Showing 276001 words to 279000 words out of 347556 words

Chapter 93 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8805

takeyi kamar ta dora min yuka a wuyana ta yankani inda ba sharia.
Daki na koma ina tunane barkatai sai ga mama uwa ta miko min waya wai Nura ke magana dani na karba yace nayi nemanki baki kunna waya ba tun jiya .
Sammako nayi zuwa kauye na sayo shanaye da mamaki na tambaya shanaye Nura yace wallahi kuwa gamuma mun kusa shigowa kaduna yanzu haka ki dai bari in dawo kisha labari.
Nura ka fadawa mama zancen kayan da na fadama zan dinka ta zaba mun yace tuni tace ta zaba da kin tashi a aiko a dauka kawai nace yanzu naso mukai dinkin gashi kuma bakama gari yace ki ban yan mintuna insha Allahu yanzu zamu karaso sai na karbo maki.
Har Nura din ya shigo gida su hassana basu gama shiri ba nima ban nemesu ba don hakan yai min daidai ina nan sai gashi da turamen a cikin wani ghana most go.
Yai min dadi babu kowa nan ya zauna ya fara ban labarin ai yana nan aka kira layinsa wai sun nemi ya Ahmed basu sameshi ba don Allah sako sukeso sukai min bayani kedai shanu suke so na dubu dari biyu da za a kawo gidan mu ayi amfani dashi ba tare da kowa ya sani ba .
Shine nace masu ai zan iya zanje kasuwan maraba nasayo kawai yau kasuwan garin shine suka turo da kudin sunce koke kada i bari ki sani gaskiya.
Nura dakai za a hada baki ko yace name daga Allah yai muna arziki ta sanadin ki bukin wa aka tabayi aka yanka ko rago a gidan nan inbake din ba da arzikinki ya haskamu.
Wanan fa ba komai bane dake dashi yake son fitarwa kunya tunda yasan bamu dashi baba baida karfin hakan yasa yake taimaka muna cikin rufin asiri ba tare da kowa ya sani duk da dai ko ba,a fadaba kowa yasan bamu da hakin hakan ai.
Ke Bantu kinsan kuwa har shanu biyu na sayo da kudin nan kuma wallahi duk manya saima idan kin gansu sallama akai mai yaron na fadin wai ance Nura yana nan ya fito ga shanun sun iso ya mike da sauri ya fice ya barni ina mamaki.
Tambayan kaina nayi nace anya irin wanan mace ko tana da wani kadari ga mijinta ko yan uwan miji ace mijine zai maku komai iyaka kawai ke adaukeki sai halinki zuwa gidan miji kawai.
Ba wani gata ko mutumcin da za a nema maki a ganki dashi anya irin wanan ba yana zubar da kimar mutum a idon jama,a duk da alaman suma basa son zancen hakan ya fito fili har wani ya sani.
Don komai a cikin wayewa da sanin ciwon kai sukeyisa ba a haukace da za a gani aita yadawa a gari cewa daga wajensu abin ya fito ba don sai dare ko safiya ake shigo muna da duk abinda za a kawo din gidan mu daga banfareshi.
Wabda nasan kuma shirin Abbas ne hakan bashi ba komai Abbas ya tsarawa yadda ya kama gaskiya komeye manufan Abbas a kanmu dai yayi kokari gaskiya abin a yabane shi din.
Gwaggona ta zaria itace ta iso a lokacin naji mama lanto na fadin lalai yar ki zatai aure kuwa kece loman farkon zuwa tana mata sannu da zuwa sai naji muryan gwaggo din da gudu nayo waje ina murnan ganinta don ba karamin dadi naji da zuwanta ba lokacin.
Bayan nagama ihun rugumar gwaggo naji daga bayanta ana fadin sannu Anty wani irin juyowa nayi nagashi tsaye da yar ledan kayanahi yana murmushi a fuskanshi.
Juyawa nayi wurin shi na rikeshi ina fadin Aliyu kaine ka zama wani bulele haka ko kaninkane dai ba Aliyun gwaggo ba dana sani jin hakan dana fada gwaggo tace Aliyunki dai Fatima.
Wani Aliyu da yanzu yafi karfina ai daga nan ina ganin duk inda kika nufa sai dashi don yace shi yazo kaduna ke nan yayi sallama da mallam ko tun jiya.
Dariya aka saka mama uwa na fadin aiko Bintu tasha yan zaman daki da yawa ke nan don ko wanan babban banzan naji yana fadin shima dan zaman dakin ne ga kuma su Amira suma.
