Showing 186001 words to 189000 words out of 347556 words

Chapter 63 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8765

min hakkina na bata min suna da tayi a cikin unguwa bama iya unguwar ba har a median an saka wanan labarin duk gari kasa kasa sunji abinda ya faru.
Kana kuma har wayau aje har gidan mara lafiyan nan a bashi hakkuri kan abinda ya faru bayan yana kwance yana jinya .
Ba bata lokaci wani dan uwan babanta yace sun yarda indai case din zai tsaya iya nan zasu biya komai kamar yadda aka basu dokan yi su dai burinsu kada ace za a shiga kotu dasu kada sunansu ya baci gashi mahaifinta dan siyasane shi.
Dan sanda yace bayan haka zasu jefata baya kanta ko a biyasu kudin tara batawa hukuma lokaci da tayi duk sukace sun dauka a daiyi hakkuri don Allah.
Bin mu tayi da kallo ta daga hannu tana fadin wai tana da magana aka bata dama tace itama tana son aiwa mai bin mijinta kashedin cewa ta rabu mata da mijinta daga ranan don Allah tana son hukuma ta shiga tsakani.
Daga can gefe wani ya daka mata tsawa yana fadi basu son shirme da shashancin banza ana kokarin ganin an kashe case ita kuma tana dauko wani zance yanzu kuma.
Haba yaya ka bari tun ba,a tafiba aimuna iyaka da ita mana ta rabu min dashi don wallahi ni ba zan yarda da hakan ba.
Dariya ta basu jin hakan yasa na kasa hakkuri na dago na kalleta nace ki dai yiwa mijinki kashedi ya daina bina don ko gobe yazo inda nake zan saurareshi tunda haka kike so.
Da ace kin bini da arzikine zan maki alkawarin barin shi har abada amma yanzu sai na shigo gidan nasa inga abinda zakiyi.
Ina fadin hakan ta wani zabura tayo kaina kamar zata shakeni nima na mike tsaye kafin ta mike Hassana da wanan yar sandar macen suka rikeni.
Nace aida da kanki kikazo bada mazan daba ba da kin san shayi ruwane mijin ki kuma shike bina bani ke binsa ba don baki taba ganin kafana a gidansa ba.
Kuma na isane ya biyoni don ke baki ishesa ba mu ukuma bani daya zamuzo ba sai ya auri mata uku mun zauna dake a gida daya muga abinda zakiyi din.
Tace min ke karamar karuwace wallahi baki isa ba kinyi kadan nace har nayi yawa kuma wanan kallama karuwa da kika kirani dashi a yanzu basai naje gida ba zan saka karanki abi min hakkina akai .
Don ba zan yarda ba ko yatsa wani na miji banza bai taba taba min ba balle ki jefeni da wanan kallaman ta karuwa jn kyaleki
Daga can wani dan uwanta yace you see dama nasan wanan mahaukaciyar ba dainawa zatayi ba yanzuma kunji abinda take kokarin daukowa mutane dai.
Na juya ina fadin office a yankamin takardan kara don Allah bayan wancan na farkon haka dai na koma masu yar daban gaske a wajen.
Suna ganin abu zai zama gaskiya nan akayo kanta ana mata fada tana kuka tace tsakaninta dani Allah ya isa tunda na shigo masu rayuwa suna zaune da mijinta kalau.
Nace yanzuma na fara son mijin naki ai don halinsa na kirki yayi min sosai irinsa ko wace mace keso dama ta aura don haka kiris ya rage muna mu aure dashi gashi ki tambayeshi kiji.
Sai lokacin yayi magana duk zamanshi wajen yace common fatima is ok don Allah ku bari hakana abi komai yadda suka tsara ayi ya fada yana mikewa tsaye.
Ya kalli office ya fito mai a surar sojan shi na kwarai yana fadin office i hope an kawo karshen case din nan na da dan lokaci za a je gidan aga irin barnan da akai masu akuma bada hakkuri ga mahaifinsu.
Saidai ita wanan din ya nuna samira data shiru ina son a saya min ita har na waiwayeta don ita takawo wanan fitinan ga baki daya.
Ta batawa yar uwarta da gidansu suna ita kuma wanan don bata da hankali ta yarda da shirmenta da son samune gaba dayansu zaku saya minsu don wanan haukan da sukayi.
