Showing 183001 words to 186000 words out of 347556 words

Chapter 62 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8768

maliyo jibi da labarai shi ta wuniyi har washe gari.
Allah da ikonsa ina kwance saigasu Jamal sun shigo tunda safe nace bari na fita dasu don an dade ban kula yaran ba indan sai masu wani abu dai hakan nan yasa na kwashesu muka fita sai usainace ta san da fitana dasu don kowa na daki dayake sanyi ne alokacin.
Allah mai iko ashe ban dade da fita ba motoci biyu suka tsaya a kofan gidan mu na yan daba guda daya kuma na su matar sojana da aka bugawa waya har kwatancen gidan mu tayo min takaka da yan daba da sandunarsu.
Kyauren gidan mu suka fara duka da sanda kafin zagi da cin mutunci ya biyo baya sai ashar suke durawa da waye fatima a gidan nan tafito ko su shigo suci uban duk wanda ke gidan ga baki daya a lokacin.
Nan unguwa ya cika sosai sai faman fitsara takewa mutane ance daga ita sai wando da rigan soja tare da wasu mata da uku da sukazo dasu din gidan.
Umurni ta bayar cewa ashiga a fito dani koda tsiya a cikin gidan namu tunda naki fitowa ita za a kawowa iskanci mijinta don ita kadai aka halince shi bada wata yar iska ba kuma.
Yau sai na fadi wanda ya tsaya min a cikin garin nan har nakai iskancina a gun mijinta nake kokarin kwace matashi ina shago jamal na kokari gwada wani takalma wayana ya dauki kara.
Na ciro ina dubawa naga isah mai shago da sauri na dauka gabana yana faduwa ko jikin babane ya tashi bayan mu ina kuma dan jin hayaniya sama sama yana tashi a lokaci ta cikin wayan.
Hankali tashe yake min bayani a gurguje da fadin naga fitanki Bantu don Allah kada ki dawo gida yanzu don ga wasu mata nan da kartan maza sunzo wai sai kin fito ko su shiga su fito dake su lalatsaki yau.
What isah wace matace wanan na fada hankalina tashe a wajen ya daici gaba da min bayani yana kara min waya ina jin cin mutuncin da suke muna a kofan gida.
Bansan lokacin dana kira soja ba ina fada mai cikin kuka yace what a gida na barta fa tana barci ki ban mintuna din Allah ga sojoji nan zan turo yanzu.
Allah ya taimaka kuwa suna kutsa kai cikin gida mu sojoji na zuwa suka datse gida sukuma suka shiga gashi kowa ya shige daki da dansa an kukule in roba in buki ko glass din window haka suke bugu.
Sojojin nan suka rutsasu a cikin gidan ga ba hanyar fita don bamu da katanga gina ya tare itako tana waje tana fadin .
Do you know whom am i waya turoku ku kamamu abundai ba dadi ranan gaskiya basu tsaya ta kanta ba aka nufi brack da yan iskan a nan aka bar motocinsu har matan da take tare dasu duk aka kamasu sai ita sukaki tabawa don matar ogace ita.
Kuma aka bar soja guda biyu kofan gidan namu shi yazo ya daukoni da yaran hankali tashe ya dawo damu gida har lokacin kofofin gidan mu suna rufe.
Allah yasa tare da usaina muke tana jin yadda yake ban hakkuri a cikin motar tare da sheda min zai dauki kwakwaran mataki a kai.
Lalai matar soja is a soja don koda muka dawo mun samu unguwar namu har lokacin cike da jama,a a cikin tashin hankali muka fito ban tsaya ba shima muna fita ya juya ya tafi da sauri.
Usaina ta fara fadin ku taimaka min ku fito don Allah yan gora zasu karani ba motsin kowa saida nace ku kyaleta mama ku fito don Allah babu kowa mune muka dawo fa.
Aka fara bude taga ana lekowa kafin su bude kofofinsu su fito suna fadin wai munga tasku yau munga yan bala,i nan kuma mutane suka fara shigowa har su hjy laraba da labari ya kai masu.
Gashi sunsan cewa yaransu na gidan mu wurina tunda na leka baba na samu yana nan kwance abinsa na dawo muka gaisa dasu nashige daki ban kara lekowa ba na kwanta a cikin bacin rai.
