Showing 60001 words to 63000 words out of 347556 words

Chapter 21 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8804

ake sayarwa da gyalenshi na daura akaina.
Gwaggo na leka na sameta zaune ta falka don magariba daya kawo jiki lokacin nayi mata sannu tare da mata tayin wanka tace dani sannu Fadimatu sannu da kokari haka.
Amma wankan nan barshi har ayi sallah don magariba ya kawo jiki sosai a yanzu na sani gwaggo amma idan kikace sai dare hakan zai iya dawo maki da zazzabin ki sabo.
Hakata daure nakai ruwan masu dan dumi sosai ta tashi ta watsa ta fito tayi alwala muka shiga sallah ina idarwa na fice gidan nama na dan yanko mata na dari biyar na dawo nakai mata tare da debo mata abinci taci.
Nakoma daki in dauko wani takardana na samu Samira ta dawo har saida naji tsoro don ganinta nayi girshi a dakin zaune tayi tagumi.
Baya na dan ja kafin nace au kece ma ashe kin karaso ke nan ya kibar mutanen gida tace lafiya suke gwaggo bata da lafiya sosai amma dai yanzu taji sauki ina guntane .
Na dauki takardana na fita daga dakin don har lokacin tana jin kanta dani sai zuwa can tayi sallama ta shigo dakin tana gaida gwaggo dake cin abinci.
Gwaggo tace kin dawo ashe eh gwaggo ya karfin jikin yanzu Bantu ke fada min bakiji dadin jikin naki ba nasamu lafiya Alhamdullahi.
Ta juya ta fita daga dakin ina ganin gwaggo ta karasa na kwashe kayan na fita dasu na dan leka samira ina fadin azubo maki abincine tace ki barshi tea zansha agadarance wai ita ta nuna min a shirye tazo ke nan.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[8/9, 10:27 PM] KYAUTA: KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
1?? 8??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,

Anyi sadakan ukku mama Aisha carofee ya Allah ka rakata makwancinta da halinta na alheri ka yafe mata kurakuranta ya Allah ka sa albarka a zurian data bari anan duniya amin.

Rayuwa tana faruwa wucewa take kamar ba,ayi ba inji hausawa abubuwa da dama suna faruwa a gidan ya habibi na rashin dadin rai amma haka yake daurewa yana hakkuri da matarsa wasila a hakana.
Yanzu ma lalashinta ya fara nason suje gida tare wurin bukin sister shi da za,ayi wata mai fita amma ta kafe kan cewa ita ba zata ba tunda ta gane yan uwansa basa sonta .
Kada taje ayi mata kallon wullakanci ko rainin wayau ganin lalashin ba zai masa bane ya murtuke mata akan dole suje tare ko kuma su rabu.
Don ba zai aje macen da zatace bata son kowa nasa ba a gidansa alhalin shi yana kokarin mutunta mata nata yan uwan ko yaushe.
Don na barki a baya mai karatu ban baki labarin dawowar yarta ba gidan wata rana ya dawo daga aiki ya sameta zaune da yarinyar a falo suna kallo don baban baby ya titsiye yace tazo ta dauki yarta tunda bata da taimako ta samu wuri a sanadinsu yanzu ta manta dasu ta samu sabbin abokai da take hurda dasu ta barsu.
Hakan yasa taje ta dauko yar kafin yai mata tijara don tasan zai iya tunda ya fada don dan giyane ba kunya ke gareshi ba hakan ya bata tsoro taje tazo da yar nata gidanta.
Ba tare da sanin shi Mahmoud din ba saidaya dawone ya ganta ya bi yarinyar da kallo yana mamakin ina ta fito don baisan yar ba a lokacin.
Bayan ta kawo masa ruwa ne ta aje ta dago tana fadin honey ga mimi zata zauna damu daga gida aka kawota yar yayatace data rasu dama a hannuna take zama.
Wani kallo yai mata yana aje cup din kafin yace da zaki daukota nan wa kika fadawa zaki kawowa yarinya gida nima nawa na kaina suna gida kin kasa rikemin su amma kin dauko min taki yanzu why ?
Juyawa tayi inda yarinyar ke zaune tana kallo tace mimi go inside ki jirani yanzu zan shigo tana daga yarinyar cikin tsigar lalashi a gareta.
