Showing 195001 words to 198000 words out of 347556 words

Chapter 66 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8736

wasu bahohin aiki haka sai bangon ginan baba da glass din windows dasuka daga na dakinshi sune barnan da akayi din.
Don haka banda hurimin cewa na yafe tunda bani nasaya masu ba banda ikon cewa a barshi don haka nagane gaskiya ya fada naja bakina nayi shiru yayin da yake faman lalubo abu a cikin motarshi ya miko min yana fadin.
Karbi wanan don zaifi kuyi aikin da kanku dan mutanen yanzu baka da gadonsu su suna da gadon zancen ka a yanzu don haka ko Ma Nura ya tsaya yayi wanan harkan.
Dan nawan karba nayi daga hannunshi kafin yace dani karbi mana ba wasu kudi bane masu yawa ai kikaiwa baba dasu mama a kara basu hakkuri.
Don ni ina jin nauyin shiga gidan nan yanzu sosai bansan da wani ido zan kallrsu ba a yanzu don an jagula min jin dadina a yanzu.
Karba nayi a mutunce ina fadin angode Allah umfana amma dai sai nake ganin kamar kudin sunyi yawa ai har yafi karfin barnan da akayi muna din yace kada kice hakan don wanan kudin a hannun iyayyen Sakina ya fito.
Don haka ba wani yawan da yayi saboda na fada maau ni ba zan biya ba shine suka sameni dashi naga kuma wanan lauya din daya tsaya maku shima an sallamesa don kada kuce zaku nemesa ku bashi wani abu daga baya kuma.
Wani nauyi da kunyane suka lulubeni lokaci guda don a gaskiya indon nice bazamu karbi kudin nan ba saidai muyi hakkuri kawai a rugumi kaddara.
Muryanshine ya katse min tunanena da yake fadin yaushe hutun ku zai kare ki koma zaria nace akwai sauran time gaskiya son sai nan da three weeks masu zuwa zan koma can din insha Allahu.
Yanzu har wanan weeks din ba zan ganki ba ke nan ya fada cikin tsigar zolayan daya saba nace yanzu da akai kwanakin nan baka ganeni ba meya faru da kai koda yake naga ka rame ai ,?
Yace ashe kin gane baby nima haka nake jin na dan fada nayi duhu nasan ba komai bane sai yawan fitinan da mukeyi a yanzu da madam dina don ta sakani gaba da fitina a yanzu kanki.
To ke dince da daukan hankali Fatima harda mata yan uwanki suna zancen ki bakiji yadda yan uwa ke magana a kanki ba tun wanan ranan da suka gan ki a office din Dss suka sakata a gaba da zolaya.
Zaka fara halin naka ke nan ko sai ana zancen gaskiya ka daukowa mutane zolaya suna aibantani ke nan yasa kake fadin hakan a yanzu.
Mun dai kai wani lokaci a tare kafin mukayi sallama dashi ya tafi ni kuma na kada kai na shiga gida dakina na nufa sallah la,asar nayi na zauna na kirga kudin nan saida gabana ya fadi don abinda nagani.
Me zancewa soja ne a duniya don nikan ya gama min komai don haka sai addua da fatan alheri da zai biyo baya a tsakanin mu dashi sai ba zan fadawa kowa zancen kudin nan ba sai idan mun kai babana asibiti munji halin da yake ciki in yasa in abin yazo da sauki sai a fito da kudin ayi gyaran gidan kamar yadda yace ayi din dasu.
A nan Usaina ta shigo ta sameni tana min gulman Samira kamar yadda mama uwa ta tsegunta mi yana faruwa banyi wani dogon magana ba na daice dasu Allah yayi muna sauki baki daya.
Mun kai wani lokaci a dakin kafin ta fita na tashi na gyara dakin ko ina na saka kamshi na leko baba kafin magariba ya karasa ya fada min yana son shan abin sanyi jin hakan yasa ana sallame sallah magariba na fita naje na sayo masa har da mutanen gidan don ban fargaban komai tunda akwai kudi a hannu lokacin.
Ban tsaya dogon hira ba a ranan da wuri na shige barci na barsu nan suna hira har akaci aka sude ban san lokacin da wai Samira ta shigo ba gida tana kuka cikin tashin hankali.
