Showing 297001 words to 300000 words out of 347556 words

Chapter 100 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8812

hakan a kanki yanzu.
Mama Bantu fa ta rigada ta shiga gaban mu sai kallo in zaku boye komai ku boye a yanzu a zauna lafiya ke kuma usaina kin ban mamaki da har kika biyewa maganan mama a yanzu.
Yarinyar nan ba abinda tayi dabata sakamu gaba ba cikin sha,anin nan yanzu kuma ki butulce mata don Allah ha badai kuyi wa kanku hissabi anan shiyasa ko yaushe muke ganin tana cigaba muna komawa baya.
Aiko ina wuta mama ta saka hassana saida ta fita ta koma dakina wajen su maryama ta kwanta a can lokacin mama uwa ta gane suna gida ashe.


Z?INAB IDRIS MAKAWA

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
9?? 4??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Allah mai iko mai yin yadda yaso ga bawansa a duk sanda yaga dama akan bawa duk abinda Allah ya jerabi bawa dashi matukar karugumishi da hannu biyu wanan abin insha Allahu watarana sai ya zamo alheri ga bawan nasa koya zamu silar alheri ga wanin sa ya Allah kaba imani da tawassali da da ni,imominka garemu Amin.
Karfe biyu nagaji da kwanciyana na tashi nayi wanka nayi sallah na dauko daya daga cikin kayan nan nasaka a jikina sai dai lokacin ban ji dadin hakan ba zama nayi don ba inda zan tafi a lokacin.
Shima a daidai wanan lokacin ya falka yafito daga wanka wayanshi ya dauki kara ya duba Abbas ne a layin yana dauka Abbas din yace kai dan iska ka budewa mutane kofa a shigo kaji.
Dan iska kawai an fadama kankane farin aure ko an fadama haka akeyi kabi gida ka garkame tun safe kana yan uwa suzo suka kwanan ku an fadama haka akeyi koso kake ka fara nuna masu naka policy din.
Dan iska kamar wani namijin kwarai kabi kofa ka garkame kamar mai wani abin kirki a ciki don Allah bude ga abincin nan tun safe mami take sintirin kawo maku ni ta dameni wai ban damu naji halinda kake ciki ba ko lafiya.
Murmushi yayi cikin muryansa dake nuna daga barci yake lokacin yace ai sai kayi dan iska ni banda lokacinka yanzu ga gidan nan an bude.
Tsuki yayi ya kashe wayan yana dura mai ashar kana ya kira mami din ya fada mata an bude gidan wai barci sukeyi dama itako tace Allah sarki ai dole dama akwai gajiya jikinsu.
Sun gama wayan da mami zai maida aljihu yaji wani kira yashigo mai ya dauka daga bangaren Fatima ya gani yana dauka suka gaisa Fadilace take fadin ya Abbas munso mu koma yau din nan ,,,,
An bude gidan kuyi hakkuri don Allah ya fada tare da kashe waya mikewa yayi ya fito don dawowanshi ke nan daga airport ya raka wasu abokansu da sukazo zasu Lagos su shiga jirgi a lokacin.
A gajiye ya shiga gida nan ma din akwai baki yan uwan matarshi da sukazo daga bauchi suna nan basu tafi ba dakinsa ya nufa ya dan watsa ruwa don tun safe yake jigilan hakan.
Wayan mamine ya shigo masa ya dauka yasan dai maganan dayace shine Bashir yana sallama take fadin kufaje ku gaida iyayye a yau din nan ya amsa da wanka zanyi mami naje gidan yanzu insha Allahu ya fada.
Ta amsa da kada dai ka dade don kasan zai bukaceka a can sunyi sallama wanka ya tsaya ya dan watsa ruwa daya ya fito ya shirya falon su ya samu matarsa da yan uwanta ta gabatar mashi da abinci ya zauna yaci kafin ya fita yana fadin su bari sai sun huta zuwa jibi su koma gida.
Suma dama hakan suke so don basu da niyar komawa a ranan saboda basu ziyarci ko ina ba agarin ana ta hidiman buki a lokacin don haka suke son su kara kwana.
Karfe ukku yana kofan gidan a daidai lokacin dasu hassana maryama da sauran yan mata tare da matan su ya mustapha da wasu yara suka firfito a mota suna kallon yanayin wanan gidan.
Fadila da hassana sukai masu jagora zuwa cikin gidan kai tsaye tare da wasu kayana da aka karbo a wajen dinki basu ganshi ba saida suka shige cikine ya kira Bashir a waya.
