Showing 243001 words to 246000 words out of 347556 words

Chapter 82 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8778

Sai bayan sallah isha,ine da yake abincin har na dare mukayi miya kawai Maryamu ta sake yin wani wanda saidata shigo take fada min ai tana kitchen tana aikine.
Muryan Ammine ke kirana da Fadima kamar dai yadda babana kan kirani dashi hakan yasa nagane sunan ya samo asaline daga mahaifiyata kila itace ke kirana da Fadima din har baba ya samu bakinsa ya saba da hakan.
Kodana fito kayan abincine a gabanta take min nuni da nazo muci abinci harsu fadila suma suna falon sun soma cin nasu suna kallo a tv zama nayi ina fadin ba zan iya cin abinci kuma saidai da safe in Allah ya kaimu.
Kafin na mayar da hankali ga abinda suke kallo din muryan Ammice ya katsemu na kallon da take fadin ya akayine naji hira dazun tsakanin ki da mutanen ki ?
Dariya na danyi a lokacin ne ta fara fada min matsalolin dake tsakaninta dasu da yadda akai auren ko wacensu ta ban tausayi sosai kafin fadila tace yau ai ya ya burgeni yadda ya fada masu magana kai tsaye.
Nace dama wani lokacin matsalan daga mazan ne saidai shu,umar mace akwai wuyan sha,ani da ita sun manta da kece kika haifi abinki a yanzu sun fiki mulki dasu ke nan.
Anty Fatima ai yau ba karamin burgeni kikayi ba lokacin da kike ja masu ayya din nan wai magana taso dasa maki a nan sai tayi sara akan gaba.
Wanan kamar halintane hakan yadda na fahinta don koda yan uwan haka take sako masu magana duk yadda yazo mata a rai bata duban munin abinda zata fada din.
Mun jima a wajen muna hiran matan yayyun nawa inda kowa ya fahinci dalilin sakewansu dani har suna fadin ashe zasu san kaduna zasu bukina insha Allahu.
Jin hakan Ammi tace wa zai tafi dasu yadda basu da kunyan nan su dai zauna a gidajensu ba zan tafi da kowa a cikinsu ba tausayi Ammi din ke ban don da gani abin yana damunta a zuciyarta.
Mun dan jima nikan na gaji na mike nashige daki naje na kwanta ban jima ba barci ya daukeni sai washe gari ko sallah da kyat na tashi nayisa ban kwanta ba na fito na gyara falo har zuwa wajen ammi din na gyaro ko ina.
Duk yan part din suna barci a lokacin ba wanda ya tashi dana gama kuma na shiga nayi wanka na saka tufafi nakoma na kwanta sai barci don haka koda suka tashi suna nasu aikin ni kuma ina barci.
Aruyawana karyane naje bakunta na nuna son jiki har azo a gaji dani don hakane ko yayane nakan bada karfina na dan taimakawa wanda naje wurinsa don hakanema da naje gidan Samira ban zauna ba,
Sai ita kuma don sheri sai kawai ta lauyeni ta canza zancen kan cewa wai nazo ina aon zaman bamza da mijinta ni yadda na tsani ya habibi kan yayansa yanzu don rashin kulawan da baya basu.
Yara sun koma kamar duk da uwa da uba suka rasa ji yadda ya mahmud suka shigo jiya yaransa tsab dasu matar tana gyaran abinta sosai ga kuma yaran da kyau sosai gaskiya.
Bayan kamar kwana biyar da yin hakan ranan tun safe nagama abinda nakeyi ina barci naji dadin barci sosai a lokacin don gaskiya zamana gidan Ammi ina samun hutu sosai nake gani fiye da ko ina dana zauna.
Can cikin barcin nake jin ana tayar dani muryan Fadilace ke fadin tashi kinyi baki Anty a hankali nake bude idona don ina jin zancenta kamar a mafalki a kunnuwana lokacin.
Na bude idanu tare da jin haushin katse min barcin da tayi din don na daukama don zamu fitane yasa ta tayar dani a lokacin.
Muryantane ta kara maimaitawa tana fadin kinyi baki yanzun malam karami ya shigo yana fadin kina da baki a waje shine Ammi tace nazo na fada maki.
Baki na fada cikin mamaki kafin nace mata ko maza don ni dai inba yan gidan mu zasu biyoni nan ba ban kawo kowa zai iya zuwa nan din ba ayanzu don ni.
