Showing 261001 words to 264000 words out of 347556 words

Chapter 88 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8759

muke kiranta dashi nidasu maryama sun dauki sunan dama shiya dace sukirata dashi a bakunansu.
Yarki tayi goshi ko makiyin Allah yasan yarinyar nan tayi dace da dan albarka Allah yasa yadda ya kawo muna kayan nan muka yaba mukasa albarka ubagiji Allah yasa ko halinsa na alheri mu sheda.
Amin Amin insha Allahu da alaman halin alheri a garesa duba da irin kokari da dawainiyar da yakewa bayin Allah da yanada wani halin banza da an fara sheda hakan tuntuni a garesa.
Hakane abinda nake fadawa yar taki ke nan tayi hakkuri zaman gidan aure ko yayane yafiwa mutum zama irin haka gida wani lokacin tayi hakkuri koma abinda ake fadin gaskiyane Allah yaga da niyar da kika shigake insha Allahu zai tausaya maki.
Ni Ammi wanan aure na Bintu ganinsa nakeyi wani hikimar ubangijine hakan Allah ya nuna muna sai mai hankali da kaifin tunane zai gane hakan.
Bazan boye maki ba a yanzu gata nan irin wahalan data sha a gidan nan sai daga bayane naga irin rayuwan yarinyar nan naga dai me tayi muna ana shirin konamu a kanta yasa nayi wa kaina fada .
Allah kuma ya kubuto dani daga kaidin ingiza mai kantun da ake muna muna musgunawa boyar Allah nan karshe kuma duk abinta dai bai wuce mu da yayan mu to me muke nema don Allah idan mutum baiwa kansa fada ba ?
Duk abinda mutum yayi don kansa uwa ai shima ya haifa dai ko duniyace gata nan da fadinta baka kuma taba tabbata a cikinta komai tsufanka wata rana saika tafi ka barta.
Allah na tuba gadai isharanan kala kala ubangiji yana nunawa bawa amma bamu gane hakan sai kara dulmiya mukeyi da son duniya.
Game tunane ke nan Ammi ko yanzu na jita a daki tanawa yaran huduban banza akan wai malam yace akawo maki kayan nan ana ba akai dakinta ba .
Nasan ko malam yana da wani manufan yin hakan indai malam ne tunda yace a kawo maki su nan nasan akwai wata a kasa amma shine wai yana son ya zarga masu sata ita da diyanta yasa yace hakan .
Don haka kowacensu ta kiyayi dakin nan a yanzu ko kayane basu taba gani ba ankawo ma wanda yafi goman hakan basu karaya ba sai wanan ?
Naji diyan guda na fadi ita dai bataji baba yace hakan ba son Allah ta bari a zauna lafiya kada mutane su shigo su tafi dasu kan abinda bashi ba.
Dayan kuma cewa tayi ko sin gani dai ba,a gidan nan ba din haka din Allah kada ta juya zancen nan kuma har hakan ya kawo fitina tsakaninsu da baban su.
Allah sarki wazam baka son aska a jikinka yanzune tasan tana da ikon yar a gidan nan Fadimatu fa Allah ne ya rufa mata asiri a gidan nan ubangiji ya nuna shige shige ko bin bokaye baikai dogaro da ubangiji karfi ba.
Bandaki na fito na samesu har lokacin zaune suna hira jin na fito take fadin Samira ta bugo waya tana tambayan wasu irin kaya aka kawo maki naji uwar ta hauta da fada a gabana.
Kai mama uwa mama Uwa hoo ko ina take samun labaran nan na fada a zuciyana koda yake yanzu nakula gaskiya akaina kawai take hakan bata faye zaman tsegumin kowa ba a gidan .
Amma duk da hakan ina zaman taka tsantsan da ita ko wani lokaci duk da nafahinci cewa tanayine kawai don na tabbatar hakan dari sama da dari a rayuwanta.
Tafiyan kwana uku gasu Ammi na batun share sati a Kaduna duk ko da tsananin mijinsu malam amma ya daga masu kafa har a kammala komai sukoma.
Ganin an kawo kayan an kuma addanasu yadda ya dacene yasa Ammi ta fara zancen komawa gida sun shiga ziyaran wurare don tun zuwan mu bata samu fita ba don abubuwan dayake faruwa din.
Karfe hudu dawani abu muka dawo gidan nikan ina daki ina cire tufafin jikina naji sallama da alaman munyi baki a zatona makwabtane masu shigowa ganib kayan don mutuncin da akeyi tsakani.