Kuna son kashe mutumin da baida lafiyane kome don haka nake son aiwa yarinyar nan hukuncin hada wanan fitinan.
Kallonsa nayi zanyi magana ya daga min hannu daga hakan ya fita daga station din kai tsaye zuwa motarshi ransa a bace har lokaci muna kallo aka izza keyan samira gaba.
Muna tsaye muna duban yadda zamuyi ga fitinar matarshi dake ta kuka yan uwa na jan ta a wajan sako yashigo min a wayana na dan daga sakonshine nagani yace.
Ki barta ta dadani abinda tayi sai zuwa dare zan sa a sakota ga mota nan brother dina zai mayar daku gida iya abinda ya rubuta ke nan a lokacin.
Nima haka yai min dadi nacewa su Nura muje gida dama hassana ta matsu mu wuce muje gida mukai labari har muka fito akwai mutanensu a wajen .
Daga nisa kanin nasa yai min hannu tare da horn na gane shine zai kaimu gidan ke nan nan kuma mutane da basu raina abin gulma aka tabo matar soja tabimu da zagi saida wanan yayan nata mai zafin rai ya kwala mata mari a fuska.
Muna kallo lokacin muka tafi bamu san yadda suka karasa ba saida muji a wajen su Nura dake baya mu mundan dauki hanya naji wana daya dauko mu yace.
Kai rayuwan turai baiyi ba wallahi wanan yarinyar ta dauka nan ma turaine zata kawowa mutane hauka kun min daidai da kuka dauki mataki haka.
Don gaba ba zata karan hakan ba tana taka kowa yadda take so ba mai mutunci a wurinta kaf family din mu yau wallahi naji dadin abin nan sosai.
Nan muke ta hira yana fada muna halaiyata sai tausayin mijinta ya kamani mutum kamar soja ace yana auren mace irin wanan har kofan gidan mu ya kaimu ya saukemu yana kara bani hakkuri ya tafi.
Hangosu Nura danayi yasa na tsaya suka sameni suna fadin yanzu a can za,a bar Samira din nace kawai kada mu bari dai baba yaji wanan maganan musan abinda zamu fada a gida ko zamu fadi mu bari sai munje daki.
Nima dama abinda nake son fada maku ke nan isah mai shago ya fada nace ni da kaina zan shiga jn masa bayanin komai yadda zai fahinta.
Kai gaskiya rayuwan samira baiyi ba wallahi Nura ya fada yana jan tsuki ya bar wajen na dan tsaya da isah yana kara ban hakkurin irin rayuwan da nake fuskanta a gidan namu.
Na shigo nasamu mama uwa tana wanki mama lanto kuma tana daukan kwanonin abinci da zata saka abinci a ciki kalla bata ce min ba nima haka sai mama Uwa kecewa kun dawo na amsa da ehh kawai na shige dakina.
Saman katifana na fada ina sake huci a bakina don raina in yayi dubu ya baci a lokacin don yadda nake ganin bakin samira banga na matar sojama hakana ba.
Tambaya kaina nayi wani irin kiyayyane haka samira take nuna min rayuwan muna baya na tuna nidai banga abinda nayi mata ba ko nayiwa uwarta meye laifi yanzu a garesu newai na tambayi kaina.
Mama uwace ta shigo tana fadin da sauki dai ko mu muna nan hankalinmu ya tashi ina ita samira din ta tsaya naji uwarta na fada wai laifin da bai shafeta ba za a sakata a ciki keda dauko rigima ina ruwanta ita.
Na dago nace duk fa ita ta kawo wanan abin mama itace ta bugawa matar waya wai mijinta yana nan yana kashe min kudi har tafiya muke zuwa tare takuma bada lamban gidan nan wai tazo har sunana da komai.
Amma ko Allah yayi yar banza bakin cikin nata da hassada har yakai haka ashe kaiwa dan uwaka na jini sheri irin haka wana zamani abin tsorone gaskiya.
Tana ina yanzu nace tana can an tsareta sai bayan sati biyu akace salati ta saka tace shike nan ah shike nan mana idan gidan su Mahmud sukaji ai shike na kuma dama hjy ba auren na takeso ba fin karfinta dai akayi kawai.
Daga kofa naji muryan mama Lanto na fadin Binta ina kuka bar ita samira din na kalli mama uwa itama ni ta kalla ta kara daga murya tace nace ina samira din ta fada tana daga labule nace bansan inda ta tsaya ba.
