da tsarin Allah akan haka a jikinshi.
Allah yajikan Aliyu gadanga mazan fama gashi kuma kusan yaki ba karamin kokari tsohon nan yayi a kaina ba don lokacin yayi yaki sosai dasu hjy Laila da kake gani don ba karamar shedaniyar mace ba.
Wanan shiyasa komai sukai min baya kamani insha Allah don nasha tsari ba kadan ba a wajensa lokacin haka zaiyi tafiya a kaina yaje ya nemo tambaya duk sabodani sai yanzu nake gane abinda hakan ke nufi.
Lalai yayi yaki akanka ya kuma ja maka bakin jini a dangi don son daya nunama ya fifitaka da yayansu a lokacib shine musabbabin wanan gaba naku da bai karewa duniya.
Ni dai tsorona kada suce zasu biyo ta hanyar yarinyar nan sun don sun fita wayo ce a cuta maku do wanda ya rigaka kwana ance ya rigaka tashi.
Wana matsalan tane har idan ta ketare iyakana hakan na iya faru amma idan ta tsaya a inda na tsayar da ita kaga duk wanan mai saukine duk abinda zasuyi dole a ganosu.
Shiru Abbas din yayi yana dan tunane kafin yasha kwana ya danna kan mota zuwa cikin get din gidansu dake bude don gidan nasu acike yake da yan uwan mami dana daddy zakice ko sune iyayyensa na asali.
Labarin dasu Hassana sukazo muna dashine ya dan sakamu a rudani don kowa yaji a daren jiya barayi sun shigo unguwar da niyar sata aka fatatakesu kamar yadda Oga Abbas ya labarta masu a mota.
Jin abindake faruwane yasa Ammi ta kafa min dokan fita na zauna a gida idan ba fitan ya kama dole ba gareni a yanzu dole kuma hakan nabi zuciyana tab da tsoron hakan.
Da yamma za ai mother's day wanda da farko banso ayisa ba don wa nake dashi dolena da zai fito ya nuna shi uwace a gareni akarshe abin zai zamo min tonon asirine gun jama,a har wanda bai sani bama ya sani.
Amma hassana suka dage akan sai anyishi din tunda anayiwa kowa hakan ya zama kamar al,ada a kasa yanzu dole na kyale naja bakina nayi kan hakan da za,ayi din.
Sai gashi a yanzu nafi kowa son lokacin yayi don aka uwana nima na fito a tsara don infita bakin mutanen dake fadin uwata ta tafi ta barni ba,asan inda take ba.
Nasan taron zaikai taro don hassana ke fada min taga hjy Saudiyafa wurin taron saka lalai da akayi ban karyata taba don nasan irin alakan dake tsakaninsu da Bashir din.
Koba komai zanso taga baiyanan mahaifiyata a gareni tunda tasan komai akan batarta bawai ina nufin in shirya da ita bane a,a ayanzu ban fatan kara hurda ta komai da hjy din don wanda yakika da rana tsaka ko gobe yana iya juyama baya don haka ban fatan hakan ya kasance a tsakanin mu kuma yanzu.
Hassana ta shigo dakin tana fadin nikan ai nazata Samira zata iso kafin saka lalai gashi har yau din nan bata iso ba me hakan ke nufi sai lokacin na tuno da zancen danaji mahaifiyarta tanayi a waya nake fadin anya Samira zatazo kuwa .
Me zai hata zuwa Usaina ta dago daga inda take kwance tana charting aure mana na bata amsa tace chabdijam wani aure yafi maka dan uwanka yanzu ?
Haba dai auren yanzu dana da can baya suna da bambamcine kuma tace sosaima kuwa ai kowa yasan wanan amma ga ubangiji duk daya suke kaidai ka rike da gaskiya shine kawai.
Amma ai zatazo sai ta gama jawa kanta aji ta iso tana hura hanci koshi ya Mahmud din inga mutunci aiya dace ace yazo aure Bantu gaskiya to dan iskane ba mutuncine a kansa ba.