Hakama yan uwansu mama suma suna zuwa daga gidanjensu don labarin lefen da akeyi naji mama na fadin ohh gun batu sukazo ke nan ta,,,,
Tafita yanzun nan mama uwa ta fada daga kofanta au ta kara fitane dara shigo din nan ashe ehh ina jin hakan sai lafe na boye ta bayan labule ina dan lekensu ko zangane su.
To ai idan tafita gaku saiku isar mata da sako don munsan bata san abinda zata aura ba kuna murna an kawo maku kaya nagani afada kun dauka yarku tayi sa,an mijine to sunan yarku gawa wallahi.
Don koga baikon nan ana iya gamawa da ita saidai ku wayi gari ku samu ta mutu abarku da gawa a cikin gida anga shanye mata jinin jiki duka.
Don haka in kwadayi ya kaiku dauka ya kubashi tun wuri ku sani sunanta gawa ba wanda baisan wanan a garin nan don wallahi anyi ba saudaya ba ba biyu kowa yasheda hakan.
Idan ta mutu aure ya kasheta mutuwa ko yaushe kuma zamansa muke a duniyan nan ko yanzu ko anjima Allah kadai yasan gawan fari a tsakanin mu nan.
Ohh yar uwa daga taimakodawo sai abin ya koma mugun fata mun kinga tafiyan mu wanan abin fa kowa yasan da hakan amma tunda akwai alaman kwadayi sai mun maku gaisu wanda yaki ji bayaki gani ba ai .
Kai ku suwaye da zaku shigo muna gida da mugun labari Nurane dake dakin mamanshi zaune yana cin abinci ya fito yana fadin hakan.
Wallahi ku fita gidan nan kafin yanzu rayukaku ya baci ya fara hauka yana neman abin duka ganin hakan yasa da sauri su ukun suka fice daga gidan suna karo da junansu.
Ehh ya tabbata kuwa dama an fada gashi tun ba,aje ko ina ba mun fara gani kai jama,a me duniyan nan ya komawa mutanene wai mutane sun mayar da sheri abin kawa.
Mama uwa ke tafa hannu tana fadin hakan daga kofan mama kuma tana tsaye ta rike labule don tunda baba ya yayi mata hakan da take ganin komawa bayane a wajenta take nuna tsame hannunta a cikin zancena.
Gaskiyane dai baku son a fada ni dama nasani aikin me mutum keyi zai jibgo maku wanan kayan kamar an bude shago ku karba kuna washe baki ni dama nasan da lauje a cikin nadi wallahi.
Anzo a fadi gaskiya kuna koransu gata gashi ai rana bata karya saidai uwar diya tayi kunya bako wanan uwar diyan ba ko mayene bawan Allah nan sai Fadima ta auresa idan taje a ranan ya cinyeta.
Kwarai kuwa hjy kwarai ki min daidai to waike suwaiba ina ruwanki cikin zancen nan ne yarinyar nan dai kin nuna babu ruwanki da ita tun tana ficiciyarta.
Na samu yarki ta nuna ra,ayin daukan min ita haka kikaita sheri kala kala akan yarinyar nan har Allah yazo ya raba zamansu Allah ya dauki ran safiya kika koma fadin a unguwa Fadimatuce manya tana da gadon maita ita ta cinye maki ya.
Unguwan nan kaf kowa yasani ko ince duk garin nan mutanen can sun rike min ita amana keda Altine yar sheri guda kukayi sanadin data dawo gidan nan.
A ranan me kikace ba zata zauna dakin kowa ba a cikinku ta kama maku kurwanku dana yayanku a banza a dakina Fadimatu ta kwana ranan gari ya waye na tattara dan abindake gareni na gyara mata dakin nan da take ciki har yau din nan.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
8?? 3??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Ya juya wurin su mama uwa yana fadin gaku koba haka akayi ba bansan me kuka gani ba daga baya ku kuma kuka sake nasam bai wuce halin Fadimatu din na kirki a gareku.
Kona fadi karya ba haka akayi ba yanzu auren fadimatu yazo ta hanyar arziki zakice kinsanta toni kuma bansan wanan ba ko uwarta ta bar garin nan kayan nan a nan zasu zauna ko akai wani dakin ban yarda dake ba kamar yadda baki dauki Fadimatu a baya matsayin diya ba gidan nan.
Ba wai mama ta kyaleshi bane tana bisa kan bakinta ko yaushe idan suna fada nan ta fara halin nata tana tonon asiriwa kanta.
