Showing 258001 words to 261000 words out of 347556 words

Chapter 87 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8767

don iyayyena basu da gata kake son ya fara dani idan kun gwada wani abu ya faru dani ya faru da banza ?
Wa,iyazu billahi kada muyi hakan dake don Allah wanan fa ina fada makine don kisan da zancen sherin da zai biyo baya don suda sukazo wasu zasu dawo daga baya da zancen nan na karya akanshi don hakana fada maki.
Ki yarda dani ba abinda zai sameki amma ba zaki gane komai ba sai nan gaba sannu a hankali zaki fahinci manufata .
Saida na kwantar da hankali da kyau nasan ke zaki dace da komai don haka kada ki fahinceni ta baibai don kina da ilimin ki gwargwado na addini zaki iya bawa Allah zabi ki gani kan abindana fada maki yanzun din idan hakinsane hakan.
Mun dai kashe wayan ya barni cikin tunane na rasa wanda zan fadawa wanan zancen ga iyayyena sai shirin karban lefe sukeyi hankalinsu kwance ba wani tunane a tare dasu.
Ganin mutane a dakin nawa yasa na koma kuryan mama uwa na kwanta ina faman tunane karshe dai naga ya dace in fada masu ko za a dakatar dasu sai anyi bincike.
Amira diyan mama uwa na tura ta kira min mahaifiyar ta tazo ta sameni nace magana zanyi daku mama amma sai kin kira Ammi a nan zan fada.
Har takai kofa ta juyo tana fadin lafiya dai ko ba wani matsala aka samu dai ko nace to kusan hakan amma bari Ammi tazo zakiji ai na fada ta juya ta fita da sauri basu jima ba sai gasu tare sun dawo.
Har lokacin ina ganin tashin hankali ga idanunta zama Ammi tayi a kusa dani tana fadin Fadimatu meke faruwa mamanki tazo ta kirani hankali tashe.
Ammi akwai matsalane fa babba don dazun abokinshi din nan ne ya kira nan dai na fada masu yadda mukayi dashi har mama uwa ta fara fadin umm,umm lalai akwai matsala babba kuwa.
Sai naji Ammi tace babu wani matsla a tunanen ki zan yarda na badake aure ba tare da nayi binke ba ina matsayin matar malamai kafin na tako garin nan saida nayi tsuyuwan dare a kanki naga komai insha Allahu aurenki da bawan Allah nan alherine babba kuwa.
Don ko malam da kansa nasaka yayi muna ya kuma bincika shima ya sheda min akwai alheri sosai a cikin lamarin dama duk kana wani abu a duniyan nan sai an dabama tabo da baya kankaruwa gareka sai dai Allah.
Nan sukai ta zancensu ban dai kara tankawa ba a lokacin don ba abinda zan fada tunda naga iyayye su raja,a akan hakan ni yanzu kuma bandana cewa a kaina sai abinda Allah yayi dani.
Ba zan kirani wata mai yawan ibada bacan amma dai ina dan kwatantawa iya karfi na iya yadda zan iya ban yarda na tabe ga baki daya ba irin dai zikirin astangafurllah,hailala,salatin Annabi da dai sauransu nakan daiyi daidai gwargwargodo.
Ko yanzun ma din bayan fitan su mama shinake karantowa hassana na turawa kudi ta sayo duk wani abinda ya dace haka sukaita aiki da yamma kuma mama uwa ta aikawa makwabta suzo taron lefe da shadayan safe.
Nura dasu Hassana sukai tsaye suka gyara gidan mu tsab komai da za a bukata ansaye an tara a dakunan su mama shadaya din kuwa mukaji isowan su kofan gidan don dirin motocin da suka packer a lokaci guda.
Ba gidan muba ko unguwar a dai dan takin mu dn nan na talakawan unguwa manyan mata masu fada aji basu taba shigowa haka ba.
Duk da gyaran da akaiwa gidan mu amma wasunsu sai yatsune fuska sukeyi kamar suna jin kyama banima gidan namuni tun safe ina gidan su hjy balaraba kwance ina barci.
An taresu yadda ya dace sun kuma gabatar da kayansu dama Ammi ta jawa kowa kunne kada wata ta yarda don Allah tai abinda zasu rainasu.
Yadda sukazo a taresu a watse lafiya sai sun tafi za ai duk wani abinda za ayi amma duk da hakan saida anty Altine taso ta bada mutane nan take su hassana suka taka mata burki a gaban mutane.
