Showing 120001 words to 123000 words out of 347556 words

Chapter 41 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8720

Mr Abbas ne ya bani ya miko min wani envelop fari dan digo na karba ya kira sectary dinshi yace a turo mai ayuba driver.
Kafin yazo na fita ko naje sallama da maj masaukina har wajen ta rakoni saida muka daga ta wuce dagani sai driver ina bayan mota inda tace in zauna muka doshi kaduna don ranan drivern zai dawo Abuja shi.
A hanya nayi tsara ban Iris, doya da manja wanda zan kai gida don a kaduna nake son in sauka in na kwana biyu sai in wuce zaria tunda weekend za a shiga lokacin.
Ni kaina nayi mamakin kayan dana gani niki niki yara na shigo min dashi gidan abinda ya fado kunnena shine kalman da mama lanto ta fada don banji kalman mama ba don itace ta fara magana a lokacin tace.
Lailai kan bariki yayi kyau sosai don ga tsaraba nan kitila kitila ana shigowa dashi daurewa nayi na shiga dakina inda ake shiga min da kayan don naji kamar incewa driver ya zarce dani zaria kawai.
Amma kuma ina son ganin babana a lokacin don in masa bayanin abinda najeyi can dole na tsaya kamar kullun daki na fara gyara kafin naji dadin zama a cikinsa da kyau don nakanji kazantan zama ban gyara ba.
Baida wani gyara wanan karon sosai amma duk da hakan na gyara na shiga ciki don na iso da wuri yasa har na samu kwanciya nayi barcin rana lokacin don akwai dan gajiyan sintiri a tare dani.
Sallah ya tayar dani na fito nayi alwala ina kallon yadda mama lanto ke kiciniyar raba abincin rana inda ta dafa wani farin jeloup rice da baiji komai na hadi ba haka aka debo min shi aka kawo min.
Amsa nayi nace nagode sai ga mama uwa ta shigo take fadin ashe kin tashi na leko har sau biyu kina barci nace eh na gajine da yawa mama gashi ban sababa don ban wani sake jiki a can ba.
Zakiko iya cin wanan abincin ta fada tana kallon abincin nace haba dai me yayi mama sai tayi murmushi tana fadin Binta kowa ya ganki ya ga yadda kika koma yanzu ai yasan kinfi karfin wanan abincin yanzu ?
Haba dai mama ai barikin nawa baikai har in ban abincin gidan mu ba ni kawai dai kallon kitse akewa rogo amma har yanzu ai rogone ni bankai can ba abincin da gwaggo ta dafa shi nake ci har gobe ni.
Ina waje ina dauraye cibi nake wanan maganan kowa najina a gidan nace kinsan barikin ma iyawane ai wani yadda ya shigeshi haka yake fita bai gane komai ba.
Ke nan kinji me suke fada nace naji komai dazun da kunne na tace min ke dai bari na rasa me yasa mutanen nan ke haka sam na fahinci ba a dai son zaman lafiya a gidan nan yanzu kirikiri mutum ya nunawa duniya nashi yake so dan wanine abin zagi a wajwn shi.
Allah ne shedar kowa don zaton wuta a makera akeyi ajishi a masaka yan bariki na inda suke nasan kulba dade sai gaskiya tayi halinta a gidan nan Allah ne kawai shedan mutum a yanzu.
Na zauna naci abincin sosai nasha kunun ayyah da take wanda yaji hadi muka dan taba hira kafin la,asar ina basu ita da yaran dake dakin wurina labari.
Saida nayi sallah la,asar na fito dakin maman biyu na shiga na gaida ita a cikin mutunci itama ta nuna a fuska kamar ba komai hussai na kwance tace bantu ashe yau zaki dawo nace eh sister ina sister hussaina tace taje lalai za aiwa kawar nan nata aure ta nan kasan layin mu din nan.
Ya zancen karatun ku kuwa kafin ta ban amsa naji uwar tace karatun nan dai su bari insunje dakin mazajensu sayi a can ban iya wanan cacan kudin hakana.
Nace karatu kan sai da kudi yake tafiya gaskiya na mike na fita suka bini da kallo ga kamshin dadi dana barsu dashi a dakin lailai yar nan tayi nisa ba kadan ba kinji wanan kamshin turaren da takeyi kuwa ?