Mutanen zaria ne haka tafe muryan mama ke fadi daga kofanta gwaggo ta juya tana kallonta tace yau kambun uwargidancin ne ya motsa daga can ake taron mu kuma ?
Uwargida ran gidace fa mama uwan ta kara fada mama takaraso tana fadin dewa ya,i wani buki saina maiko Hannatu kika taso tunkan a rufa yar taki.
Lasan maiko dadi ka sakashi don kowa nason maiko a rayuwan shi kinji manya sunce hannu mai maiko aka lasa yar mu taja muna lasan maiko Allah yakai mu ga dadi abinda muke gani gidan mutane ko muji labari yau gashi gare mu ba dole mu garzayo ba ayi damu.
Nikan na karbi kayan hamnun Aliyu ina masa iso da mu shiga daki a dakina mama Lanto takaiwa gwaggo kayanta don sunsan yanzu nan take sauka idan tazo.
Ruwa Mama Uwa ta kawo masu a nan dakin aka aje suna can suna cacakan baki da mama suna fadawa juna magana a fakaice shigowa Nura da shanu katakata yasu jada baya da sauri kowa na gudu a wajen don tsoro.
Meye wanan kuma Nura ina kafito da shanu haka har cikin gida yace zaku wasa baki sai kun gaji mama shanun bukine aka kawo kirji mama ta daka tana fadin wai da gaskiya yace.
Mama kin taba ganin ko kaho gidan nan inbada bukin nan ba ya wuve da shanu zuwa wurin filin dake baya da aka kara zageyemu dashi wanda kusan yanzu a can ake aikace aikace nagidan.
Saida suka daure suka fita suka shigo da wani kuma tunda mama ta shiga daki ba,a dadeba ta fito tana fadin zata unguwa duk abin nan baba yana daga waje inda yake zama yanzu don ya daina fita zuwa kasuwa saidai zaman gida tunda bai gama warwarewa ba.
Mun tafi mun zuba kudin dinki har na ankon bukin su hassana da nawa muka biya muka dan biya gidan kawaye sai yamma lis muka dawo gidan har lokacin mama bata dawo ba.
Haje haje muka dawo muka samesu ankawo kwando kwandon tumatur tatasai da Albasa gasu mai kwalin maggi da sauran su cabej karas green beans kai komai mai yawa ankawo a gidan.
Muna shigowa suka azamin guda dayasa naji har antana saida ya kada saboda tsoro da fargaba lokaci daya daya sauka min shike nan fa auren nan ya tabbata akaina ke nan.
Daki na fada ina tunanen wani irin aurenw haka bashiri yazo min ikon Allah a take zuciyana ta bani amsa bandaki na fada na dauro alwala don magariba da yakusa a lokacin.
Kodana fito gwaggo ta shigo dakin tana fadin uwarku fa tun safen nan data fita har yanzu bata dawo gidan nan ba don yau ta razana gabanta ya fadi bata taba zaton hakaba a rayuwanta.
Sai gashi taga abu sai gaba yakeyi cikin gadara da isa da hamdalan ubangiji dole yau ta kasa zaune ta kasa tsayw Suwaiba makiran mace ce wallahi yanzu hiranta kuka sama suna min a tsakar gida ai.
Abin Suwaiba ya shahara sai addua a yanzu don babu alaman rahama ga wanan macen da take jayaya da ubangiji saidai bakin cikin nan ko ya kasheta insha Allahu.
Murmushi nayi nakai zaune nace gwaggo Aliyu fa tace wa wana???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?n dan garine ai ni dai run dazun da suka fita da Nura ban sake jin duriyanshi ba har yanzun nan.
Ina jin sai bayan magariba mama ta shigo don ko baba yana ta aikawa a dubo masa ita ace bata dawo ba tana dawowa hassana ta hauta da fada fitan da tayi din.
Bayan sallah isha,ine baba ya kirasu har gwaggo yana masu bayani yadda abubuwa zasu kasance sai lokacin yan gidan mu sukaji cewa a sokoto za,a daura aurena ashe ba a kaduna ba.
Lalai namiji makirne malam aure Bantuce za aje har sokoto a daura sai yanzu ka tuna da yan uwan naka da adacan baya ka manta dasu yace kwarai.