Gani saukowa ya fada yace kuna dai da baki gidan don gidan cike yake da mutane yanzu what ya fada cikin mamaki kai dan iska yanzu aika fara ganin mutane gidan nan ke nan tunda akwai mace cikinsa yanzu.
A daidai lokacin nagama cin abinci ina zaune wajen naji shigowansu Fadila da maryama da hassana suka sameni a dakin da ihunsu suka shigo nan suka hau min sheri amarya amarya na dan hararesu.
Idona kai a kayan nace wallahi kin kyauta min da kayan nan take fadin wanan na jikinki fa nace a nan na samesu tace cabdijam yarinya kice kin more miji bayan wancan din na gida wasu kuma kika sama a nan kuma.
Ki duba ki gani na nuna closet din ta mike da sauri ta nufi wajen tana budewa ta kasa nace ja zakiyi ya bude ta gwada ihu ta saka duk suka mike zuwa duban cikin drower din kayane na alfarma a jere ciki irin na shan iska da wasu ni ban ko duba ba sai lokacin.
Kin kai karshen sutura kekan Fadila ta fada iyaka ke nan ai wanan tare da matan su yaya muke suna falo zaune na juyo ina fadin akan me su shigo mana maryaman ta juya tazo dasu lokacin ina sauya kayan jikina zuwa wani shadda mai kyau mai kama da kamfala amma kala biyune a jikinsa.
Kakin soja da dan yellow kadan da aka ratsa masa dinkin yan mali telan yayi min dashi har kasa sai dan kwalinsa babba dana keta faman kokari in daura a kaina lokacin na kasa matar ya Mahmud ta karba ta daura min shi na dan dora gyalenshi a kafadana.
Ki kira muna angon naki mu gaisa don sammako zamuyi gobe mu koma gida mu naji matar ya mustapha ta fada saida gabana ya fadi na wayance da fadin kilama ya fita ai don tun dazun banga shigowanshi ba kuma.
Ke kardai kiyi wanan sakacin waike kunyan nan makale masa ki manne masa kamar chewing gun duk inda yake kina banne dashi inba haka ba yanzu kiji cikin dangi sunce ga diya an baka gidan sauratane baida wuya hakan yanzu.
Mikewa Fadila tayi tana fita daga dakin har takai kofa naji tace Fatima zo don Allah hakan yasa na mike dan dogon corridor muka tsaya take fadin.
Kada ki soma yin wanan watau da wani zai gane cikinki dana gidanki haba sai kace ba mace ba yanzu duk yadda za,ayi ki zo muje ki duba idan yana nan yazo din su gaisa dashi tunda haka suke so ayi din kansu tafin.
A nan hassana ta samemu itama ganin ta baisa ta fasa fada min abinda take fadin ba a lokacin tambayana tayi ina wayana sai lokacin na tuna nadan ja tsuki ina fadin.
Ya karba tun jiya yana hannunsa ayya shiyasa muketa nemanki ashe bamu samu ba wayan yana kashe lokacin computer ke fadi na dan bata fuska ina tambayan Usaina.
Tana gida wai bata tashi zuwa ba dazun munzo da safe mu kawo maki kaya gidan yana rufe shine tayi fushi kinsan mama bata son a zauna lafiya don suna magana na hana shine wai tayi fushi yanzu da zamu zo.
Dan murmushin yake na sake ina fadin wallahi barci mukeyi kowa ya gaji nasan shiya hana a bude gidan da wuri dama kallon Fadila kawata nayi ina fadin nifa ban masan ka gidan nan ba ko a ina zan sameshi na kira masu shi.
Karan budan kofa mukaji muka juya wanan Samuel din mai aikonsane ya fito wani lungu nan nake tambayan shi ko oganshi yana gida yace eh amma yana waje zaune da Oga Abbas.
Ya nuna min hanya da hannu jin hakan yasa na gyara gyalen kaina ina fadin ina zuwa nabi hanyan oga Abbas yana zaune cikin motanshi kuma yana tsaye a gabanshi ya bada baya tare da rike marfin kofan motan ya dora kafa daya saman matakin motan suna magana yana dariya zakice bashi bane.
Abbas daya ambaci ahh Fatima yasa ya juyo yana kallon inda Abbas din yake kallona a cikin daurewa na karaso inda suke din ina gaida Abbas din ya amsa min a cikin raha yana fadin .
