Showing 54001 words to 57000 words out of 347556 words

Chapter 19 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8803

sai yamma zan koma nace baida matsala Allah ya kaimu lafiya.
Ina gama shiri na shirya da yar ledan vaco na wanda shinkafan nan ne dasu hjy suka aiko muna na dashi na dibawasu gwaggo saura nakaiwa baba ayi amfani dashi a gida lokacin.
Don haka na fito nasa key na rufo dakina wanan karon mama uwa nakaiwa key dina don ko akwai bukatan budan dakin idan ban nan kuma na lura yan kannena suna takura da kallon da basuyi idan bani gari yasa nake barin key yanzu a gida.
Normally na sallami kowa na gidan kamar yadda na saba a baya nace zan koma ina fitowa tare da kannena dyan wurin mama uwa wanda ada can baya har yaran mama lanto ake rakani amma yanzu banga ko mutum daya ba dana fito.
Muna fitowa din muka hade da Alh kakansu jamal wanda ya fito gidanshi zai shiga gari a cikin motarshi.
Muka tsaya gayar dashi yake fadin a,a Bintu ce wai ikon Allah Bintu na dade ban ganki ba kona tambaya sai ace min kina makaranta sai jiyan nan yara suka dawo da abin arziki wai kece kika saya masu.
Nagode Bintu nagode yanzu dinne banda karfi kamar farko abubuwan sai a hankali komai ka samu a rayuwan yake tafiya sunyi min magana amma banda halin hakan yazu.
Nagode Allah yayi maki albarka ya baki miji nagari a rayuwanki wanda yasan kimarki da mutuncinki na amsa da amin baba Alh nagode zan komane zarian yanzu.
Addua yayi min sosai tare da nasiha na ciro kudi duk da nasan jakata tayi rauni don yanzu mun dan fara samun matsala dasu Auwalu ba kamar farko da nake zuwa in samu kudina ba.
Yanzu sai su kawo min wasu matsaloli su ban dan kudi kada da kyar nake hada uwar kudin a yanzu hakan yasa nace dasu su barshi idan ya kare wanab karon kada a basu wake saina dawo zanci gaba dayi da kaina.
Wanan din bai hana inbawa baba Alh dubu biyar ba duk da nasan ina iya takura ina mika masa da sauri ya girgiza kai ganin hakan yasa na zube akasa ina rokonsa da fadin baba don Allah kada kace bazaka karba ba raina bazai mun dadi ba ko baba nakan bashi ya karba yasa min albarka.
Shiru yayi yana tunane a zuciyarciyarshi kafin ya miko hannu ya karba yana fadin ikon Allah Bintu keda zaki makaranta kece da kyautan kudi haka ubangiji Allah yaiwa rayuwanki albarka Allah yasa kifi hakan a rayuwan ki amma dai ki raba biyu in dauki rabi rabi kuma ki kara a mota.
Don Allah ka karba na kara mika masa hannu biyu ya dan kara kallona kafin ya mika hannu ya karba yana min addua.
Yace to muje in saukeki ko da sauri nace a, a baba mun samu lift ne nan gidan zasu tafi zaria yau shine zan bisu yace a, a to hakan yayi kyau sosai ai Allah ya tsare ya kare nace amin ya tafi.
Sai lokacin na fargada ashe yaran mama lanto biyu sun biyoni muna kai get din gidan na tsayar dasu a nan nabi kowa da naira hamsi sai Nurane dake dauke da dan buhuna muka shiga gidan tare nan na hango an wanke wata mota mai kama da jeep don bansan sunan motoci ba a lokacin.
Ni dai na sallami Nura na bashi dari biyu tare da masa fadan yaje makaranta in na dawo zan masa sayayya dayace.
Ya tafi yana murna yana min saina dawo na gyara kayan na shiga ciki da sallamata a nan falon suke gaba dayansu a cikin shirinsu ina shiga Al,amin din gidan ke fadin gata nan ma yar halak kin zauna kina batawa uncle lokaci ko.
To dan sheri komai sherin ka dai uwarsace shi ba zai dauka ba tunda yana son albarkan haihuwa suna ko limzamine in ku baku sani ba shi ya sani yana mutumta mai sunan mahaifiya koda ba ita bace din kuwa.