Don cewa tayi a,a lalai Bantu kan dole a lake don angaci su kuma suka amsa da kin daiga bakin mu a zaune idan zaki zancen wata don Allah ki bari mu sallami bakin mu.
Nan su Usaina din cikin halin dattako suma suka fara fito da kayan da aka tanadar masu suka zube a gabansu sai mamin Abbas ce tace to ga kayan dana sun shigo gidan ku da fatan zaku karba da farin ciki.
Ku ban sarakuwana nan bada jimawa don bamu son a dauki wani lokaci mai tsawo don azumi dake gabatowa dana ya gaji da Azumi gwauro.
Aka dan wasance tsakaninsu dasu Ammi dasu ummah hauwa nan aka kwashi kayan aka kai masu waje son haka al,adan ya koma yanzu ku kawo a kai maku kuma duk ko da rashi kudin nan da kasa ke ciki.
Amma haka iyayye ke nuna bajintansu wajen fitar da yayansu kunya ako wani bangare gidan miji suyi gidan amaryama su mayar masu komai kankanta wani a yaba wani yazama abin gulma a tsakaninsu.
Nikan ba laifi don muna da labarin masu zuwa din haka kuwa muka fitar da kudi akai masu sayayya na ban girma aka basu a matsayin tukwaici sai kudin samane mamin Abbas din tayi tsaye sukaki karba sukace wanan din ma ya isa koshi da sunsan za,ayi da sunce a barshi don abin ya zama riya.
Guda kan mama uwa tayi kamar ba gobe su kuma sukayi mata kari suka fita ana farin ciki a kofan maman biyu aka shmfida tabarma nan aka aje kayan.
Anyaba sosai an karasawa
albarka makwabta an bisu da dan take away da aka shirya donsu kowa ya tafi yana fadan abinda ya gani a lokacin.
Masu yabo suna yabo masu tofawa suna tofa abinda zasu tofa sujawa kansu nauyin sekeli don haka mutane suke da daukarwa kansu zunubi jan abinda bai shafesu ba.


Don Allah ayi hakkuri nagaji ne ban samu karasawa ba


ZAINAB IDRIS MAKAWA
KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
8?? 2??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Wani tsuki taja tana kawar da kai gefe daya tare da fadin nikan nasani ba wani mutumin arziki da zai dauki danshi yaba wanan miskilin da sunan aure.
Nina zata gidan wani minister ko director ko wani basarake ko wani attajirin dan kasuwa haka ke kodai wani mai fada aji a kasan nan zamu kawo kayan sai inzo inga wanan gidan mai tarkace marasa tarbiya.
Aure ba inda baya kai bawansa walau mace kuwa ko namiji meye laifin wanan gidan gidane na mutanen da suka san ciwon kansu tunda antaremu cikin mutunci da girmamawa da alama sun san darajan dan adam sosao dama abinda ake nema ke nan don suma dai basu da kasawa da gani alama ya nuna hakan.
Ga kuma alaman sanin kai mutanen masu addinine da mutunci da iya karama bako nikan gidan sun min gaskiya mami da suka manta tana cikin motan ta fadi hakan daga can baya inda take zaune.
Dama don haka tace mota daya zata shiga da mutanen gidansu Bashir din gashi ko zarginta ya fara zama gaskiya hjy Asabece ta gyara zancen don sanin ya yake da mami din tace.
Koma wasu irine shiya daukowa kansa shi kuma zai zauna da abinsa mu namu idda sunna mun koma zo tunda har munyi albarkan da za a tuna damu munyi amfani ke nan.
Ba wanan motar ba duk sauran motocin tafiyan sai gulman hakan sukeyi alhalin mami ta soka mutanen ta cikin kowani mota da sunan ba waje a wurinta.
Stil gidanta aka koma duk sa basa so amma dole suzo tunda mazajensu sun umurcesu da zuwa din bayan hakan suma kuma gulma na cinsu kada a basu labarin daba daidai ba gara suzo sugani da idanunsu yafi.
Wasu matan unguwar mami tasa suka raba kayan da aka samo din suka kai masu nasu a mota su kuma suka dauki na bangarensu data hau a yanzu watau fannin uwa ke nan don kowa ya ya gama sanin itace uwarshi a yanzu din.
Don ta dauki girman dasu matan ubansa da gwaggwaninsa suka kasa dauka a gareshi tun yana karami sai yanzune suke cizon yatsa ga lamarin don shi bai yarda a bar mami din a bayan duk wani sha,aninsa ba.