Yarinyar ta mike ta shiga tana dan waige wasila din ta jiyo gareshi tana fadin honey kayi hakkuri bawai naki daukan yaranka bane kaima kasan yadda mutane suke za aga ina kuntata masune duk abinda nayi masu ba zan tsira a bakin mutane ba.
Musanman yadda yan uwanka suka nuna basu kaunana din nan is hard ma a yarda ka kawo minsu fahintar hakan yasa kaga banyi karanbanin cewa aban su ba mu zauna nan tare dasu.
Amma kayi hakkuri nayi kuskuren dauko wanan din ba tare dana fadama ba don Allah kayi hakkuri honey ta hade hannayen ta wuri daya tana dan murzawa a hankali.
Shiru yayi baice komai ba a lokacin ganin hakan yasa ta mike inda take zaune tana dan kame kame tare da fadin a kawo ma abincine yanzu kai ya gyada mata ya mike tsaye ya bar wurin.
Binshi tayi da kallo saida ya shige cikine tayi mai gwalo tana jefa mashi dakuwa da hannayenta biyu irin na yare.
Wanan ne dalilin zaman yarta mimi a gidan ya habibin dole kuma ta tursasashi ya saka mata yar nata makaranta kuma akai hakan nashi nacan ya bari a wahalce tsohuwa tana wahala dasu.
Kodama ya turo kudi don yaran ba laluransu akeyi ba sai abi wani hanyan rayuwa da kudin a manta dasu yasa yaran suke wahalace idan ka gansu.
Shima dai kamar an danbalashi don bai damu da yaran nasa ba sam bayama kula lamarinsu sai can ba,arasa ba zai danyi masu sako da sunayensu.
Saidai hakan bai hana yaran shiga wani rayuwa na daban don gaskiya kowa ya rasa iyayyen asali ya rasune har abada ba a sanin hakan sai haka ya shafi mutum zai gane me nake nufi .
Shine yanzu zancen zuwa gida yayi ta nuna masa ita indai gidansune bata zuwa shi kuma yace zasu rabu dashi ke nan kan wanan dalilin .
Ta ya ko zata yarda ta rabu dashi bayan yanzu daga ita har iyayyenta akanshi suka dogara yanzu komai nasu shine yakeyi masu yayi mata kuma yayi masu ya aika masu har kauyen jos din.
Don haka ta nasa azuciyarta cewa samun shi zatayi in lokaci yayi ta lalasheshi har ya manta da zancen zuwan da ita dayace zaiyi din don Allah ya gani yadda ta fahinci basu kaunarta haka itama ta tsani duk wani danginshi a zuciyarta.
Bayan kamar sati hudu dayin zancen su ranan ya dawo da alama yana cikin farin ciki a ranan don yana shigowa gidan tana zaune falo tana kallo tare da yarta dake kwance saman two seater.
Shima zama yayi a wurin da take kan kujera daya tare da dan matsa mata hannu saida ta dan sake kara kadan ya danyi dariya yana fadin sorry kinji zafi ko ?.
Ta gyada kai tana fadawa jikinshi yace sorry this weekend mai zuwa zamu tafi kaduna fa nasan dai baki manta da date din ba ko ?
Dan dagawa tayi a jikinshi tana tabe baki tace waikai honey suncema suna son ganina wai daka matsa inje kaduna har yau fa don suna fushi ka aureni ba wanda yazo garin nan da sunan ganina.
Wani irin juyowa yayi ya kalleta take yanayinsa ya canza yace kadaki manta sune fa suka haifeni banda wasu bayansu har kike fadin wanan magana ?
Basu kaunatane yasa nima naki su a yanzu da sun nuna suna sona aiba zanki zuwa gunsu ba nima amma tun auren mu mace ko namiji a cikin yan uwanka babu wanda yazo gidan nan don yaganni don haka kaida kake nasu kaje kai daya mana .
Ido ya kura mata yana mata kallon mamaki na yadda ta iya karfin halin fadin magana haka game da iyayyenshi a gabanshi can ya nisa yace.
Ok ba zakije ba kenan kike nufi tayi kasa da kai tana fadin ni gaskiya ba inda zani na fada maka yace good tunda ke kika zabawa kanki hakan.
Yana fadin hakan yayi kokarin dagawa daga inda yake ta wani tabe baki tana fadin fushin me zakayi kuma ai gaskiya na fada.
