Showing 309001 words to 312000 words out of 347556 words

Chapter 104 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8794

lokacin suka hau dan kitsawa tare da neman in masa iso ya shigo ina kula da yadda mahaifiyat tawa take dan satan kallona a gefen idanunta don tunda muka gaisa bata sake dago kai ta kallo waje da nake zaune ba.
Bashir baku huta ba kuka taso ai gobe muke da niyar zuwa wajen ku sai gaku don jibi in Allah ya kaimu zamu tafi kano jumma,a da dare zasu bar kasan nan mijinta ya matsa su dawo ta bar yara gida.
Yace gaskiyane mama mun gode shine na kawota nan kafin kuje gobe din mu gaida ku don mami ta fada min jibine zaku tafi din yasa muka taso kada kuzo gidan ban kawota ta nan ta gaidaku ba don jibi muma zamu tafi Abuja daga nan zamu fita sai bayan azumi zamu dawo Nageria.
Dago kai nayi na kalleshi don bansan wanan shirin ba a takaice dai zamuyi kamar wata uku ke nan acan yadda ya fada din nan Ammi ke dan jansa da hira kadan kadan nagane a kage yake lokacin.
Nasan maganan dole yakeyi a lokacin don haka na dukar da kaina kasa ina saurarensu can nake wasa da dan hajja Zaina dake tokarana da kafanshi yana wasa hakan ya bashi daman fadin zai dan fita ya dawo ya daukeni.
Bayan fitanshi ba,a jima ba saiga yara suna shigo da kwalaye cikin gidan suna fadin mai motan nan ya bayar a kawo baifi mintuna biyar ba kuma saiga yaro yana fadin ance in fito don haka na karasa zance da mukeyi da ita bayan kamar minti biyar na fito muka dauki hanyar gida.
A wani waje yayi packing ya fita ya shiga ya dan jima ina zaune cikin motan na hangoshi ya fito wani ya biyo bayansa da kaya niki niki leda biyu.
Muna ya saka mai bayan mota ya zagoyo ya sallamishivya tayar da motan muka tafo muna isa na fito daga motan ban tsaya jiransa ba na shiga ciki kai tsaye dakina na nufa duk da gidan yai min wani irin girma a idona .
Ban tsaya jiran komai ba bayan nayi sallama nashiga na fara rage kayan jikina saura min dan unders din ciki ya shigo dakin yana fadin sauri me kikeyine haka ki fito muci abinci bana jin cin komai har ya juyo yaji hakan ya juyo yana sauke min kallo.
Kamar ba zaiyi magana ba naji yace me kike nufi nayi shiru ya juya ya fita na karasa abinda nakeyi kafin na shiga na dan kara watsa ruwa na feshi jikina da kamshi ranan banyi gigin shafe shafe da yawa ba na mara din nan dai na dan goga saboda kamshisa yana min dadi a hancina.
Tsab na fito na sameshi falon zaune yana waya ya kunna tv tashan Al,Jazeera suna news yana kallon su nayi sallama kujeran gefenshi nayi niyar zaunawa sai naji yana min alaman inzo nan kusa dashi in zauna hakan yasa na dago na gane nufinsa amma sai na share kamar ban fahinceshi ba.
Wayan ya daga yana fadi bakiji bane ya kara taba inda yake son na zauna din da hannayenshi dole na nufi can din na zauna a kusa dashi din na kurawa tv idanu zuciya kuma tana zance.
Kada kiyi saurin nuna masa zakewanki Fatima ki bishi kamar wawiya a yanzu ki zama daliba ya zamo master nan gaba hakan zai maki dadi shawaran Fadila kawata ta kt ke nan a gareni.
Nuna masa kema kin waye kada ya daukeki kidahuman yar kauye baki waye ba sai a gidanshi ki nuna masa kema A ce don kada ki daukarwa kanki raini shawaran yan uwana Usaina ke nan a gareni cikin biyun yanzu wane zan zaba na tambayi kaina a wajen.
Idan kin nuna ke kin waye ma,ana kinsan komai kenan kafin aure ba akansa kika san zama da namiji ba ke nan naba kaina amsa don haka shawaran Fadila din dai na zaba a kaina.
Zuba muna wanan din muci kan mu kwanta ya fada baya ya dan daga wayan nasa gefe kallon ledan nayi akwai plate a wajen don haka na jawo na fara kiciniyar budan ledan.
