Showing 240001 words to 243000 words out of 347556 words

Chapter 81 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8782

falon muka hadu muka gaisa take fadin tunda weekend ne ya kamata na shirya a kaini gidan yayanta banki ba na soma shirin hakan.
Mai karatu na katse maki labari baya don a ranan dana cika kwana biyun tunda safe babana ya kirani yana tambayana kona tasone don ya dauka ranan zan dawo.
Amsan dana bashi shine ban taso ba baba naso na kwanawa Ammi biyu kafin in dawo da farko bai fahinceni ba sai daga baya kuma ya kara tambaya watace hakana ?
Nace Ammi yar mahaifiyata dake nan Gashuwa ina wurinta yanzu ya maimaita yar mahaifiyarki nace ehh Umma salma yar uwar mahaifiyata da take garin nan.
Umma Salma yaushe kika sanda ita nace a satin can baba shine nazo ganinta don in na fada ba za a barni nazo yadda nazo yanzu ba za ace sai an shirya niko na kagu dana ganta.
Ki gaida ita ya fada ya kashe wayan jikinsa a sanyaye yana tunanen a ina na samu labarin umma salman din da abin ya dameshi shine ya fadawa iyalinsa cewa ashe gun yar mahaifiyata dake kasan nan can na tafi ban fadawa kowa ga inda zan tafi ba.
Kai duniya akwai munafunci yanzu har an samu wanda yasan da matar nan ya kwarmatawa yar nan labari mama ta fada.
To kuma daine da abinku banda aon zuciya ai tuni ya kamata a fada mata wanan zancen tunda sunyi fushi sunki su biyo bayanta su dubata su aida ku kun sauke girman kai kunkaita tasansu.
Mama dake wankin tufafinsu ta dago tana fadin hakan wa baba da mama ta dauko zance tana shirin zuga baba a kan tafiyana duk da nasan da wuya ya yarda da hakan a yanzu.
Zai dai nuna min bacin ransa amma kuma ba zai rike sosai har ya bata min irin yadda take son ganin amin din.
Daga haka kuma baba din bai kara kirana ba yaji nima har wanan ranan kuma ban kirshi ba da tafiyan kawai nayi ko zan kirasa yafi a kirga don yaji lafiyata da inda nake.
A bangarensu Abbas kuma shima sin munyi waya dasu ranan bayan mun kunna waya na sheda mashi na iso lafiya ya dan zolayeni yana fadin aini da Boss dinsane tunda na fada mai bakar magana.
Nace ba bakar magana bace ai gaskiya na fada lokacinne yake fada min ai shima baya tare da mahaifiyarshi ta rasu tun yana da shekara bakwai a duniya.
Haka ya taso maraya a cikin gidansu yasha wahalan duniya sosai da kike ganinsa don yan uwa a lokacin duk sunki kamashi karshema kakansa dake rikonsa yazo ya rasu .
Shiyasa kike ganin sa wani lokaci yana abubuwa kamar yana kyaman mutane kada ki dauki wanan wani abu rashin jansa a jikine da yansuwa basuyi masa ba.
Yanzu shi kuma daya girma shine ya fita batunsu babu ruwanshi dasu yana nuna baisan suba shima a yanzu da sauri nace dashi ai ba a biyewa mutane sai su kona mutum karshe.
Da kyau kanwata wanan yasa nake kara sonki wallahi akwaiki da hangen nisa amma shi yaki ya gane hakan yana biyewa jahilcinsu ko yaushe.
Don Allah ki kula sosai ki dinga sakashi a hanya nan da sauri nace ni asuwa kaida kake kusa dashi ai zaka dinga fada mashi gaskiya zumuncin nan fa Allah yace muyisa kuma idan mutum ya barsa sai ya halaka.
Zakifini kusa dashi ai dan lokaci kadan mai zuwa don Allah ki kula da hakan ki mun alkawarin hakan a tsakanin don abokina yana bukatan saiti a yanzu.
Kai yayana ke nan ni kan sai anjima don zancen ka yafi karfina mutum da hakoransa talatin da wani abu tab a baki karama dani zan zauna ina masa wani huduba ai saiyace ya koreni aikin da nake dan dogara dashi a yanzu.
Ai da wani aiki kike dogara wanan dan kudin da muke tura maki duk wata kike zance nace wanan bada bane son bani kadai ke amfana dashi ba a yanzu har kowa nawa yana cinsa.