Tace kamar mazane fa yace don ummi ta tambayeshi yace mazane sunce wajen ki sukazo kuma zaune nakai ina mamaki tare da fadin maza kuma wajena fa ko babanane na fada ina tashi tsaye a lokaci guda.
Zata fita na kara fadin suna kuma kofan gidan nan tace eh amma ina ganin an bude masu falon baba don yanzu ya shigo ya diba masu ruwan alwala zasuyi sallah.
Na mike ina mamaki a kasan zuciya cewan waye kuma ko dai ba gurina akazo ba sunane kawai yai kama da nawa din suka dauka cewa nice haka na shirya sama sama ina tunane na nufi kofan gida inda zanga ko suwaye ke min sallama din.


ZAINAB IDRIS MAKAWA




????????
7?? 7??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Hauka kayine kake dariya kai kadai ya kara murmusawa yana gyara zama yace kalau nake da amaryanka nake charting yau ta hau online.
Fuska ya daure lokaci gudu don yaga Abbas din yana son yaja mashi raini da wullakanci daga hakan bai kara furta komai ba kowa yayi shiru a garden din yana abinda yafi sauki.
Kagane dolefa sai munje garin nan kafin yarinyar nan ta dawo shiru yayi yana ci gaba da danna computer dinshi Abbas din yace bakaji bane wai jin hakan yasa ya dago kanshi yace ehh.
Cewa nayi sai munkai kafarmu yobe din nan kafin yarinyar nan ta dawo kaidawa ke nan kai mana ya fada yana wani irin dariyan shakiyanci.
Amma baka da hankali yace kwarai ai shiyasa nace sai mun tafi son ko bamuje yanzu ba dole zamu tafi nan da dan wani lokaci mu kai gaisuwanmu kagako gara mu tafi tun tanacan musan waje kuma a san mu.
Mene wai kana nufin in dauki kafata daga nan har zuwa yobe hauka kayine kai nifa kai naga kana wani zagewa a cikin zancen nan naka kuma ka riga daka daureni a wajen mami ba yadda na iyane.
Nasani amma kada ka manta har bauchi muke dakai lokacin da zan auri Hamida sai yanzune zakace ba zakaje yobe ba to barin fadawa mami abinda ke faruwa wata kila idan tayi ma magana zaka tafi.
Kai banzane wallahi wani lokaci saika dinga yin abu kamar karamin yaro kafadawa mami don ranta ya baci ko don me ?
A to ya kake son nayi tunda kana kokarin nuna kai ba zaka ba yanzu ya dan dago ya kalloshi yace wallahi dako kasan halina idan mami tasan zancen nan .
Waini ka auri yarinyar nan mana idan sonta kakeyi ka daina lika min ita hakana na kula itama kanta yarinyar bata dauki zancen nan serious kamar yadda kai ka dauka ba kaike wahalan banzan ka kawai.
Ehh dama nasani shiyasa na nace da ita din don kalar matan data dace dakai ke nan bata da zalama ko saka ido balle ku samu matsala a tsakanin ku itace daidai dakai kuma kai ka zabo abinka Allah ya hadaku kuma a hakana shi abin Allah yawa gareshi.
Kada ka damu abokina zakayi alfahari da hakan nan gaba kadan don da alama yarinyar nan zata dawoma da farin cikinka in sha Allahu.
Lokacin ya kara dagowa yana fadin na fadama banda farin ciki a yanzune ko me ko munyi dakai hakan is OK please yanzu yaushe zamuje mu sameta mu kai gaisuwa a can.
Kamar idonshi zai fado kafin ya juya yana jan tsuki yace duk lokacin daka saka rana before Friday don kasan zanyi tafiya a ranan nasan jira kake in fadi wani abin kakai karana ga mami yanzu to kayi picksing din date mu tafi ina shike nan ko ?
Ya dubi time ya daga zuwa wajen famfo don ya daura alwala don magariba dayaga ya gabato a lokacin yana kuma maijin kuna da zafin abokin nasa a zuciyarshi.
Wanan ne yasa sukai tafiyan dana gansu kwatsam a gashuwa lokacin na bazata don ban yarda su bane saboda zuciyanama bai kawo min cewa su din bane na daifi saka rai ga baba ko su yaya Ahmed da Nura a lokacin.
Kodana leko mota kawai nagani a wajen malam karami dan kishiyar Ammine ya dago yana fadin gasu can a masallaci suna sallah dama na fadi ai kedin babbace tunda naga kowama naki kulawa a gidan nan ko yaushe kina daki kwance.