Ni suzo ko kada suzo yanzu ba matsalana bace wanan tunda wanda ban tsamaci zuwansu bama sun taho me zai dameni a yanzu shikan hassana tafada kafin tace ni wallahi bana gajiyada kallon Ummah duk sanda na hadu da ita.
Kina mamaki kema ace ita ta haifeni ko na tambayi hassana din tace wallahi har saidana tambayi mama a daki wai dagaske itace mahaifiyar ki kuwa ?
Nima sai nake ganin abin kamar a mafarki don bana gajiya da kallonsu saidai da alaman tana jin nauyina da kunya son ba wani dogon magana a tsakanin mu har yau din nan.
Ai bata kara shigowa gidan nan ba dazun ma da muka kai masu kaya ina rike a hannunta tana fadin idan ta ganni ba zata ganeni ba ai in ba nan data ganmu ba.
Ke bari ba laifi matar ta hadu wallahi ita kika biyo sak ga komai daga inda Usaina take tace ba dole su mama su hanata zama ba.
Wanan na gida wazai kalli su mama ashe kin gane Usaina nima saida nayi wanan tunanen a raina hassana tace wai mutum kamar shiya halici kansa haka wajen kyau.
Muryan matan dake guda yasa mukayi shiru a dakin lokaci guda don son jin meke faruwa a wajen wani sautin ne ke tashi wata marokiya mai babban murya tana fadin.
Dewa ya,i yau munga karyan arziki donga lefen ango wasu sunce namu daban da nasu t?bbas haka gaskiyane don ganau muke yau va jiyay muke ba dankari ba fashi arziki yana inda yake ashe garin dadi na nisa .
Ummh bari mu fita mugani kar a bamu labari Usaina ta fada sai gata ta dawo da sauri tana fadin din Allah kuzo ku gani kada in fadi ba daidai ba lefe aka hadawa angonshima.
Har muna hada baki wajen fadi lefe kuma tace ga jakkuna can kosu abin kallone an cikasu makil da kaya har guda ukku da sauri duk suka mike sukaje kallo saini kadai suka bari kwance cikin dakin ina tunane.
Hassana ta fara dawowa dakin sai naji ta rugumeni tana fadin ikon Allah lefe kuwa wallahi kamar na mata wai haka al,adansu mommy Nuratu yake dolene sai iyayye sunwa ango kayan sakawa na amarci Bantu ki godewa Allah wallahi.
Cikin godiya nake ga ubangiji har kullun sister Allah shike tsarawa bawansa yadda yaso a rayuwa nasani Allah yana tare dani tun ina karama sister.
Bakiga kaya ba Bantu wai nikan ai nayi shiru wallahi don kada inyi karya sanan da kudin waje masu yawa aka dora saman kayan, wai kudin daya kashewa yarsu shine aka mayar masa.
Usaina tazo da vedio kayan tana nuna min nikaina nayi mamakin hakan duk na kayan bai ban mamaki ba sai kudin nan masu yawa dana gani.
Shida jallabiya kan sainan da shekara ashirin kila masu zuwa wai kala bance ba nayi shiru ina kukan zuci don abin kamar a mafalki yake zo min nake ganin ni Fatima Binta Bantu dana kasance abin kyama ga jama,a saboda sherin mama.
Yau ni Allah yaiwa wanan gata haka Annabi yayi gaskiya daya koyar damu akidar musulunci banje wurin boka ko malam ba da kafana na tsayawa kaina da yawan addua ina sadaka ina taimakawa wanda naga nafi nayi hakkuri da duk wani cin fuskan matan ubana da yan uwa haihuwana.
Yau sai gashi ba zato ba tsamani Allah ya wadatar dani da ni,imominsa masu yawa a gareni ya sadaukar min da miji na shiga tsara ya sadani da farincikina mahaifiyata ta baiyana a gareni yan uwana suna nuna min kauna ta tsakani da Allah yauni Fatima wani kalan godiya zanwa Allah sai dai ince Alhamdullahi bini imatihi Alhamdullahi ala kulli halin.