Amarya amarya da fatan dai kin tashi lafiya ya gajiyan taro kuma ya tambayeni nace alhamdullahi ban tsaya ba nace dama matan yayyunane sukazo min sallama gobe zasu koma suke son ku gaisa kan su tafi.
Goben nan Abbas din ya fada yake fadin akwai nisa mana tun basu huta gajiya ba zasu dau hanya kuma gobe suna cikine ya tambaya yana dan kuramin idannunsa a kaina.
Hakan yana naji nauyi da kunya na amsa da sunanan ciki sun shigo dazun nan OK gani tafe ya fada na juya na koma ciki nakai kofa naji sunyi dariyan dake saka mutum cikin tsarguwa lokaci guda bandai san me suka fada ba a lokacin nadai dan tsarguni da hakan.
A falon na samesu zaune don banda mai falo na gidan acikin ko wani part kuma akwai falo mai dan girma shima da zai iya daukan set biyu na kujera da kayan gyaran falo an hadashi komai akwai a cikinsa nako wani daki.
Don haka suka fito falon suka zauna a nan na samesu nima na nemi waje na zauna daga gefe daya ba,a jima sosai ba sai gashi ya shigo yana sayene da jallabiya a jikinsa baka mai adon gwal din zare agaban rigan doguwace har kasa rigan.
Sallama yayi suka shigo shida Abbas din kowa ya tsura masa ido suna amsa sallaman tare da kare mai kallo Abbas ne yake fadin sannun da zuwa a cikin raha.
Direct kujeran da nake zaune a kai ya nuna ya zauna a bakin hannunsa jikin mu yana dan gugan juna kadan danashi ga zaman namu.
Lokacin ya fara masu sabon gaisuwa yana masu bangajiyan buki sai kuma yai shiru Abbas yai saurin fadin ashe gobe zaku koma gida yanzun take fada muna hakan .
Insha Allahu tunda angama buki lafiya zamu koma gida saboda karatun yara ta fada yace hakane aimu godiya gun mazajen idan ankoma suka amsa da insha Allahu zasuji.
Ai sun koma yau din nan da safe tambaya yake basa ganewa yana fadin wani hanya suke bi sukace dashi ta jos yafi sauki nan da nan ake kaiwa yace OK yana mikewa ya kara fadin angode Allah ya tsare hanya suka amsa da amin.
Shima Abbas din yabi bayansa har sunkai kofan fita yake fadin zomana Fatima na mike na bishi yake fadin yaushe zasu koma gida ina nufin nan unguwarku malali.
Idan sungama naji suna zancen shiga kasuwa OK ya fada ki biyoni ki karba masu sako Abbas bari na shirya sainazo mu fita muje gun mami din.
Abbas din ya amsa da bari na dan leka Yusuf kafin ka fito yau duk bamu hadu ba kasan jiran ango yana dadewa gara naje yin mai fisheni in dawo No kajirani nace dan iska kawai banza ya fada a fusace maimakon inga fushi a fuskanshi sai dariya naga ya kwashe dashi mai karfi ya juya yana fita daga part dina din.
Tun a falo na fara sarewa don abinda idona ya gane min kamar aljannan duniya komai na mare rayuwa akwaishi falon nan bai tsaya ba ya nufi ciki dole nabi bayanshi a dadare har uwar dakan
Dankari na fada bayan shigan mu din ina furta wa,iyazu billahi don sai ince wane dakina dawanan duk da kowa ke santinsa da wanan don dakin nasa komai fararene sol a cikinsa sabanin nawa da yake mixe color baki da farin kuma akwai banbanci da ganin kayan duk da wanan din ya nuna na mazane amma fa a nawa ganin.
Daga kofa naja na tsaya na dukar da kaina kasa ya nufi wajen cloister dinshi kafin ya juyo yana fadin kin tsaya can mana tsoron dakin naki kike jine kuma ?
Bansan lokacin dana girgiza masa kai ba ina fadin a,a na dan tako zuwa tsakiyan dakin ya juyo da kudi a hannunsa yana fadin ki basu wanan suyi tsaraba dashi akwai sako a wajen mami za akai masu gida kansu tafi.
Hannu biyu na mika ina karba tare da dan rusunawa ina fadin angode Allah ya umfana kaina nayiwa ya fada nidai na juya da sauri ina fita daga dakin kamar ankoroni.
