Showing 90001 words to 93000 words out of 347556 words

Chapter 31 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8742

farin ciki sosai da jin hakan idan har zai kasance to amma Alh kasan komu ba ai muna dole ba balle ni yanzu nace zan tursasa wanan yar akan dole tabi ra,ayina.
Don haka idan na zauna da ita har na fahinci tayi na,am da wanan zancen wallahi Alh kasan nafi kowa farin ciki da hakan amma har in ta nuna min bata da ra,ayin hakan don Allah Alh sai ayi hakkuri.
Kuma kada aimin mumunan fahinta tun farko banayiwa yarinya dole sai wanda kika kawo min kikace kina so in hankalina ya kwanta in duba inya dace in hadasdake.
In harkan anyi dace bata mussa hakan ba wallahi Alh nayi farin ciki da wanan abin tunda dukkansu daya suke a wurina idan kuma an samu akasi akan hakan sai yayi hakkuri ya duba cikin yan uwanta ya zabi wata ayida ita tunda daya suke a baki dayan su ni shine maganata.
Gaskiyane malam garba mun kuma gode don yadda kai muna hakarci karo na barkatai haka an gode yanzu zan dakace ka muji yadda zakuyi da yarinyar sai a sanar muna.
Shi din ma yace gobe ko jibine zai koma can fatakwal din don kasuwancinsa amma ba zai dade ba insha Allahu zai dawo .
Masha Allahu Allah dai ya tsare ya kare dama abinda muke masu fata ke nan a rayuwan mu su samu inda zasu dogara muma mu shiga innuwan tasu mu huta ciki.
Yanzu kan ai Mahmoud Alhamdullahi gaskiya yana samu saidai kasan halin dan yau wanan yasa nima da yazo da zancen ita Fatima kaga nayi na,am don yarinyar tasan yakamata tun tana karama da wanan suka rabu da junan su kan baba yace su bashi dan lokaci zai zauna dani din yaji.
A cikin mamaki baba ya shiga gida don bai taba tunanen akwai wani rana da har Mahmoud zai juyo gidansa da sunan neman iri ba da zancen zaizo kuma sai ya fada inda bai zata ba duk da tun farko daya kama yadda ya dace koshi me daukan Fadimatune ya bashi ai koda shima bai nuna ra,ayin hakan ba.
Shiko Alh da Mahmoud din yazo gaidashi da safene yake masa bayanin cewa sunga juna da mahaifina ya kuma nuna farin ciki sosai in hakan ya kasance amma matsala dayace yanzu shine yardan yarinyan.
Don haka zai tuntubeta yaji ko zata yarda da wanan hadin naku in har bata amince ba ya bada wani daman daka duba cikin yan uwanta ko da wace tayi masai ayi da ita.
Amma shi baiwa yarsa dole akan aure tun farko yana ba yayansa zabi akan abokan rayuwansu don haka mu dakaceshi yanzu muji.
Fara,an Mahmoud din ne ya koma ciki lokaci guda don wanan salon na baba zai iya jawo nakasu indai da ra,ayina haka zai faru ya zauna ke nan amma yanzu Alh hakan na iya kawo wani tsaiko kuma.
Ibrahim naga kamar kanada ja a cikin zancen nan niba zaka mayar dani karamin yaro ba yadda ya tsara gidansa haka zan bishi don nima nawa tsarin gidan ba yai min shishigi kunji maganata ke nan dan zaman jin sukayi a falon kafin su mike su fito zuwa part din iyayyensu mata.
Baba ko yana shiga gida redio shi ya jawo ya kunna bbc yana saurare don kullun safe labaransu baya wuce shi saiga mama uwa ta shigo mai da kulan sauran tuwo ta aje tana gaidashi da kwana.
Take fadin malam yau ka dan jima a waje bakashigo ba shiyasa na gyara saura tunda akwaishi da dan yawa don aci tunda ban karbi kudin dama koko ba.
Wallahi ina kofan gida na dawo zan shigone na samu Alh Inusa a waje yana jirana nan muka bata lokaci dashi Alh yunusa kuma mama ta tambaya ?
Ehh wanan makwabcina ba yazo ne zancen kara hada iri da dansa keson yi a karo na biyu gidan nan kuma mama Lanto tana tsaye kofan tana jinsu.