Wani kamshi naji a lokacin yasa ban tsaya nayi sanya ba don son ganin abinda ya tsukar min da yawuna da kwalwan kazace a cikin kwali har lokacin da zafinsa sosai .
Na dauki dan yukan ina dan yaga a cikin yanga naji yace miko?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? min yukan na hana su yanka muna ne don bansan tsabtan hanayesu ba yana yankowa ya nufo bakina yana kokarin bani na noke kaina alaman kunyar hakan yake fadin karbi mana bazan barki bafa sai naga kin koshi sosai.
Nace ai a koshe nake yace idan ba zakici ba zamu kwana a nan zaune dake hakan yasa na dan bude bakina ya saka min yaci gaba da yankawa yana tarawa kafin na taune na bakina ya jawo cup ya tsiyaya ruwan milki din Ahhard na dake cikin kwali da photon shanu sai da cup din ya dan tasa ya aje a gefe daya.
Ya kara dauko wani yankar yana mika min na bude bakina da kyar ya saka min kafin na hade ina fadin kai ba zakaci bane sai naga ya lumshe idanunsa yana fadin baki ban bane.
Jin hakan yasa na dan dago kai na kalleshi ciki kunya kafin na mika hannu a hankali ina dauko naman ina bashi a baki jefi jefi har muka dan kosar da kanmu ga hakan.
Muna gamawa na tattara kayan da niyar nakai kitchen don kitchen din yana da dan tazara da falon gidan ya dakatar dani da fadin barshi zasuzo su kwashe idan mun tashi.
Idan zaki dauko wani abu a daki ki dauko muje mu kwanta yau nagaji bana son nawuce goma ban kwanta ba ya fada yana mike tsaye daga inda yake zaune yana tatara wayoyinshi zuwa ciki.
Ba zance bansha wuya ba saidai ba kamar na ranan ba don shima bai zure min hakan ba gudun samun matsala kar na kara jawo masa magana a bakin Abbas kuma.
Kinga yaron nan dan iska nagane shima yana da shiri a kan mu don kamar yasan duk abinda muke shiryawa akansa ni nagaji da wanan abin gaskiya duk dai abinda muke hasashen yaron nan zai zamo kamar yazama a yanzu ko.
Tunda bai dogara da kowa a cikin mazajen mu dama dai avin tsoron mu shine yazo ya dafa daya daga cikin mazajen mu yaran mu su koma bayansa .
Yanzu yabi wani sarkin ya dafa har ya samu ya mike yanzu meya saura kuma a cikinsa aikin gama ya riga ya gama ko tunda yaron nan ya bunkasa fiyema da tsamanin mu.
Dakata hjy maryam so kike ki fada min kin sare da zancen yaron bashir kome bari kiji ban taba sarewa ga hakan sai naga bayanshi wallahi sai ya koma ko abin sayen goro .
Ga dama ya kara samu a yanzu da yai auren nan da matar tasa zan hada kai inci galaban dan banza a saukake yanzu ba tare danyi wani wahalan biyan kudi ba ga kowa yai min aiki ki dai sa ido kiyi kallon mamaki da shu,umancina kawai.
Anya ya kamata muyiwa kanmu fadan ta natsu fa a yanzu ko don cigaban namu yayan nan gaba don ba zamuso aiwa yaya mu hakan ba ai don Allah abar wanan zancen haka zai fi.
Yarinyar nan ba kamar yadda kike dauka bace tasan kanta fiye da tsamanin ki Laila gara karma ki soma wanan shirin a kanta zaifi maki sauki .
Maryam nace ki barmin komai a hannuna ni kadai na isa inyi komai ku saka min ido kawai kuyi kallo tana fadin hakan ta kashe wayanta.
Murmushi hjy maryam din tayi tana fasin daukan wasa kikaiwa wanan yarinyar karan dafice ta sosai da ake kira mata dama lokacin nasan zai auretane nayi wani abu a fasa auren nan tun lokacin zan yarda da shawarki.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
9?? 8??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Bayan na fahinci kokarin shi a kaina nason na sake jiki dashi ko yaushe hakan yasa na dan fara sakin jiki a gidan don tunda mukayi sallah asuba na koma na kwanta ban jima ba na fito don ida abinda nake son yi.
