Showing 168001 words to 171000 words out of 347556 words

Chapter 57 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8747

ina dubawa don rabona da waya ma har na manta .
Tanada caji full don haka na shiga duba miscalled barkatai harda su Samira sai hakan ya bani mamaki nice samira ta kira abin akwai mamaki gaskiya.
Ban fito ba sai misalin karfe hudu da rabi na yamma na fito falon na samu kowa a zaune banda ummu sunce tana ciki ta shiga yin sallah.
Salimace ta dauko hiran bukin nasu tana yabawa ni dai ina kwace har lokacin da sauran gajiya a tare dani a jikina don hakane dana samu sarari sai inkai kwance ina mikewa .
Salima ta kalloni tana fadin meyake damunkine naga tun safe kina kwance yanzuma gashi kin kwanta don ban saba ganinki hakan ba ko duk gajiyace hakan ?
Dan mika nayi ina gyara kwanciyata ta hanyar fuskantar ta ina dan murmushin yake nace bari salima jikin nan nawa duk ya mutu kamar an min duka nake jinsa.
Muryan ummuce a bayan mu take fadin ai dole dolene kuji hakan gaskiya anyi taron da ba,a taba yinsa ba kuma taron yayi kyau ya kayatar sosai kowa na fadin hakan a wurin.
Da sauri na mike zaune don ganin ummu danayi na sauko ina gaida ita ta amsa tare da fadin ya gajiya ai nace su barki ki huta nasan gajiyace tasa kika kwanta.
Murmushi nayi nace an daiyi angama lafiya Allah kuma yakai kowa lafiya gidansa suka amsa min da amin suna kallona ke ai dole kiji jiki yaron yaron nan na mutane daya dafe maki.
Amma fa kina da kokari haka kawai wanan yaron yaki uwarsa saike khariya ta fada tana dariyan mugunta na kalleta na dan shagwabe kafin inyi magana hjy ce ta farayi.
Farin jinine dake mamata na kula da hakan sosai yanzu akwaiki da saurin shiga ran jama,a nan take badon komai ba kuma sai kyautatawanki da saurin sabo irin naki.
Murmushi nayi a raina nace banda yan gidan mu da nake zaman makiyiya a garesu koda yake ba zance haka ba tunda ba duka gidanne basu sona ba.
Wai dama kin san wanan Bashir din ne fatima ko dai a nan kawai kuka hadu dashi khariyace ta jefo min wanan tambayan.
Saida na dan kalleta nayi murmushi nace Ogan mune a wajen aikin a nan na sanshi nima nayi mamaki dana ganshi a nan ai ?
Na dauka ba zai ganeni ba tunda daga nisa muke haduwa sai gashi ashe ya sanni harda sunana ban yarda na nuna masu cewa nasanshi sosai ba don bansan ya alakansu yake ba don haka na dan gyara zancen a bakina.
Hjy ta kalloni tace gaskiya nayi mamaki yadda akayi ya sanki ai don shima dan uwan Alh ne a gurin mu ya fara tashi saidai zaman bayi nisa ba yabar wajen mu.
Amma umma wai ya yake da Abbune ta tambaya sai naga uwar ta kalleta galala tace ke yanzu baki san connection dinku ba dashi kike nufi ko me ?
Ya zan sani tundama ni ban sanshi ba sai a cikin yan shekarun nan naji ana fadin ai dan uwan mune shima ni kuma ban matsa insan ko ya muke dashi ba.
Nakan dai ji su Al,amin suna hiransa wani lokaci uwar tace zumuncin zamanine ballesu ai sun dauka nice ban bari Alh ya kula dasu don hakane kikaga ba kowa kuka sani ba.
Mahaifinsa da Abbu uwarsu daya shi yana wani kauye yana dakaci a can tun yana da kurciya ita kuma mahaifiyarsa banufiyace yar Nager state rasuwa tayi don bata da rai.
Haka yasa ya taso maraya mara gata a gidan uban sallaman ummah hani data shigo falon tana magana da hjy ya katseta ga dan bayanin data farayi a lokacin akan ahalin.
Shiru nayi ina tunane don sun fara buga min kai alokacin wayatace ya shiga kara na dauka ina dubawa hussainace ta gidan mu.
Sai ban dauka ba na barshi har ya katse saboda nasan in nayi hakan computer zatayi masu bayani a cikin larabci wanda hakan zaisa su san ba kano din da sukace zanje in lafe bane naje din kamar yadda suke son sani.