Juyawa tayi ta tafi nace batin je inga baba mama yana zaune na sameshi na fara mai bayani baya mun gaisa alaman gamsuwa da abinda nake fada mashi din don naga yana kada kai.
Aiko mama lantone tsaye a kaina ta cabe zancen da fadin kika barmi yarinya a can wurin yan sanda don sheri da bakin ciki Bantu lalaikan kin nuna min ke yar ubace ta gaske.
Keda dauko rikici yanzu kuma ki juye min kan yarinya lokacin da kike bin mazanki baki tunanen haka zai faru ba ni meye laifin yarinyar na a cikin maganan nan ?
Laifi kan ai itace mai laifi ko kana abu karka hada da gayya yanzu ace Samira don sheri ta dauki waya ta kira matan bawan Allah nan don hassada ta kwashi karya da gaskiya ta fada mata don bakin ciki kawai.
Yau naji ikon Allah a gidan nan yau kuma Bintu ce kika shigarwa fada kuma yaya lalai abin mamaki yanzu baida wuya a wurin mutane .
Dama hada baki akayi ai mata hakan don kawai a tozarta mu don ana bakin ciki damu a gidan nab ni ku fada min ko sani wuri in tafi.
Kije ina mama bafa ko wurin yansada take ba kuma ko kije wayw zai kalleki case din gidan masu kudine fa ta jefa kanta sukan sun karbi yarsu sun tafi ita dai data fada aka bari a can .


ZAINAB IDRIS MAKAWA
KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
5?? 8??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Dama nasan za,a rina mama lanto idan taji zatayi muna fiye da hakan already hassana ta labartawa mama komai a dakinsu sai ga mama din na fadin.
Dakata Lanto dakata don Allah kada ki tara muna gida da jama,a yanzu wani abin kunyar da bakin ciki ya sake samuwarmu kuma a unguwa bayan wanda ya faru kuma.
Wanan idan kinsan ciwon kanki dana yarki ai ba abin daga murya bane gareki yanzu don Samira ita taja komai kuma bata boye ba tayi bayani a wajen yansanda da akaje cewa itace ta kira matar mutumin nan tayiwa yar uwarta cune a wajenta don kawai azo nan ayi muna wullakanci.
Duk akan bakin cikine ko hassada da yai mata yawa a cikin jini kome oohoo inba rashin wayau ba har kiyayyan da takewa yar uwa yakai taja muna wanan bakin cikin a gida?
Ahhye nanaye wai inda ranka kasha kallo yau kuma akan Bintu kike wanan maganan da bakinki yaya a gidan nan lalai abin mamaki baya karewa duniya.
Yanzu ba wanan ne a gabana ba yadda yata zata dawo gareni nake son ji tunda duk abinda ake ciki nagane hadin baki akayi daku don kawai a tozarta ta a idon mutane saboda ganin Allah ya rufa mata asiri zata gidan miji akewa hakan bakin cikin .
Ke kuma Bintu indai yayane kinyi da banza don wanda zatayi maki nan gaba sai yafi wanda ta saka kikaiwa yar uwanki a yanzu don rashin tunane ki rasa wanda zaki hada kai a tozarta yar uwarki sai su yaya ?
Kai haba haba mama ki daina wanan daga harshen don Allah kowa ya kwaso sherinsa yace Bantu bantu dai bantu dai haba don Allah wanan abin fa a gaban mu gaban isah mai shago akaui case din nan.
Samira ta fadi gaskiya har yadda ta samo lambar matar sojan nan ta wata kawarta duk ta fada yanzu kuma kizo nan kina kokarin lauye wanan zancen idan badkn ita Bantu din da tace kada mu tayar da wanan zancen unguwa a sani ba don Allah aida zance yabi unguwa tunda tare da isah mai shago mukaje a gabansa akai komai kuma.
Amma ta taramu ta rokemu don Allah mu rike wanan maganan kada zancen ya fita aji don baida dadin ji gashi kuma Samira aure zatayi cikin kwanan nan mu rufa mata asiri don Allah kada aji zancen nan .
Koba haka ya faru ba Hassana ya juya yana tambayan Hassana din tace ai ba zata fahinci hakan ba wallahi yau danice Bintu banga abinda zaisa in boye duk wani mai son ganin bayana a duniyan nan .