Wayata yayi kara na duba sojan ne ya bugo yana tambaya basu taba wani ba nace saidai kada a kara tunda sun farfasa muna gina sun buge duk wani abu da suka gani a waje tsakar gida.
Yace oh lord innalillahi amma sakina zata hadu dani wallahi zata san ta tabani a garin nan ban tsaya jin karashen shiba na kashe wayan cikin takaici na koma na kwanta.
Nidai bai kara kirana ba ga hiran yaki karewa ga yan unguwa da yan gidab mu kowa da abinda yake fadi ranan akan abinda ya faru ni kan dai sai kara min bacin rai da sukeyi kawai gashi kuma anki barin zancen.
Tunane kan nayisa har da wanda bai dace inyi ba zafin rai na dauka da sojana sosai don duk yadda muke daga ranan na rabu dashi ke nan na nasa a kasan zuciyana.
Gashi kuma shakuwan mu dashi a yanzu yayi yawa kusan kowama dake tare dani a family yasan da sojana don suma haka yadda nake kiranshi suke kiranshi suma.
Sai gashi yau matar sojana ta nunawa duniya tafi karfin mijinta waceni da wanan fitsararrar mace yadda ake fadin tayi din nan ai sai mace tasan abinda ta taka zatayi hakan.
Allah da ikonsa a ranan Oga Abbas ya kirani muka gaisa ya tambayi jikin baba nace da sauki yadda yaji ina magana ya fahinci raina ba dadi a lokacin.
Yake tambaya injin dai ba matsalan jikin Abba din bane naji muryanki wani iri mana nace bakomai yace a,a kanwata kada muyi haka dake mana fada min meke faruwa.
Kuka na fashe dashi ina labarta mai cin mutuncin da matar tazo tayi min alhalin ga mahaifina a kwance yana jinya yake fadin wanan wata irin shu,umar mace ce haka ?
Wani mataki aka dauka a yanzu nace nima ban sani ba yayana ina hakan ba zataci bulus ba wallahi ko waye mijinta ko ubanta sai mun nuna mata kema mutunce ba banza kike ba.
Banso yace hakan ba don mutuncin mijinata a kaina don haka nace ya barta kawai ai yadda mijin yayi ya dauki mataki yayi kokari yace yaji.
Aiko da safe wakan kaina samira ta saka min bansan ko a ina ta samo MP ba sai waka ke tashi na habaici dake nuna bankai ba ban isa ba bata ko damu da baba dake kwance a gida yana bautan Allah ba.
Wani yarone ya shigo yake fadin wai ance barrister Auwal kankia na sallama da Fatima Garba a waje jin hakan yasa mama ta kalli samira cikin tsawa tace kiwa Allah ki rage muna karan wanan abin muji gari.
Wanan ai rashin tarbiyane da rashin sanin ciwon kai yayama mahaifinka na kwance ba lafiya har zaka sake kida haka don rashin tarbiya.
Yaron dai yana tsaye ya kara fadin abinda ya fada ta shige daki tana kunkuni lokacin kuma mama uwa ta shigo ina barci ta fada min zuwan mutumin na tashi cikin mamaki na gyara na fita.
Ina fita bakon fuska nagani muka gaisa ya gabatar min da kanshi da kuma abinda ya kawoshi gareni duk da yaji nace babu ruwana to mahaifina dake kwance ba lafiya zasubi masa hakkinsane.
Banda bakin magana haka na bashi statement ya dauka ya tafi yana min godiya nima din nakoma gida cike da tunane a zuciyana.
Banji komai ba sai washe gari misalin karfe dayan rana saiga kiran sojana ya shigo min a waya kamar kada in dauka saina dauka ba sakin fuska sama sama muka gaisa yace baby duk matakin dana dauka na kama erea boys din nan ya akayi kuma human right suka shigo cikin case din nan kuma yanzu ?
Cikin mamaki kamar bansan komai ba ba sake tambayanshi da huma right kuma sojana ni bansan da zancen nan ba saidai idan wanine a gidan mu yakai kara .
Ok zan kiraki don sun zo sun tafi da madam don ita taja ina son su koya mata darasi don tayine ta bata min suna kawai amma din Allah kuyi hakkuri please ?