Har saida kiran ya katse kafin wani ya sake shigowa na dauka ina sallama muka gaisa ace min ga wanan ga wancan duk yan gidan mu sukai ta karban wayan suna gaisawa dani.
Da muka gaisa da mama uwane nace da ita ga hjy su gaisa din su tabbatar na mika mata wayan suka gaisa a cikin mutunci da girmana juna har hjy take tambayan baba.
Take kuma karayiwa mama uwa din godiya da zuwana sun dai gaisa take fada mata sai bayan aikin hajji zan dawo Nageria insha Allahu.
Aiko suna gama wayan gida ya dauki ihu masu murna nayi masu bakin ciki sunayi har yakai mama ta kasa boye damuwanta tace aikin banza yiwa kare wanka.
Ko anzama hjy aiba fin mu za ayi ba wama yasani ko ga aiki aka dauketa yi a can saudiya din don yanzu dabi,an da akeyi ke nan a dibi yan mata akaisu can suna karuwanci ko kuma suyi aikatau duk musan wanan ai ta dauki roba tayi daki hankali a tashe.
Ko irin wanan tafiyan ai kowa naso inda zai sauke faralinsa a saukake saudiya din nan dako kafiri yana son zuwansa dan darajan wurin .
Yarta hussanace ke fadin hakan ga uwar cikin rashin damuwa Samira dake daki tanajin ana wayan bata fito ba sai wanan lokacin da kowa ke zancen zuwa na din.
Ai kuwa dai ashe bani kadai ke wanan tunanen ba nima wallahi saida nayi tunanen kada wanan matar ta kaita can tana takari gashi ance da kaje zasu karbe ma passport dinka.
Sai ka nemo masu kudin jirginsu su sallameka kashiga garari cikin saudjyan dole ka koma bin maza ai bin maza yanzu ba abin fadawa wani bane kowa bi yakeyi harda masu kwance hassana ta bata amsa .
Uwar najin hakan tayi saurin kwaban yarinyar da cewa nifa banson hakana ki barsu suyi zancen su yanzu da anzo maida magana naki zai fita .
In kina da hankali tun a yanzu zaki gane hakan don haka kija bakinki ni wanan abin ya isheni hakana don Allah ai kuwa kafin uwar ta rufe baki yan biyu sukai cikinta da cacan baki dama neman magana su yaba mata shi sukeyi.
Gidan mu ke nan gidan dadi gidan fitina gidan gori gidan sa ido gidan makirci ko yan daki daya sunawa juna kazafi da gori idan tsiyan ya motsa.
Yaran ya habibi kan saidai Allah ya raya yasa albarka duk da yanzu yana dan basu kula amma dai ba irin can din nan ba kowa yasan da hakan akansu.
Gashi ubangiji yayi mai budi a yanzu sosai amma kuma yana da halin mako bai faye wasa da kudi ba saidai kawai ace an godewa Allah .
A wanan takin kuma ya shigo kaduna da zancen auren Samira a bakinshi iyayye sunso suja amma kuma ya samu manya suka shiga zancen nan aka tsayar da magana cewa an yarda za ayi nan da wata uku mai zuwa insha Allahu.
Sosai mama ta tada hankalinta tayi ji dali tayi masifa abu har yakai mama da yaji tabar gidan baba wai duk kan a fasa auren amma baba kamar wanda akashe yayi kememe akan bai magana biyu.
Hassanace ta kirani da safe tana kuka take labarta min abindake faruwa a gidan namu da farko cewa tayi min Bantu ya can na amasa da Alhamdullahi.
Ya kowa a gida tace lafiya ba lau ba Bantu kinsan wanan yar cin amanan tayi sanadin barin mama gida ita da uwarta.
Gabana naji ya fadi da sauri nace subbahanallahi wake nan Hassana tace samira mana da uwarta akansu baba ya rufe ido yace sai mama ta bar masa gidansa.
Na kara maimaita innalillahi garin ya haka ya faru da girmansu kuma zasu aikata hakan bayan kowa a tare ya samesu tun suna da jajayen sawunsu.
Kedai fadi ai don kawai mama tace bata yarda da hukuncin da baba ya dauka ba shine suka fara fitana har yakai da saki a tsakaninsu.