Yanzu dai ba wanan ba kamata yayi a zauna aji yaya za ayi ita samira din tafito yanzu shiya kamata ace munyi ba wanan don wa yancan ma da suka karbi yarsu masu haline sosai duk abinda akace a bayar sun bi doka ita dai samira dince aka rasa wanda zaibi mata a cikin mu don bamai karfi Nura ke wanan bayanin.
Wani irin kuka mama Lanto ta sa lokaci guda tana fadin abinda nake fadawa yarinyar nan ke nan baka kai mutum ba kace kakai kanka inda Allah bai kai kaba shi arziki na Allah.
Idan kobana Allah bane da wasu basu kai inda suka kai a yanzu amma saboda halin irin na dan yau yarinyar nan bataji maganata ba saida taje ta aikata abinda zai kaimu ya baro a karshe.
Ko yaushe ina mata fadan kawar da kai ga wani da abinda yake amma duk bata ji wanan ba lalai kan dan yau da uwayen yau sai a hankali don zaka san yaro na abinda ba daidai a rayuwa amma kana gudun zuciyar shi kada ransa ya baci har yakai ga jawo maka abin kunya mama Lanto ta karasa.
Kallonta kawai tayi ta juya ga Nura don yanzu maganan Nura shi tafi yarda dashi tace Nura yanzu meye abinyi don Allah ?
Ah mama nikan yanzu tunda banda kudin kaiwa ayo bellinta me zance gadai wace ya kamata ayiwa magana yanzu itace kuma tayi wa laifin sai a nemi sulhu gata zaune aji yadda za,ayi don itace lamba taran gidan mu yanzu ai.
Ko bata bada kudi ba tayi magana ansan yadda za ayi dasu son dai wallahi mutanen nan basu da imani ki duba fa ita matan mijinta babban sojane amma haka suka wullakantata a gabanshi ba tsoron shima mai kaki ne.
Kaima kasani ai duk abinda zan fada a yanzu Bintu tana cikin zafi damu ba zatajini ba don zataga kamar da sanina hakan ya faru ku dai zakuyi mata magana don Allah kila tafi ji dani ai.
Dan murmushin gefen fuska nayi nace mama ke nan nikan kaf gidan nan bana kwana da kowa a raina balle in rikeshi abinda tayi ai karshe kanta ya koma yanzu don me zan tsaya fada baya ubangiji yayin da kansa.
Yanzu dai kuje kuji halin da ake ciki in yaso sai a san yadda za,ayi daga baya kuma inyaso sai mubi don yanzu nasan tana can cikin damuwa gaskiya na juya ina daukan ledan maganin baba don in bashi yasha yana zaune sai ido yake bin kowa dashi babu abinda zai iyayi nasan a zuciya yake magana lokacin tunda yana fahitar meke faruwa.
Nan dai suka fita da Nura suka bar kowa na nasa fadan a tsakar gida don mamaki ya kama kowa kan wanan abin da tayi mama kan tafi kowa jin dadin hakan a cikin zancenta mutum zai fahinci hakan.
Sunje da kyar aka bari sukaga Samira din koshi don kukan da mamake tayine taba yan sandan tausayi amma tasha bakar magana duk Nura na recording komai akansa.
Kafin suka bude mata ita ta fito Nura yace duk ta fada lokaci guda tayi kuka kamar ranta zai fita a lokacin fada sosai mama din tayi mata a can tace tayiwa kanta taja masu abin fade wa zai yarda ya dauki kara da kiyashi yasaka a zuriansa yanzu kan ai aurensu da habibi sai Allah.
Har lokacin da aka basu su ganta yayi suka fito don ance sai nan da sati biyu zava nemesu su ji nawa za a biya don ita wacan zasu kashe wurin miliyan daya saita gyarawa baba gidansa datasa aka bata ta biya kudin wasu abubuwa kuma.
Nan suka juyo hankalisu tashe suka barta tana gunjin kuka suna jin muryanta har suka fito cikin station din wani office yana daka mata tsawa da ta rufe masu baki munafaka kawai .
Ranan mama idan tasan yadda zata hadi rai ta huta data yishi a rayuwanta din yadda take jin kamar zuciyar zai bullo ya fito.
Ni dai koda


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login