Shigowan Fadila tana min magana a lokacin yasa mukayi sallama dashi wanan na manta in fada maki daga ranan kuma ban sake waya dasu ba suma ina zaune tare da yar mahaifiyata a lokacin ina jin wani irin shauki na uwa da yarta a zuciyana wanda ban taba jin irinsa ba.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
7?? 6??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Duk saurin da nakeyi na shirya don ganin harsu maryamu dazamu fita sun shirya ni kadai suke jira lokacin yasa nadan kama jiki ina murza turare a kayana maji muryan Ammi daga falonta tana kwala min kira.
Hakan yasa na amsa na aje turaren zuwa jin kiran turus naja a waje daya don ganin wasu kyawawan yara maza biyu dake gefen Ammi din zaune cikin shiga ta shadda mai ruwan blue an kafa masu hula kube maikyau a kansu.
Saidana karasa fitowa daga falon naga uwar da uban a zaune ashe yayan mustaphane da matarsa hakan yasa na juya garesu cikin yar fara,ata ina gaidasu.
Shikan mijin ya amsa min a cikin fara matar daine tayi wani dunkukun kamar an tilasta mata zuwa dole ta amsa da fadin lafiya kalau tana maida hankali a wayanta da take duba ga miji fari sol mata baka kirin da dan hanci ba zakace itace mai wanan diyan ba idan ka gansu garama da Allah yasa shi suke biyowa ba ita ba.
Ashe kuna tafe yanzun nan muke shirin zuwa gidan ku mu gaidaku ai aiya ai gamu sunzo maki sannu da zuwa ya fada juyawa nayi zuwa wajen Ammi inda yaran suke zaune nace ku ya kuke ya makaranta.
Ina riko hannunsu Iokacin mukaji wani sallaman sauran ne tare da matansu suka shigo nan aka tsaya gaisawa dukan su ukku idon su a kaina caraf naga biyun sunyiwa juna signal da ido.
Duk yayan nasu su suke biyowa a wajen haske don matayen nasu gasu dai ga kamarsu amma kowa jin kanta takeyi.
Nikan hankalina na mayar a yaran ina tambayansu sunayesu a cikin harshen turanci nan ya sagir din ke fadin ai karatun nan suna dai biyan kudine kawai amma ba wani abinda ake koyawa yara da zasu fahinta kuma wai private school.
Budan bakin matarsa sai cewa tayi ai bada karatun boko za a lahira ba suma masu yi din dasuke tinkaho dashi ai iyakarshi duniya.
Nace hakkun hakane na jawo mata ayyan dake nuni da kayi karatu tare da haddisan sa lokaci guda sai naga sun kalli juna har mazan.
Ya Mahmud ke tambayana me nakewa kaina planning yanzu tunda na kare makaranta nace to gani nan dai already ina aiki da wani company na digital global nayi masa bayanin wajen ya sagir ya karbe yace ya gane wajen yana masu bayani.
Ok na wani guy ko ina ganinsu a tv suna tallan wajen ai wajen yana da kyau sosai gasu nan a titin Wuse suke nan hamkalin mazan ya dauku a kaina muna hira aka fita zancen matan dake wani cin magani.
Su a dole kada mazan su wani yace zai aureni basu san ni na wucesu bama me zaikaini auren hadi a yanzu ina matsayin macen data san kanta.
Hira muke sosai cikin sakewa dasu kamar mun dade da sabawa can naji matar ya mahmud din taja wani uban tsuki ta daga tana fadin? zanshiga wajen su umma ni sauran ma suka bita har lokacin yar macen yar ya mustapha tana makale a jikina.
Saida suka dan dade da fitane naji ammin ta nisa tana fadin matanku nada matsala a rayuwansu wallahi idan naso ku kara aure akwai wace ta isa ta hana hakan kyalesu nakeyi duk iya shegen nan da suke min don kawai a zauna lafiya ba wai sunfi karfina bane.
Da za,ace yau a gaban kowa suna iya nuna banda daraja ko kima a idanunsu yanzu ku duba yarinyar nan bakuwankuce amma ji irin taron da sukai mata.
Wanan shi zai hanayi wani abu agareni idan na tashi zantar da hukuncina akan dayanku shiru kowanmu yayi a falon don ni gaba daya ban fahinci abinda ya batawa Ammi din raiba a lokacin.
