Showing 114001 words to 117000 words out of 347556 words

Chapter 39 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8733

harkalan ba don nasan duniya zata zageni kan hakan don abune da zai iya jawo min barnan suna kila a karshe ma a jefeni da mugul kalma.
Nayi duk wanan tambayoyin garesu saidai sun min bayanin kan cewa ba haka tsarinsu yake ba don zaki fitone a matsayinki na yar arewa bahausa mai shigar mutunci ki nuna muma nan arewa musan muhinmancin wanan abin da suke son nunawa duniya fakat.
Ina ganin kuma ba karamin kudi da daukaka hakan zai sama maki ba don kinsan yadda tallan company yake shiyasa nace da farko kin zama mai sa,a acikin dubu duk fadin arewa akanki zaben su ya tsaya.
Don haka kije kiyi tunane akan hakan kiyi shawara da magabatan ki idan sun yarde maki kina da daman zuwa kiyi signing takardan tana nan zasu dawo karshen wata su karba sukace.
A sanyaye na dago kai ina fadin malam nagode zanje na fada a gida in an yarda zan dawo nayi singing din namike tsaye yace hakan nada kyau suma hankalinki da suka yaba dashi tun ranan yasa suka zabeki a wanan tallan.
Nayi mai sallama na fito na samu har yan uwana sun shiga aji na shiga da sauri daukan darasin dai nayi amma zuciyana fam take sa mamakin kasancewa hakan a kaina.
Haka na dawo gida cike da tunane mutum na farko data fado min a raina itace maman saudiya hjy hajjara gashi kuma yanzu ita bata kasan.
Sai na biyu ina son in fadawa sojana amma bansan yadda zai dauki zancen ba shima tunda fata nake ya aureni ba zanso nayi abinda za a koma anace min assha ba da tir da Allah waddai.
Damuwa yayi damuwa har yakai yana son shafar lafiyata kwatsam ranan jumma,a da safe ina kwance sai ga wayan Al,amin ya kirani naji dadin hakan sosao inda muka gaisa na tambayeshi mutanen gida ?
Yace duk suna lafiya ya fara zolayata da yaushe zakizo saudiya ne Fatima sai naji zancen kamar gatse yake min don haka nace ko yau ina hanya ai don kullum da fatan haka nake tashi a raina.
Yace au kin dauka wasa nakeyi ke nan bakuyi magana da Ummu ba ke nan kan zuwanki na bar gida akan zata kiraki ku saka time don Abbu yace azo dake don halartan taronsa da za,ayi wanan shekaran a gidansa.
Wai da gaske keyi har ka sako sunan Abbu a cikin zancen yace wallahi na dauka kunyi magana da ita ai kun aje time insan lokacin da zakizo don na dawo gida kinsan yanzu ina nan Riyadh ina karatu.
Gaskiya bamuyi wanan maganan ba amma nasan zata kiraki ya fada koda yake naji ta fara nuna cewa in anyi hakan za a takurawa karatunki don kada a bata maki tsarin ki.
Zanzo mana na fada ba tare da jin komai ba don nasan babana ba zai taba hanani zuwa wurin hjy din ba in har yaji cewa ta dalilinta zan tafi.
Mun dan dauki lokaci tare dashi kafin na jefo masa tambaya yace wani irin talla kuma kawai ki sharesu zai fi hakan na aje a raina tunda naji Al,amin din ya fara fadan hakan.
Don haka na fara wasan buya da duk wani abinda zai kani ganin HOD din mu duk da nasan aikin banza nayi lokaci guda zai turo a nemoni duk da zabi ya bani dama amma nasan rashin amincewana bai mada dadi.
Wata kawata na daure mukai hiran take fada min ke wallahi cewa sister dinki tayi kawai meye a ciki tallan kaya hajarsuce fa kawai ba wani abu ba don nayi mata karya nace wata sister dinace keson yi.
A hakan dai har aka nemoni ina zuwa ba tare da tunanen komai ba na saka hannu akan zanyi kawai na cika har number wayata da address din gidan mu da komai saida na rubuta na mika masa ya karba.
Ban fadawa kowa ba haka na danne abin a raina ko soja ban fada mai ba na dake kawai da zancen a zuciyana saidai ina rokon Allah akan hakan kullun.
