Showing 33001 words to 36000 words out of 347556 words

Chapter 12 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8719

shigo sai fadan ta mukaji tana fadin wanan ai iskancine a shige daki a taru wai ana kallo mutum yayita sallama sai ku kyaleshi.
Yarinya karama ta mayar da mutane yan iska wai ita adole gamai kudi har ina kudin yake da take faman ruga maku karya kuna binta ku kuma wawaye.
Jin hakan yasa yaran da juyowa gareta suna fadi anty ina wuni tanaci gaba da fadan sai abinda ya fito bakinta a kaina lokacin.
Amma duk abin nan da takeyi baisa na dago kai na kalli inda take ba ina cigaba da jin labarin da yarinyar ke fada min a lokacin ganin haka yasa ranta ya kara baci dani tace.
Bantu wai me kike ganin kin takane ke yanzu da har zanzo ina magana kiyi banza dani sai lokacin na dago kai na kalleta nace ai ban dauka dani kikeyi ba don naji kina maganganun da bai dace ace sun fito a bakinki ba kamar ba babba ba .
Cabdijam lalai da ban yarda ba jinakeyi ashe iskancin naki yanzu har a kaina ya kawo ke nan to bari kiji bintu ta kira sunana da kyau don insa dani takeyi a lokacin.
Tace bar ganin baba ya kama maki kina iskancin ki yadda kikeso ni wallahi ubanki zanci a gidan nan haka kawai yar iskan yarinya zaki zauna kinawa mutane iskanci yadda ranki keso a cikin gida.
Dariya abin ya bani don nasan neman magana takeso dani don da gani akwai magana dama a bakinta saboda kwana biyun nan mamansu ji take kamar ta jefani a wuta.
Wai ni kikewa dariya ga irin yar iskan nan kingani ko toni ubanki zanci inga wanda ya kama maki duk garin nan da zai kwaceki a wurina .
Kai kashe kallon nan kafin na shigo tarwatsa dan iska kallon yaron nayi nace kai kada ka taba min kaya jaye a wurin karna karya ka a nan jin hakan yasa uwaryaron tace kai auwal taso wurin nan don Allah .
Ganin zata shigo min dakin yasa nima na mike zaune ina kokarin tashi zuwa wurin nace ina ruwan ki da kayana kin shigo bakiwa mutane sallama sai ki hauni da zagi kamar dama donni kikazo gidan.
Au ashe baki sani ba dama donkifa nazo yau gidan nan nazone nayi maganin iskancin da fitsaran nan naki a cikin gidan nan don samun wurin yayi yawa hakana kina kokarin adole sai kin juyewa kowa kai a cikin gidan nan.
Na kalleta shekeke nace daga baya ke nan kuma yanzu kuma wace bata da gata da galihu ina zata iya hada kan mutanen gida don kingansu nan wanan kuma ai wani abin zumucin ne da Allah ya riga ya kulla a tsakanin wanda ba wanda ya isa ya hanasa saishi Allah da kansa tunda muna wuri daya muna rayuwa ai doleko a ganmu tare.
Oh nufinki ke nan nace kwarai anty kema ba gashi kin shigo ta dalilin hakan ba daba dalili aiko kallon muma ba zakiyi ba ban maki komai ba tsakani dake girmane wanda Allah yabaki kuma kullun ina baki wanan ko a gabanki ko bayanki daidai da rana daya ban fatan ingaza da hakan tunda dakune nake alfahari.
Jikinta yai sanyi naga ta dan rage tamke fuska tana fadin ni abinda ya ban haushi shine don me za a shigo a samu gidan nan tsit duk kuna daki kuna kallo.
Saboda su da suke zuea makwabata kallo ana rigima kullun na sayo masushi amma ai gasu ki tambayesu idan nina damu da wanan kallon nan anjima kadan wurin sana,ata zan fitani na barsu nan shine kuma laifina anty don nayi masu hakan .
Bai yuyuwa nace nakai kayan kallon nan wani daki a cikin gidan nan dole nima yasa na ajeshi a nan don kawai suji sauki a rayuwansu.
Amma aini ba haka naji ba donni cewa akai min kina sai kuma tayi shiru to wai banda abinki Altine kema yanzu hakan baifi maki dadi ba gamu nan gaba dayan mu har yaran zaune a wuri daya inkin debe yaya da kallo ita bai dameta ba tana daki kwance abinta.