ZAINAB IDRIS MAKAWA
KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
5?? 7??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Sukan human right sun saka a kamata tazo da farko da fitsaranci saida taga case ya juye ba wasa a cikinsa ta fara shiga hankalinta tana fadin a kira mata mijinta.
Anyi kiran duniya sojana yaki daukan waya saida aka sameshi a wajen aiki wani yayanta yazo yake fadamai case din yayi tsauri don sun taka doka sosai .
Ana son a juya zancen zuwa wani na daban saboda ta shiga gidan matan aure musulmai da katti ga mai gidan kuma a kwance baida lafiya lafiya kusan wata daya yana asibiti kwance.
Da farko duk da yayanta yazo baisa yaje ba saida zancen mahaifansu suka shigo dole mahaifinsa yasa ya taso ya tafi yadda dan uwan nata ya fada mashi shima hakan ya fahinci zancen nason ya juya kansa a yanzu zata dauko masa rigima da barnan suna a gari kawai.
Bincike yakai bincike saida kyar aka samu aka bada bellinta basu je gida ba gidan iyayyensu suka nufa don hankalin kowa a tashe yake a family din kan abinda tayi din.
Din gidajensu ga gida ga gida suke a unguwar GRA nan dai aka tasa ta gaba da tambaya da fada kafin ta fara masu bayanin cewa itama watace ta kirata da wani lamba ta fada mata .
Har kuma ta bata address din gidan da sunan yayinyar shine taba kawayenta shawaran suje sukayo mata hayan yan daba don suje su tsoratasu.
Nan aka fara bincike bayan sun gama mata fada wani dan uwan mijin dan sanda yace abari yayi tracking din number su gano maishi.
Inna lillahi don na,uran tracking din baj tsaya ko ina ba sai a kofan gidan mu ya kawosu suka aika zasu shigo yin wani aiki aka barsu suka shigo ciki.
Kowa ya dauka cewa sunzo duban aika aikan da yan daban nan sukayine sai gashi kuma zance ya juya don sai dakin mama Lanto kai tsaye macen yar sandan ta shiga sai gaban Samira dake kwance ta tsaya.
Ta kallo samira din tana fadin you are under arrest mun kamaki da laifin da ake tuhuma mai wanan lamban wayan daya boye ya kira matan soja ya hada fada da wata yarinya.
Zata tsaya magana yar sanda ta kifa mata mari da sauri su mama suka iso kofan dakin sai dai basu shigo dakin ba suka tsaya daga kofa.
Nan aka tasa samira gaba hayaniyar hakan ya fito dani dakin don ina daki na zama mujiya yanzu tunda wanan abin ya faru akaina.
Ina fitowa yar sandan nan mace na fara tozali da ita tana kada keyan Samira zuwa waje da sauri nace innalillahi wai lafiya haka meke faruwane wai don Allah ?
Nan ake mun bayani kafin na karaso har sun fice da ita daga gidan don dan uwan sakina matar soja yana waje yana dakon fitowansu shida sauran mazan da sukazo.
Ba wanda yasan kan maganan saida muka firfitone hankali tashe dan sandan ke cewa daga cikin ku waye Fatima ?
Nace nice daga gun da nake tsaye yace zaki samemu a office din mu ki kara muna bayani sir ita wanan din fa nayi karfin halin fada yace ita taja komai daya faru a kanku gidan nan don ita muka samu da lamban da aka kira matar Soja dashi.
Wacce tazo tayi maku cin mutunci har gida tare da yan daba don hakane hukuman human right sukai karanta kan tashigo gidan magidancin dake jinya no taciwa iyalinsa mutunci ta hanyar tura mai karti a gida sukai masu barna.
Babban magana na fada a raina kafin nace offoce kayi hakkuri mu tafi tare don Allah ko don gujewa surutun mutanen nan dake kewaye suna kallon mu ba matsala kuna iya shigowa mu tafi tare na juyo na kallo Usaina dake gefena nace muje tace ina wai gun yan sanda bantu ?
Can mana na bata amsa cikin haushi tace wallahi badani ba ga dai hassana nan ku tafi hassana din ta???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ce muje Bantu tunda munsan bamuyi komai ba.