Hayaniyansune ya tayar dani daga barcin dana samu din don muryoyin mama Lanto da Samira da yake tashi a gigice na fito dagani sai daura gaban zani don ba wutan Nepa a lokacin.
Jin abinda mama lanto take fadi sai kuma naja nayi turus ban karasa ba don sai faman Allah ya isa mama Lanto keyi yayin da ita kuma mama ke fadin an fadi don taji inda dadi ai suma hakan sukai masu sai ji sukayi ya koma kan Samira din ai.
Kai wa, iyazu billahi na fada don na rasa zancen wanda zan saurara a cikinsu lokacin da karfi na fara fadin haba haba dai jama, a wanan abin dame yayi kama don Allah ?
Wai shi ya habibi din nan dan gwal ne ko shine autan mata wanan abim kunyan dame yayi kamane yanzu don Allah fada akan namiji na mijin ma wai mijin yar uwarmu.
Kun zama macizai da baku ramin kanku saidai a gina ku shiga don me ko wacen ku ba zata nemo nata mijin ba sai mijin yar uwarmu data rasu ta barshi da yaran ta.
Dole akwai manufa ga hakan da kowa ke nufi a kan aurem nan ina hadaku da Allah ku daina wanan abin kunyan da kuke jawa gidan mu a yanzu ku tausayawa wanan bawan Allah dake kwance yana bautan ubangiji mana.
Daga samira har ke hassana kuyi hakkuri da junan ku tunda Allah ya hada rayuwa a wuri daya duk yadda kukesonshi a yanzu na tabbatar da bazaku taba kai ya safiya data tafi ta barshi ba ciwo ba.
Indai ya habibine Samira ki saka a ranki cewa kin aurensa kin gama insha Allahu ni daice kikaowa sheri da banji ba bangani ba nivdin kuma zanje har gurin shi in gyara wanan zance ke kuma hassana ki saka a ranki Allah zai kawo maki wanda yafi ya habibi da komai insha Allahu.
Amma har sai kun yarda kun barta tayi aurenta a zauna lafiya hakan zai kasance a gareki ni banga abin tsayawa anawa kai tonon asiri irin haka ba a gidan nan makwabta suna nunamu ana muna dariyan hakan.
Gidan yayi tsit zakice wata babbace ta shigo take wanan maganan bani Bantu yar tsakar gida bace a yau nake tsawata masu har kowa don dole akai shiru don na gama magana duk mai hankali zai gane inda na dosa da zancena a lokacin.
Juyawa nayi zuwa daki na kwanta amma barci ya gagareni sai dare sosai na samu barcin ya dan dauke ni a tunane na rasa haukan da kowan su keyi akan wanan mutumin ayanzu wai ?
Washe garine da safe gidan yai shiru don rayukan da aka kwana dashi a bace sai ita mama Lanto din dake girki take dan shawagi a tsakar gida nasan abin karyawa take kokarim hadawa a lokacin.
Allah ya gani tausayin mahaifin mu nafi ji fiye da kowa a yanzu don haka nagaida ita da kwana na nufi dakin shi inda na sameshi a kwance cikin wani irin yanayi na zazzabi mai karfi a lokacin.
Hankali tashe na karasa wajenshi ina dan taba jikin nasa da yayi zafi radau jin an tabashi yasa ya bude idonshi ya sauke a kaiba a rude nake mashi tambaya da meke damunsa ne kuma , ?
Yayi min nuni da hannu da cewa duk jikinshi yana masa ciwo sosai a lokacin na gigicw don haka a rude na shiga tono maganinsa ina dubawa son likita ya bashi harda na zazzabi din a cikin na sallama.
Can kuma na tuna ai bai karya ba don haka na fito da sauri na samu mama din ta dora ruwan zafi a lokacin shina diba na hada mai shayi mai kauri duk da baison amma na samu yasha nan ya Ahmed ya shigo ya samemu shiya taimaka muka bashi maganin duk na rude ina fadin mukaishi asibiti.
Yace mu dakata dai mu gani ko zai samu sauki ganin hankalin mu a tashene ya jawo hankalin iyayyemu garemu nan dai suka fara shigowa dakin suna duba baba din .
Ya Ahmed ya fara fada sosai kan abinda yaji ya faru yana fadin shiyasa jikinshi ya tashi ashe Allah kadai yasan a irin halin daya kwana yaiwa mama fada sosai a gaban kowa.