Lalai abinda suke gudun zai faru nan bada jimawa ba don wullakancin yaran nan ya fara isata yanzu murya mahmud mukaji yana fadin kina inane a cikin tsawata jin hakan yasa na dago kai na dan kalleshi waya ashe waya yakeyi da matar nasa yace ki dawo nan yanzun nan.
Yana fadin hakan ya kashe wayan yana mayarwa a cikin aljihun rgansa ya dan kalli yan uwan yana fadin rsinin wayauce kawai irin nasu in bashi ba ya zakuzo sai kufice ba tare da kun fadawa wani ba a nan.
Koma meye nidai na haifi diyana tunda hakkurina da kawar da kaina bai ya,yi aisai a nunawa kowa gwaunewarsa tunda hakan sukeso a daidai lokacin matar tashi ta shigo dakin.
Taji kakamin Ammi di na karshe ta zauna tana fadin gani ya dan basar da ita kafin yace nan kukazo ko wani dakin na fada maki bana son haka bana aon yawan tsegumi.
Kawoki nayi nan don ku duba yar uwarmu datazo tunda ta dade bata tare damu meya kaiki yawon wani part can kuma har ku zauna ina sauran suke dan uwan ya tambaya.
Ta wani yatsune fuska tana fadin suna can gurin umma tashi naga yayi ya nufi part din da suke basu jima ba sai gashi dasu sin dawo saidai suna sa,insa da matar wansu a lokacin inda yake fada mata bakar magana kai tsaye ba wanda yai masu magana ta zauna a tsarge cikin mu.
Basu dade da shigowa mazan suka mike suna fadin zasuje su dawo akwai inda zasu lokacin matar Sagir din ta kalleshi tana fadin amma na fadama ba zan zauna ba a nan na bar aiki a gida kasani.
Haba madam nan ma aigidane ki zauna mu danyi hira mu saba da juna mana daga zuwa ina marnarinku kuma kice zaki wuce toni ban gaji da ganin ki ba .
Kece fa baban anty a gaba dayan mu dakin nan yanzu idan kin tafi ai wurin ba zai bada cita ba kawai ki zauna aiki ai baya karewa mace dama.
Wani kallo tayi min kamar zatayu magana sai kuma tayi shiru tana kawar dakai gefe daya nace kokefa anty yaushe zamu saba kina guduna kuma.
Watau aiki na baro a gida aishi ya sani bawai banson zama bane nace idan wankine ki aiko min gobe na wanke maki har da guga duk zan maki anty.
Aiko kinyi kanwa wanan akwai iya,yi nikan aina yafe ta fada daga hakan har muka fara da hira jefi jefi dasu wanda ya shafi garuruwa tambayan da matar Mahmud ta sako min shine amma a kano kika saka hakorin nan naki yana da kyau sosai kamar na gaskiyan.
Keko ai ana samun na kwarai din ma a nan iya kudinka iya shagalinkane kano meye ba,a samu tunda suna kusa dasu komai kuma da saukin kudi.
Nawa dai a madina aka saka min shi two years ke nan yanzu dana sakashi a can sai naga sun kalli junansu au umurah kikaje nace wanda yaje saudiya idan ba baida rabo a wajen Allah ba ai dole yai umurah.
Watana shidda a saudiya munje tare da yayata da mijinta da nake wajansu kafinta rasu shine muka tsaya mukai aikin hajji ni don karatuna dake son ya tsaya na dawo na barsu a can na shata masu karyan hakan.
Me ai wanan daganinta kasan bata wasa bace dama ai yan kaduna duk wacce za a gani kanta a waye yake dama komai kankantata mace kuwa zaki ganta so wise.
Nace haba dai sherin da kuke mana kuma ke nan amma dai kin kusa aure ko nace insha Allahu wanan yasama na nemi Ammi nazo kada nayi aure ba tare da yan uwan nahaifiyana a kusa ba.
Eh gaskiyane hakan gaskiya ba dadi din kowa nason yaga nasa a kusa dashi kamar kada in fadi hakan sai hira sosai ya soma a tsakanin mu har mutum zai iya jin dariyan mu a falon.
Su Fadilako suna kitchen suna faman girki hakan yasa na saci jiki naje gurinsu na karba nina girka muna abinci don tuwon shinkafene kifin kuma na gyarashi na dan rage masa karfi sosai ba kamar yadda sukeyinsa basu.