Kallonsa nayi kafin nayi magana Oga Abbas na hango ya fito daga cikin masalacin yana goge goshinsa da hannu yana kuma kokarin saka takalman shi ya dan duka.
Gabanane yayi wani irin mumunan faduwa lokaci guda Oga Abbas ya biyoni har wanan garin take naji wani irin rashin sukuni ya lulubeni lokaci guda.
Don hango Boss din mu da nayi a bayanshi yana gyara masa nasa takalaman yana kokarin tura abu a cikin aljihunsa na gaba jikinsa saye da wata shadda dark milk colour haka dinkin kayan na matasa akaiwa yadin shada da ya dan fito masa da suransa a fili zan iya cewa yauce na fara ganinsh??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????i cikin kaya na gargajiya yasa a jikinshi.
Mesukazo yi na tambayi kaina lokaci guda naga malam ya barni ya nufesu yana faman washe baki a garesu bansan me yake fada masu ba na daiga ya nuna masu hanyar kwatan bakin ruwan garin da hannu duk suka daga kai suna kallon wurin.
Audi driver wanda kan kaini gida wani lokaci shine ya fito daga karshe a cikin motan ina tsaye imani ya kashe min zuciyana abinda ya fado min a raina shine watau tambayan da Oga Abbas yai min da kamar wasa shine ya kawosu har inda nake ban sani ba haka.
Watau babba dai babbane ko yaushe idan mutum ya girmeka yafika wayau ko ya kake da wayaun kuwa sai ya nuna ya fika a hankali naja baya na koma cikin gida ina shiga a daidai lokacin da na shiga na samu Ammi tsaye ana shirya masu abinsha.
Kallon mamaki na bisu dashi ganin irin rawan jikin da Ammi din keyi a lokacin duk da bata san kosuwaye ba uwa ke nan da matan gidan mune a lokacin Allah Allah sukeyi kawai a miko masu dumus yanzu ko ga Ammi kokarin ta fitar dani kunya takeyi a nata azancin.
Shiyasa tun ganin ammi din ban dauketa a matsayin yar uwa ba kawai a uwan data haifeni nake kallonta don son datake nuna min a fili.
A cikin kaya na alfarma nan danan aka shirya Fadila ta dauka zuwa falon gidan inda suke zaune sunyi mamakin hakan sosai suda sukazo yanzu an hado nasu kaya haka an aje a gabansu cikin alfarma da mutuntawa.
Shiru falon yayi kafin Abbas din yaji yana sauke ajiyan zuciya daga bakinsa wanda hakan yasa ya dan juya ya kalleshi tare da yunkurawa ya fara bude kulolin abincin da aka aje a gabansu lokacin.
Abu biyu yafi daukan hankalinsi na farko kunnun gyada sai na biyu kuma sayayyan kifi da aka aje masu manya manya yanka masu tsoka zallah da yaji a gabansu cikin wani plate.
Kai nasan gurin nan za ai abin kunya wanan kifi ai bana ci bane a nan ya dan kalli Abbas din don jin abinda ya fada kana yace ni dan zuba min kunun nan nasha don ganin yadda kunnun yayi kyau yayi fari sol gwaunin ban sha,awa.
Sunsha sosai har sun kara basu ko samu taba abincin ba saida suka gama Abbas ya kalleshi yace kadafa barci yadaukeka wajan nan yadda ka bude ciki kasha kunun nan ?.
Ga dan iska ai sai kayi mi shimfida in kwanta tun yanzu idan nayi barci sai kira mutanen gidan suzo su sameni a hakan dariya sosai Abbas din ya kwashe dashi har yana buga kafa a daidai lokacin na shigo falin da yar sallamata a bakina.
Dukkansu suka kallo kofan suna amsawa kallo daya yayi min ya kawar da idonshi daga kallona din sai Abbas ke fadin kanwata ashe wayau da kikai muna ke nan kika gudu zuwa nan ke kadai.
Kallonsa nayi cikin mamaki don ban fahinci me yake nufi ba a lokacin yace eh gashi kuwa daga zuwanmu duk da ba,asan da zuwan mu ba amma mama ta cikamu da kayan dadi haka muna taci muna sha.
Dan murmushi na sake a fuskana kafin nace dasu sannuku da zuwa ya hanya anzo lafiya naja bakina nayi shiru tare da dan dukar da kaina kasa ina wasa da gefen kujera dana dafa.
Alhamdullahi mun maki bazata ko irin wanan yasa bamu fada maki zuwan namu ba ga kuma abinda muka sama duk da ba,a sanda zuwan muba an muna tarbo na arziki haka ashe damun fada aida ba karamin abu ashe zamu sama a nan din ba ke nan.