Har saida aka koma bashi hakkuri Nurane daya shigo ya fada mai don baisan anyi bashi don ba anan gida yake kwana yanzu ba can gidan kakaninsu dama ya tashi.
Nan dai Allah da ikonsa saiga baba din ya fara samun sauki har ya fara dan alaman zufa a jikinshi hakan ya hana mu karasa asibitin dashi don ganin ya samu sauki sosai.
Zuwa sha daya na bar dakin zuwa dakina wanka nayi na shirya tsab kafin na nemi abinda zan karya kummalo dashi bayan nagama na dauko wayata kira daya biyu layin da nake nema ya shiga.
Saida ya dan bata lokaci kafin ya daga da alaman barci yakeyi a lokacin don yadda ya amsa min sallamata din naji muryan nasa.
Gaidashi na fara yana amsa min a dadare har muka gama gaisawa kafim nace dama magana nake sonyi dakai na kira kafin inci gaba yake fadin .
Bangane dawa nake magana ba fa ya tambaya kamar ya kagu daya aje wayan nace Allah sarki kana magana da sister ka Fatima kan war tsohuwar matar mariganya ya safiya.
Dan murmushi naji ya sake a bangarenshi kafin yace wai dama kece lafiya dai kika kirani yau din nan don naji mamakin hakan ?
Lafiya kalau sai alheri dama wani zance nake ji akaina don ni bansan da zancen bama akan amaryan ka samira sai jiya nake jin wai wasu sun canza labarin sun juya zance akan samira kuma.
Look Fatima ki fada min kawai kina son juya zancem a kan wani abu dai nace Allah ya ba hakana bane duk wanda zai fada ma yasan komai karyane.
Abinda ya kawo sunan Samira a cikin zancen shine don tare ya sanni da ita kuma ita din yar uwatace shiyasa aka hada da ita amma aimu mukai kara basu ba munafukin daine baisan komai ba ya fadi karya.
Look fatima koma meye kece kika jawo hakan da kin yarda dani tun farko daduk wa yanan abubuwan basu faru ba dama yanzu kin dade a gidana.
Koda yake yanzu nagane nufin ki don kina son ki kai wani matsayi da ban taba zatonshi daga gareki ba sai jiyan nan na kara gaskanta hakan dana gani da idona.
Babu komai a zuciyan ki sai duniya da yan iska da suke hure maki kunne kina daukan kanki ke wata tsiyace a yanzu.
Ido na runtse cikin takaici ina ba zuciyata magana don ba yanzu bane lokacin bashi amsa tunda bukatane a gareni wurinshi yanzu din har yasa na kirashi.
Da kyat na iya fadin Allahne shedata da abinda kake zargina dashi amma ka tuna koda anty Safiya bata raye har gobe da tarbiyan nan da kuka bani kaida ita nake amfani don har yau ban canza sunana daga Fatima bintu ba daka sani.
Allahne shedana ga hakan ni yanzu na kirakane in fadama gaskiya abinda na sani don in fitar da yar uwata daga zargin da kake mata ka huta lafiya ina kokarin kashe wayan naji yana magana ban tsaya sauraren shi ba na kashe wayan ga baki daya.


ZAINAB IDRIS MAKAWA









KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
6?? 2??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Oga Abbas ya kirani kan likitan da zaiga baba yana Nageria don haka mu taso kafin ya bar Kazan hakan yasa na dira Kaduna ba shiri don tafiya da baba din alokacin.
Tafiyan ya kasance ba shiri da mama da ya Ahmed mukai tafiyan naso ace munje da Nura don yafi ya Ahmed kazar kazar da iya kulla da baba din.
Amma ba yadda na iya yadda sukace hakan za ayi don sune manya a gidan namu dole a bisu yadda suka tsara muna mota lafiya na daukan muna shata har zuwa Abujan.
Da yake tafiyan safe mukayi lokacin sai muka isa da wuri don goma da wani Abu muna cikin garin abuja din a ranan don haka na kira oga Abbas na fada mai isowan mu garin.
Bai dauki way a ba lokacin har kira biyu nayi masa bai daga wayansa ba hakan yasa muka samu wuri mai dan innuwa muka tsaya saboda baba a lokacin.