Bai tsaya kulata ba dataga hakan da gaske yakeyi tace ni dai shi ke nan Allah ya kaimu amma gaskiya ni kwana biyu ko ukku zamuyi mu dawo don mimi da zan bari nan.
Har lokacin bai tankata ba ganin hakan yasa taja bakinta tayi shiru bakin ciki da takaicin wanan tafiyan yana cinta a zuciyarta shima da mamakin wauta irin nata ya shiga daki cikin fushi.
Naso kiran uncle mu gaisa in masa godiya amma sai naga ai mama zata fada masa tunda na kirata na fada mata kuma komai daya faru don haka na share ban kirata ba.
Samira tana wani sallo tana yanga tana kada tea tana sha tana wani yanga harda buga gwangwanin madaran ta tura akwatinta ta rufe tasa key ta danna masa wai duk saboda ni.
Nura zai fita naji yana fadin bai karya ba nace Nura zakasha tea ko koko zaka fita ka saya yace tea big girl shayi aisai ku manya ina naga kudin shan shayi yanzuni.
Ka dauko kofi kazo ka hada ga komai nan a dakin nan har bread akwaishi wani kallo Samira ta watsamin lokaci guda sai kuma ta juya taci gaba da abinda takeyi.
Yazo da cup din yayi sallama na juyo ina fadin ok don Allah Nura shigo daga can ga kayan tea a wurin ka bude ka diba yadda zai maka.
Wurin ta kalla ya daga wani zani nawa nace dauko wancan blue leda din suna ciki har lokacin kallon mamaki takeyi taga ya jawo leda yana fadin .
Wanan gayen yakai gaye naso na gansa tun jiya ko yau saida umma ta kara min maganan shi tace wai dan balarabe yazo ya kaiku asibiti.
Kai Uncle dinane fa ba wani ba ya jawo katon gwagwanin madara peak milk babban duka duka yace wanan zan bude ko Nido din nace bude peak din kabar Nidor din kada ka taba shi.
Ya bude har millo din ya bude kwalin sugar duk tana kallo ya diba yana godiya ya tafi nace bread fa yace aff kinga har na rude na manta dashi.
Irin bread din nan mai tsada da zai iya kai sati har fiye da sati ya juya ya fita sai naga jikinta yayi sanyi lokaci guda ta samu tagama shan shayin nata dataso yi min iskaci dashi .
Sai Allah mabuwayi ya taimakeni ya rufamin asiri alokacin ya nufa nima ina dashi don haka duk wani iskacin sai ya lafa naki kuma fita saida ta tafi na rufo dakin na wuce da key a jaka na don nasan tana iya dawowa alokacin.
Satin mu hudu mukazo gida koshi don bukin zainab nazoyi saukan dare mukayi don haka ko ina ban kara fita ba a ranan tunda na shige dakina.
Washe gari kuma tunda safe na tafi wurin gyaran kai da kafa bana son kumshi don hakane za a gyara min kafa kawai da jikina .
Sai karfe hudu na dawo lokacin yunwa ya dameni sosai hakan yasani sauka a gidan hjy hajjara tunda na bude get na hango motocinsu a gida na gane duk yan gidan sunan basu koma ba ashe.
Sallama nayi falon na shigo mazan ne zaune a falon sai naji nauyi da kunya ya kamani lokaci guda duk na daburce suma wai basu ganeni ba saida nagaidasu .
Al,amin yace wonderful wai Fatimane dama kina garin nan ashe nace a,a jiya nazo da dare na kara gaidasu nace ina mama ?
Tana ciki yanzun ta shiga sai gata ta leko tana fadin kai miko min glass dina inda na zauna mami kinyi bakuwa fa saita fito tana fadin a,a wai mamatace yau ban gane ba.
Kunya naji sosai nake dan noke kaina nace ina wuni mama ta karaso tana fadin wai yaushe kikazo garin nan ne nace jiya da dare muna da bukine shine na shigo.
Aiyo na dauka kin kwana biyune a garin nan nace a,a mama yanzun ma na dawo daga cikin gari tunda safe na fita sai yanzu na dawo.
Halan daga wurin gyara kike ko nace eh mama kema kina saka wanan karin da malamai keta wa,azin baida kyau a daina yinsa da sauri na bude kaina nace a,a mama gashinane aka wanke min shi .
Gaba dayansu suka kallo kan nawa naji tace masha Allah wani kan dai kina da hadi da buzayene ko yan shuwa don kamanin ki yana matukar kama da tasu sosai ko fulani Al,amin ya fada daga gefenta.