Innalillahi na kara ambata nace saki fa hassana akan wani zancene wai tace zancen samira da ya Mahmoud mana ko baki sani ba an bashi ita yau saura wata uku a daura aure.
Aure Hassana shi baba din ya jaye dokansane dayayi tace min ba dole ba an hadashi da boka da malamai kai ya dauki zafi ikon Allah na ambata nace kin ma huta wallahi .
Ita Samira karatun nata fa idan tayi aure ko a kaduna zai barta ta zauna tace waya sanarwa yan iska dama wani karatun kirki takeyi can nan dai take ta fada min maganganu marasa dadi da suka faru.
Nace ita Anty Altine bata zo gun baba bane har ta bari hakan ya faru ai itace ya dace tayi magana ba mama ba gashi har ankai ga abinda ba,ason ya faru ina dadin hakan don Allah ?
Ni dai a karshe nace koba ya habibi ba aida mama tasani ta barta tayi basai ta bata baki ba indai wanan mutumin ne gata gashi ta aure mai hankali zai gane idan ya kula da yadda yakewa yayansa da kuma iyayyenshi.
Na dai basu hakkuri nace kuma zan kira baba in basa hakkuri don layin baba din kona kira baya shiga sukace sun gode suka kashe wayan mukai sallama.
Kaina nakai saman filo nayi rigingine ina kallon derking din daki tare da tunane akaina Allah ya rufa min asiri bani bace nayi wanan sanadin da har mama ta bar gidan baba da sunan saki kan wanan auren.
Idan ma data sani tayi shiru indai wanan da yanzu gaba daya ya canza ba komai Samira zata gane da aurensa ba haka kuma ita mama idan ta hakkura zata sha kallo nan gaba.
Saidai basu gane hakan saboda idanunsu sun rufe akan shi ya Mahmoud din kowa na ganin jin dadi da hutawa a gidansa yanzu.
Samira kuma tausayi da takaicinta ne ya rufe min ido don nasan zatayi hasaran karatuntane kawai da take da buri dashi donni ta fini buri kan karatun mu.
Kamar ance damu da mun gama zamu samu aikin da muke so din kawai munyi karatu alhalin milliyan din masu kwalin shedan karatu suna nan zaune a gida wanima zakace bai taba shiga ajiba a rayuwansa.
Haka dai nayi ta tunane barkatai a karshe na dauko waya ina gwada lambar baba amma yaki shiga ashe abinda ban sani ba shine.
Wayan na baba ya shiga wani wuri sai yaba Samira ta saita mashi shine tayi blocking din layina don haka ko nakira layin nawa ban samun baba din sai ya katse.
Wanan maganan yaso ya caza min kai karshe na tsiri zuwa massalaci ina wuni can dani da salima sai hakan yasa na manta da komai a zuciyana inata zuba ibadana don cikin watan azumi muke bamu dawowa gida sai dare.
Ibada kan munyisa sosai gaskiya munyi umurah har sau biyu zama a can muna zuwa makka yin umurah mun kuma roki ubangiji Allah saukin abubuwa a rayuwan mu.
Har zuwa lokacin da aka fara daukan haramin zuwa aikin hajji gari ya fara cika da baki masu zuwa sauke farali.
Sai gab da sallah hjy tace muyi niyar hajji mukayi kwana tara a nan muka dunguma zuwa makka don sauke farali bamu da matsalan masauki a makka don ashe can khariya take tana auren wani haifafen mazauna maka din amma dan Nageria neshima saidai basu zama garin haka kuma suma su hjy din suna da gida a makka amma anbada hayanshi ga mahajata don haka bamu sauka a can ba gidan Khariya muka sauka .
Na hadu da yan kadunan mu da yan uwa suka basu lambata don kawai su sheda gaskiya mukaje har masaukinsu muka gansu suka kuma ganmu hjy tayi masa alheri din na fada mata makwabtan mune unguwarmu daya dasu.
Mun bar wajensu hjy ke fadin kai dan adam da kwakwayake don kawai su tabbatar ko kina saudiya nasan aka basu layinki nace nima abinda nake tunane ke nan mama.
To ai na fada masu komai na fada masu sunji sai suji dadin zuwa su karasa kafin ki iso nidai nayi murmushi kawai don muna cikin aiki banson abinda zanyi na sabo gara da hjy ita bata san iya nata aikin ba niko wanan ne na farko gareni don haka na tsaya ina abina yadda zan samu lada a wajen Allah.