Mama uwa take fadin wai Mahmoud ke nan kake nufi yace shifa ya aiko mahaifin nasa akan a nema masa yarki ta maye gurbin yar uwanta yanzu kuma.
Wace daga cikinsu yace ai kinji nace yarki ina nufin Fadimatu mana wai ita yake so ko wata a cikin gidan nan sai lokacin mama Lanto din tace malam ina kwana ya amsa mata yaci gaba da fadin abinda yake fadi a lokacin.
Yace na fada masu banwa diyana dole sai naji ra,ayin ita fadimatun kan hakan in basu jittu ba takiya sai ya canza wata tunda ba ita kadai bace yanzu.
Daidai lokacin maman biyu ta shigo itama taji kalman karshe nasa binsu tayi da kallo kafin mama Lanto tace ta yama zata kiya tunda bata da wani tsayaye dama.
Wai wacece ake zance to nima dai ban saniba don nashigo na samu suna zancen na hau akan fadimatu muke magana yanzu Alh Inusa ya bar nan kan suna neman kara hada iri karona biyu a gidan nan shi Mahmoud ya turasa wurina.
Zancen banza sai yanzu ne hankalinsa ya dawo gareshi har yake neman ka hada iri dashi kuma yanzu nasan dai ba zai wuce su yan biyune yake so ba aiko niko banyi niyar basa su ba.
A,a baiko ambacesu ba Bintu dai yace a basa ko malam mama uwa ta fada tana kallon mijin nasu Bintu kuma Bintu fa ta fada cikin mamaki.
To ai kaji zancen shi baizo gidan nan da sunar yarki ba ya turo a nema masa yardane ya auri Fadimatu tunda itace suka fara zama ai tare da marigayiya ko ?
Wanan ma ba zai yuyu ba ta fada tana fita daga dakin mama uwa ta bita da kallo tana fadin ikon Allah wata sabuwa ke nan kuma zata bullo dashi yanzu bintu din ma ina aka ganta.
Niko ina can dumu dumu muna fama da karatu gida suna nan suna halako a kaina ban san kome ke faruwa ba amma haka mama tayi ta daga jijiyan wuya bayan fitan baba kasuwa tana fadin maganganun da bai dace ba a kaina.
Mun dawo daga lectures gidan muka nufo kasancewa Friday ce don haka karatun ranan da dan sauki mun shigo mun samu gwaggo tana girki daki na shiga na kwabe kayana na fito munayi tare.
Mun kusa gamawane har lokacin Samira na daki ta kunna wayanta ina iya jiyo sautin karan gida daga inda muke din can sai gata ta fito tana fadin gwaggo ina zuwa zan dan fita kadan don Allah.
Gwaggo din ta dago daga gyaran ganyen miyar da takeyi tace to samira kada ki dade don Allah kin san mahaifinku yana iya fado muna ko yaushe.
Yanzu zan dawo ta bata amsa ban dago na kalleta ba saida tace dani sis saina dawo nace to ta fice ni kuma naci gaba da wanke wanken da nakeyi a lokacin.
Ah wai yar nan ko a gida haka take ne koni ta raina nan dai take min wanan dabian nace da dai gaskiya ba hakan take ba amma yanzu ko a gida haka take.
Kinsan baba baya zama gida sai yamma yake dawowa don haka bai san halinda kowa ke cikinsa ba shiyasa kowa ke abinda yaga dama yanzu.
Amma ko sunci amnan yaya don ko bainan ai su sunan kuma yayansune ai bashi kadai kedasu ba itama dai samirace yanzu kamar kada mu fara karatun nan sai take nunawa kamar tafi kowa a yanzu.
Har muka gama na koma daki samira bata dawo ba banson inyi barci yasa na dauko handouts dina ina dubawa a lokacin wayata dake gefena ya bada karan shigowan sako.
Da hannu daya na mika na dauko wayan ina duban sakon meye ya shigo min sai naga happo jumma,at mubarak tare da addu,oin dace ga ubangiji.
Addu,an yai min dadi dai dai bansan daga wanda ya turo min saboda banda layin maishi amma an taba kirana ba ai magana ba da layin.
Don haka na share sakon naci gaba da karatuna Samira bata dawo ba saida akai sallah isha,i ta shigo tare da dan leda a hannu ta aje saman katifan da nake tana kokarin kwabe hijjab din jikinta.