Ko uncle ya fada yana juyawa inda uncle din yake zaune kamar baima san na shigo falon ba you're very stupid Al,amin wai ina wasa da kaine ?
Al,amin din ya dan ja baya yana fadin no uncle kawai dai naga kaika san kama shine na fada Ukuthi kiwa wanan yaron magana kafin na tatakashe wurin nan yanzu kuwa.
Ai gaka gashi tunda dan rainin wayaune shi ana magana zaka ambaci sunansa kaji yayi magana ne da zaka sakoshi a zancen nan iam sorry please ya fada.
Lokacin na juyo nace uncle ina wuni ya gajiyan tafiyan ranan gwaggo tace idan nazo in mata godiya sosai a wuku mama taji sauki ko nace tun wanan treatment din da akai mata aita mike.
Dama ai itace taso kasheta a gida nace ni kuma a cikin mamaki bai tsaya kulani ba yaci gaba da abinda yakeyi wayata ta dauki kara ina dubawa naga wani course mate dinane na dauka.
Nan muka juye harshe muna turanci dashi akan maganan examination din da mukeyi a lokacin ina masa bayani na kashe wayan na dago kai Al,amin na dariya yace yanzu dai tunda kinzo kafin ki tafi yaushe zaki hada muna abincin nan naki ne ?
Aika bari dai ta huta ballema buki tazoyi kaji ta fada da bakinta ai yanzu wani irin abinci yake so bar dan shirme ina zaki iya wai tuwon garin doya da miyan egushi dayaji kunyi lokacin bukin khariya.
A mama dakin kirani dana sa yan gidan mu sunyi masa ai kayan hadine kawai abin bukata tunda na koya masu sun iya yanzu suma zasu iya masa.
Naki dai mukeso ci muji don mama ta bamu labarin abincin akwai garin da naman kai akwai amma aiya dade a fridge ba zaiyi dadi ba yanzu kila .
Gobe insha Allahu zan shigo muyi sai dai sainaje kasuwa na hado kila na samu zuwa yau din nan ko kuma gobe.
Aiba abin sauri bane ki bari goben idan kin huta saiki tafi nace to mama ke meye sunan wanan maganin da kikaba gwaggonkine ya Aliyu ya fada.
Jin hakan yasa na juya da sauri na kalli inda uncle din yake zaune sai na dukar da kaina cikin kunya yace don Allah fada muna shi uncle bai iya fada bane ?
Aji garau sai naga duk sun kwashe da dariya har shi nace to ai haka muke kiransa a nan banice nasa mai sunan ba indai mutum naji jin jiki ko tsamin jiki dayasha shi yanzu zaiji komai ya tafi.
Larabci naji yayi duk suka karba mashi a cikin harshen larabcin suna dariya ke daga unguwa kike tashi ki shiga kitchen akwai abinci na nan ki dauka ki rabu da wa yan nan yan sherin .
Har kasan raina naji dadin hakan yunwan da nake ji bai bari nayi mussu a ranan dama donshi na shigo don nasan ban fita gidan sai anyi min tayin abinci indai kazo.
Kuna muna dariya muma muna dariyan wasu behaviours naku idan kunyi na fada ina mikewa da kyau mamata ai gara da yanzu baki kyalesu kema.
Garau garau na juyo nace aji garau fa akace dariya sosai na barsu sunayi a wurin nashige kitchen din na debo abinci a can na tsaya naci abincin har drinks muna hiransu da mai aikinsu.
Saidana gama na fito mama take fadin wai a can kika zauna kikacine nace eh na samu iya a ciki muka tsaya muna magana har naci kai mamata kinko ci kuwa ta fada tana kallona.
Nace wallahi naci mama nagode Al,amin yace ai gata garau taji garau yanzu mama bari in na fita zan sayo makashi ka gwada idan kaji ciwon jikinka .
Suka kara kwashewa da dariya nace mama ina su anty Aisha tace Allah sarki sun tafi maiduguri tun satincan kinsan ita matar wanan yar can ne shine suka tafi ganin su .
Nace Allah sarki gaskiya dai ban gansu ba nace zan tafi sai dai gobe zan rama mama don yaji sosai zan sakawa miyan attah sai Al,amin yayi hawaye idan yaci daki kyauta don kamar maye wai sai yaci yaji nasa iya tayi masa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login