Alhamdullahi angama lafiya munyi komai yadda addini ya sharadawa musulmi muka dan kara kwana muka huta mukayi sayayyan abubuwa na fidda kudina da wanda Ogana ya ban da wanda wanan mutumin jirgin ya bani salimace ta rakani muka sayo wani sarka dan Dubai mai kyau da nauyi gaba daya kudin na hada na sayo sarkan dashi.
Saida muka dawone na nunawa hjy don kada tace na munafunceta ban fada mata ba karba tayi ta duba naga ta dago kai da sauri ta dan kalleni tare da tsura min ido tana fadin.
Ke kika sai wanan sarkan mamana kidinsa fa yana da yawa nace eh mama aina fada maki ina da kudi kikace naje na sayi duk abinda nake so shine naga wanan zan saya insan inda kudin suke.
Gaskiya mamana kina da dabara don sai kinje najeriya zaki san kudin sarkan nan ba karamin kudi bane sai ta miko min sarka bata kara min magana ba kuma sai hakan bai mun dadi ba a raina.
Don ina ganin kamar ranta baiso haka ba ko wani abu don a gaskiya hjy ta dan nuna min reaction akan sayan wanan sarkan da nayi kwana biyu bana gane kanta sai hakan kuma ya koma yana damuna.
Sai ana gobe zamu bar makkah mu koma madina ne muka dan fita sayaya tare da ita kowa nata sayan abinda yake so ina binsu mun shiga wani shagon dogayen riguna take fadin mamana ba zaki saya bane ke kallonta nayi kawai nayi murmushi ina dukar da kaina gefe daya.
Ga riguna masu kyau da daukan ido a wajen ina gani hjy nacan na magana salima ta dan kyafaceni tace idan kina sone mu saya kawai ki hada ya kudaden da suka saura a hannunki kisaya.
Don na fahinci wani abu mu kyaleta kawai mu dawo daga baya musaya hakan ko mukayi muka koma muka sayo riguna masu kyau masu tsada na hada tsarabana fan yan gidan mu kaf na sayo masi tsaraba muka dawo Allah ya taimaka bata gane ba kota gane ma batayi magana ba ai.
Nan na gane mutum sai Allah dan tara yake bai cika goma ba don ban taba zaton hakan ga hjy ba ko a mafalki amma bansan dalilinta na yimi haka ba kuma.
Mun dawo mun zama alhazai mun sauke falali sai shirin komawa gida ya rage muna yanzu kuma hankalina ya koma ga karatuna da iyayyena.
Gashi kuma banji hjy tana zancen yafiya na ba har hakan ya fara sakani a damuwa kyau kan ba a maganan shi gareni nayi kyau sosai jana ya kara fitowa kamar ina shafa mai a jikina na danyi kiba bul bul dani tubarakallah masha Allah.
Salimace ta sameni a daki kwance take fadin nifa banji matar nan ta fara zancen komawan mu ba fatima kinsan dana koma ni aure zanyi nace ni kuma karatuna nake tunane don na dan wuce lokacin da aka diban min gashi kuma naji mama na fadin zatayi tafiya ?
Dole muyi magana Salima ta fada nace me zamuce tace haka zamuyi ta zama a nan bayan kowa harkan gabanshi ya baro a can gida karshe dai tace ita zatayi magana gaskiya.
Ke nifa naga canji ga idon hjy don tun ranan da akai zancen sarkan nan da kika saya hjy ta fara daure muna fuska koke baki kula da hakan bane wai bashi bama ni cewa tayi min in tabbatar da bani taba mata komai nata dai me hakan ke nufi ke nan.
Dagowa nayi na kalleta nace Allah nagodema da ban shishigin shiga dakin kowa a gidan nan balle tayi zargin abinta nake dauka sai kawai gaba daya naji ta zube min watau abinda Oga ke kokarin fada min akansune ke shirin faruwa ke nan na tambayi kaina.
Kinsan fa dole tayi haka tunda tana ganin bamu kai ba sai mun nema a wajenta sai gashi kuma lokaci daya kin tashi da babban sarka haka kece dai baki san halinsu ba nake ji salima ta fada.
Munyi haka da kwana biyu naga su Abbu da uncle sun dawo tunda nayi masu sannu da zuwa ban kara sasu a idanuna ba don ban faye fitowa ba gaba daya zaman haka yafara damuna a yanzu yasa ban ma fitowa sosai.
Hjy sun fita da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login