Mamata kin shigo kin gama shirin naki ko na dago kai in bata amsa naga wanan uncle din ya dago ya kalleta a daidai lokacin da take tambayana idan na gama shirina din.
Sai kuma ya mayar da kansa da sauri a wayanshi ta mike tana fadin zo muje daga ciki kafin ku tafi don naga kunyar wa yan nan yanzu yana hanaki sakewa a gidan nan.
Hannuna ta rike tajani zuwa ciki har dakinta karo na biyu ke nan da nake shiga dakin nata fada min kada kiji kunyata ni uwarkice meda me kike da bukata yanzu ?
Da sauri na dago kai nace a, a mama hakan ma nagode akwai kudin sana,ata dana karba a hannuna kai haba mamata kudin sana,a akullun idan ana tabasu ai karewa zasuyi keko.
Amma bari ina zuwa sai naga ta fita ina zaune ni ina bin dakin da kallo irin kayan alatun da aka zuba a dakin sai gata ta shigo kuma tana fadin kinga tashi kuje an hutar dakema da daukan kaya uncle din ku yace zamu bata masa lokaci .
Amma ga wanan ki rika ta dauko jakka ta ciro kudi ta mika min nayi saurin girgiza kai nace mama don Allah ki barshi amsan data ban ya girgizani tace idan uwarkice ta baki zakiki karba mamata?
Hakan yasa na sauko na rusuna ina karban kudin daga hannunta tare da mata godiya tace No ki bar min hakan dana kowane ai tausayin rayuwanki nakeji don naga kina kuma da nasuwa sosai.
Muka fito mun samu har ya shiga motar suna wurinsa suna magana yake fadin zuwa yamma zan juyo da zaran na gama da mai martaba din.
A dan marairaice nake fadin kayana zan saka a motar au kai Muhammad bude boot ta saka kayanta a ciki kamar baiji mai ta fadaba a lokacin ko juyowa baiyi ba inda yake zaune din.
Sai ganin boot din ya bude mukayi nan mama din tasa Al,amin ya dauki kayan ya saka cikin motar shiga mamana ta fada daga gefena ni kuma sai nadanyi dabur dabur na rasa inda zan shiga na kama baya ina budewa naji Al,amin yace ashe zaku kwasa da uncle kije gaba kada yanzu yace ya fasa baida wuya ga uncle kuwa yanzune.
Tsayawa nayi ina kallonshi sai ya kama dariya kafin yace wai ina zata zauna uncle kafin ya bada amsa mama tace je gaba a nan zaki zauna jeka don Allah bude mata tashiga takecewa Al,amin din yace lalaima zo badon halinki ba.
Ban tafi ba din na tsaya nacewa mama nagode mama Allah ya kara arziki da wadata da nisan kwana nagode kwarai mama na juyo na tafi kafin na kewaya ta isa wurinshi suna magana kus kus dashi.
Innalillahi na ambata don sanyi da kamshin daya daki fuskana lokaci guda haka na shiga kamar mara gaskiya cikin motan na zauna ya rufo min daga baya shima ya rufe muka dauki hanya yana masu horn.
A takure nake zaune banko dago kaina ba muna barin unguwar namu can na hango Auwalu yana shan minerals da burodi nace a cikin kudina ke nan dan duniya ya guda daga erean mu kada a ganshi yana busha shanshi asashi a baki.
Uncle din naga ya kai hannunshi yana kunna redio motan ina nan zaune a takure naji sautin kira,an wani balarabe mai dadin murya yana tashi.
Muna dan barin cikin gari kada inda ba yawan jama,a alokacin ya fara sharara gudu yanayi yana bin kira,an mai karatun wani lokaci suma nayi zaune ina mamaki don idan ka gansu a cikin gidansu zakace irin diyan kabilune ko diyan hausawan dake koyi da akidan nasara.
Ban san lokacin da barci ya daukeni ba don sanyin AC daya takurani na dan make a wuri daya abu ga dan tallaka ba,a saba ba kuma ga gajiya a jikina don gaskiya ban hutu koda nazo weekend din don neman kudi.
Gashi ban iya ganin ana aiki ban saka hannu ba saukin abin yanzu da ban saka hannu a aikin mama da mama uwa ita mama na dade da daina taba mata aiki idan tanayi tun watarana da take aikin soya milki nazo na kama mata sai ba samu sayarwa ba shine take fadin.