Ranan kwatsam ina kwance sai ga kira wai daga Abuja nake magana da manager na customer care A,A digital global da farko turanci muka fara dashi ina jin yana murmushi kafin ya juya min da hausa yaci gaba da tambayana ina bashi amsa yace done ina maki murna shiga cikin mu.
Zamu nemeki ashirin ga bakwai ga watan nan a nan office din mu na Abuja domin cika wasu takardu kizo da takardun ki a hannu nace banda su saina secondary a yanzu yace dana primary nace nagode.
Nayi tunane kala kala karshe na kira baba ban boye mashi komai ba kan hakan yake fadin hakan dai bai sabawa sharia ba dai fatimatu don banson abinda zai zama na asha a gareki nan gaba don Allah.
Sai bayan naji amincewan babane nake fadawa gwaggo da soja yaso fada kan hakan karshe yace in hakane alheri gareni Allah ya tabbatar min nace amin muka kashe wayan.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
3?? 5??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Gabana ke faduwa sosai kasancewa ashirin da biyar ba fashi nasan tafiyan nawa ya karaso a lokacin ban taba fita wani jahaba tun barina Fatakwal da nayi lokacin kuma ba zan karas da komai sai abu guda shine dan bude ido don yanzu duk wani abinda zan gani bai bani mamaki don na riga na irinsa a kudu.
Wanan bai gushe min ba a zuciyata don haka banda ruwan kauyawa duk da rashin gatan da banda shi yanzu saina Allah dana mahaifina da ban hadashi da komai ba.
Rashin uwa takamaimai a kusa dani da zata dinga dan sani a hanya yasa na taso zuciya bushe gyaran ubangiji shi Allah ya saka min sanyin hali a zuciyata.
Ba komai zan iya yinsa kai tsaye ba don banda mafadi na kwarai akusa dani don zamana da mama uwa da gwaggo komai nayi daidai ne a wurinsu don ba nuna jan ido a kaina komai zanyi daidai yake.
Akwai bambamci sosai a irin tashin nan don ba kowa zai gano haka ba sai wanda bai tashi tare da mahaifiyasa a kusa dashi ba walau mace ko namiji sun san wanan zancen.
Dan kit dina mai cin kala uku na dauko na jera komai da zan bukata a ciki na mayar gefen filona na aje ina tunanen me zan fadawa Samira akan tafiyan nan kafin taje ta bata min suna a banza.
Ina kallon lokacin data shigo dakin taga na hada kayan waje daya saida ta dan kadu sai kuma ta basar kamar bata gani ba ta dauke kai nima banyi magana ba.
Tsohuwar wayata na dauko sim dina na mtn dake ciki na cire na saka a sabon wayan na aje gefen filona don nasan washe gari sammako kila zanyi muryan gwaggone tazo tana fadin.
Fadimatun na kusa kuwa na amsa da eh gwaggo gani na mike na fito hakan yasa nabar wayan a nan inda na ajeshi ganin haka samira da sauri ta dauka tana kallo kanta ya daure ga baki daya lokaci guda.
Dana fita ban samu gwaggo waje ba ta koma daki a lokacin don haka na sameta a dakin tace naga yar nan na cikin dakin yasa banyi magana a can ba ki karbi wanan kisha ki shafa a fuskanki da safen gobe da zaran kin sallame sallah asuba.
Ki kula da kanki ki kula da mutuncin ki mutuncin mace shine kimar darajanta daya zube baki da wani daraja a idon jama,a kuma ina fatan kin fahinci me nake nufi na gyada kai.
Kijeki Allah ya tsare ya kare nace amin gwaggo sai naji dadin wanan kulawan da gwaggo tayi min har kasan raina sao nace barin basa a nan ajima zanzo in dauka idan zan kwanta tace toh.
Na gane samira ta dauki wayata don ba yadda na ajeta na sameshi ba bandai yi mata magana ba don na sakawa wayan security ba yadda zata iya budeshi.
Har mun kwanta haka na daure na kira sunanta da Samira gobe in Allah ya kaimu Abuja zan tafi insha Allahu.
Tana kwancene ta bani baya sai naga ta juyo da sauri tana fadin Abuja Fatima yin me kuma Abuja wa kike dashi can kuma da zaki Abuja ko can sojan naki da kike fadane yake ?
