Showing 219001 words to 222000 words out of 347556 words

Chapter 74 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8779

lokacin bata kai karshen zarginta ba ta hango dan nata daya ya tsame hannunsa yana kokarin wankewa da ruwan wanke hannun da aka aje masu a gefe daya don hakan.
Dana Bashir ya hakan kuma bakaci ya kai loma biyar ba kana kokarin wanke hannuwanka kuma ko abincin ne bai maka ba a girkama wani ta tambayeshi .
Kai ya dago yana dan sake dariyan yake a fuskanshi yaci gaba da wanke hannun yana fadin na koshine mami amma abincin yayi dadi sosai kuwa.
Tunfa zaman ku wurin nan nake karatun yanayinka kamar kana cikin damuwa ko bacin rai a yadda na karance ka a yanzu.
Don hakane nake fadin kayi aure ko yaushe dan zama da iyali a kusa yana gushewa mutum wani bakin ciki ko tunane .
Yayinda hankalin mutum ya karkata gana iyalisa zaifi bada muhinmamci sosai akan hatkokin iyali wanda hakan ke dan saka rayuwa cikin shagaltuwa ga bawa.
Good mami kin tabo min zancen da nake son ayi ke nan a yanzu dama don wallahi bawan Allah nan da kike gani har,,,,,,
Dakata fadin abinda yayi niyar fada a lokacin yayi saboda kallon da hjyn nasa ta watsa mashi lokaci guda tace gori zakai mai don kaga kana da yaya biyu yanzu kome ?
Jin abinda ta fada yasa ya dan sauke murmushi a fuskanshi yana fadin fada mashi dai mami don yanzu gani yake shifa ya girmeni tako ina.
To bashir aikaine din da antabo ma zancen aure saika birkicewa mutane da tuni kaima kayi auren nan ka fita sahun kwatance hakana ni dai har kullun tunina dayane shine dan rayuwan nan da kuke gani na dan lokaci kalilan ne duniya ba matabbata bace a wurin bawa.
Kai ya dukar kasa yana tunane don zancenta ke nan ko yaushe idan sun hadu don tayi lalashi tayi wa,azi amma kamar tana zance da dutsene ko wani lokaci.
Allah ya gani yadda take son danta Abbas haka take son shima Bashir din tun lokacin daya fara shigowa rayuwan dansu lokacin suna federal government college a tare.
Idan an samu hutun meet time tare suke zuwa gida weekend dashi haka donjin dadin gidan da yakeyi yasa ko hutu aka samu sai ya tsaya nan yace a nan zaiyi hutu saita kaishi har gun iyayyen shi da kanta.
Har yakai sungane akwai matsala suna barinshi a nan yayi hutu tare da dan nasu Abbas don sun auna hankalin yaron sum fahinci baida wani matsala ko illa a rayuwan sa da zasuji tsaro kada ya gurbata masu yaro dashi.
Da haka ya zama tankar dan gidan a yanzu kowa nasu yasan Bashir shima yasansu sai hakan ya zamo zumunci a tsakaninsu mai karfi.
Amma mami da kibani dama inyi magana Abbas ya fada lokaci daya duk suka kallosa yace mami ai yanzu kam saidai ku kara da addua da kuma tsawatawa don yana da wace zai aura.
Wani kallon mamaki yayiwa Abbas din yace kwarai don akwai wata yarinya yar nan cikin kaduna da Allah ya hadashi da ita kuma har mahaifinta ya furta koda bayan ransa ya amince da aurenshi da ita .
Yanzu haka nasan bawan Allah nan ta bangaren mu yake jira yaji amma kinga wanan mai kaifin tsiya ya cije ko zancen bai tabayi ba tun wanan ranan.
Saidai ni ina iya kokarina a kai don na fahinci yarinyar itace ta dacw dashi don hankali da hakkuri da sanin ya kamata ga kuma kamun kai a tare da ita.
To indai hakane Alhamdullahi yar gidan waye a garin nan ita yarinyar da sauri Abbas din yace a,a mami ba yar kowa bace don ubanta irin tallakawan nan ne masu neman abin yau dana gobe da zasu saka a bakinsu.
Shine ya taimakawa uban ya dauki nauyinsa zuwa asibiti ita kuma yarinyar anan ABU zaria take karatu yanzu haka tana wajen service din ta ma,ana dai ta kammala karatun ta ke nan.