Na kallota nace sai yanzu take fadin wallahi gwaggo tayi maganata ko nace a,a tana daki ai tunda ta shiga magariba zaune takai tana fadin bari kedai malam Ar,miyau ya kwasheni muje gidansu sai yanzu muka dawo.
Gidansu samira ?
Wai ke bakijin tsoron hakan ne ke kada wata rana wani mumunan abu yazo ya sameki meyasa baki gudun zuciyan babane ke ?
Bantu kada ki daukeni bansan abinda nakeyi ba fa iyaka dai kice zai iya reping dina ko to ni messes ma nakeyi yanzu kin sani Allah ya sauwaka na fada.
Naci gaba da duban littafina can naji tana murkusu da leda kafin in fara jin tana tauna sai kamshin daya bure dakin duk hakan baisa na dago ba naji tace min ga nama.
Kaina kada mata nace bissimillah nagode ba tare dana kallota ba taci tasha ta kora da ruwan lemo tana gyatsa takai kishingide a gefena kafin can tace dani wallahi zafi ya kamata mu samu fanka dakin nan ko dan karamine tunda wanan ya zama hoto bai aiki.
Haka naso nima amma kada suga mun masu katsalandan a gida yasa ban kula ba to yanzu mu hada kudi idan baifi karfin mu ba sai mu sayomana.
Kafin in bata amsa wayata yayi kara na dauka wanan mai kirana bai magana shine ya sake kirana dai kwana biyun nan haka yake matsa min da kira a daidai wanan lokacin kuma bai magana.
Idan na gaji da kiran sai in danna wayan kudinshi yayi ta tafiya a banza hakan kuma baisa yayi magana na ba ko yanzu ma din haka nayi masa na danna baiyi kuma magana ba.
Samira taci gaba da magana duk maishi yana jin komai da muke fada har ya gaji ya kashe barcine ya kwashe samira ni kuma naci gaba da karatuna.
Muryan gwaggone take fadin waiko samira din ta dawo fadimatu nace ta dawo gwaggo tunda magariba har tayi barci gata kwance.
Tow,wooo abinci fa ba zakuci bane nace mun koshi gwaggo samirama tayi barci ko na fada tace to ku tashi ku rufe daki don yanzu dan uwanku ya dawo yake fadin yan banzan nan sun fara halinsu ko daren jiyan nan sun shiga nan gidan makwabcin mu.
Duk da ban fahinci suwa gwaggo ke nufi ba mikewa nayi da sauri zuwa kofan na rufo na sa sakata ina addua itako samira bata damu ba sai barcin ta take shaka lokacin.
Misalin karfe daya na sululin dare daidai lokacin nasamu barci ya fara daukata saina ji wayana dake karkashin filo da nasa kaina ya fara ringing dan zabura nayi na lalubo wayan kirane ke shigowa a lokacin.
Don haka cikin yanayin na wanda ya fara barci na dauko na kara a kunnena ina danna dauka muryan dana tsinkaya a kunnena yasa na watsake lokaci guda.
Naso na sheda mai maganan alokacin amma barci ya hana in gane hakan saidai kafin nakai ga tunane ko waye naji muryan na fadin.
Da fatan zakiyi hakkuri don nasan yanzu kinkai ga barci na tasheki na hanaki jin dadin barci kada hakan yasa kiyi fushi dani tsananin sonkine ya hanani sukuni da natsu.
Don haka na tsinci kaina da kasa natsuwa sai naji muryan ki a cikin daren nan sonki ya hanani sakat da sukuni ga baki daya.
Wai wake magana hakane na fada cikin kakausar murya sai naji yayi murmushi yace baki da laifin in yanzu har yakai baki iya sheda muryana a yanzu.
Kiyi hakkuri nasan nayi kuskure don haka ba zan gaji da baki hakkuri ba a yanzu don nasan kin rike abin a zuciyar ki sosai har kin kasa boye hakan a fili.
Sai da ya fadi wanan maganan muryan shi ya fado min a raina sak don haka na furta wai yaya habibi dama kaine kake min wanan wasan haka ?
Nine fatima kin ban mamaki da har baki saurin sheda muryana ba a yanzu don nazaci ko kowa ya manta hakan keba zaki taba mantawa da muryana ba ai.
A rana nace dole kace hakan don kun gama gana min azaba kaida matarka a baya wanda a yanzu dan zamana a gidan gwaggo na fahimci hakan.