Tun tunkaran mu wajen iri motocin da muka gani yasa muka fahinci case din yayi karfi sosai ga mutane gungu gungu suna yan maganan ganu a tsakanin su zuwan mu yasa kuma kallo ya koma a kan mu mun iso daidai dasu Nura da Isah mai shago da suka hau mashin suka biyo bayan mu.
Nan muka shiga Allah ya taimaka tun safe da natashi nayi wanka saboda ina fashin sallah a ranan wani dogon rigana na yan Thailand's rigar cotton ne an mata dinki kamar bubu namu na don haka hannunta karamace amma baya fitar da sura a waje .
Sai dan gyalenshi dake kaina kana gani kasan samun rigan ba dai a kasan nan ba ga kaina na daure da ribon pink don rigan assh color ce sai aka bishi da dingon pink a ko ina jikinshi wanda ya karawa yadin ma,ana.
Takalmana mai dan tundu pink don nayi niyar idan na tashi inje gidan su hjy ne sai barci ya daukeni haka da shirina a waje sai kuma ga wanan hayaniyar da yatashini karshe kuma gamu a office din dss a karkashin human right kan bincike.
Ba laifi gaskiya ga yan gidan mu ba zaka taba hango munin wanin mu farat daya haka ba sai idan ka matsa muna da kallo zaka gano inda munin namu yake watakila.
Mun shigo ciki muka samu yan gidan nasu har dashi soja da iyayyenshi da nata duk a wajen da yan uwa da kuma lauyoyin mu.
Tun daga kofa babban su ya dakatar damu muka tsaya ya nuna mu yana fadin a cikin su wa aka samu da wanan layin sai yar sandan ta nuna samira.
Su wa yan nan fa tace sisters dintane suka biyo mu nan wanda ya bamu umurni muzo yake tambaya daga cikin ku akwai Fatima waxe aka kaiwa wanan harin.
Nayi karfin halin fadin nice yace zamu bukaceki kema ki shigo daga ciki kuna iya shiga ai dukkan ku nan muka shiga aka fara jerowa Samira tambaya ta dauki abin wasa da farko saida taga yadda wanan matar sojan tayi yasa jikinta sanyi.
Mai tambaya yace ko meye dalilinki na kiran wanan matar da layinki ki fada mata zancen mijinta da wata kin tayar mata da hankali haka kinsa taje tayi abinda bai dace ba a gidan mutane ?
Kallon mamaki nakewa samira din wace ta dago tace ni bansan zancen da kukeyi ba banma san wace kuke magana a kanta ba .
Tsawa dan ss din ya bugamata yace idan kika bata muna lokaci zamu kaiki cell mu rufe na sati biyu idan kinji wuya a can zaki fito ki fada muna gaskiya ko ya abin ya faru.
Dukar da kai tayi kasa ba tare da magana ba aka kira matar soja tazo sai alokacin ma nasan cewa shima yana wajen don tare suka shigo dashi.
Kallo daya nayi mai na dukar da kaina a kasa ban kara dagowa ba balle in kalli irin kallon da yake min a gaban mutane din na kurewa a lokacin.
Waya bugo maki waya suka tambayi matar soja din tace ba zance gata ba a cikinsu don ta waya mukai magana da ita.
Kinsan ita wace kika kaiwa wanan takakarn har gida ko zaki ganeta idan kin ganta ko bata fada maki koma akanta kawai dai ta fada maki kikaje gidan ?
Shiru tayi ashe maganin shege gaton uwa don ta dauka arziki da isar mijinta da mukamin wasu yan uwa zata iya amfani da dama ta taka duk wanda taso dashi .
Sai gashi ta gane itama din ba kowa bace ashe don hukuma na iya taka kowa idan ya saba mata tiryan tirya ta mayar da maganan
Nan kuma aka tambayi samira dalilin hakan bayan sun tabbatar mata da an gane itace ta dukar da kai tana fadin wai anyi hakkuri don Allah sherin zuciyace
Nan lauyan nan ya tashi yace ba za a hakkura ba ana rokon kotu tasa sai an biya kowa hasaran da akai mai don yadda tasa aka far fasawa baba gida da kuma hasaran da akaiwa iyalinshi.
Kana kuma abi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login