Kinga asa lokacin ki fadawa Daddy aje aga iyayyenta a sulhunta ayi maganan aure shike nan kinji halin da ake ciki kuma na tab,,,,,,
Dakata Abbas a yadda kake zancen kan nan kana nufin ayi masa dole ke nan kome don na fahinci kamar shi baima san da zancen nan ba gaskiya a yadda ya nuna.
Kai kuma kana bayanin cewa ya kyautatawa mahaifin yaji dadi ya dauki yarsa ya basa shine kakeson a duba ayi wani abu akai kada a watsawa mutumin kasa a ido ko ?
Baki fahinceni ba mami asali fa ta dalilin Bashir muka san yarinyar nan don shima yana da ra,ayi a kanta kawai dai halinsa bai bari ya nuna hakan a fili.
Hjyn ta juyo ta kalli bashir din yace kwarai mami amma saiya fake ga sunan yana tausayinta yana kula al,amarinta sosai kowa yasan da wanan a cikin mu har yakai mahaifinta baida lafiya ya daukeshi zuwa asibitin Abuja yayi jinya a can.
Mami za,ace kuma kamar ana son masa cushe a nan tashi sallon soyayyance haka dai shiyasa na kawo wanan zancen a gabanki kuma gabansa don kada ki dauka ina son masa wani sherine baisan da zancen ba ya sani gashi nan ki tambayeshi.
Kallon Bashir din tayi da sauri ya dukar da kai sai Abbas din yace kingani ba mami na fada maki yasan da wanan zancen don ya jima yana dakon soyayyan yarinyar nan amma ya kasa furta hakan har Allah ya nufa mahaifinta yakai ga furta hakan saboda yasan dawainiyar da yakewa yarinyar.
Sake kallo Abbas din yayi ya bude baki zaiyi magana uwar tace dakata Bashir dama irin hakan nake son ji a gareka yasa ban matsa maka ba nasan matarce Allah bai hadaku ba a lokaci.
Yanzu ko Alhamdullahi tunda naji zan sanar da Alh idan ya dawo sai ya samu sarki aje aga iyayyen yarinyar aji a saka rana nagaji da ganin ka haka bashir mutane na maka kallon banza suna jifanka da kalma marasa dadi a rayuwanka.
Shiru yayi ya kasa magana Abbas din ya samu fadin nasan zakuji dadin wanan yarinyar sosai wallahi don a gaskiya saida ya garje ya natsu Allah ya zabo masa wace zata iya daukan kwaran dinshi .
Duka yakaiwa Abbas din bashiri don yadda yake jin zuciyar shi a lokacin don me Abbas zai fadawa mami wanan zancen a yanzu bayan yasan bai furta ko nuna alaman hakan ba akanta.
Bayan yasan kalman da mami da mahaifinshi ke zaman jiran ji ke nam gareshi a kullun ko yau din nan saida sarki yayi mai wanan magana na aje iyali yace dashi da dan sauran lokaci adai kara bashi dan lokaci har ya samu natsuwa.
Meye a cikin aure banda fitina da nauyi shi yaushe yake da lokacin wata mace macan da har zai masa wanan sherin haka a gabansa duban yadda mami ke farin ciki tana saka masu albarka tare da fatan alheri yasa yaja bakinsa yai shiru a lokacin.
Rashin Alh a gida lokacin yasa sukayiwa hjy sallama suka fito daga gidan don zuwa gidajensu su kwana a can duban Abbas din da tun fitiwansu ba wanda yaiwa juna magana a lokacin.
Yace what's the time now dan iska ya furzu kafin ya daga yace to nine yanzu dare baiyiwani sosai ba ai OK zamu iya zuwa mu duba bawan Allah nan ai kalloshi cikin basarwa.
Duk da Abbas din ya ganewa yake nufi amma saiya basar yake tambayanshi wake nan fa cikin yanayin dan kalloshi yana fadin wake nan fa ?
Wanda ka makala min nauyisa a yanzu ohhoo kace min surukinmu mana our in law amma kace min wani bawan Allah can duk da bawan Allah din ne amma ya kamata a wurin ka harshen ka ya tausasa kiran sunnan sa a yanzu.
Irin baba ko mahaifin matana ko malam baban wance din nan aizaifi amma malam ka fake da wani fadin bawan Allah bayin Allah nawa na sani a karkashin kani ?.
Zaka gama don kamaka zanyi kayi da kyau lokacin kane yanzu amma kasan banda time din wata mace a rayuwana gaba daya yanzu ?