Duk dasu mama uwa kan fada min cewa daukan munakisa akai min ai a lokacin amma rashin wayau bai bari na fahinci hakan ni iya gaskiyata taimakona daso da kauna yasa anty safiya ta daukeni ai.
Afili ce masa nayi ya habibi ke nan yaya bazan manta muryan kabani a yanzu tunda ka dauka zan kara wullalanta fiye da yadda na tasone a baya.
Stop joking muyi maganan gaskiya please duk da dare yayi a yanzu bani son in bata maki barcin ki amma insha Allahu gobe zan kiraki muyi magana good night.
Wani dogon tsuki naja lokacin da naji ya kashe wayan na mayar da ita a inda take da farko idanuna na lumshe lokaci guda tare da fadi a fili me wanan mutumin ke nufine wai ?
Barcin da ban koma ba ke nan ina faman tunanen duniya game da bayana sai goshin wajajen asuba na samu barci yayi gaba dani har ina makara da sallah asuba a ranan.
Washe garima da tunanen zancen sa na kwana Allah ya taimaka bamu zuwa school ranan don haka masha barcina da safe nabi sahun Samira muka shaki barc???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?in mu a dakin ban fito na taya gwaggon mu aiki ba kamar yadda muka saba.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[8/22, 9:31 AM] Maman Aslam: KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
2?? 8??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Kiran wayan Al,amin ya tayar dani daga barci hirana dashi zaki dauka wasu abokan wasane don yadda yake zolayana don sunan kakansu da nake dashi.
Hiran da yawan dariyan da nakeyi ne yasa na manta da kuncin dana kwana cikinsa wanan yasa naga Samira dake kwance a gefena itama ta daga ta mike ta dauki buta zuwa kewaye.
Ina aje wayan na yunkura zan mike wani kiran na sake shigo min na dauka wani layin na daban wanan karon ya kirani dashi mai special numbers da zakayi saurin hadacewa.
Ina dauka muryanshine naji wanan karon ban tsaye mamaren ko waye ba don na sheda muryan nasa a yanzu muka gaisa sama sama dashi ya fara din.
Fatima nace yau zan kiraki dama muyi magana don nasan yau da wuya in zaku shiga school.
Ido na lumshe nace eh sai dai ai bansan dalilin kiran ba in har akan zancen ranan ne ka damu kanka dashi ni har na manta da munyisa daga bangaren shi ya lumshe idon shi cikin kunan rai.
Amma ya daure yace min don Allah ina son ki saurareni ki fahinceni ki gane mezan fada a yanzu bai tsaya yaji abinda zan fada ba yaci gaba da fadin.
Kinsan ance dare daya Allah kanyi bature toni ba baturen akayi ba don a lokaci daya Allah ya dora min kaunarki a zuciya don tun ranan dana dora idanu a kanki ubangiji cikin hukuncin shi ya jarabe da mugun sonki so kuma na aure da zamu kasance tare har abada.
Da sauri na tareshi da fadin what ni din kuma ya habibi don maganan yazo min a bazata da kuma tsoro da mamaki matuka.
Ban gane me kake nufi da wanan kalman ko ka manta kai din yar uwana ka aura a baya Allah ne ya kare zaman ku tabar maka yara marayu.
Dan murmushi naji ya sake yana fadin amma dai kinsan Allah bai hanna ba ko abune da ubangiji ya halasta muna yinsa don hakane nake shs,awan hakan ya kasance a tsakanin mu ki dawo ki maye min gurbin yar uwarki dana rasa muci gaba da rike yayan mu a kusa damu.
Don wallahi fatima a yanzu banda wani buri a rayuwata daya wuce in bude ido in ganku a kusa dani muna rayuwa a tare.
Son da nake maki bakina ba zai iya fada maki irinsa tsananin halin da nake ciki a yanzu ba fatima a yanzu rasaki zai iya zamo silar rushewar rayuwata.
A fusace na tare shi da fadin kadafa ka dauka ko da fatiman daka sani a da kake wanan maganan a yanzu.
Sai dai ba mamaki don naga kai wanan ba abin kunya bane a yanzu wurinka tunda har ka iya daukan wanan tsamin karyan mazan kazowa mutane da ita wai mata.
Kada ka dauka nima irinsune kace yanzu kuma ka dawo gareni don ku maza haka kukewa mutane ku dauka duk mata haka suke basu da tunane.
Toni ba yar iska bace irin wasila ka tambayeta idan tana


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login