Mama ina ruwanki kinyi magana baba yace ki bar masa yarsa don Allah mama ki bar irin zancen nan ko mu dai ai bamu iya fita haka ba turare balle Bantu yanzu yadda ta koma din nan.
Ko yanzu nasan maganan da naji tanayi dazun kila wani yace mata yar bariki ta bada amsa a tsakar gida ni yanzu ban son irin hakan mama don Allah .
Tayi ta bada amsa karya muka fada ai gaskiyane gata a fili aikin me taje tayi data dawo da wanan uban kayan haka da zakice kada mu fada an fada din ta mutu.
Muryanane ke fadin mama a raba wanan kayan a aje min wanda zan kaiwasu gwaggo idan zan tafi don dama kudasune nasoyowa tun can.
Kinji fa mama tunda doyan nan ya fito kuke maganan doya a gidan nan yanzu gashi ta sayo makuahi kamar abin banza ba kudi aka saka akasaya ba.
A banzane mana aka sayoshi dama wayasan abinda taje tayi ta samo kudi haka tazo don ta burge mutane dashi tunda kin sheda hakan mama kada kici kayan nan gaskiya.
Hakan yaso ya zama fitina a tsakanin su da mama tazo tana tambaya sai kowansu yayi shiru don ba amsan da zasu iya badawa a lokacin.
Da yamma baba ya dawo ya samu na dawo muka gaisa sai bayan ya dawo daga sallah naje wurin shi muka zauna ina mashi bayanin abinda mukayi acan din.
Shiru yayi kafin ya dago yace dani tau Fadimatu ni dai Allah ya gani bani shedunki akan zaki iya wani abinda ba daidai ba bayan idanuna.
Saidai mutane su basu gane hakan kuma gaskiyane ace mace matashiya baliga ta bar gida zuwa wani waje inda ba wani muharraminta a wurin gaskiya akwai hatsari babba ga hakan.
Don gashi tun yanzu mutanen gidan nan sun fara yada maganan dabashi akanki ina ga yan waje su kuma ?
Mutane basu fadin alheri akan dan wani yanzu saidai neman abin asha daga gareshi su samu abin yaddawa sai dai muce Allah ya kyauta gaskiya.
Shiru nayi ina sauraren baba har ya gama na mike jiki ba kwari don gaskiya baba ya fada son yanzu hankalina yakai da zan gane abinda duniya ke ciki a yanzu.
Daki na koma nura ya shigo na aikeshi yakai min sako gidan su hjy mairo mahaifiyan su ya habibi don nasan tana son Irish sosai da manja da doya nace akawowa su Jamal.
Lokacin yaran suka san nazo kuma dare ya soma sosai a lokacin nasan dana ganesu sunzo wurina kafin ya dawo na kulle daki na kwanta ranan dakin samari yan uwansa ya kwana.
Ina zaune ina sa hula a kaina naji wayana ya dauki kara na daga ina dubawa Sojana nagani a rubuce kamar zan share naki dauka sai can na daga wayan ba tare da sallama ba a lokacin na dai kara a kunnena kawai.
Babyna abin ba maganane yau kuma to ya Abuja din ko kina wani abune yanzu kada in dameki don da alama kina busy ko yanzu?
Ka auna signal dinka ka gani ko me nakeyi ba kanada ma,auni ba a idanunka dake yadoma duk abinda kake son ganin inayi a yanzu.
Yanzu na gane kina fushi dani ke nan dan hakan kike magana dani yau a hasale kina inane a Abujan ya tambaya cikin son basarwa da zancen.
Nace gani kwance a gidan ubana kaduna yanzu kaji inda nake ko zargi ya fita a zuciyanka ke nan sai naji yace kina nufin bakije Abuja din ba ke nan ?



ZAINAB IDRIS MAKAWA

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
3?? 7??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Wai kina nufin kaduna dama kikazo ba Abuja ba dama zolayata kikeyi kome Fatima har naji dan sanyi a raina danaji hakan.
Katseshi nayi da fadin soja naje Abuja har mun dawo dani da sister dina kwanan mu biyu muka dawo ban yarda ba yace nace to shike nan idan baka yarda ina kaduna ba har yanzu.
Ki ban address din gidanku da safe zan shigo in duba in gaskiyane ya dauka ba zan bashi ba na rabatabo mashi yadda zai sameni yace an gama bamuyi wani hira ba muka kayi sallama yakashe wayan.