Don ko ita Fadimatu zata fada gidan sarauta dole in mata gata tunda Allah yayi mata ke in kina da mutunci aiba zaki fadi haka ba duba ga irin halarcin da yaron nan yayi muna.
Ya gyara muna gida badon komai ba sai darajan yarinyar nan da nasa ya wadatar damu da abinci da sutura masu kyau mume muke dashi da zamu saka masa yanzu bayan wanan ?
Kaika sani ta tashi ta fita cikin fushi tana fada tana maganganu daya jawo hankalin kowa nagidan ga sauraronta a lokacin akan bata yarda ba ace wai sokoto za a daura min aure yadda aka daurawa kowa aure a kofan gidan nan nima dole haka za ayi min kamar kowa don ba finsu nayi ba ai.
Rigima sosai mama tayi a ranan tana koke koke amma gwaggo ta hana a tanka mata tundai baba da yaso magana amma gwaggo ta hanashi hakan dole ya kyaleta tana fada ita kadai.
Sai su yan biyu da suka gaji da bata hakkuri suka saka kuka suka daga waya suka kira ya Ahmed duk abinda yakeyi ya dawo gida a lokacin don yayi tafiya tunda na dawo baya nan .
Amma yasan da zancen auren zuwa jibi yace zai dawo gida dama saigashi su yan biyu sun kirashi cikin tashin hankali sun labarta masa haukan da mamakeyi a gida.
Tun a waya yayi mata kaca kaca ya kuma kira maman tudun wada har anty Altine suka taushe yasa tayi shiru washe gari aka tashi da aikin gyaran naman shannu da aka yanka tun da Asuba masu aiki fawa sukazo suka yanka shanayen.
Ina daki da gwaggo kwance don mun raba dare muna hira mai kama sa nasiha da take min tayi min fada sosai na zaman rayuwa inda ta luran dani gidan da zan fada da irin rikicin da zan kuma sama a can din.
Wanan yasa da safe nayi barcina sosai har gwaggo ta fita zuwa wajen aiki ban sani ba ina kwance ina ta barcina sai da wayata dake kara ya tayar dani lokacin na falka.
Ina dubawa bansan lokacin dana watsake ba don ganin me kiran nawa Ammi ce da sauri na daga wayan suna hayaniya a wajen haiya haiya can take fadin Fafimatu.
Na amsa sai na sa kuka take fadin na barkuka muyi magana amma ina ban saurara mata ba hakan yasa tayi magana a gurgunje tace gasu nan tafe amma wanda suka biyo mota sun kwana a jos da safen nan zasu karaso.
Matan yayyunki dukansu da yan uwana su Fadila da maryamu duk suna tare dasu na amsa a cikin sheshekan kuka da tou Ammi tace kiyi hakkuri mun tafi Samalia ne yasa baki jini ba saidai idan munzo din kyaji komai ta kashe wayan.
Daga kofana nake kwalawa mama Uwa kira bata amsa sai wata ke fada min tana baya suna aiki ga gidan ya dauki kamshin kayan cikin da suke zauka a lokacin.
Sai gata tun daga nisa nake fadin mama akwai baki tafe yanzun zasu karaso daga wurin su Ammi cikin murna tace Ammi ta kira nace ta kirani yanzun nan na fada mata yadda mukayi nan da nan abu ga taro gashi dama aikin mune aka dora abinci na alfarma mama Lanto ta tsaya dasu yan biyu nan da nan sun kammala gida ya fara cika ke nan kuma da jama,an arzikin mu .


ZAINAB IDRIS MAKAWA
KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
8?? 8??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Tun da gida ya fara cika na rasa inda zansa kaina Aliyu da kansa ya tattara min kayana a waje daya ya faka minsu a manyan ghana most go sai hakan ya karawa dakin fili sosai.
Zuwan yan Gashuwa ya dagawa kowa hankali irin bus din nan na local government ya mustapha ya dauko dashi sukazo maza da mata kamar yadda malam ya tsara masu zuwa din.
Suna zuwa dakina aka saukesu tukuna sukaci sukasha a dai dai lokacin Oga Abbas ya kira wayana jin hayaniyan yayi yawa yasa yake tambayana ina inane haka yaji hayaniya sosai a wajen.
Nake fada mai yan uwanane sukazo daga gashuwa yace kai haba dai har sun fara isowa ke nan nace eh gida ya cika tun jiya wasu sun isoma daga Zaria ai kai ashe buki ya kan kama hakane nayi murmushi.