Motocin Alfarma suka jeru har guda biyar zuwa gidan mami don can hjy laraba suka sani can din kuma suka kai lefen angon sunyi mamakin ganinsu da wanan kayan donsu a iya saninsu dai ana kaiwa ango kudun kwanko ga al,adan bahaushe amma shi wanan din yayi yawa gaskiya.
Bata bar kayan a gidanta ba dauka sukayi gaba daya dasu zuwa unguwar sarki inda family house din su Boss din yake anyi daidai gidan ya cika da yan uwa suka gansu daga sama da wanan kayan na ban mamaki.
Kowa ya fara tofa albarkacin bakinsa saida suka tambaya yaya zasuyi mami tace tukwici zasu bayar mai tsoka tare da abubuwan sha da zasu tafi dashi suma.
Sun dawo suna murnan irin taro arzikin da suka samu a gidajen biyu don ko a gidan mami ta rakasu da abin arziki mai yawa gashi anyi sa,a har mazan na gida suna meeting a lokacin kowa ya tofar albarkacin bakinsa.
Sun barsu wasu na bakin cikin rashin kama bashir din alokacin da yake da bukatan hakan garesu gashi yanzu wata bare tazo tana cin gajiyarsa a banza sunsan sun tafka kuskure don a gabansu mahaifin Bashir din yace aba mami din kayan ta tafi dashi gidanta tunda sune iyayyensa.
Sunji zafin hakan da mahaifin nasa yayi amma sunsan basu da bakin magana su sukai sake tun farko harta samu wanan gara basan data taka a yanzu din.
Karfe hudu aka fara haraman tafiya yin event din mothers day da za,ayi a DOCTOR ZALIHAT BASHIR SQUARE EVENT CENTER wajen da kowa yasan ya amsa sunan shi ga karban taron manya sai diyan manya da wanda sunansa yakai yake iya kama wajen don zaka dauka a kasan waje kake ba a Najeria din nan ba kuma cikin kaduna.
Motoci kan na nunawa tsara kowa kagani tana takama da nuna isa don ranane na fito na fito da mata keso su nunawa juna iyakarsu.
Kwaliya ba tsohuwa ba yarinya haka za ai gasan fita da nuna hali nake waye ke waye mijin ki keme kika taka aci asha ayi raha ayi gulma a soki wacan haka dama taron mata yake.
Yauma dai bata canza zani ba don duk kwalliyan da akai min da rantsatsen lace din dake jikina amma haka aka kawo wanan lafaya din ta ban girma aka dora min saman kayan ga wani takalma da jakka sak da lafaya din mai hill akafana na rike dan jakar sai sarkan gold mai tsawo da Ammi ta saka min a sama.
Mun fito daban don duk wanda ya fito daga bangarena lafaya ya lailayawa jikinsa saman anko din indai ke macen aurene yan matana sune suka bambamta da matan auren a wajen don suma ankone a jikinsu.
Duk kyau da isa da nuna takama da izzan iyayyen angon nawa sai ji sukayi gaskiya suna muzanta don ana masu abinda basu zaci hakan ba a wajen bukin don babu yadda zasu ja dun basu dauki abin haka ba.
Hajiya maryam mutanen nan sun shirya akan mu fa hjy halima ta fada don tana kusa da hjyn Saudiya din tace bari hjy halima ni nasan ko wasuye a nan son zuwana bukinsu biyu a maroco.
Yauma nake ji ashe uwar yarinyarce matar shi Abbu Sifyan yanzu ko kinsan siyasa ya koma a kasansu sosai can suke zama kamar sun bar London din a yanzu ai.
Haba nikan nace wanan abu kamar yayi yawa ke kama kanki wallahi zaki ga zinari iya ganin ki indai wa yan nan ne duk sune su Mahmud mai soft air line fa ubansu daya da uwar yarinyar shima matansa suna wurin nan akace.
Wai zancen gaskiya kikeyi hjy maryam wallahi ko nima Antiya na kira dazu da safe nake tambayanta take mi bayani a kansu ance ikon Allah baya karewa duniya suma ai yan sarautan kasansune a can din.
Chabdi ba wasa a wajan nan ta wurina ashe dan iskan yaron nan tantirancinsa yakai haka ya akayi ya zakulo wanan yar a cikin kasan nan ne ?