Zakayi ya fada yana masa dariya a daidai lokacin daya dauki round din da zai sadashi da gidan namu bai tsaya ba sai kofan gidan mu shima baisan an iso ba ya daiga motan ta tsaya a gaban dan gidan namu mai dauke da mutane al,bidadin a cikinsa.
Don su suna ganin wai baba ya auri mata da yawa ko wace kuma tana haihuwa a cikinsu an tarawa baba sin yaya nauyin hakan yai masa yawa a yanzu.
Basu san wanan bai taba damun malam bashaushe ba a haka ake rayuwan cikin ikon Allah kuma ubangiji yana rufa asiri ta hanyoyi da dama.
Sunyi mamakin ganin gidan a duhu gako wani layi da wuta layin Nura ya kira ashe yana zaune wurin isah suna hira a lokacin sunga tsayawan motan kofan gidanmu Abbas din na kiransa ya taso don yana da layinsa dan zaman su jinyar baba da sukayi Abuja.
Kana ina gamu kofan gidan ku yanzu yace au kunw kuka tsaya da mota ashe ya taso zuwa wajen su shima Abbas din ya fara dan waige waige yaga inda zai fito sai gashi gabansu.
Nura yana masu sannu da zuwa Abbas na fadin malam Nura ya naga kamar baku da wuta wasu gidaje da wuta haka yake fadin wallahi mun kwana biyu gidan nan bamu da wuta hakana muke a cikin duhu.
Subbanallahi ya akai haka ita Fatima tasani sai Nura din ya danyi dariya yace ta sani mana ya zatayi abubuwa sun mata yawa aka ba karamin kokari take a gidan nan ba damu.
Wai nace ko baba nanan mun shigo gari mukazo mu dubashi don sammako zamuyi gobe mu koma kaduna Boss ya fada cikin katsesu.
Yana nan yanzun nan ma suka shiga gida bari nayi maku iso a gunsa har ya juya zai shiga sai kuma ya juyo yana fadin son Allah kuyi hakkuri ko gaisawa bamuyi ba mun shiga zance No ba komai jeka kawai ya fada.
Wanan karon baba din ya dan dogara ya fito da taimakon Nura suna hangoshi da sauri suka karasa Oga Abbas ya fara zubewa shima ya bisa yayi yadda yayi din suna fadin ai da ka bari mun shigo baba da baka fito ba.
Yace ina yana fada min kune nace ya kamani mu taso muzo ya jasu zuwa dan dakalin zamanshi na kofan gidan mu yana masu iso dasu zauna akai don Allah duhune a wajen kuyi hakkuri tunda muka dawo babu wuta a gidan nan wallahi.
Sun tambayi lafiyasa da kuma karfin jiki kafin suyi mai alheri su tafi yayin da mamake cikin gida tana fada da Nura dataji cewa sune sukazo har sun tafi kuma tana fadin wanan ai sherine da bakin ciki.
Ka bari su shigo mu ghana sai kai wani jan malam zuwa waje don sheri dariya sosai kowa ya kwashe dashi gidan lokaci guda don sun gane me take nufi da wanan fadan.
Don sani megidan yana gida yasa na wuni a daki ga kuma na fahinci Samira kota manta waye tana sin nuna min rawan kai ita adole ga mai miji yasa na kama kaina amma duk da hakan da yamma saida yasa na fito falo muka dan taba hira duk a kage nake don yawan kallon da yake min din da sunan yana jana da hiran baya zaman mu nada dasu.
Dawowan Wasila gida da naga ta dan shiga yanayin firgici yasa na mike na koma daki don ganina bai hana shi fara ci mata mutunci ba a lokacin Samira na kitchen tana aiki.
Ban kara fitowa ba sai washegari da zan wuce na shirya tsab wasu wando da riga na saka wandon farine sol na mata sai bakar riga mai dogon hannu da dan fadi tare da wasu aninaiya manya a gefen hangun rigar.
Na kawo bakin hula na dora a kai mekyau da dan ribon dinsa sai half sunna dan fari da takalma masu tsini boot na mata farare masu kyau gaske.
Nikaina nasan shigar yai min kyau sosai ga kamshi na tashi mai dadi a jikina da yake tashi Samira na shigowa ta kalleni sai ta hade rai tamau tana fadin wanan shiga haka aikin saje da arnan.
Nace ai garinsu nazo kinga dole mu saje dasu amma ke kinsan akwai bambamci ko goshina kika kalla balle shiga ta wace kafira ke shiga haka ko a arewa sai ta danyi murmushi.