Ku dai gyara idan zaku gyara makirci ba abin yi bane banda rayuwa irin nakuma na rashin tunane duk ku hade a daki daya da yara wai kuna kallo.
A,a, a Altine ki san abin fadi a nan kuma ba wanda baya kallo a dakin nan dukkan mu uku kuwa don kawai yau yayi daidai damu kika samune amma duk na muke rage dare ai muna kallo .


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[7/29, 11:23 PM] Maman Aslam: KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
1?? 0??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,

Masu iya magana sunce abinda babba ya hango yaro ko ya hau tsauni bazai hangoshi ba don dai kan yanzune ya habibi ya fara hango matsalan auren Wasila da yayi.
Matsalan farko a tsakaninsu shine sakaci da ibada ya kula da bata son addini sai son yawan rayuwa a tare da ita yayi hakkuri don yana ganin zai iya shawo kanta a lokacin.
Saidai abin nata kullun baya canza zani zai bata lokacin shi ko a wurin aiki yake zai kirata yace kinyi sallah idan tace lokaci yayine yace ki tashi ki kiyi sallah amaryata ki daina wasa da sallah don shine na farkon abinda zai ceceki a wurin Allah.
Takan mede baki tace dashi taji yanzu zata tashi tayi idan bai gida harta gane idan ya kira sun gaisa sai tace ai yanzun ta idar sai daga baya ya fahinci kwata kwata bata masan shi kansa addinin ba.
Don hakane ya tsiro mata koyarda ita addini idan yana gida irinsu wanka sallah daidai sauransu sai ya fahinci bata daukan komai daga abinda yake koyar da ita din hakan sai ya fara jawo masu matsala.
Yau bai zai fita da wuri ba saboda ya kasance lahadine suna dai fitana ko Allah zai bada sa,a don hakane yake zaune a gida.
Barcin safe yayi bai saba da hakan ba yasa ya fito waje don ya zagaya gidan da falo ya fara cin karo da kaya a ko ina warwatse daga nan ya fita zuwa wajen gidan nan ma alama ya nuna tun sharan da yayi na karshe a wurin.
Ya dawo ya bude kitchen kayan abincine har sunyi hunhuna wasu sunyi sun bushe ya a wajen yabi kayan da kallon mamaki dakinta ya nufa don tunda yatayar da ita tayi sallah ta fito da niyar zata dakinta tayi bai kara jin duriyanta ba kuma har lokacin.
Kofan ya tura ya shiga nan ya hangota tayi dadaya saman gado tana sharan barci haka kuma alama ya nuna cewa batayi sallah safe a lokacin gashi har tara saura na safe.
Ranshine ya baci sosai a lokacin yakai mata maka a saman cinyar data baza din tana shan iska wani irin zabura tayi ta bude idanunta ta sauke a fuskanshi kafin ta danja tsuki tana gyara kwanciya.
Yace for god sake wasila ke wace irin mace ce wai ace mutum yabar kayan amfaninsa haka har sunyi rima saboda son jiki irin naki.
Ai zan wanke idan na samu lokaci tafada tana mika wani irin haushine ya kume masa zuciyarshi yake fadi a hasale will get up my friend barin fada maki gaskiya ni ba zan dauki wanan sha shancin ba a gidana.
Don ni mutumne maison tsabta da kula amma gida haka kamar gidan matan kauye wani irin rayuwane hakan nan kamar wace bata taba zuwa school ba ?
No malam aikin nan fa nice zan yisa na meye zakazo ina barcina yanzu ka dameni ido ya zaro waje cikin mamaki yana kallonta kafin yace ni kike dagawa murya wasila dama haka kike ashe ban sani ba ?
Yana fadin haka ya fita a fusace ranshi yayi matukar baci da lamarinta sosai dakinshi ya shiga ya zauna ya fara tunane yana fadin ashe gaskiyan bahaushe da yace matar farko itace mata.
Sai yanzu ya kara yardan ya rasa mace ta gari a gidanahi watau anty safiya yake jin mutuwan nata ya dawo mashi sabo a rayuwan shi.
Hawayene yazo mashi lokaci guda yakasa tare su lalai yayi sakaci sakaci kuma mai yawa da har ya kasa daukan shawaran iyayyenshi ga auren shi na bariki da yayi yanzu don gashi tun ba a kai ko ina ba ya fara karo da matsala babba a rayuwan auren nasu.