Na kwanta sai barci washegari ina barci da safene Hayyatu dan wurin mama lanto ya shigo gida yana haki tare da fadin sojoji a kofan gidan mu wallahi.
Nan danan su mama suka firfito ana sauraren shi yace naga suna magana da isah mai shago yana nuno masu gidan nan da hannu shine na sheko.
Baki gansu bafa da kaki da bindigoginsu a rataye ba mai dariya a cikinsu kowa yasha toka yana fadin hakan aka kwala sallama Isah mai shagone har ta cikin gidan mu yashigo yace wai ana sallamawa Fatima tana nan ?
Innalillahi su mama suka fada da lokaci guda mama ke fadin ai kaji irinta dada abinda akewa gudu ke nan gashi tun ba aje ko inaba zance ya fito .
Ina ubanta yau yazo ya ganowa idon shi nikan na sani karyane wallahi ace wai yar nan abin arziki taje yi abuja ita tafi kowa sa,a a gidan nan ko me yanzu gashi akwai abin kunyar dayafi nan sojoji su biyo diya mace har gida su kamata bama polisawa wai soja.
Mama lanto tace nidai in ba wani gagarumin sata tayo can ba aka hadata da sojoji suzo gida kamata mu namu ya samemu muna zaman zaman mu gidan nan ?
Kace gata fitowa mama din ta fada ina jinsu nayi murmushi nace ni fatimatu binta zahara naga ta kaina wurin wanan matan kofa naji ana buga min nace waye ?
Fito dan Allah kinje kin daukowa mutane abin kunya kinzo muna gida dashi saiki tashi kije ga sojojin nan kofan gida sunce ki fito mama din ta fada hasale.
Naji mama na bata amsa ina tashi daga kwancen na zauna kifa fito don soja ba ruwan shi yanzu suna hadamu dake musha dukan banza bamuciba bamu sha ba sunan mu ya baci a banza.
Kai zo kira muna malam don Allah yazo da sauri kada a rutsa damu shida ya yarda da karyanta yau ga asiri ya tono an gama abin kunya cikin unguwa suna ya gama baci kuma yanzu..
Lekowa nayi nace kai hayyatu don Allah jekace mashi barci nakeyi gani fitowa yanzu sai naga hayyatu din yai min wani irin kallo nace kace ina fitowa nace maka.
Wa ni wallahi a tsiyace na shigo gidan nan dana sani ma wallahi ban shigo ba kada suzo su rutsa dani gidan nan Amira leka kice masu ina zuwa don Allah nace wa amira yar wurin mama uwa tace ba zasuyi min komai ba Anty ?
Nace jeki kawai naji uwar ta leko tana fadin jeki mana amira ki fada kada suga ta dade na koma daki na kwabe rigan barcin dake jikina na jawo dogon rigan dana sa da zan dawo jiya na mayar a jikina.
Na dauki wayata na fito zuwa duk suka bini da kallo sai mama uwa ce tayi karfin halin fadin ba zaki tsaya har malam yazo ba yace gashi nan zuwa fa .
Ina kuma mama na tambaya cikin mamaki tace yaya ta kirashi ta fada mai sojoji sunzo tafiya dake yanzu ihun Amirace dake fadin wallahi naga soja ya ban kudi.
Yace naki kowa gidan nan yazo ya karba Lah,illah ha,illahu hussai ta leko tace bana fadi ba dama nace kilafa wani abune ba kamata sukazo ba ni dai ban tsaya ba nasa kai na fita har nakai kofa na juyo ina fadin don Allah mama ku kira baba kuce ya bari kada yazo don Allah Mohammed ne fa yazo ibn Sa,id shine yazo wurina.
Da baya baya naga mama ta danja ta jingina jikinta da karfen daketa kofan su mama uwa ta zuba min ido har na fice tana tsaye tayi shiru tana bina da kallon mamaki.
Kamar yadda yake min can nan ma unguwar namu haka yayi ya zauna ya bude mota yana kallon masu wucewa saidai ganin shi sa kaki yasa mutane sunsha jinin jikinsu dashi a nan din.
Gidan namu ya zubawa ido yana kallon kofa na fito na nufi wuein shi ina kallon yadda sauran sojojin nasa suma suke kallona sai hakan yasa ina jin kamar a harde nake lokacin.