Bashir bashir kamar shu,umi yake ai komai nasa da sa,a yake zuwa masa yanzu kinga ya kashe muna baki a nan don ni koda wasa bai fada min ita zai aura ba don yasan na santa ko last month fa muna tare yaje saudiya.
Amma sam bai mun wanan zance ba Muhammad dina yaso ta amma saboda zancen mu dake hjy Laila na birewa zancen na hanasa ko jiyan nan saida ya fito min da zancen ai kinsa suna nan tare mukazo dasu.
Wai yarsuce dama a hakan kinsan abinda ya ban mamakine hjy laila sai yadda dan amaryan soft air ya makalewa yarinyar nan kamar ya santa har yaki yarda da uwarshi a wanan ranan kowa yana mamakin hakan ashe da dalili.
Duban shigowan mu afili ya daukewa hjy lala din hakali itama ta juya taga me take kallo a lokacin nan ta fahinci me ya dauke mata hankali a lokacin.
Kamar a falki take kallon lamarin wai Bantu dai Bantu Fatiman data sani a baya mai sunan mamanta yarinyar datake daukar ta da mutunci a matsayin uwa dataki a yanzu don wani nata dalilin da yanzu ya zama mata sabon tabo a zuciyarta.
Saboda duk ta kyala ido taga yarinyar nan wajen event din bukin nan sai taji kamar hannun agogo zai dawo baya akoma irin da yadda ake.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
9?? 1??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Abinda Ummu ta fadawasu hjy Laila gaskiyane don kowa dake wajen fitowansu ya dauku hankalin kowa don an kadu kaduwa bana wasa ba .
Ashe kuma dama su al,adan su shine nuna halin agani a wuyan matayensu shine shedar kudin mutum har in yakai mai kudi a kasarsu.
Tun fitowan matan su ya Mustpha da sukazo sukai min likin kudi hjy Laila ta kallisu Ummu take fadin kai mu motsa jiki fa kada azo a raina muna wayau muda garin mu ace za a nuna muna iyawa kuma.
Nan suka mike yan kungiyarsu na iyayye matan gidan su bashir din hjy Laila tace a basu fili don Allah su iyayyen ango zasu fito don haka daga Amarya sai su suke so a cikin filin.
Anko basu din ina tsaye cikin lafaya tsakiyan fili kidi aka saka masu wakan Naziru ashe amaryan nan da dangi taka kuri rawa rawa nan mata suka dauki rawa wuri ya kaure da ihu da watsin kudi mata suka haukace lokaci guda.
Nikan ganin zan fadi yasa na dan fara ja baya don wata sai tazo saitin goshina ta dangwara min kudin wata kuma kan mamana ko saman tsakiyan kaina haka dai sukai ta nasu bajinta ji tsakiyan fili ana ihu.
Ji nayi anja min hannu ana fadin fita a filin nan muje ki zauna ashe matar ya Mahmud din Ammine take min rada abin nasu ya zama iskanci wai kuma iyayye a angone a haka.
Bayan na zauna muna kallon ikon Allah can wani table kungiyar wasu mata ke gulma yau muna kallon ikon Allah a wajan nan.
Hjy Laila ai duniyace ita indai tana waje ai zaki sha kallon mamaki don itafa bata da tsoro bata da kunya kuma kaf Family din nan nasu tsoronta suke ji.
Dan gara gara su hjy maryam sun fita saukin kai gaskiya balle wanan bukin ai kamar da gaiyya sukeyinsa keda gani kinsan ana abu a duhu a wajan nan basai an fada maki ba kema.
Wani table kuma cewa sukeyi su kawai matan nan na larabawan nan suke son su fito suma akwai kallo idan sun fito don shekaran jiya sun burge mutane sosai wallahi da al,adansu.
Sukuma wanai table nagaba suna gulmane akan amarya da ango gardama sukeyi kan abinda suka sani game da ango wata kuma ta dauko hiran amarya aka dauka kowa na fadin abinda ya sani.
Sai wani table din matasan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login