Me zakaiwa fada a nan yanzu ana muna maden cewa yarinya tayi goshi ashe sunanta gawa gashi Allah ya tona asiri tun ba,akai ko ina ba munji komai da har anawa mutane rawan kai a gida ita game goshi da sa,a.
Ke kuma uwa kowa a nan yasan mekikewa rawan kai tuntuni shine kumce da dan ihim da ake maki kota mutu ko tayi rai ba matsalan ki bace kuma banga laifinki ba tunda takanki kikeyi a nan ba don Allah ba.
Bakin,ki yaya ya sari danyen kashi Allah ne shedata tun yaushe nagane gaskiya a gidan nan na bar bin sherinki don na gane kome a yanzu niban damu da duk abinda zaki fada a kaina ba yanzu tunda Allah shine shedata kan hakan.
Amma wanan abin baiyi maku dadi ba da wani kuke son muji don Allah da zancen wa yan nan mutane da suka fita koda naku hayaniyar zamuji.
Duk akan yarinya guda sai kace ita kadaice diya a gidan nan don Allah kubar yariyar nan taji da abinda ke damunta a zuciyarta baka taba jin wani fitinan aure ya tashi a gidan nan sai akan yayan wasu daki wanan ai abin kunyane.
Nan take ta koma kan mama Lanto din data fadi haka ita kuma da sauri tace a,a meya shafeni ciki gani nayi dai hakan bai dace ba ai mutanen nan sunzo da maganan tashin hankali an samu sun tafi.
Yanzu kuma ace kuna haka a tsakanin ku duk akan mutum daya haba don Allah kubar fadan nan asan abinyi akan zancen nan shiyafi.
Kaji ki da wani zance ke nan dabance wani abune bakuyi ba a gidan nan kan Bantu din keda yarki kokin dauka har an manta hakanne ko ?
Kukan danasa wiwiwi yasa jikinsu sanyi kila nan su mama din suka shigo kuma dakin nawa suna ban baki ni dai banyi magana ba sai faman kukan da nakeyi din.
Wai Bantu kan me kike kuka haka zancen matan nan keda ganinsu kinsan yan iskan matane balle na fada maki na sheda dayansu ba yar unguwar su maman tudun wada bace nafa santa zaman kanta takeyi Usaina ta fada.
Ta tare hassana din dake magana ban sun shigo dakin bama saida naji muryansu suna magana din na dauka zamu samu matsalane dasu yadda akace mama tayi masu warning akan lamarina.
Har su mama uwa da mama Lanto suka fita suka barsu a dakin guna nan na dan samu nayi magana ina fadin don banda uwa gidan nan yasa ake min haka ko me ?
Komu dake da uwaye a gidan me muka zama ni yanzu nagane ban yarda a hadani da kowa wallahi ga ya Altine nan koda yan dakin mu bata shiri da mazan na duka saboda halinta na banza.
Ni ina zan yarda da wanan kema kika tsaya masu kuka ai wallahi kawai ki sharesu kiyi laluran dake gabanki a yanzu hassana ta fada.
Don ni banma so ki kula wanan zance nasu mama don bai zama bakon abu a wajen muba yanzu gidan nan ba,a taba zama lafiya a gidan nan kin sani.
Abinda Ammi ta fada gaskiyane ai kowa mutuwa zaiyi wanda ya mutu kwanansa suka kare duk yadda akayi matan nan sheri ya kawosu gidan nan ba gaskiya suka fada ba.
Ammi dake fitowa daga bayi ta dauro alwala tace shine gaskiya Hassanan tace aida aikinsane shan jini dana baba zai fara sha shida yayi jinya kamar zai mutu a gidan nan lokacin kuma ai yaje asibitin dubashi yafi a kirka ta fada.
Dama munsan da zuwansu ai jirace nake dasuzo ina nan saiga Allah ya aikosu din marasa hankali kuba yara ba ayo hanyanku kuna aikata barna irin haka.
Yanzu dai ni tafiya zanyi gobe inta biyewa mutane ruwanta idan kuma ta kwantar da hankalinta ayi komai a tsanake shike nan sai suji kunya suda wanda ya turosu din.
Ranan haka mukayi kusan kwana a zaune da Ammi tana min nasiha tare da ja min kunne kan matan gidan mu kan na kula sosai kada in yarda subar min abin magana yadda suke yabona a yanzu ko bayanta kada in yarda wata ta ban shawaran daba daidai ba in dauka.