Lokaci na dan bada na sake kira bai dauka ba dan guntun tsuki naja ina kallon baba din sai nayi wani tunane kafin na daga waya ina neman Number a wayata.
Boss nagani kamar yadda na rubuta a wayan nawa cikin fargaba don rashin sanin abinda zai biyo baya na danna masa kira naji wayan busy yasa na tura mashi sako baifi minti biyu ba sai ga kiran Oga Abbas a wayana.
Yana fadin sorry kanwata ashe kinta kira ban kusa da wayan muna meeting da Boss a lokacin yanzu kuna ina ya tambaya ?
Driver ya fada min daidai inda muke na fada mai yace in ba driver din waya suyi magana yayi mai bayani yace ya gane wajen muka nufi can kai tsaye.
Nida ya Ahmed muka fita muka fara neman wanda yace mu tambaya din idan munje aka nuna muna office dinshi keda ganin wajen zaki gane gidan kudi mukazo da baba din.
Mutumin yana ganin mu kafin in masa bayani yace daga Mr Bashir ko nace eh ya mike ya fito yana kiran wasu nurse suje su shigo da baba din suka dauki while dinsu zuwa waje ina biye a bayansu.
Wani daki suka kaishi bamu ko kaiga zama ba aka fara duba baba din nan take muna waje zaune aka daura masa ruwa da sauran treatment irin nasu don karfin jikinsa ya dan samu.
Kula kan mun gashi har driver daya kawo mu din ina batun sallamanshi aka kawo muna abinci daga oga Abbas din don haka muka dakatar da driver ya tsaya sukaci da ya Ahmed wanda yana da sauri sabo mutumin kamar yadda wasu dribobi suke da sakewa.
Ya gama lokacin oga Abbas ya iso wajen a cikon motansa ya gansu bai ganesu ba ya wucesu saida ya shigone ya sameni a dakin mama tana sallah a lokacin.
Muka gaisa dashi yake tambayana jikin baba din nace da sauki ya taka zuwa gadon inda baba yake kwance yana barcin bautan Allah ya dan dade tsaye yana binshi da kallo.
Kafin ya juyo yana cewa dani likitan ance bai shigoba ko sun dai fara dubashi a yanzu bayanin da sukai min a waya .
Mama ta idar da sallah tana mashi sannu da zuwa suka gaisa irin ta al,adan malam bahaushe yadda yake gaisuwanshi tare da tambayanshi iyalinsa aiki da sauransu yana dan murmushi.
Bayani ya kara mata inda mamake fadin aiba matsala dama lafiyan akazo nema ai dole sai anyi hakkuri anbi a sannu Allah dai yasa a dace kuma an gode.
Ba komai ya fada yana ficewa tare da kara fadin driver din ya biyoshi suje ban fita ba don ganin ya Ahmed ma ya bisu a baya don ya karbi number driver din don sako.
Saida aka jima ya Ahmed din ya shigo dakin da leda ya zauna yana fadin komai garin nan tsadane dashi kafin ma in samu wani aikine babba don babu shagunan unguwa ko ina kaf layin nan.
Dan murmushi nayi nace ya This is Abuja's city a ina zaka samu shaguna yadda kake nufi din nan aiko naga alaman hakan sosai don saida na hau Nape zuwa wani unguwa .
Likitan ya shigo dakin don ya duba baba a nan yake muna bayani karfe bakwai zasu daukeshi za ai masa awo na musanman don a gano abinda ke damunsa don haka muna iya tafiya mu koma gida sai gobe mu dawo.
Nan su ya Ahmed din da mama suka so sa gardama basu tsaya kulashi ba suka fice suka barmu na zauna ina fahintar dashi abinda ke nan ya daiyi shirune ba don ya yarda da wanan tsarin nasu ba.
Saboda na fito bayi na samu suna tsegumin da mama yana fadin wanan ai kafirci ne ace kabar majinyaci a hannun kafirai suyi jinyarsa gaskiya tsarin baiyi ba.
In ma ance hakan a ina ake son muje mu kwana ke nan yanzu ni dai ban masa magana ba na tayar da sallah don gabatar da la,asar naga ya fita.
Dumuwana shine Allah ya tayar da kafadan baba ya samu lafiya a yanzu hakan shine burina har kasan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login