Na iso ina mashi sallama ya dago yana aje computer dake jikinahi yace baby na hanaki barcin ki ko wallahi na dauka ba gaskiya kike fada ba sam.
Dan harara nayi nace ai gashi kazo ka dagawa iyayyena hankali da kakinka sun dauka wai kamani kazo yi duk suna ciki sun rude su haba dai Iam so sorry suyi hakkuri ninazo inga baby dinace bacwani abu nazo yi ba a nan.
Dan daure fuska nayi nace na gane baka dai yarda dama ina kaduna ba ke nan nadawo tun shekaran jiya kwana biyu kawai mukayi muka dawo.
Kin dai je din ke nan babyna nace naje gaskiya amma kamar nace kada kije ai nace bamuyi hakan da kai ba ka dai tambaya na fada ma bakace komai ba ka kashe wayan .
Iska ya furzo daga bakin shi kafin yace dani anyway kin dawo lafiya ko nace lafiya kalau ya dauko min maganan aikin shi cewa suna son su turashi calabar aiki amma bai tabbatar ba nace to Allah ya tsare ya kare aikinsune hakana dama ba zama wuri daya.
Kawo wayan nan ya fada ya karba yana dan jujuyawa kafin ya danna yaga da security ganin hakan yasa nace kawo na cirema security din ya miko min nacire na sake mika mashi.
Gidan photo ya shiga yana dubawa yaga photon da nayi da wanan matar da yaranta yace su waye wanan din nace wace na sauka a gidantane yace OK yanzu na yarda dake lalai aiki kikaje yi don naga komai da nake son gani.
Kallonsa nayi nace dama baka yarda dani bane ashe yace nayarda ai tunda nace ki ban waya naga kin miko min na yarda dake yaushe zaki koma zaria din nace sai Sunday idan Allah ya kaimu.
Idan ina nan zanzo na mayar dake nace nagode ka rufa min asiri kafin kasa a daukeni da wata manufa zan dai bi motar kasuwa in koma ciki a dai dai lokacin aka aje babana da mashin ya dan kalli inda muke ya shiga cikin gida.
Nace kaga har matan gidan mu sun bugawa babana waya gashi ya dawo a gigice ance sojoji sunzo kamani innalillahi ya fada.
Wai meyasa mutane suke daukan soja wani mugune ko za azo kamaki ai ba hakaba kamar wace tayi wani baban laifi ?
Mugun fatane kawai suke min ban gane ba mahaifiyarki bata gidanne da zaki fadi haka ya tambaya yana kallona na nace.
Ni bansan mahaifiyata ba ai tun ina karama suka rabu da baba har yau din nan kuma bata kara zuwa nan garin ba ko gidan nan sabodani.
What kina nufin kwata kwata baki santa ba baki san wani nata ba kuma ko garinsu baki sani ba ko me ya tambaya kafin na bashi amsa.
Sai gasu jamal suka rugumeni yadda muka sabayi dasu nan nake mashi bayani yace no warder dama nakanyi mamakin wasu behaviours dinki ashe ba a arewan nan kika tashi ba Allah yayi mata rahama nace amin.
Ya ba yaran kudi suna murna suka juya zuwa cikin gidansu nace kusan daya nake dasu yanzu shiyasa nake tausayin yaran sosai wallahi.
Agogon hannunsa ya duba yace zan shiga office idan na fito da wuri kila zan dawo idan zan gane wurin nan nace nagode da akai mefa nace daka bata lokaci a nan mana.
Murmushi yayi yana fadin shiyasa nake kara sonki don godiyan nan bari dai na dawo zanfada maki dalilin hakan nace Allah ya kai mu na danja baya kadan zai rufo motan tace tsaya in baki sako don Allah ya juya cikin motan .
Zuwa can ya juyo yana fadin wanan kiba baba sai wanan kuma kiba matansa da yara nace wanan ma ai zai isa ya jefo min wani irin kallo da sauri na karba ina fadi angode Allah ya umfana saura ya rufo motar yaja suka tafi sauran sukabi bayanshi.
Wurin Isah mai shago naga ya tsaya na fara tafiya zuwa cikin gida ina jin tashin motansu a kofan gidan namu sun tafi zansa kai in shiga gida muka hade da baba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login