Sunga hakan tun wajen wani taro nasa na gudanar da company daya gayyaci yan uwa da abokan arziki taro na alfarma amma mamice suka tsaya a matsayin iyayyensa komai da akayi da turawan da sukazo mami da mijinta yake gabatarwa a wajen.
Hakama sauran kayan aure da yake aikawa itace ke jagorantan tawagan gata indai sarautane sun san ta gajeshi gaba da bayanta don ba bace take ba daga ita har mijinta din.
Kai idan akace maku mace hamshakiyace kada ki kara koki rage shadancine a cikin wanan kalman na sunan hamshakiya din don sai kin zama shu,uma mai zaman kanki ake nada maki wanan sunan .
Ire irensu ne a gidan baffanan Bashir din masu ji da kai da daukan duniya matabbata a garesu ba a tunanen mutuwa sai in ya fada kan wata za a dan tuna duniya ba matabbata bace a wajensu.
Ayi dan jimame na dan kwanaki a koma ruwa a dora a inda aka tsaya ba abinda ya damesu asiri kuwa ko ba mijin ku daya ba zaki jefi duk wace ke son ta kawo maki wuce wuri a cikin karkashin kasa ta kasa gaba da baya a rayuwanta.
Daki mami din ta shiga don tayi sallah bayan wucewansu bayan ta idarne ta dauki wayan dake ringing a gefenta Abbas dantane a layin suka gaisa kafin yayi magana ta rigashi fadin Abbas mun kai tun dazun mun dawo har kowa ya watse zuwa gidansa ai.
Mutanen arziki masu karamci sun yaba sosai sunyi godiya sun nuna jin dadin zuwan mu ba wani hayaniya suma sun muna shatara na arziki sosai wallahi.
Yace haba mami tace sosai kuwa mutanenka ai sun fara sukan gidan na taka masu burki haka motar da ya ghana take a ciki ita nan suka kwasa dasu a cikin motar gaskiya abu yayi kyau sosai wallahi.
Sai idan kun shigo kukawo min ita sarakuwan tawa na ganta akwai maganan da nake sonyi da ita kafin aure basu jaba da date din da mukaje masu dashi suma dai akwai wayayyu acikinsu sosai gaskiya.
Sundayi zance da mami din duk yana zaune yana jinsu kafin ita mami din tace dashi wai ina dan nawane ko baya kusa dakaine wai ta tambaya ?
Jin abinda ta fada yasa yadan gyara zama ya sauke hannunshi daya dafe goshinsa dashi yana fadi cikin sauri saurin magana dake cikin abinda baison yawan magana don mutane na fadin basu fahintarshi sosai idan yana magana saboda dan in inniyar da yake danyi a zancensa.
Ma?mii gani ina jinki ai ya fada ta yadda zata iya jinsa din na,ggode kwaraiii na?a gooode ta tareshi da fadin akul na sake jin godiyan nan a bakinka Bashir sai batama rai hakan yasa danyi dariya yana fadin tttuuu,ba nake maaamiiie.
Abbas ne ya kwashe da dariyan keta yana fadin mami ba dole yai maki godiya bai sani ba yaga ya kusa zama ango ko baba dole aiya gode maki.
Kallon Abbas din yayi ya kwace wayan ya kashe yana fadin kaikan Allah dai ya sauwaka mamin kake fadawa haka kai meyasa wanan kawai yadameka a aure koda yake ba laifinka bane laifin wanan figagar matar takace nai kama da chiwengun kowani lokaci kuna manne da juna kamar kaska da ita.
Au sherin da zakaiwa madam dina yanzu ke nan kuma ti bani waya in kirata in fada mata yau ka shigo layinta itama saita daina shigar maka yanzu.
Yace karyana fada ba hakan bane shiyasa kuke zaton kowama hakane abinda zaiwa aure ke nan kai baka ganewa kanka kawai kasani shiyasa dan iska ya mike yabar masa office din ya fito waje.
Can saman su ta inda idan mutum ya tsaya zai iya hango Abuja har sakiyanta ya dinga shakan yanayi har iska tana dan kadashi a hanka ya fado tunanen lamarinsa yana tambayan kansa meye laifinsa wajen yan gidasune ?
Gashi har mami ta kira tayi masu bayani amma su daga bangarenshi har zuwa lokacin ba wanda ya kirashi ya sanar dashi komai bai wuce kumacsun dauki laifin kayanda ya fito daga gidan mami din da suka gani ya jawo wanu tsegumi kuma yanzu.