Mukayi maganan da zamuyi dashi dama akan wajen da zamuyi event din mu na kamune da suka kama muna shine ya kira yana fada min bayan mun gama magana munyi sallama sai kuma ya kara kirana baya wani dan lokaci mai tsawo saiga kiranshi kuma .
Na dauka yake fada min kince mutanen gashuwa sunzu ko nace eh yace Nura zai shigo yanzu za a kaisu masauki a nan cikin unguwan kune ba nisa sosai su zauna a nan tare da duk wani bakonki da yazo gidan akwai komai da zasu bukata zamu kai masu komai wanda babu a yanzu bai jira me zance ba kawai ya kashe wayanshi dip.
Ikon Allah watau dai mutanen nan a shirye suke da komai na fada son kamar sun shiga raina sungani a lokacin don tunane nake inda zamu saukesu ko mukaisu gidajen makwabta sai ga wanan zancen ya fito a yanzu.
Watau idan ka auri diyan tallaka baka huta ba hakama in yar me kudi ke nan ta auri tallaka suma basu hutaba ashe wanan dalilin yasa basa son auren na kasa dasu don dawainiyace sosai a wajensu amma mutane suke ganin laifinsu.
Duk da ba duka bane da irin zuciyan zaki zuciyan girma da sanin ciwon kai don su wa yan nan ma abar zancensu don kamar a shirye suke komai.
Abinda ban sani ba shine suna sama da jagorancin Mamin Abbas ce data san komai ciki da wajen malam bahaushe yasa take toshe duk wani kafa da za a samu matsala ta hanyar basu shawaran daya dace a cikin kulawa iri na uwa bazataso ace an samu wani matsalan komai ba a wanan sha,anin insha Allahu saidai abinda ya fito daga Allah zuwa garemu.
Hakama jirage sun fara sauke bakin Boss daga bangarori na duniya cewa za,a daurin aure a sokoto kuma fadan da kowa ya sani ya kara mai karfin gwiwan watsa katin auren shi ga jama,an da yake hurda dasu ciki da wajen kasa wanda kowa a yanzu yake son ya halarta don mu,amulansu dashi din.
Wurinkan ya kice da jama,a zakice ansaka lalai a lokacin ma ana shirin daurin aurene sai ga Nura da yara suna shigo da abin sha katon katon a gidan Nura shi ya zamo min jigo a wanan lamarin.
Mama na daki dasu Anty Altine data shigo tsomai tsomai gaida wa yanda ta gani waje tayi kawai ta shige dakin uwarta maman Tudun wanda itama tazo duk suna daki.
Zuwan su kawayena yasa ban tsaya nazarin meke faruwa ba saida gwaggo ta fada min cewa mama ta shige daki tun safe taki fitowa bakin ciki yana shirin kasheta a dakin.
Na kalli gwaggo nace akan me gwaggo take fadin yaro dai yarone yau ko yar gwauna kike ai iya gata ke nan Allah yayi maki a yanzu ki godewa Allah da wanan baiwan da yayi maki yar nan.
Zaune suke a falon nasu saukan safe sukayi ta kano jirginsu ya sauka don haka basu dade da zuwaba amma hakan bai hana Al,amin fitowa ba lokacin har layin mu yake yaga mutane suna shige da fice ga gidan mu daya sauyawa Saninshi a yadda yasanshi a baya tsohon gida dayasha zamani sai gashi a yanzu yaga ginan zamanine awajen.
Sun gaisa da Isa mai shago amma bai ganeshi ba yake tambayanshi don Allah ko fatima tana nan ko har tayi aurene ko isa din ya kalleshi yace batayi ba zata daiyi don bukinta kaga anayi yanzu haka.
Bai karaba ya juya ya tafi yayi kiran wayana ban dauka ba lokacin yasa ya koma gida kai tsaye inda ya samu gidan ya dan kara yawa su hjy maria sunzo kannin Ummu da abinci don zuwansu din anata hira.
Kallon Ummu tayi tana fadin iba kaje ga abinci ana nemanka kaci yace na dan fitane kallonshi tayi kawai batayi magana ba don bata kawo a ranta cewa gidan mu ya fito ba a lokacin.
Don a tsamaninta anyi auren nawa ko lokacin gefe ya koma yana cin abincin shi yana kuma sauraren hiran iyayyen nasu sai da yaji hjy maria na fadin ai ance a nan unguwar matar shi Bashir din suke.
Hjy ance ya zuba mata kaya bani da kaya ba labarin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login