Ita shiyasa bata son a saka mata hannu a cikin aikinta don arzikinta baison hakan ina ji tun wanan ranan ban kara taba mata komai ba saidai in gaida ita idan tana aikin.
Ita kuma mama Lanto a yanzun tun farkon faruwan matsalan mu da samira ta daina bani fuska ni kuma nama daina kula da komai nata a yanzu.
Sit din da nake zaune ya dan buga da karfi abinda yasana falka firgigit kenen sai lokacin na tuna a inda nake fuskana nadan shafo ina jan tsuki babban signbord din tallan MTN ne da aka kafa a hanya ya tareni .
A lokacin nagane mun iso garin zaria hakan yasa nace kai sai ya dan kallo inda nake niko ina furta zaria kamar iska mefa ya tambaya kunya naji don ban dauka yaji abinda na fada ba lokacin.
Tafiya mukaci gaba dayi kamar ba zai mun magana ba sai zuwa can naji yace ko motar aljannu kika shiga yasa kikaga saurin zuwan mu ko ?
Yi hakkuri don Allah na fada da sauri ke me kikai min da zaki ban hakkuri please nayi maki maganane sai naja bakina nayi shiru tunda naji suna fadin shi dan ka,idace dama.
In kin gama barcin ki fada min inda za,a saukeki ba kauya kawai daga shiga mota zaki farawa mutum barci kamar ya dauko gawa duk laifin Ukuthyce data hadani tafiya da yar kauye.
Kowama asalinsa kauye ai tunda ba daga madina mutum ya fito ba na fada kasakasan murya amma ba irin naki kauyancin ba da baki ko iya boye hakan gareki.
Juyowa nayi na kalleshi cikin mamaki sam fuskanshi babu alaman fushi kamar yadda na zata zan ganshi idan na dago din sai naga sabanin hakan.
Ina zan saukeki a hankali ya fada wanan karon nace samaru zaki gane hanya nace eh sai ki fara nuna min inda zanbi idan mukai round nace hago ko dama har muka shiga layin su gwaggo din.
Sai tsuki yake ja kafin can yace wai a nan kike zama haka ya tambayeni cikin mamaki a fuskanshi?
Nace bakaga mutane bane a unguwar ni wacece daba zan zauna ba unguwar akwai mutane sosai suna da mutunci da karamci ga daraja dan adam babu tashin hankali irin sauran unguwar garin nan .
Dawa kike zama a nan din ya tambaya nace tare da gwaggon mu muke zaune a gidan mijinta don baba bai yarda mu zauna a hostel ba.
Amma da hostel din kuke zaifi maku sauki da cacan kudin abin hauwa nace ko a hakan ma mungode tunda ya barmu munzo karatun har nan garin.
Wancan gidan na tsakiyane gidan namu nafada da muka shigo layin wani burki naji yaja ya tsayat da motan yana dan kallon wurin ban kawo cewa kwantan daya gani a layin yakewa ba sai da naji yace .
Wanan wurin kuwa zan iya shiga da motana dan rabawa yayi gefe ya samu yakai kofan gidan na fito shi kuma ya bude man boot na dauki kayana na aje daga kofan gwaggo din.
Nagode uncle Allah ya kara arziki da wadata yasa kafi hakan a rayuwanka agaida mama idan ka koma nagode baiyi magana ba yaja mota yana tafiya a hankali ya fice kwatan da yake tsoron a layi kafin ya harba mota ya hau titi.
Duk ina tsaye ina kallonshi har ya bace na juya na dauki kayana zuwa cikin gida ina sallama muryan gwaggoce ta amsa min da kyat daga cikin dakinta.
Na isa kofan ina aje kayan na samu tana kwance bata da lafiya sosai a lokacin gata kwance ta rufe jikinta ita kadai a gida.
Subbahanallahi gwaggo baki da lafiyane haka dama na tambayeta cikin damuwa bata iya ban amsa ba don yanayin da take ciki.
Shiru na danyi ina tunane kafin na kara mata sannu nace kin ci abinci gwaggo na fita na samo magani tace koko kawai na iya sha kuma na amayeshi dazun.
Ina zuwa na fada na juya na fita na tafi madafanta don in dora ruwan zafi nan ma basu da icce nasan gidan da suke sayo iccen na fita da sauri zuwa gidan na kwaso kashin icce na dubu daya na dawo.