Murmushin karfin hali nayi nace fata nagari lamiri a zatonki zan iya barin gida koda sunan unguwa in tafi wurin wani kato da sunan lalata kome ?
Ni interview zan tafi yi na wani form da muka cika da nagani a internet suna tallan link dinsu na cika shine suka nememu gobe zamu tafi insha Allahu.
Yanzu Fatima shine baki fada min ba nima in cika ko Allah zaisa nima in dace amma ba laifi Allah kaiki lafiya ballema irin aikin nan ai ba kowa suke dauka ba sai diyan manya irinsu dake kusa dasu wanan duk burgan aiki zakuje yi kawai tana fadan haka ta koma ta kwanta.
Murmushi nayi ina fadin aikin gama addua tunda kin min fatan inje lafiya in dawo lafiya me kuma ya saura yanzu da zaki fada min Allah dai yasa mu dace.
Cikin dare na tashi nayi alwala nayi sallah na roki Allah yasa wanan abin da zan tafi ya zamo alheri a rayuwata gabaki daya na shafa na koma na kwanta.
Karfe bawai muka bar garin zaria zuwa kaduna inda Allah ya saukemu lafiya drop na nema da zai kaini company su kamar yadda sukai min kwatance idan iso Abaja.
Mai Okada yana saukeni na biyashi ya tafi lokacin na daga kai na kallo company mai kyau an tsara mai gini kamar na kasan waje gaskiya wurin ya kawatu sosai da gani ba sai an fadama cewa sabon wajene ba kana kallo daya zaka gane hakan.
Gasu kuma a tsakiyan gari suke amma duk da hakan ba hayaniya a wurin sosai saidana karewa wurin kallo na taka da yar jakkata zuwa wani kofa danaga wata mota ta fito.
Ina shiga wani ya taso yana fadin miss Fatima Abubakar from kaduna na gyada kai alaman eh yace you are welcome dama ke nake jira a nan oga Abbas yace nazo nan najira zuwanki don kamar ke kadai suke jira don sauran member din sunzo.
Jakar dake hannuna ya miko hannu ya amsa sai kuma ya juya harshe yana fadin follow me nabishi a baya kofan ya dana ya budu yace min na shiga ya biyoni a baya.
Wani sanyi ya fara dakar fuskana ga kamshi wurin zakace bankine yadda mutanen wajen sukai shiga zaka dauka wani bankine kazo rigace sky colour mai dogon hannu da wando baki haka takalma bakake a kafansu abin daban sha,awa
Binshi nake a baya suna dan dago kai suna kallon mu a sace sai su duka da sauri daganin wajen akwai mataki sosai a kan ma,aikatansu.
Sama muka hau inda wasu office office suke jere antaresu da glasses kana dan iya gango duhun na cikinsu zaune ya tura wani kofa ya shiga nabishi ciki fuskan mutumin nan daya taba zuwa office din HOD nagani wanda ya kawo min waya da laptop ne.
Waya muka sama yanayi don haka ya nuna muna kujera sai dayan ya dan gyara min yana fadin ki zauna mah.
Naji kalman wani bambarakwai a kunnuwana haka nakai zaune ina wasa da yan yatsun hannuna akan dai busy ne yake wanan dogon turancin nasa har ya gama ya dago yana kallona yace sannu da zuwa miss Fatima ya hanya ?
Company gaba daya ya maki barka da zuwa digital globalization mai harkan naura da masarrafansa wanda nake fatan zaki farin ciki da shigowa cikinsa a yau.
Haka kuma muna mika godiya ga tayin mu da kika karba ba tare da rejecting din mu mun gode zamu shiga gwaji daku ya kamata ace mun shiga tun karfe takwas da rabi amma saboda mu jiraki ki karaso yasa na dage zama zuwa goma da rabi don zuwan ki nada muhinmanci sosai a wajen mu dakema.
Alhamdullahi kin iso a cikin lokaci yanzu wana zai kaiki wurin cin abincin mu ki zabi abinda kikeso kici sai mu shiga taron a fara.
Yi hakkuri don Allah sai karfe biyu nake karyawa idan nayi sallah na fada a sanyaye ya dago kai ya kalleni da sauri yace kuma kike haka ?