Mun kawo harda sherinsu bari suci miyan yan gayu suji tun da sun dauka ba zan iya aikin kwarai ba ana bude abincin ko yadda sukaga kwasan abincin ya bambanta da nasu.
Hakama miyan shima ya hadu tun a ido muka kawo masu komai yadda na balle jakkata na aika fadila ta sayowa kowa avin sha harda sauran part din kowa ankai masa nan kuma suka fara wani gulman a nan.
Sai yamma mazajen nasu suka dawo suma sun zauna sunci abincin amma ina daki lokacin ina sallah la,asar har dakin matar ya sagir ta biyoni tana fadin to fito yayanki yace sai kinje kin koya muna wanan girkin kafin ki tafi.
Tare muka fito zuwa lokacin na sauya kayan jikina zuwa wani dogon riga mai duwatsu a gaba saidai yaddin rigan pure cotton ne da dan gyalensa dana dan rufawa rabin jikina.
Kai mata hoo nan kuma kishi ya dan motsa a fuskansu ina fadin sannunku da dawowa yaya suka amsa na dan zauna ana hira jefi jefi kafin hiran kuma ya koma atsakanin mu ana hiran yadda nayi girkin.
Mamakin yadda suka samemu sukeyi kafin suyi muna sallama suka tafi kowa na fadin sai sungani a gidajensu Ammi dai tana dakinta abinci ma a can muka kai mata taci do bata fito falon ba lokacin kuma.
Nima tunda suka tafi na gyara falon nagama nakoma daki na kwanta muna charting da hassana dake min gulman samira ance kowa da abinda ya sameshi nasani na fahinci suna fatan suga wani mugun abu ya samu rayuwan yar uwarmu a gidan mijinta.
Wanda ni kuma ban mata fatan hakan adduana ta dai zauna a gidan auren saboda yanzu dawowan samira gida ta zauna sai ya shafi kowan mu abinda suka kasa ganewa ke nan don na tabbarar sai baba ya sake faduwa ciwo kuma saboda tashin hankalin da za aitayi a gidan namu ko yaushe da ita.
Yanzuma gulman da take min shine wai Samira ta bugowa baba waya tana kuka wai ita ba zata zauna a gidan ya mahmud ba saboda duka da zaginshi gashi kuma yana bin matan kabilu yana kwasa.
Nace ita dai tayi zancen tsakaninsu amma banda wanan dama ai tasan dan duniya ta aura yanzu don ba ya mahmud din da aka sani bane a baya ni ban magana da ita dana fada mata gaskiya.
Duka kuma sai ta kiyayye tunda ita tacewa mutane taji tagani yanzu ko sai tayi hakkuri kowa hakkuri yake a gidansa bar shegiya ta dawo ko ruwa saiya gagareta sha a gidan nan.
Yar uwarkice bari mata fatan ta dawo gida don Allah kishine kawai namu na mata dake damunta ba komai don ni naje nagani abinci wallahi yana basu abinci mai kyau kuma .
Ita dai ta tsaya ga cewa bai bambaruwa kudi ko kadan wanan kan akwaishi kowa ya sani munyi charting sosai a ranan har take fada min wai anty Altine ba lafiya sosai jiyama a gidanta suka wuni nace Allah ya bata lafiya.
Don yadda na tsani Anty Altine ko mama ban tsana hakana ba tunda nagane bata kaunana ko kadan tun ina yar kankanuwata take nuna min rashin so a fili da munanan zagi yasa ta fice min a raina ga baki daya yanzu banjin zan iya ko zuwa gidanta in gaida ita.
Bayan mun gama da itane har zan sauka online din naga sakon Oga Abbas na bude nashiga sallama yayi min har sau biyu ban taba charting dashi ba na amsa mashi ashe yana online sai gashi yayi magana.
Yana fadin anya basai mun biyoki garin nan ba don naga baki da niyar dawowa kada wani dan yobe yayi muna kutse.
Dariya na kwashe dashi na dan sake mai audio ina fadin yayana kasan dadin uwa kada kuga laifina ina nan ina shan dumin mahaifiyace.
Wai wani gari kike nema a yoben na fada mashi yace gidan wa na fada mai don naga kamar yana zargi bai yarda da inda nake ba yasa yake min tambaya haka.
Mun daiyi sallama dashi na dan kwanta kafin a kira magariba don weekend ne ranan don haka kowa yake available akan median ana hira hakan ya daukw min hankalina.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login