Washegari karfe shidda malam Audi yazo ya daukesu ina kuka su Fadila na kukan rabuwan mu na dan sabon da mukayi dasu na kwanaki a tare don mun saba sosai da yaran.
Na dade a waje tsaye ina jin zafin tafiyansu din kamar dai in bisu in koma nake ji a lokacin nasan hakan ba zai yuyu ba don in nayi haka ban kyautawa baba irin yadda ya jajirce min a rayuwana.
Shiyayi tsaye a kaina shine uwa shine uba a wajena shiya koyar dani duk wani abinda uwa zata koyar da yarta na rayuwa yanzun kuma baiyanan yan uwan mahaifiyata nace na gudu na koma wajensu har kwana nawa ya rage min nayi a gidan nasu yanzu da zan kasa hakkuri.
Haka naja kafata na koma daki na yayin da yan cikin gidan mu keta harkokinsu na yau da kullun a tsakar gida kowa yana nemawa yayansa abinda zasici na karin kummalon safe duk da akwai kunu da kosai da shi baba yake bayarwa a karya a gidan donshi yafi karfi hakan kesa su kuma sai kowa ya kara da dan abinda ya sauwaka masa a dakinsa aci.
Zuwan su mamane dama ake samu ayi wani dan abu a dafa aci a gidan har kowa wanda kusan nice mai bude jakata ayi hakan garesu don gaskiya su mama uwa da mama Lanto sunyi min kokari sai ga hakan ba laifi tsakani da Allah.
Dakin nabi da kallo don mun yamutse kayana su Fadila sun dauki wasu abubuwa nawa da ba zan yafi dasu aure ba irin kayan dana dadema bani amfani dasu a lokacin duk sun kwashe saukin abin ma a motar gidane zasu koma don haka ba matsalan yawan kayan da suka dauka din.
Zama nayi bakin gado ina sauke ajiyan zuciya Ammi ke nan naji kamar kada in rabu da ita inaga in mahaifiyata din tazo ya zanji dan murmushi nayi ni kadai a daki don tuna yadda Ammi din ke nuna min jajircewanta a kaina ko yaushe ta nuna min ita uwace a gareni kamar a cikinta na kwanta har na fito diniya.
Mama Uwace tayi sallama a dakin ta shigo tana fadin Bintu na zubo maki taliyane ki karya dashi shi muka dan dafa sai ta sameni a zaune cikin yanayin damuwa da tafiyan Ammi din.
A,a kina zaune ne kin na kewan Amminkine ai sun tafi yau sin barmu da kewansu wallahi bako rahama gareshi ai albarkacin bako kakan samu alheri mai yawa wanda baka zata ba to mun sheda hakan zuwan nan na Ammi gidan nan.
Kiyi hakkuri kwana nawane zasu dawo buki yazo ai nan zamu zauna da ita nasani a debo maki taliya din ne kici ta sake tambayana hakan tana kallona.
Kaina dan girgiza mata kafim nace nagode mama ba zan iyacin komai yanzu ba ina mayar da jikina gefeb bango na jingina dashi ina dan lumshe idanuna a hankali.
Bintu duk abinda kikaga ya samu bawa rubutattacene ga ubangiji hakan gareshi tun farko kaddaran bawa rubuce yake ga mutum don haka ki godewa Allah taki jerabawan da alaman sauki yazo maki sai ki godewa Allah ga hakan.
Ya rabaki da mahaifiyarki tun kina kankanuwa ya saka maki da abubuwan alherin da masu uwa a kusa basu samu ba yau shiya komai mukaga Allah ya hukunta a kanmu yana da dalilinshi nayin hakan.
Nagode mama na fada tace Allah ya bamu ikon cinye jerabawan mu na amsa da Ammin sai maganan kuma ya tsaya min a zuciyana sosai dan wanan nasihan nata ya kara min karfin gwiwa a zuciyana sosai.
Dan barci safe na samu don akwai barci a idona na samu na danyi barcin sosai sai zuwa shadaya na falka daki nafara gyarawa ya koma tsaba akwatunan nawa na aure na tarasu waje daya a dakin nawa.
Ina gamawa na shiga wanka na fito ina shafa mai Nura ya shigo dakin nawa muka zauna muna hira dashi akan matan nan da sukazo har ya kyalla idonsa kan akwatatunan auren yace.
Kinsan wani abu Banta dago ina kallonshi nace a,a saika fada yace zaman kayan nan gidan nan bai min ba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login