Ya dade a kwance a cikin wanan halin kafin yaji shigowan ta ta isowa ta fada mashi saman jiki tana fadin honey yau baka sayo muna breakfast bane ?
Wani irin mamaki da haushine lokaci guda ya rufe har ya kasa bata amsa ya kyaleta fadawa tayi saman jikin shi tana fadin dakai nake magana yau ba a gida zamu karya bane wai ?
You are very stupid kada ki mayar dani wani soko mana meye bamu dashi a gidan nan da zaki kasa dafa muna komai na fannin girki na sayo na ajeshi a gidan nan ki girka kawai zaki zauna kullun na fita naje sayo maki abinci ko ?
Wai lafiya ko kake har yaushe na huta da zan fara shiga kitchen ina dafuwa gaskiya ni ba zan iya hakan ba yanzu .
Ok kina nufin dama ba zaman aure kikizo yi a gidan nan ba ke nan tunda har kike ganin akwai lokacin da zakikai ki fara girkin da zamuci wai mako wasila kin san addini kuwa a zuciyarya ki ?
Me kake nufine wai don naga kamar wani zafina kakeji a yanzu don kawai nace ba zanyi abinci ba ka tambayi maman baby din kaji ko a gidanta ni bani aikin komai .
Yace ashe dake da mama baby din dukkan ku munafukaine do kun munafunceni kuwa kada ka zagemu fa don tun farko banyi ma alkawarin cewa zan dinga aikin wahala ba haka.
Zakiko bar gidan nan ke nan don ba macen da zan aje ta zauna bata gyaran gida da sauran aiki sai taci kawai ta kwanta ba haka al,adanmu yakeba mu.
Tureta yayi gefe ya tashi key dinshi na mota ya dauka sai waya ya fice ya bar mata gidan tana sababi ya danyi nisa ya samu wuri yaja ya tsaya ya kifa kai a saman sitiyarin mota yai shiru yana tunane.
Meya daukowa kansane haka anya Wasila macen da zai nuna a gidane kuwa sam bata dace da zama suruka a irin gidansu ba don yayama zai kalli iyayyenshi yace wasilace zabinshi daya bijere masu ya zabo.
Indai wanan halin zataci gana dashi anya zasu ko dauki lokaci da ita a matsayin mata da miji kuwa matukar ba canzawa tayi ba ta yaya zai iya dauko yaranshi biyu su zauna tare da macen da ita kanta bata da tarbiya balle taba wani.
Amma zai gwada kai karanta gun ita maman baby da a sanadinta yasan wasila din har ya aureta ko za,a iya tsawata mata taji.
Inda sukecin abinci yaje yaci ya kama harkokin shi amma kallo daya zakai mai kasan yana cikin damuwa a ranan karfe hudu ya nufi tsohon unguwarsu kofan gidan maman baby kawar anty safiya marigayiya ya tsayar da motar shi.
Kidane na mawakin ibo a cikin harshen turanci kamar kullun ya tashi a gidan kusan ma duk layin haka yake faruwa ko wani lokaci.
Mijin maman baby ne ya hango zaune saman step yana busan sigari dagashi sai dan gajeren wando a jikinsa yana hangoshi ya shiga washe baki tun daga nisa.
Haka ya fito daga motar ya nufi wurinshi suka gaisa sai tsami yakeyi don ba zancen wanka a gareshi sai shaye shaye kawai yau lahadi kuma a haka wai musulmine shi.
Bayan sun gaisa sun dayi halin maza na ansan juna ahi Mahmoud din yake tambayan maman baby din yace ko tana ciki wurinta yazo ?
Yace tana nan ita amaryan naka dai tana lafiya ko yace lafiya kalau akan zancentane ma nazo yanzu tare suka shiga ciki daga ita sai daura gaba gidan duk komatse tako ina .
Mamaki yayi a zuciyarshi kuma yana zargin kansa da bai tsaya ya tsaya ya fahinci hakan ba tun ba aje ko ina ba sai yanzun yake hango illan taraiya dasu a fili.
Sun zauna aka gaisa nan ya fito da zancen daya kawoshi din akan amaryan nasa hankalin ita maman baby din ya tashi sosai miji natane ke fadin.
Amma dai yarinyar nan sakariyace ashe Allah ya hore maki gidan hutu a sauke zata tonawa kanta asiri yanzu kuma.
Maman baby da hankalinta a tashe yake tace oho ashe wasila bata da wayau yarinyar banzace idan zaman gidane bai isheta ba saita dawo mu zauna.