Wai in kin shirya ki fito yana jiran ki ta fada tana wani daurewa yan mata nufinki ke nan nikan ya tafi zan hau taxi in karasa na fada mata ba kunya naga ta juya ta fita zuwa wajenshi.
Sai gata ta dawo tana cicika tace wai yace baison shegantaka ki fito ya saukeki ni kinja min zagi a banza wajensa ta zauna mikewa nayi da jawo dan troler na nakayana ina fadin to nikan sai gani na biyu kuma zan tafi ke nan.
Lokacin ta dago ta kalloni tana fadin wai tafiyan ke nan nace ai kinsan Camp zamu shiga ba zancen fitowa garemu kuma zai zama min wahala hakan.
Wani ajiyan zuciya ta sauke yanzu na kara gaskanta manufar Samira din watau a takaice dai tana cikin wani hali zuwana gidansu din tun bayan dawowan mijin nasu ke nan.
Don ance labarin zuciya a tambayi fuska don hakama nake son zama a camp din in badon baba ba daya matsamin wallahi da saidai suji labarin cewa ai nazo garin daga baya.
A falo na sameshi zaune tana bayana tunda yaji fitowana ya dago kai ya kallo inda nake gaidashi nayi da kwana ina kokarin ajw yar jakata na nufi part din wasila don muyi sallama.
Abin mamaki tana kwance ta kifa ciki da alama kuka takeyi a dakin nata lokacin na gaisa da ita sama sama nake fada mata zan shiga camp sai wata rana ke nan na fido da kudi nace a sayawa baby alawa don Allah idan ta dawo nace na kuma gode da kokarin ku gareni duk da nasan batayi min komai ba amma ai gidansu nazo.
A nan inda na barsu na dawo na samesu a tsartsaye saidai kowa fuska a daure na duka zan dauki jakata yace barshi ta daukar maki mana da sauri na dago ina fadin haba yaya antynace fa ko banza.
Na sungumi jakata nikan na fara yin gaba ban tsaya ba sai bakin motan tun fitowanshi ya danna ta bude hakan yasa da sauri na bude baya na jefa jakkar na zagaya zan shiga dayan gefen yace ni zan zama driverki ko ?
Na juyo na dan kalloshi dole na bude gaban mota na zauna ya zagaya ya shiga sao lokacin na kula da Wasila ashe ta fito itama muka harba saman titi.
Saida ya hau titi da kyau naji yace they are all stupid ace mace bata san kanta ba sai halin jakkai ina regret din aurensu dukkansu wallahi ba abin haushi kamar Samira banda kishin tsiya bata iya komai ba banyi expecting dinta haka ba wallahi.
Banyi magana ba shiru nayi kamar ban cikin moton don ko hakkuri banyi gigin basa ba a lokacin duk ko da iye iyen dana iya wanan karon shiru nayi har ya gama banyi magana ba don nagane mekw gudana a gidan dama.
Mun isa bakin Camp din na dauka a get zai ajeni amma sai naga ya shiga ciki dani har inda ake registration saida na kammala komai ya bar wajen yayi min gata irin na dan Nageria.
Kai Allah mungodema mun godewa iyayyenmu kuma Abbas ya fada daga gefe duk da yasan ba zai kulashi ba amma yaci gaba da fadin don Allah ka duba yadda bawan Allah nan yakw rayuwa a wahale ga ciwo gata da kula yake bukata a yanzu amma babu shi.
Har lokacin bai samu bashi amsa ba sai faman duba waya da yakeyi a lokacin wanda hasken wayan ya dan haska fuskanshi a cikin duhun daren .
Yana ganin sun isa ya sauka daga cikin motan bai tsaya wani zance ba yasa kai ya shige cikin ya bar Abbas din a nan donji yake a ranan kamar ya shake Abbas din don haka yake jin haushin duk wani abinda Abbas din yayi a lokacin.
Shima bai tsaya kulasa ba yaja mota zuwa nasa gidan don a gajiye yake sosai a lokacin don dan wanan zirga zirgan da sukayi yinin ranan.
Yana shiga wanka ya fara yi ya samu wuri ya kwanta don ya huta amma kuma sai barci ya gagareshi saboda tunanen daya addabi zuciyarshi a lokacin.
Ba abinda yake tunowa a ransa kamar yadda ya samu mahaifinshi a yau don yasan tsufa da kuma ciwo yasashi a gaba yanzu kan ga kuma nauyin jama,an gari dake kansa kuma.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
7?? 0??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login