Ina jin wani na fadin ke gaki da kyau babba yarinya dake kika dauko wanan uban iccen haka ban kulasu ba na shige gida wuta na hada na dora ruwan zafi daya kama.
Nan na fita zuwa wurin mai shagon unguwan na hado kayan tea har wanda zatasha gobe na biya chemist na sayo mata aji garau don shine maganin yan gidan mu.
Na dawo na samu ruwan yai zafi na dauko kofi na juye na kara dora wani ruwan zafin masu yawa da zata watsa a nan na hada shayin mai kauri na sameta a daki har lokacin a yadda na barta kwance take.
Gwaggo ki tashi kisha ga magani ki hade da kyar na samu takai zaune na aje na debo ruwa da wani tsohon baho na kawo mata ta kurkure bakinta saina miko mata shayin ta karba ta dan kafa kai nace daure gwaggo kisha zai taimaka maki ki rage jin sanyin.
Haka ta daure tasha na bare maganin na bata tasha ta koma ta kwanta wutan yana ci sosai na samu ruwab yayi zafi yadda akeso na juye a bucket nakai mata bayi bayan na dan surka mata shi ya rage zafi.
Na dawo dakin na tayar da ita muka nufi bandakin saida ta shiga na koma na gyara wuta na dora muna abinci tunda akwai shinkafa a wajena danazo dashi na shiga dakin na gyaro mata kafin ta fito daga bayin ta gama ta fito tana min godiya.
Ta koma ta kwanta na fito na gyara wuta kafin na fita zuwa bakin titi inda masu kyan miya suke na kashe dubu daya na hado kayan miya na dawo.
Shinkafa da miya na dafa na gama na kwashe a babban kula wanka na shiga na fito na saka wani dogon riga nawa yar kanti na yaku bayi don ba wani mai tsada bane kuma ya tsufa.
Kodana fito na samu gwaggo, ta fito tana zaune kofanta tayi tagumi nace gwaggo kin fitone ya jikin tace yar nan Allah ne ya jefo min ke daidai lokacin daya kamata ki taimaka min.
Kila badon kinzo ba da mutuwa zanyi a lokacin tunda yadda naji yau din nan sai Allah nace ciwone gwaggo Allah ya kara sauki ta amsa da Amin tare da fadin yanzu kuma wani zafi nakeji sosai yana fita min a jiki sai zufa nakeyi yasa na fito.
Akawo abincine gwaggo na fada tace abinci yar nan ko abin kari yau dan uwaki yayi muna koko da safe suka karya shine malam ya matsa min na dansha na amayeshi kuma.
Ga abinci nan na dafa ai na kwashe a wanan kulan da kike zuba abincin gida a ciki Allahu Akbar dan mutum mai rana yau kece Fadimatu kike wanan hidimar dani haka.
Yau in mahaifiyarki ta baiya da wani ido zamu kalleta dashi matar da Saratu tasa mukai mata koran kare a gidan yaya Sule har yau har gobe idan na tuna da wanan abin yana cimun rai sosai a rayuwata.
Don kamar abin sihiri lokacin haka saratu take juya kowa yadda takeso gidan nan kai bari saratu tayi iya shege a gidan yaya har yakai ta kiramu kamar sakarkaru haka mukazo muka tasa boyan Allah gaba yaya hausatu ta fisgeki a bayanta.
Ta juyo tana kuka tana fadin har da yar ba zaku barmin abinna ba yaya hausatu tace an karba kada ki koya mata tsafi tasa mukai mata sheri kan abinda bataji bata gani ba.
Sai naga ta fara sharan kwalla tana fadin ina zanga boyar Allah nan na roketa gafara wanan abin yanzu yana damuna sosai a rayuwana.
Sallamu Alaikum wai Fatima tana nan wani yaro ya fada daga soron gidan nace eh waye ke nemana kafin inyi magana yaron ya fice da sauri.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
[8/9, 10:27 PM] KYAUTA: KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
1?? 7??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,

Allah ya kai haske a kabarin musulman da suka kwanta dama marasa lafiya ubangiji Allah ka basu lafiya masu lafiyan Allah ka kara masu lafiya da wadatan zuciya da imani da kai ya Allah.
Allah ka karemu da shiga ciwon da tashin hankali damu da yan uwan mu ya Allah ka sassautawa musulmai ka agajesu kabuda masu ta hanyar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login