Yana dan murmushi yace well bari na danzo yana tashi ya fita ya barni ni kadai a office din ina karewa office din kallo na dan lokaci nace kafin na kurawa rubutun dake kafe jikin wani dan karfe da akaiwa ado an rubuta ABBAS SALIHU MAKARFI MARKETING MANAGER A,A DIGITAL GLOBAL acikin manyan haruffa.
Ajiyan zuciya na sauke bayan na gama karantawa ina gyara natsuwata a wajen don sanyin AC ya fara shiga jikina har ina neman fara kaduwa a lokacin.
Naji an turo kofa an shigo na dan juya shine da wata mace a bayan shi yake nunani yana fadin she is our guest here ki kula da ita sosai don Allah zata sauka a wajen ki don nasan zaki bata kulawan daya dace.
A ba komai Sir is a honour to me Sir zan kula maku da ita yadda ya dace sosai bai zauna ba ya kalleni yana fadin ga Sofia nan itama tana marketing ne a nan zata kula dake don mace sai mace yar uwanta.
Yadda naga wurin kuma na dauka a raina cewa komai zaiyi wuya ashe abin ba hakana yake ba illar kawai zamu koyi yadda zamu gwada tallan ne na minti goma sha biyar a cikin yaruruka da shiga mabambamta a jikin mu.
Mun gwada inda zanyi da hausa da kuma fulatanci inda mai koya min din yadda zanyi na fulancin ya fara koya min cikin kwana biyu kuma na iya komai tsab.
Abinda ake zaton zanyi sati daya ina koyo saj gashi kaina yasa ya dawo cikin kwana biyu hakan ya rage kwanakin da zanyi a can din hakan na nufin kuma har na gama komai a daukan da sukayi min din sai takarda da zan saka hannu kawai washegari ya rage min.
Inda nabar baya da kura don ko Samira nacan ta buga waya gida tana fadin na bunkasa yanzu na shara ina can naje Abuja nabar karatuna wani ya daukeni nabishi zuwa Abuja.
Su kuma yan gidan namu munafukai aka hau zancen ana ta fadin abinda akaga dama har gulma ya kwashi mama da ta kasa hakkiru don taji dadin wanan zancen a ranta dama burin ta ke nan akan karatun da Abba ya barmu muna yi din.
Lokacin da baba ya dawo kasuwa taje wurin babana din da zance tana fadin dazun Samira ta bugo waya tana fada muna wani zance mara dadi .
Wai Bantu tabi wani namiji sun tafi Abuja dashi yau kwananta biyu tana can bata dawo ba shine hankalin mu ya tashi da jin hakan kada kace kuma an munafunce ka.
Ikon Allah ita fadimatun kuma ta aikata hakan tace kwarai jin suna maganan yasa mama Lanto matsowa tace malam din ma ban fadama komai ai yarinyar nan ba karamin abu take gani ba a can .
Wai fa don ta mayar da ita yarinya bata san ta gane inda zata ba sai cewa wani abin makaranta zasuje yi a can abuja din ta tafi inda gaskiyane ai tare zasu tafi da ita.
Wayan shi da basu san ya danna ba a lokacin ya daga sai ji sukayi yana fadin Fadimatu kinga na sake kiranki baya mun gama waya dake dazun ko ?
Kowa yayi shiru a falon suna sauraren mu yace maimaita abinda kika fada min dazun nace baba cewa nayi maimakon sati daya da sukace zanyi munyi abin kuma naci zan dawo gida gobe insha Allahu ko jibi ba sai mun kai sati daya ba a can kuma sunce.
Wani dauka a nan kaduna zamu tsaya muyi ba sai munzo nan Abuja a nan zamuyi komai kuma ina sa ran sun daukemu ne don sunce zamu dinga ganin alert ko wani lokaci.
Masha Allahu ga iyayyen ki suna gaida ke nace a gaidasu baba na tafi ban samu zuwa gida ba na sallamesu ina gaida su Nura da sauran yan uwa.
Mukayi sallama ya kashe wayan ya nisa falon yayi shiru sai mamace tace dama ashe kasan da tafiyan ta ashe ?
Akwai abinda fadimatu zatayi duniya yanzu bata fada min ba tafiyan da akai wata daya ana shirin sa za ace wai tabi wani namiji holewa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login