So nake na hada muna breakfast da kaina a matsayina na macen gida wanda ga al,adanmu na hausa nice da alhakin yin hakan ga mijina.
Don ban yarda da wanan akidan turawa da yake son kawo min ba na ina kwance ana min girki girkin ma wani katon arne da bai sallah zai girka muna muci wai.
Dakina na shiga na sauya kayan jikina nafito zuwa kitchen din gidan babu kowa a cikinsa sai manyan na,uran wuta dake aiki su kadai a kitchen din.
Hakan yasa na samu daman aiwatar da abinda nake so har saida kamshi ya ziyarci hancinan mutanen gidan saiga wanan Samuel din ya shiga yana ganina saida ya dan kadu .
Ya fara gaidani cikin inda inda na amsa mai don naga yadda Ummu kewa yan aikinta a saudiya tana daukan girman ta da jan aji.
Bai wai nayi hakan bane don fadin rai bana dai son yana shigo min inda nake: bayan mun gaisa na juya naci gaba da motsa abinda naKe hadawa din lokacin kuma naji muryanshi ashe bai tafi ba yana tsaye bayana.
Yake fadin Can I help you mah da sauri na juyo ina fadin a,a nagode zaka iya tafiyan ka ba matsala ni zan dinga girma muna abinda zamuci daga yau .
Har fuska ba zuciya kawai ba saida fuskansa ya nuna rashin dadin hakan nikan na juya ban tsaya ta kansa ba naci gaba da hada muna breakfast din.
Bansam lokacin daya bar wajen ba don na mayar da hankalina ga hadin pancake din da nake muna wanda na koyo a saudiya hadi na musanman.
Karfe takwas da rabi nagama hada abinda nakeson hadawa kulolime gasu nan sabbinsu sai wanda na zaba a kitchen din na shirya komai na koma daki don in tsabtace jikina.
Har na fito na shirya banji motsin shiba na dauka bai tashi daga barcin ba don haka nayi zamana a daki don kada na shiga na bata mai barcinsa.
Ba waya tv dakin kuma ban iya hadashi ba ina kunyan in tambaya ya daukeni bagidajiya a idonsa yasa naja bakina nayi shiru lokacin ga wayata daya karba ban san manufansa na karban wayan a hannuna ba.
Don bai bani ba ban kuma ga wayan a dakin ba koda yake iyakata da dankin ai sau biyu na shiga na kwanta na fito yau dai nake son shiga in gyaro dakin da kaina insha Allah.
Irin wanan tunanen nakeyi daga inda nake kwance na lafe jikin katifa zakice barci nake a yadda na kwanta din na lafe daga nisa hancina ya sanar min da fitowanshi don kamshin turarenshi daya ziyarci hancin nawa duk da haka ban motsa a yadda nake kwance ba.
Murda kofan yayi ya shigo yana fadin Fatima barcine har yanzu na dan motsa tare da juyowa ina fuskantarshi daga inda nake nake fadin ina kwana lafiya ya fada yana miko min hannu tare da fadin ki taso muyi breakfast.
Sai dan an jima zan karya kizo ki ban zamu fita da Abbas yana hanya tafe ya fada, har lokacin hannunsa yana hade da nawa ya dagoni ba musu na bishi na mike.
Ya dan rikoni muka fito zuwa falo inda dining din cin abincin yake har lokacin nasan baisan cewa ninayi aikin ba don banji yayi min magana ba nima hakan nake so din.
Tun daga nisa yake kallon yadda aka hada komai ba irin hadin Samuel dinshi ba da zamu zauna ya sake min hannu ya kai zaune ban zauna ba tunda yace na bashi abinci shina fito in bashi din .
Yana zama wayanshi na daukan kara ya dauko yana magana har na bude na fara zubawa kafin na aje a gabanshi na gyara cup din ruwa da gora a gefen shi nayi niyar barin wajen in zauna lokacin naji ya riko min hannuna.
Na juyo yayi min alaman in tsaya dole naja na tsaya ya gama maganan da yakeyi da yusuf dayan aminin shi dan gundura nayi da tsayin har na lula duniyan tunane naji muryanshi ya dawo dani daga tunanen da yace.
Na dauka ai kece zaki ban yasa na dan kallo inda yake gashi na zubama ai na fada ina wani mus,musu da idanu cikin jin kunya nace gashi ai na zubama .