Common please ka faye surutu da yawa don Allah ka tashi mu tafi kada muyi dare a wanan hanyan kuma ka zauna kana zuba haka kamar karamin yaro kana santi.
Ya danyi dariya kafin yace dama tsoho nake aida kaima ba,a soka ba dadin abincin zaisa mu tafi ba tare da mun gaisa da maman mu ba duk wanan dawainiyar datayi muna haka.
Ai bakonka Annabinka ku bakin mune bako rahamane a waje na fada tare da dora fadin nagode da kulawanku gareni bantaba tsanmanin zuwa zakuyi har wanan kauyen sabodani ba.
To aikinsan kulawa nuna alaman kaunace idan bamu kaunarki ai ba zamu kula harmu san kiyi tafiya zuwa nan ba kinsan abokin nawa shi baya magana.
Duk da haka na fahinci damuwanshi na rashin ji daga gareki don haka na dauko makishi na kawoshi ya ganki ko zuciyarshi zatayi masa sanyin rashin ganin ki.
Nina matsu ayi wanan abin ko zai samu sukuni a zuciyarshi kumafa yana da gaskiya tunda a yanzu dukkanku kuna bukatan kasancewa tare da junanku a waje daya.
Yadda yake kallonsa nima haka na dago ina kallonsa din cikin mamaki akan abinda yake fadi zakice yasan mu a tare mun dade da juna ko wani abu maka mancin hakan a tsakanin mu sai gashi ya kare da fadin yi muna sallama da mama din mu gaisa kinsan shi agogo sarkin aikine don muna son mama din tasan damu muma mu santa.
Dago kai nayi na dan sake kallonshi don nakasa fahintar maganansa kai tsaye yana jefa zuciyana a sarkakiya lokaci guda
Ji nayi yace kinga tashi yi muna iso da ita idan ciki zamu shiga ko kuma nan zatazo mu gaisa sai mu sani sauri muke yanzu so muke yau komai dare insha Allahu mu isa abuja shi malam Audi zai kaimu yobe ya dawo nan ya zauna tare dake harki gama kwanakin da zakiyi ki dawo gida.
Nikan wanan bawan Allahn yana daureni da yawa me haka ke nufine wai kardai ince zancen baba suke dauka da gaskiya ba yadda zanyi dolene tunda sunzo har nan su gaisa da Ammi a yanzu tuna hakan yasa na mike na shiga cikin gida wurin Ammi din.
Aisu shigo kawai Ammi ta fada na juya wajen Fadila nace jeki masu iso su shigo nan su gaisa da Ammi din ta mike da sauri zuwa tsohon falon gidan donta fada masu sakon.
Ina daga ciki inajin maryamu ta saka kamshi mai dadi ta gyara ko ina na falon dama can naji sun shigo daga ciki suna gaisawa da Ammi din kafin Abbas ya fara gabatar mashi da kansu a matsayin sarakunanta insha Allahu.
Kana kuma yayi godiya kan halarcin da akai masu itako Ammi din sai albarka take saka masu tana fatan Allah ya nuna muna lokaci lafiya.
Kana ta jefo masu zancen mahaifiyata da cewa duk da waje yayi nisa a yanzu tafiya zuwa Somalia ba karamin aiki bane ga mutane amma tana kyautata zaton zuwan mahaifiyata idan sun kammala siyasarsu ta kasan don yanzu bata a cikin natsuwa balle ayi zancen zuwanta.
Sai lokacin naji muryan Boss din cikin dan saurin maganan nan nasa yana mata bayanin baida matsala da zaran an gudanar da komai zamu tafi can din mu gaisa da ita ai taji dadin hakan daya fada.
Don ya nuna mata zuwa Somalia ba matsala bane amma ayi hakkuri har a kammala komai sai mu tafi mu gaida ita ta ganni sukai mata sallama ni dai naji tana godiya suka fita.
Da kyar na iya fita mukai sallama dasu don yadda na birkice lokaci guda banda wani sukuni a tare dani sunyiwa duk wanda yake wajen alheri kafin su tafi muka dawo cikin gida nidasu maryamu da wasu yan gidan da suka rakoni zuwa sallamansu.
Bayan mun dawo cikin gidane Ammi din ke nuna min abinda suka bata kudine masu yawa bazance ga adadinsu ba daki na koma na zauna ina faman tunane a cikin raina.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login