Sai lokacin na kula a gefe daya muke dashi ashe a tsarin ginan saidai akwai dan tazara a tsakanin mu kadan da nasa ginan amma a hade suke gefe daya.
Shigowana falon suka kura min idanu na mikawa matar ya mustapha dana lakawa Anty babba a cikinsu ina fadin yace a baki wanan kuyi tsaraba dashi akwai sako da za a kawo can gida wajenku kan ku tafi.
Nan kowa ya shiga fadin albarkacin bakinsa akainjimaa waina zauna lafiya Allah yaban miji dan mutunci shiru nayi ina wasa da yar wajen ya Mubarak basu ba sukai min sallama har waje haraban gidan na rakasu ina jin wani irin yanayi a zuciyana har suka tafi muka juya dasu hassana zuwa cikin nan muka zauna babban falon muna kalle kalle a falon.
Can muka mike kuma muka koma ciki hassana ke fadin ni har yanzu mamakin Samira nakeyi na rashin zuwanta bukin nan tunda ance cikinta bai tsufa ba ai.
Au cikine da ita ashe na fada ina cire dan kwalin kaina zan shiga alwala don na fahinci la,asar yayi lokacin kada mu shagala jiya jiyan nan wanda ban zaci jin nasiha a bakinsa bama yai min akan shagala da duniya mume zamu jira kuma ga hakan yanzu sai rashin sani da bata kuma kadai zai tsayar da bawa ga hakan ai.
Na hankada filo inda na aje hulana ina dauka nadago ina sakawa nace ko don wanan ai a mata uzuri kila laluran cikine yasa bata zaba din ba gashi anyi lafiya an kare ba garama ta huta kawai don da yanzu kuma wani abin ya faru rashin zuwan nata shine alheri.
Kallon Fadila kawata tayi tana fadin narasa gane irin halin Bantu fadila ko kecewa baki taba ganin bacin rai ko wani damuwa tare da ita kan abinda wani yai mata saidai kai kaji haushin hakan idan kana kusa.
Nabarsu fadila na fadin nasani nasan halinta ba mun zauna tare ba a saudiya ai a can ta sameni har muka dawo tare naje lokacin da sunan karatune amma haka aka barni ba karatu sai aikin gida da zaman gida har nagaji na dawo Nageria shine na fada karatun a nan yanzu.
Halinta daban yake nasani har nayi alwala nafito suna zancena dana Samira sallah na tayar na barsu sai kusan na idar fadila ta mike ta shiga bayi itama don ta dauro alwala lokacin.
Mun idar ne mukaji bell yana ringing ashe akwai intercoms ako ina gida fadilace tagane hakan ta nuna min na dauka daga kitchen ake sanar muna da abincin rana.
Akawo mukace don zasuci nikan sai dare zan dan saka wani abu a cikina nakeji suna gab da gamawane muna hira mukaji sallaman su mami mahaifiyar Abbas da Ammi hjy battula sun shigo da sauri na fada daki na dauko mayafi nafito nayi masu sannu da zuwa.
Bayan mun gaisa dasune suke fada min in shirya zamu tafi cikin gida watau family house din su Baahir ke nan mu gaida iyayyebshi hakan yasa na mike nashiga na shirya tsab na fito.
Mota biyu mukai amfani dashi harsu Hassana muka tafi gidan cike yake da jama,a dagani kowa na nan wai ashe meeting sukeyi har hjy lalai ta kawo karan mu wai Bashir na nuna masu tsageranci da yawa ba kansa bane faraun aure aida zai nuna basu suka haifeshi ba.
Ta kawo maganganu da dama wai yayi masu shine aka kirashi yazo aji dalilinsa nakin bin al,adan gida da akaiwa kowa amma dayazo kansa yaki yarda da hakan.
Kai tsaye yace dasu ra,ayinshine hakan abar ganin laifin kowa akansa shiya tsarawa kansa hakan sun san halinsa nan dai mahaifansa maza suka haushi da fada yana dan daga masu kafa sosai a daidai lokacin akaji sallaman mu mun shigo wata ke fadin Amaryance aka kawo ai gasu nan sunzo ma.
Bata so hakan ba don sai ga plan dinta ya rushe hakan yasa tafurta mai shu,umi ba tare da tasab kalman zai fito lokacin a bakinta ba ta fadi.
Gaskiya ba laifi haka mata ke fitowa daga dakunan gidan don suga amarya don wasu basu samu ganina da kyau ba a wajen dinner dakin matar kakansu muka sauka tsohuwa mai haba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login