Ina sam hakan ba zai yuyu ba saida ta koma gida can taci gaba da zuwa gona amma nan kan ba zata sake zama damu ba gaskiya ko yarinyar nan da aka bari gidan nan yanzu hakkuri nakeyi da zamanta a yanzu.
Kanaji baban Jamal kayi hakkuri zan mata magana gobe zan tafi gidan naku zamu zauna da ita insha Allahu zata daina duk wani halin banza nata.
Ni bashi ba don in rabu da ita ba komai bane gareni dama saida iyayyena suka hanani nace naji na gani ita nake so zan aura yanzu kuma tazo tun ba akai ko ina ba zama yaki dadi a tsakanin ta yaya kike ganin har zan kwaso mata yarana su zauna da ita.
Kayi hakkuri zanzo gidan naku nan dai ya taso har waje ta rakoshi tana bashi hakkuri ya tafi tun kan ya isa gida a waya suka kira wasila suka fara zagin ta da fada mata maganganu masu firgitar da ita.
Sosai yaga canji lokaci daya iso gidan nasa don bai dauka yadda suka rabu zata fito ta tareshi ba amma sai gata waje har ta share harabansu tana kwashewa tana ganinshi ta nufoshi tana masa sannu da zuwa ya amsa a dakile ya shige ciki ta bishi.
Zaune yakai saman kujera yana kallon falon duk da gyaran dai sama sama akayishi amma falon yadanyi haske kadan lokacin.
Ta zauna a kusa dashi tana bashi hakkuri wani warin hammata yaji ya daki hancinshi wanda ya dan dade da fara jin wanan bashin nata haka dai ya daure ya zauna tana bashi hakkuri.
Yace ban auroki ba son mu dinga samun sabani a ko wani lokaci ba haka na aurokine sin in samu farin ciki da gamsuwa a wurin ki sai gashi tun yanzu kin fara min da hakan.
Idan kika bi dokana zamu zauna lafiya dake zakiji dadina fiye da zaton ki wasila sai kukan munafunci wai tayi kuskure ba zata kara hakan ba insha Allahu.
Mikewa yayi yana fadin kin mayi wanka kuwa kinga hakan na cikin abinda zai dinga sakani fada dake don bana son ganin mace a haka.
Mikewa tayi itama tana fadin yanzun nan idan na karasa aikin nan nake son nayi wanka sai gaka ka dawo ya girgiza mata kai ya shige ciki shi da kanshi ya gyaro dakin nasa don yasan ko tayi ba tsayawa zatayi gyara masa yadda yakeso ba tunda alama ya nuna bata iya komai ba tun a gida.
Lailai bariki tayi bakin yan iska duk suyar awarane da za a bakin hayaki da wanan kwalliyan haka maman biyuce ke fadin hakan daga kofanta inda take zaune.
Fita nake da kayan aikina don yanzu na rage zuwa islamiya sosai tunda na sauka amma akwai ranakun dana ware nake shiga daukan karatu.
Don hakane yanzu na kara fadada karfin sana,ata inda mukeyin shi tare da wasu matasan unguwarmu da basu da girman kai suna dan samun kwabon kashi suma ta wanan hanyar.
Zakice wata yar kasuwace a wurin yadda wurin ke cika yanzu da jama,a masu sayar da abubuwa da dama don unguwar ta rayu sosai yanzu ba sai kayi wahalan zuwa wani wuri sayen kayan miya ba duk akwaishi a wanan wajen.
Motoci ko har daga wani unguwa suke zuwa saya awaran mu da soya milk mai dadin hadi ga kunnun ayya da zobo da ruwan sanyi sai sauran kayayakin da wasu ke ajewa suma a waje.
Zubin farkone yunusa ya zuba ina kokarin ganin wurin ya natsu min wata mota ja tazo ta parker a gaban mu wasu matane a cikin motan suka fito.
Naji dayan na fadin lalai wurin nada kyau sosai kuma ga tsabta tana zuwa ta tsaya saitin kaskon suyana daga can inda nake tsaye na dago ina masu sannu da zuwa.
Suka amsa dayan ke fadin don Allah ina me wurin nan ace muna macece ko na amsa da nice ai tow takara min kallo kafin tace ikon Allah dama ashe ma yarinyace karama haka na dauka wata babban mace zangani idan munzo don Allah munzo muna son wani


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login