Wancan karon sunce laifinsa ke nan yanzu ya basu kudi sun saya sukai Allah kadai yasan abinda zasu kai din ta wajensu nan kuma mami tayi nata bajinta ita da daddy sai kara masu kudi kawai yayi sun hada nasu laifen na alfarma dasuma zasu dashi wanda kuma yaji dadin hakan har kasan ransa.
Don shi mutanem sun masa komai arayuwa ta yadda ba zai taba mantawa da hakan ba a rayuwanshi asanadinsu har yazama wani abu a yau yake taka kasa sai yanzune yan uwa suka san dashi bayan sun gama tozartashi suna koranshi suna masa kazafin sata dana bin yayansu mata.
Ido ya lumshe a hankali yana tuno kalaman su akanshi don ba kake a fili hjy Laila tazo wata rana tasamesu gidan baba Amadu mijin hjyn saudiya take fadin nan kuma wanan annoban ya sauka maku ?
Nakan rasa irin zuciyanki hjy maryam da sai kisan abu kuma ki tsaya saiya cuta maki gaki da yara mata dare daya ya bisu ya lalata maki su ba yadda zakiyi kuwa ace kiyi hakkuri gidane ai.
Shiko duk da karantanshi ya dago yana fadin hjy yarwa nataba batawa a rayuwana nan tace yayi mata rashin kunya ta haushi da zagi ta uwa ta uba ta hada duk abubuwan da take ji game da yaron ta zageshi.
Saida wanan kanin hjy maryam din ya korashi waje ranan yayi kuka kamar ransa zaifita yana jin hjy maryam din nafadin ya zanyi laila maimartaba da kansa ya daukeshi ya kawo munashi gidan nan kinga aiba yadda na iya ke nan dashi.
Kada ki daukarwa kanki mataki sai yayi maku illan da ba magani ki nunawa mijinki kawai baki yarda da zamanshi nan ba a mayar dashi gida.
Wanan yasa hjyn saudiya ta dinga nuna masa jan ido ita tayi kaninta yayi saida ya gudu daga gidansu karshe da aka ganesa akadawo dashi shine mijinta ya tattaroshi ya dawo dashi gida.
A lokacin kakansa na cikin tsananin ciwon tsufa ba,a dadeba ya rasu ya barshi sai mahaifinsa ya kaishi barewa college karatu a nan suka hadu dashi Abbas din suka zama abokai.
Ya dade tsaye yana bin kayan da ido kafin ya girgiza kai yana fadin ke Usaina uwa ku kwashi kayan nan kukai dakin Fadimatu wa uwarta.
Saboda me za abawa uwarta hakan nace a mikawa uwarta koda wani magana bayan wanan ya fada yana kallonta ta fahinci akwai magana a bakinsa yasa ta kawar dakai gefe daya bata tanka masa ba.
Haka sukaita kwasan kayan suna kaiwa a cikin dakina nan suka gyara gefe daya suka loda kayan waje daya mama uwa ta dauko manyan zannuwan gado ta rufa masu wai don kura.
Tun ina gidan su hjy labari ya sameni na kayan set hudu masu kyau da tsada da daukan ido a cewansu su dai basu san irin akwatunan ba a nan gaskiya.
Sai yamma na shigo gidan inda na samu gidan namu ba kowa a waje kowa yana dakinsa shida yaransa sai mama Lanto a tsakar gida tana aikin girki na gaida ita da aiki na wuce dakina kai tsaye.
Da sallama na shiga nan na samu Ammi a kishingide tana jan tasbaha a hannunta muka shigo nida fadila da maryama da muka bari a bayan mu don ta tsaye sayen chewing gun shagon isa.
Muna gaida ita naga ta mike zaune alaman inzo wurinta tayi min da hannu da sauri na karasa wajen nata ta rugumoni a jikinta tana min yarensu na yan Somalia da banjin me take fadi amma na dau hannu adduane saboda sunnan Allah danaji tana fada a cikin bakinta lokacin.
Ga kuma Fadila dake tsaye bayana tana amsawa da amin hawaye ya fara zubo min daga idona yana dan gangarowa zuwa fuskana.
Kaina yana kasa duke na gurfana kamar me rokon gafara ita kuma ta dafa min baya tana adduan a haka mama uwa tashigo dakin ta samemu.
Taufa yata akewa addua haka ta fada tana karasa shigowa hakan baisa ta daina ba saida takai karshe tana fadin Alhamdullahi Alhamdullahi Allah kulli halin.
Amin Ammi mama uwa din ta fada tana kaiwa zaune don suma sun fara kiranta da Ammi din kamar yadda


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login