Sai naga ya dan lumshe idanu ya mike tsaye kujeran dake gefe ya jawo kusa da inda ya tashi ya kawo bayana ya aje min yana fadin zauna a nan ya koma ya zauna.
Dole na zauna a kusa dashi ya dauki cibi ya fara dan juya abincin kafin ya diba ya kai bakinsa yana bissimila yana taunawa naga ya dago kai ya kalleni sai ya koma ga dayan plate din ya diba ya dandana ferfesun dake ciki ya kalloni yana fadin .
Wayayi girkin nan a hankali na bashi amsa da nice na dukar da kai kasa ya dan kura min ido sai kuma naga yaci gaba da cin abincin baiyi magana ba kuma bai dago kansa ba saida yake son ruwa ya dan dago yana fadin zuba min ruwa don Allah.
Lokacin na motsa na jawo cup din na fara tsiyaya masa ruwan a cikinsa a daidai lokacin Abbas ya shigo falon yana sallama ganin yadda muke zaune yasa ya tun tsure da dariya yana fadin.
Shiyasa akace ganin kwam samako gidan amarya da ango kai kana nan zaune a binka da matarka kana karyawa ni kuma kun hani tsayawama in karya da iyalina.
Kujera ya nuna masa kafin na katseshi da fadin ina kwana brother don haka ya juyo yana fadin kun tashi lafiya kanwata ya gida ya bakunta kuma ina fatan dai baki cikin takura dai ?
Dan murmushi nayi ina girgiza masa kai naji yace dashi zauna kaci girkin kanwar ka tace bata son Samuel yana mata aiki ni kuma bani da ra,ayin mata tana shiga kitchen.
To yanzu alkalanci kake son nayi ke nan ya ware masa idanu tunda naga yana jan kujera zai sauna nayi kokarin tashi wurin ya kalloni yana fadin ina kuma zaki ana magana na koma na zauna kamar yadda nake.
Ina fatan dai ta iya girki abu na farko ke nan idan baki iya ba kinji mijin ki yace ya hutar dake ga komai yanzu mai zaisa ki takurawa kanki haka ya debi abincin yakai baki .
Sai naga ya dago ya dan kalli bashir din gyara zama yayi yana fadin wane Samuel ke nan dama haka kika iya girki Fatima ya dan kalloni yana kokarin diban abinci a plate din.
Wanan kan ba alkalin kwarai bane ashe ya fada yana gyara zama yana kokarin jaye plate din dayaci na farko din zai dauko na ferfesun yasha.
Gani hakan na jaye Abbas tace kaga aure ke nan kayi aure tun tuni ka more ka tsayawa mutane burgan aiki yanzu gaka ka zamo sarki a gidan ka.
Ni ya nuna mai da cokalin dake hannunsa yace metayi yace ka tambayeta meyasa bata zo da wuri munyi auren ba tunda itace Allah ya kaddara min a macen aure.
Don haka Laifin tane ita dataki baiyana da wuri mukai ga auren sai yanzu data baiyana kuma gashi kun muna korafi kuma yanzu na meye inba so kake in kara wata amaryan ba wani sati.
Cokali Abbas din ya aje yana hararansa kafin yace kanwata kake son lissafawa lissafin da sassafen nan ka mata mata yini da bacin rai murmushi nayi ina fadin baida matsala indai nice nasan suna tafe ai tunda hudu Allah ya sharada maku yi ni banda matsalan hakan ai.
Naji Abbas din yace wallahi bai isa ba kin isheshi ke kadai ina zaya da mata hudu sai kace zai kaiku kurmi sayarwa kece dai ta farko kuma ta karshe a gidan nan insha Allahu.
Brother ke nan kaji mutum ya fara zance ko sati banyi a gidansa ba ai hankali ya sanar da mutum gaskiyan ciki tunda ya fada hakan ne ra,ayinsa dai.
Bako wanan gidan ba Abbas din ya fada yana hararansa suka hau musu ni dai ina zaune ina kallonsu lokacin banji komai ba sai bayan sun fitane yace ba zasu dade ba idan su Ammi sunzo a kirasa suyi sallama dasu suka fita suka barni zaune .
Kayan na tattara na dauraye na kara gyara kitchen din kafin na dora abincin rana wa bakina kafin suzo na hada komai na koma na koma daki naji sallamansu.
Har su mama uwa da mama lanto wai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login